Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   37 / 94

108K to 111K   out of 279.4K words

budurwata chika, zata iya mana wannan aikin”

Da sauri Jan ido yace “yauwa kirawota kawai a wuce wajen”

Kiranta Dayan yayi cikin mintuna kadan ta karaso a napep, wata budurwa ce ta fito ta tunkaro motar tasu, Bakinta bakin kirin da alamu yar hannu ce, fiskanta babu kyan gani tsabar lalacewa da tayi saboda bleaching,kanta uban attach ne gaban motar ta tsaya tayi masu knocking kafin su bude motar, tana shiga ta jefa cingum din Bakinta ta fara tauna tace “Nawa zaku bayar?”

“Dubu hamsin baby” saurayin nata ya fada

Gwalo idanu tayi tace “chap, kisa fah? A dubu hamsin? Kudai ku dan Kara gaskia”

Saurayin ta ne ya matso kusa da ita yace “ke bari kiji, idan har kikayi nasara ma alhaji zai baki double”

Washe baki tayi tace “angama, saidai Zan buqaci taimakon…”

Bata kaiga karasawa ba Jan ido ya tare ta da cewa “basai kin buqaci komai ba, wannan allurar zakiyi mata kawai, room number 4”

Karban allurar tayi tace “ku jirani nan da minti goma”

Fitowa tayi daga motar ta shige asibitin, duban ko’ina ta fara yi ganin babu cctv yasa ta fara bin hanyar dakunan asibitin, ganin wata kofa an rubuta staff room yasa ta shige ciki ta rufo kofar, nurse din dake zaune ta dago ta kalleta tace “madam lafiya? Bakiga an saka staff room ba zaki shugo kai tsaye babu knocking? Ku matsalar hausa people kenan, common sense baku dashi, fita nan restricted area ne kije reception ki tambayi….” 

Kasa karasawa nurse din tayi sakamakon bugun kanta da budurwar tayi da wani karfe, nan take ta fadi wanwas don ko ihu bata bata damar yi ba, tana faduwa chika Tayi saurin sabule kayan nurse, saida tayi mata zirr kafin ta soma cire nata kayan ta saka na nurse din, zaro face mask tayi ta kafa a fuskanta kafin ta dauka wani dan tray dake dauke da magunguna ta fuce daga dakin.

Direct hanyar room four tabi, ganin sojoji a tsaye bakin dakin yasa tadan tsorata, tsaida natsuwarta tayi ta nufi hanyar, daya daga cikin sojojin ne ya miqe ya bude kaita kofa ta wuce ciki don bai kawo komai a ranshi ba.

Tana shiga ta sauke wani irin nunfashi, da sauri ta maida idanunta kan meeda dake kwance, gefenta kuma kakarta ce tana gyangyadi akan kujera sanyin ac na ratsata harda munshari, ba tare da bata lokaci ba ta karaso Har inda suke ta tsaya, hannun meeda ta Kaya ta saita allurar, saida ya zuba duka allurar kafin ta tabe baki tace “ita kuma wannan ko me tayi haka suka kudiri kasheta,” tabe baki tayi don ita wannan ba damuwar ta bace, kakar meeda ce ta farka saboda motsin dataji, ganin nurse a tsaye Tayi saurin cewa “au laa malamar asibiti kin dawo ashe, dan Allah yaushe zata Tashi?”

Wata bazawarar dariya chika tayi tace “Anya zata Tashi kuwa?hmm”

Tana kaiwa nan ta fuce abunda, mai zogale dai da idanu ta bita tace “daman ma aikatan asibitin nan basu da mutunci, la’ananniya da ikon Allah jikata zata warke” chika najin ta tayi banza da ita ta fuce, tana barin wajen tayi hanzari fucewa tabar asibitin ba tare da mutane sun zargi wani abun ba harma da sojojin.

