Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   91 / 94

270K to 273K   out of 279.4K words

wanda yayi mata cif, kanta ta nade shi da hula hannunta ta rike wayanta dashi, babu abunda yake sai baza kamshi don da alamu wanka tayi kafin ta sauko tana saukowa kasan, tana karasowa Ind a yake ta tsaya kikam bata ce mashi komai ba,

Already tundaga kan stairs din ya hango ta kafin ya kauda kanshi, ganin harya karaso batace mashi komai ba ya sashi mikewa ya fara duban ledojin yana shugowa dasu kitchen, tana Ganin haka itama ta soma diban ledojin tana nufa kitchen din dasu, yana hangota kuwa yayi saurin amshewa yace “just wait for me inside the kitchen let me do the job of packing it”

Yana kaiwa nan ya fuce daga kitchen din, da mamaki take kallonshi, Wai Anya kuwa? Kodai he’s possessed ne? Ta tambayi kanta,, tana cikin wannan nazarin sai Gashi ya dawo da wasu ledojin, haka ya dunga fita yana shugowa dasu akan idanunta saida ya gama tass ya rike kugunshi yana kallonta “Wai ashe it’s not an easy task, now it’s your turn, saiki fadi abunda Zan tayaki”

Kauda kai amra tayi bayan ta gama sauraron nashi bata ce mashi komai ba Har lokacin fuskanta babu yabo ba fallasa, haka ta fara bude ledojin tana sorting dinsu ba tare da tace mashi komai ba, “wifey let me help you out”

Kai tsaye tace “ka barshi Zan ita ni kadai”

“No bazan barki kiyi ke daya ba aikin da yawa zaki gaji, let me help you please” ya karashe yana kashe mata murya wanda yasa batama san tace mashi, “okay Ka saka waennan a fridge”

Murmushi kawai yayi don yanxu karantarta yake sosai yana Ganin abunda yake sosai don Ganin abunda yake so da how she react on abubuwan da yake mata.

Yau saiga General guda Ana sorting abubuwa a fridge da freezer, dukda ba magana take mashi ba yaji dadin yanda suke ayyuka atare yana taimaka mata Har suka gama sorting komai, tana wanke hannunta ta fuce daga kitchen din, shima hannunshi ya wanke a gaggauce kafin ya futo, lokacin harta kai stairs yayi saurin cewa “wait… ga grilled chicken na sayo”

Dan tsayuwa tayi kafin ta dan juyo tace “na koshi saidai zuwa gobe”

Tana kaiwa nan ta wuce sama abunta.

 Ak hanata tafiya ba don haka ya juya wajen dining ya dauka kadan ya wuce dashi kitchen ya saka a cikin fridge don shima a koshen yake….

The next morning….

Da kanta ta Tashi ta wuce kitchen tayi masu breakfast, da farko cikinta kawai taso dafama sai kuma daga baya ta danji babu dadi don koba komai gidan shi take zaune don haka ta daga hardashi ta ajiye mashi a dining ta wuce sama zuwa dakinta.

 Amar kuwa sai wajen karfe goma sha daya ya Tashi, wanka kawai yayi ya sauya kaya zuwa na zaman gida kafun ya fuce daga bedroom din,

Kamar kullum bai tsaya ko Ina ba sai kitchen ya hada tea ya fito, da mamaki idanunshi ya sauka kan dining data jera plates din abunci akai da flask sun ruwan zafi mai kyau, ahankali ya soma takowa fuskanshi dauke da murmushi ya soma bude plates din, English breakfast ne tayi pancakes da sausages sai oatmeal a cikin wnai bowl a gefe, saurin ajiye cup din tea din dake hannunshi yayi ya zauna ya fara cin breakfast din, 

Shida baya cin abunci sosai sai gashi ya tashi da abuncin tass bai rage komai ba, yana gamawa ya dauka plates din da bowl din ya aje a kitchen, Har zai futo yaga ko’ina clean don haka ya wanke plates sun da kanshi don baya son yana bata wahala….