Bayan fitar ta ko minti biyu ba ayi ba meeda ta fara wani irin jijiga kamar zata mutu,hankali atashe kakarta ta miqe tana salati tace “na shiga uku ke yar nan” ganin jinigar taqi karewa ga nunfashinta na daukewa yasa kakar saurin fitowa hannunta aka tace “na shiga uku, jikata ku taimaka,” da sauri sojojin da wani doctor suka shugo dakin basu kaiga karasawa rai yayi halinsa, doctor ne ya tattaba ta Ganin bata nunfashi yasa ya janyo blanket din yace “she’s gone, time of death 3:15pm”

Yana kaiwa nan ya fuce sojojin ne suma suka fito daya daga cikinsu ya fara Kiran asad don ya shida mashi mutuwar, kakar meeda dai salati ta dunga dokawa hannunta aka tace “shunkenan daman tace kasheta za ayi na shiga uku na mai zogale kaicho na da wannan rayuwa, Allah ya jiqanki yar nan”

Asad dake hanyarshi ta dawowa bayan ya sauke Amar, shima damuwa kwance a fuskanshi, wayarshi dake gefen dashboard tayi ringing, daman already yayi connecting wayar da Bluetooth yana Ganin call daga yaranshi yayi saurin daga wa, anatse ya fara sauraron abunda yaron ke fada mashi kan cewa meeda ta rasu, da karfi yace “whatttt!!!! Awa biyu kenan fa  da barina daga asibitin how??”

“Oga yanxu nan likita ya shiada hakan”

Katse wayar asad yayi ya daki steery yace “shittttt!!!! No”

A guje yaja motar Tashi Har zuwa asibitin yana parking ya fito ya shige cikin asibitin, dakin da aka kwantar da ita ya shiga, karasowa yayi har gaban gadon ya tsaya ya kafa mata idanu, mai zogale na Ganin shi tace “shikenan an kasheta, daman tace kasheta ake sony”

Shuru shima asad yayi don lokacin daya bar asibitin she’s recovering sosai don allura Akwai doc yayi mata da Karin ruwa wanda zai Kara mata kuzarin jikinta, yaranshi dake biye dasu ya kalla yace “did anyone enter the room aside from me? Or did you sense any suspicious activity around?”

Atare sukace “no sir, bayan kai babu wanda yazo”

Shuru asad yayi yace “call the doctor”

Daya daga cikinsu ne ya futa ya kira doctor suka taho tare, kallonshi asad yayi yace “what’s the cause of death?”

Tattara idanuwa doctor ya soma yace “pulsate attack”

Shuru asad yayi yana nazari, suna nan tsaye wata nurse ta taho da sauri tace “sir we have an emergency, na shiga staff room naga nurse T akwance tana bleeding, it’s looks like anyi attacking dinta”

Da sauri asad ya dago yana kallon nurse din dake bayani kafin ya bisu da idanu don Har sun fuce, bin bayansu shima yayi shida mutanen shi, cikin dakin suka shiga Ganin nurse din a kwance tsirara sai wani kaya agefenta, da sauri Duk sukayi baya aka gyara nurse din ta hanyar daukarta aka daurata kan gadon marasa lafiya, taimakon gaggawa doctor yayi mata kafin su asad suka shigo, suna nan tsaye matar ta farfado tare a furgice kamar zata gudu tace “lord save me,”

Kallonta sukayi su duka, doctor ne ya soma tambayarta abunda ya faru, nan take ta shaida masu abunda zata iya tunawa, nan take asad ya kalli yaranshi hankali tashe yace “Akwai nurse din data shiga dakin kafin ta mutu?”

Su ku yar dakai sukayi daya daga cikinsu yace “Akwai wata nurse data shiga bayan fitar ta da minti biyar mukaji ihun wannan tsohuwar,”

Saurin runtse idanu asad yayi ranshi ya gama baci, don ta tabbata kasheta akayi, dakin da gawar meeda ke kwance suka shiga, asad ne yayi saurin cewa “kaka, bayan fitata daga dakin nan Akwai wanda ya shigo?” Ya tambayeta 

Kallonshi tayi tace “babu wanda ya shigo bayan futarka kaida liktannan sai wata malamar asibiti,”

Da sauri ya sake tambayarta “Akwai abunda tayi mata lokacin data shigo”

Shuru mai zogale tayi tana nazari kafin tace “lokacin data shigo Ina gyangyadi dana farka naga kamar allura ahannunta,la’ananniyar yarinya, dana tambayeta zata Tashi kuwa tace min babu ranar tashi mutuwa zatayi ashe da gaske take” ta karashe tana hawaye

Ran asad ya gama baci don tabbas Akwai lauje cikin Nadi, don ya gama tabbatar da komai kashe meeda akayi ta hanyar amfani da identity din nurse dinnan, wayar Amar ya soma dialing akashe Ganin haka yasa ya aje wayar yayi clearing komai aka saka gawar meeda zuwa kauyensu.

Harda asad aka tafi zuwa chan kauyen aka sallaceta aka kaita makwancinta kafin ya juya zuwa abuja.

Karfe takwas ya iso abuja, direct asibiti ya koma yayi bunciken da zaiyi, cctv daya ne kawai a cikin asibitin shine na reception nan ya shiga duba daga time din daya bar wajen, ya dade sosai yana bunciken Har Allah ya nuna mashi inda wannan budurwa ta  shigo da doguwar rigar jikinta nan take nurse T ta shiada itace tayi attacking dinta.

Nan asad yasa aka fara baza hotonta a ko Ina aka fara nemanta, cikin awa biyu aka gano inda take saidai itama gawar ta aka tsinta bayan gari.

Cije lebe asad yayi, ya furzar da nunfashi ya fuce daga asibitin.

Akan hanyarshi ta zuwa gida ya sake Kiran line din Amar still a kashe, tunanin kodai ya wuce taura estate yake chan kuma kawai ya bari zuwa gobe saiyaje yaji lafiya.

Yana karasawa gida wayarshi tayi ringing, duban number yayi ganin research team ya dauka wayar, tunda ya fara sauraron su ya runtse idanu, saida suka gama mashi bayani kafin ya kashe wayar ya daki gaban motarshi yace “Alhaji kabiru!!!!!!!”

Ya dade a cikin motarshi yana waya da mutanenshi kafin ya futo ya shige cikin gida jikinshi a mace don yaji zafin mutuwar meeda sosai.

Alhaji kabiru’s secret hideout….

Alhaji kabiru ne zaune, murmushi kawai yakeyi yana magana da kanshi shi kadai “kai yaro yaro ne, kayi kuskuren shiga inda bai kamata kaje ba.” 

Tun bayan kiran shi da Jan ido yayi ya shaida mashi cewa sun gama aiki yaji wani irin sauqi aranshi, ba tare da ya damu yasan yanda suka kasheta ba yace su tabbatar basu bar wani evidence dinda za a san sune ba, nan take hankalinsu ya tashi musamman Jan ido don haka yana kashe wayar Alhaji ya kalli inda chika take zaune tana jiran su bata kudinta ta Kara gaba, fitowa Jan ido yayi ya dawo baya inda take zaune yace “kinyi kokari baby Ay yanxu dubu dari da hamsin ma Zan baki” hannunshi ya saka cikin aljihun kamar yana shirin zaro kudin,

shammatarta yayi ya zaro allurar nan ya Chaka mata a wuya, da sauri saurayin chika ya gwalo ido yace “kai mazaaa ya haka? Maysa zaka kasheta”

Bai kaiga karasawa ba ta fara jijijga cikin mintuna kadan nunfashinta ya dauke, kallonshi Jan ido yayi yace “kai kana tunanin sojojin nan baza su ganota ba? Kai kasan waye wannan sojan?Lieutenant asad abdallah alqali ne fah? Shine wanda ya kama tsohon oganmu Duk karfin da yake dashi, don haka bazamu janyo ma kanmu ba” yana kaiwa nan

Ya fito ya shiga gaba tare da fuzgar motar zuwa bayan gari, dakanshi ya fito ya jefar da ita anan.