****

Zaune take a bakin gado tana yanke farcenta incoming call ya shugo mata, cikin hanzari ta dauka wayar Ganin sunan anty Madina, 

Da sallama amra ta dauka wayar tace “anty Madina……. Kun manta dani sai yau”

“Sorry my dear Wallahi na shiga busy kwana biyu, na dawo fah, nazo yin wani aiki ne ammah Zan koma,“

“Dan Allah kin dawo? Kai ammah naji dadi sosai” amra ta amsa ta

Dariya Madina tayi kafin tace “Ay dazu na kira hajiya mu gaisa, take shaida min kin tare ma, Toh Masha Allah naji dadi kinyi abun arziki kenan? Na dauka zakiyi taurin kan maki ne”

Dan turo baki amra tayi kamar taba gabanta “kai anty Madina, nidai yanxu yaushe zakizo?”

“Ki tura min address din gidan Zan shugo gobe Insha Allah,” Madina ta amsa ta daga chan bangaren wayar

“Toh shikenan anty Madina sai kinzo”

Sallama sukayi kafin amra ta kashe wayar, ta cigaba da yankan faratan nata.

Karfe buyer na yamma ta sake saukowa kasan don dora dinner, sanye take da doguwar rigar atamfa tayi mata kyau sosai don yanxu tafi saka su sosai ba kamar da ba da take yawa saka doguwar rigar abaya,

Wayanta na gefenta ta kunna wata slow music mai dadin saurare don tafi kaunar sauraron irin wannan wakokin don suna bata nishadi sosai, haka kawai saita tsinci kanta tana murmushi idan tana sauraron wakar.

Anatse take komai bayan ta fidda veggies din da zatayi amfani dashi, cikin kwarewa take Sarrafa girkin nata tana dan takawa, gaba daya ta gama shagala a cikin wakar tana miming “love me like you do love love love me like you, touch me like you do touch touch touch like you baby”

Amar dake saukowa daga sama tundaga stairs ya soma jin kamshin abunci ta daya bade duka gidan, daman da yar yunwar shi ya sauko kasan don haka bai tsaya ko Ina ba sai kitchen, lokacin daya shugo kitchen din turus yayi yana kallonta, wani irin murmushi ne ya kubce mashi akan kyakyawan fuskanshi lokaci data daga wooden spatula da take juya abunci dashi tana rausaya “love me like you do baby….oh touch me like you do baby”

Kama habar bakinshi yayi yana admiring dinta Har baisan lokacin da dariya ya kubce mashi ba, a furgice ta juyo don bata san da tsayuwar shi a wajen ba, bin kykyawar fuskarshi ta soma yi da kallo, inda yake shafa sajensa yana bitting lower lip dinshi harya shigo cikin kitchen din yace “daman jin iya waqa haka? Looks like you’re enjoying your moment ki cigaba da abunki please Inason gani”

Wata irin kunya ce ta luluba ta saidai da yake ita din Akwai kafiya don hakan ta matse fuska ta kashe waqar gaba daya ta fara kokarin futa daga kitchen din, saida tazo dab da Ind a yake ya sanya hannushi ya rike hannunta gentle ya soma  magana anatse “oh noo please, saboda nazo ne zaki gudu? Bari na futa tohm ki cigaba da abunki” yana kaiwa nan ya fuce daga cikin kitchen din.

Bun bayanshi tayi da kallo harya fuce kafin ta koma bakin gas cooker ta tsaya tana wani tunani…..

Koda ta gama dafa abunci, a cikin warmer ta zuba mashi ta wuce dining ta ajiye mashi kafin ta wuce kitchen din, tana shiga ta fiddo da plates da serving spoon da cokali Harda juice mai sanyi a jug kafin ta futo ta sake jerawa a dining din, already an kira sallan son haka ta tattara kitchen din ta wuce sama, sabon wanka ta sakeyi kafin ta dauro alwala, tana futowa ta shirya a gaggauce ta zura hijab dinta ta fada kabbara, saida ta tsaya tayi sallar isha’i tana idarwa ta mike tsaye ta janyo wayarta ta fuce daga dakin, anatse take saukowa kasa harta karaso wajen dining din, 