Bangaren amar sai wajen karfe sha daya ya bari wajen ammah, yana fitowa ya wuce gida direct, saida ya dawo gida ya lura da wayar daya fasa dazun, abubuwan da suka faru ne suka dawo mashi take, saurin runtse idanunshi yayi ya dauka wayar, gaba daya ta gama fashewa tass SIM card dinshi ya cire daga wayar kafin ya jefa ta cikin dustbin,cikin closet dinshi ya shiga ya bude briefcase dinshi ya zaro dayar wayarshi wanda yawanci acahn dubai yafi amfani da ita itama iPhone 14 pro max dual sim dince latest black color, bude wajen sim yayi ya saka SIM card dinshi kafin ya kunna wayar, wayar na kawowa ya aje ta ya wuce closet ya sauya kaya zuwa na barci, kwanciya yayi kan gadonshi ya jawo wayar ya saka iCloud din waccar wayar data fashe kafin yayi setting komai nan take ta dawo kamar waccar Har video din da wannan mutumin ya tura mashi ya dawo kan wayar,baiyi gangancin kallon video dinba ya tura cikin private portal dinshi, kurama wayar idanu yayi yana tunani, kamar wanda aka tsungula ya shiga contact yayi dialing wani international number da baiyi saving ba, saida wayar ta kusa tsinkewa ta daga tare da cewa “assalam alaikum”

Shuru yayi yana sauraron muryarta Wani irin sanyi na ziyartar zuciyarshi, jin shuru yasa asanyaye ta sake cewa “hello” 

Gyaran murya yayi nan take ta gane shine, shuru tayi bata sake cewa komi ba chan kuma tunawa da maganar da sukayi da haifa inda take ce mata tabishi ta Lallama don ya saketa tunda Sauran su few kwanaki su gama housemanship.

Anatse cikin muryarta mai dadi sauraro tace “Ina wuni yaa..yaaaa?”

Yanda take jan yaya dinnan ba karamin sauke mashi kasala take ba, her voice is melodic and sexy at the same time, saurin daidaita natsuwarshi yayi yace “hope everything is okay over ther?”

 Tayi mamaki jin tambayar da yayi mata dan haka Tayi saurin cewa “Alhamdulillah!!”

Shuru ne ya biyo baya sai sautin nunfashin juna da suke ji a kunnuwansu, shi yanda take sauke nunfashi a kunenshi har wani irin yake ji ita kuwa barci ne ma ya soma dibarta, Janyo duvet din ta tayi ta lulluba  tare da lumshe idanunta  tace “uhm Zan kwanta kaina yana ciwo”

“What’s the time now over there?” Ya tambayeta 

“4pm” ta bashi amsa ataqaice 

Jin yayi shuru ta sake cewa “Zan kwan…”

Katseta yayi ta hanyar cewa “na hanaki ne?”

Itama adan harzike tace “Toh Ay karna kashe kace nayi laifi”

Banza yayi da ita don haka ta aje wayan agefenta ta bata barcin hankali kwance, shima samun kanshi yayi ta barin wayar a kunne bai katse call dinba yana sauraron yanda take sauke nunfashi Har barci ya so soma dibanshi, tunani ya fara yanda lokaci guda magana da ita da yayi yaji gaba daya danuwarshi ta warware, what he’s feeling is different don lokacin dayaje yaga amma yaji sauqin damuwarshi saboda hirar da sukayi saidai ita wannan yana kiranta yaji kamar an cire shi daga damuwar dayake ciki, he found peace and harmony lokaci guda.

Washe gari da wayar asad ya Tashi inda ya samu munmunan labari daya tayar mashi da hankali sosai, mutuwar meeda ta girgiza shi, he felt so bad to the extent that ya fara blaming kanshi don shine ya nemi taimkonta Har rayuwarta ta salwanta,hankalinshi bai gama Tashi ba saida asad ya tabbatar mashi da Alhaji kabiru ne yasa a kasheta, idanunshi sunyi jaaa don kamar ya zauce, nan yake shaida ma asad abun da ya faru jiya da abunda ya gano akan mutuwar dada, ba karamin rudani asad ya shiga ba shima, nan suka tabbatar da babu abunda Alhaji kabiru bazaiyi ba, don abu nashi yayi nisa sosai, kisa a wajen shi ba komai Bane ba, zai iya kashe kowa ma Duk sanda yaga dama.