Duban abunci da zai ishi cikin ta tayi tana gamawa ta nufi hanyar stairs, a daidai nan ya shugo cikin gidan anatse, daga nesa ya hangota harta wuce sama,

Shima bai hau saman ba saida ya tsaya ya ci delica dun data daga masu kafin ya wuce sama, 

Part dinta ya fara tsayawa yayi knocking, tana budewa ya kalleta daga Sam shar kasa, sanye take da wasu silk kayan barci pink doguwar Riga, kanta babu wani dan kwali, 

Skin dinta sai sheki yakeyi wanda yasa ya kasa duake idnaunshi akanta, saida ta kafe shi da ido tace “Yadai?”

“Sorry uhm, Zan ita samun coffee please”

Gyra tsayuwar ta tayi sai kawai wnai irin murmushi ya kubce mata kafin ta hade rai, “wato yana son yayi using trick dinshi na kai mashi coffee daki kenan? Lallai ma ya…”

Katse mata tunanin nata yayi ta hanyar cewa “idan zai samu ki ajiye min akan dining Zan sauko na dauka thanks wifey, goodnight”

Yana kaiwa nan ya wuce sama, da mamanki take kallon shi harya bace mata da gani, meysa Yanxu Duk abunda taje tunanin akai bashi yake yi ba? Kodai wasa yake mata da tunaninta ne? What sort of game is he playing yanxu kuma”

Haka ta tsaya tana tambayar kanta ganin babu mai bata amsa yasa ta rufe dakin ta wuce cikin bedroom din, 

Daukan plate din data gama cin abunci tayi ta sauko kasa, within 5min ta hada mashi coffee a cikin mug, tana gamawa ta ajiye mashi akan dining kafin ta wuce daki ta rufe kofar ta ta kwanta abunta.

Amar dake tsaye a dakin sa tsawon minti goma yana zarya hoping zatayi tunanin kawo mashi daki saijin shuru yayi, 

Murmushi kawai yayi yana tausasa kanshi don baya son takurata don haka ya sauko kasan da kanshi, yana zuwa kuwa ya tadda ta hada mashi coffee din ta ajiye kamar yanda yace, daukan coffe sun kawai yayi ya wuce sama yana cije lebe yana murmushi,

Washe gari sunday, baije ko’ina ba yana zaune a gida, kwata kwata baima ganta ba yau da safe don bata sauko ba, yana shirin hawa saman ne saigata ta sauko

kasa, sanye take da abaya yau, tayi kyau sosai don ko mayafin abayar bata saka ba, fuskanta fayau babu komai akan fuskan nata, 

Batama Lura dashi ba din haka ta wuce kitchen ta hada tea ta fito tana ya tsine fuska, 

Tana shirin hawa saman ya tako inda yake sai alokacin ta Lura dashi ma “good morning, meysa baki sauko da wuri ba yau?”

Wani irin kallo ta mashi kafin tace “banyi raayin sauko wan bane”

Tana karashe wa ta dan cije Bakinta saboda ciwon marar data Tashi dashi dukda yanxu ciwon ya ragu sosai ba kamar da ba, 

Dan shuru yayi kafin yace “are sure you’re okay?”

“If I’m not zaka ga na sauko ne? Waima tsaya meysa zaka damu?tun adaa baka damu ba sai yanxu ne zaka dunga nuna min Ka wani damu dani, nifa bari kaji Wallahi I hate abubuwa da kakeyi, stop pretending to be nice baya maka kyau ma, Ka koma yanda kake kawai don ni ban ganema wannan actions din naka ba”

Knocking din da akayi ne yasa ta dan jinkirta kafin ta gifta ta gefenshi ta wuce sama abunta, yana kallo ta wuce sama baice mata komai ba haka zalika Baiji haushin ta ba saima murmushi kawai yayi ta gefen baki “I never knew masu shuru shurun nan rigima ne dasu”

Wani knocking sun aka sakeyi wanda yasa ya wuce wajen kofar, yana bude kofar yaga security a tsaye “morning sir, Akwai wata baquwa tace she’s here to see ma’am”

“What’s her name?” Amar ya tambaya

“Take sunanta Madina” 

Shuru Amar yayi don kamar ya san sunan saidai bai gane ko wacece ba don haka yace “okay let her in”

Yana kaiwa nan yabar kofar a bude, nan amra ta sauko hannunta rike da cup din data hau saman dashi, kitchen ta wuce direct ba tare da ta kalleshi ba, tana futowa daga kitchen din ta nufi janye stairs, saurin tsaidata yayi “I’m sorry if na bata maki rai okay? Bakyason Ina tambayar lafiyar ki ne?”