Tunda suka zauna shida asad babu wanda yace qala kowannensu da tunanin dake ranshi, asad ne ya katse silence din ta hanyar cewa “oga gaskia mutumin nan abun tsoro ne, ya kamata kayi wani abu akan family dinka tunda har yanxu he’s wearing fake mask yana tare daku,inaga muyi arresting dinshi kawai, because your family is in danger”

Shuru Amar yayi yana nazarin maganar asad yace “but that’s not the plan dude, idan mukayi presenting wannan evidence din na kashe dada da yayi is not enough da zaiyi roting a jail, I want him to suffer, inason yayi regretting, inason ya wulaqanta, I want him to be miserable, I want to fight him not just for dada but for all the people that have suffered because of his dirty doings”

Shuru asad yayi ya sake cewa “but kasan Barinshi yana yawo haka is risky, I’m sure he found out Muna neman downfall dinshi,

what if….”

Da sauri amr ya katseshi “he’s an old jerk, I’m sure ya kashe yarinyar nan ne saboda ya rufe Bakinta”

Asad ne ya sake cewa “Yanxu dai you need to think about family first, Alhaji kabiru can do anything don kar asirinshi ya tonu, just look at how he mercilessly kill….”

Dago da jajayen idanunshi yayi ya zuba su kan asad yace “I will find a way to protect them from him,”

Asad ne yace “shikenan but we have to work smartly dole mu samu evidence cikin gaggawa nasan yanxu yasan bamuda komai against him so bazaiji tsoron komai ba.

Tattaunawa sukayi kafin ya fuce daga office din asad Ganin kusan karfe uku na rana.

Tun bayan fitarshi daga office sun asad maganganunsu na dawo mashi arai, what if Alhaji kabiru yayi yunkurin cutar da family dinshi? No he won’t allow that ya bama kanshi ansa, tunani ya fara yi akan yanda zaiyi ya kubutar dasu.

A daidai asibiti yayi parking ya fito ya shige ciki, saida ya fara wucewa wajen family doctor dinsu ya mashi bayanin progress din da ammah ta samu kafun ya bashi sallama tare da jaddada mashi kan maganar kula da ita yanda ya kamata tare da hanata shiga damuwa ko wani abunda zai sata fargaba.

Yana fitowa ya wuce pharmacy ya karba mata magungunan ta kafin ya wuce dakin nata, yana shiga bakinshi dauke da sallama yace “ammah na good afternoon ya jiki”

Karasowa yayi gabanta ya rungumeta yana me jin kaunarta a aranshi, shafa bayanshi tayi tace “you’re acting like the little Amar”

Dariya Har kumatunshi na lobawa yayi yace “I’m still the little amar”

Dariya itama tayi tace “ are you okay son? Inajin kamar kana cikin damuwan wani abu?”

Hijab dinta ya gyara mata yace “babu abunda ke damuna, I’m just stressed gashi kwana biyu bana ganinki a gida that’s it”

 Murmushi tayi tace “yanxu Ay zamu koma gidan ko tunda naji sauqi”

Atare suka fito Har zuwa motarshi ya bude mata bayan motar ta shiga kafin ya rufe ya shiga, tunda ya fara driving suka fara hira, tayi mamakin yanda yake magana ba kamar da ba, don kwata kwata bashi da surutu bashida hayaniya ma gaba dayanshi don miskili ne sosai maganar ma wahala yake mashi, a yanxun ma kamar yana forcing kanshi ne yana magana don inyaji tayi shuru saiya dago wani zancen wanda hakan ba karamin dadi yake mata ba.

Suna isa gida su salima suka fito da gudu salim harda tuntube ganin ammah, atare suka rungumeta salima ce Tayi saurin cewa “wayyo ammah na, ya jikinki we’ve missed you alot “

Shafa kanta amma tayi tace “ay gani na dawo, ya kuke ya makaranta I missed you too dearest”

Zama Amar yayi yana kallon yanda suke ma junansu, he’s so happy, mahaifiyarshi uwa ce ta gari, batada dagawa, bata da halin wasu matan.

Anan zaune ya barsu suna hira ya wuce dakinshi, shower ya sakarma kanshi kafin ya fito, tsayawa yayi ya karema jikinshi kallo kafin ya sauya wasu kayan zuwa marasa nauyi.

Aranar dai gidan was so lively, don shima fitowa yayi suka ya zauna tare dazu duka yana

37 / 94