“Yes please, bana son waennan Abubuwan da kake yi, stop being nice to me tunda I didn’t ask for it,”

Marairaice fuska yayi yace “Tohm na bari kin hakura?” Ya tambayeta yana kallonta, 

Gyaran murya da akayi ne yasa suka saiga gaba dayansu, Madina da tun da suka fara magana ta shugo, ta tsaya daga bakin kofa, tana kasa motsawa saboda wani irin tukukun baqin ciki daya turniketa akan abunda amra keyi, bata taba sanin amra bata da hankali ba sai yanxu, namiji na binki kina yin abunda kikaga dama Wai Harda ya daina nuna kulawar shi a gareta abunda mata da yawa suke lacking a gidajensu kenan ita kuwa da Allah ya bata shine take neman yin iskanci, babu abunda Madina keyi sai cije lebe tan takaici ta,

Ganin tana shirin tafka shirme yasa Tayi saurin gyara murya, 

Wani irin murmushi ne ya lulube amra wanda Har hakoranta saida suka futo waje, cikin saurin ta matsa ta gefen ta tunkari inda take “anty Madina… sannnu da zuwa”

Tana karasawa ta rungumeta, Madina dai babu abunda yake sai yaqe don bata son ya gane taji maganar da sukeyi shida amra, “yau gani a gidan amarya,”

“Welcome shugo daga ciki mana,”

Amar daya tako sitting room ya zauna kallo daya yayi masu ya kauda kanshi gefe, suna gab da wuce shi Madina ta tsaya tace “Ina wuni baban triplets”

Kai tsaye ya amsata ba tare da ya juyo ya kalleta ba “lafiya lau Alhamdulillah”

Sama suka wuce inda amr ta jata Har zuwa bedroom dinta Har lokacin murnar Ganin ta take,

Suna shiga daki Madina tayi saurin ajiye handbag dinta a gefen gadon amran tare da wayarta da mayafinta gaba daya kafin ta fuskanshi amra “Aisha please ki fada min dan Allah meke damun brain dinki ne? Ke ko Anya kinsan darajar aure kuwa? Wallahi azeem ban taba sanin bakida hankali ba sai yau,”

“Anty Madina me nayi kuma” amra ta fada tana tabe baki

Janyo hannunta Madina tayi don ta mike ne da zummar dauko mata drinks

“Kinga zauna, nan gefe tukunna,”

Nunfasawa Madina tayi tace “fada min? Ya rayuwar auren ku take? Kinyi amfani da was in dana tura maki?”

Shuru amra tayi kafin tace “anty Madina I’m not ready gaskia, nan huce ba Har yanxu”

“Aisha kiji tsoron Allah, Wallahi azeem mala’iku na tsine maki, Allah yana fushi dake, ke hatta sallar ki bata karbuwa akan Abubuwan da kikeyi, ke wai meke damun kanki? Are you sure bakida aljanu?”

 Jikinta ne ya danyi sanyi “bani da komai Wallahi”

“Toh meysa kike yin haka?”

“Ni Wallahi haushinsa kawai nake ji akan abubuwan da yayi kin abaya “

“ uban yayan kine fah? Mijinki ne fah? Ke bakya yafiya ne?”

“Ina yi” amra ta amsa ta

“Toh yanxu me kike so? Auren nashi ne bakya so?”

“Ah ah ni kawai dai….”

Saurin katseta Madina tayi “Wallahi yanda kika san na kwade ki haka nake ji, kaii kin bani kunya Wallahi”

Ganin Madina ta dau da zafi yasa amra tace “dan Allah kiyi hakuri, ni na kasa gane dalilin da yasa ni jin kasa gane abund ake raina, it’s so hard…”

“To forgive him or what?” Madina ta katse ta da tambayar 

“Yes, ni inajin kamar pretending yake yi”

Hannunta Madina ta rike “dan Allah ki sauke kanki haka, yau watanni Nawa yana fama dake kinji dan Allah indai kin dauke ni a matsayin yar uwa kuma kinsan bazan taba cutar dake ba Ina rokonki da ki sauke kanki kiyi abunda ya dace plss”

Madina ta fada mata cikin lallami don amra saida haka,

Sauke kanta kasa tayi tace “Toh anty Madina zanyi”

“Promise me”

“Toh anty Madina promise”

Murmushi Madina tayi tace “kinga yanda kika Kar kyau kuwa shiyasa naga ya kasa dauke idanunshi akanki dukda kina mashi hauka,”

Dariya amra ta danyi ta waske zancen “me Zan kawo maki Kisha?”

“Kinga dawo tukunna, wannan sai anjima, yanxu zo ga tsarabar danayi maki alkawari,”

Jakar da Madina ta shugo dashi ne ta bude ta zazzaga mata akan gado, set of wasu matsiyatan hadaddun English wears ta sayo mata masu kyau daga uk kusan Kala biyar Riga da wando da dogayen riguna gefe kuwa wani turare ne mai suna let’s meet mai shegen kamshi

Kallon kayan kawai amra tayi kafin tayi mata godiya 

“Kinga nasan halinki in kinsan bazaki saka ba Zan kwashe kayana”

“Wallahi Zan saka” amra ta bata amsa tana dariya

Hira sukayi sosai inda Madina kw nuna mat Wai abubuwa sosai daya kamata ta dunga yi, sai wajen yamma likis tayi mata sallama t wuce gida.

The next day….

Bata Tashi da wuri ba sai wajen karfe sha biyu,

Wayanta ta fara duba nan taga videos din babies dinta da salima ta tura mata, tunda ta kalla videos sun mood dunga ya sauya zuwa na farin ciki, she’s so happy Ganin yanda sukayi wayo sosai,

Ganin lokaci na tafiya tana daga zaune yasa ta mike ta wuce bathroom

Ci kin Yan mintuna kalilan ta futo daga bathroom , agurguje ta shafa mayukan ta ta fesa turare kafun ta wuce closet dinta, harta janyo abaya idanunta y sauka kan kayan da Madina ta kawo mata, wani tunani ne yazo mata “let’s test him first”

Ta fada ahanakli tana murmushin mugunta kafun ta janyo wata arniyar rigar,

Saida ta feshe jikinta da turaren let’s meet din da Madina ga kawo mata kafin ta fara kiciniyar saka yaloluwar rigar

Gaba daya riga kasa gane gabanta tayi da bayanta haka sai ta samu ta zurata da kyau son ta kamata sosai don Har ass dinta na lobawa a jikin rigar, 

Tunda ta daga nake kallonta Ina Masha Allah, she look so sexy a cikin rigar, gaba daya rigar ko knees dinta bata kaiba, a gaban kasan rigar an yanyanka rigar ya zama kamar taliya, gaban rigar kuwa anyi amshi v neck daya fudda cleavages dinta sosai, hannun rigar kuwa dan micici ne, fadin irin kyawu datayi a rigar ma bata lokaci ne, daukan wnai band tayi akan dresser ta makala akan gashin ta, yanda yake motsa jikinta ma dakyar yasa taji kamar ta cire rigar saidai tunawa da kudurin dake ranta yasa ta daure kawai, dan kohl dake gaban dresser ta duaka ta goga a idanuta tana ajiye kohl din idanu ta ya sauka kan anklet dinta, wani murmushi ta sauke wanda ita kadai tasan maanarsa, 

Babu wani bata lokaci ta saka anklet din ta fito da daga dakin hannunta rike da waya, kasa ta fara sauko ta wuce kitchen ta danyi

91 / 94