Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   8 / 94

21K to 24K   out of 279.4K words

akan idanunshi Har zuwa lokacin da tayi yar karar, tare da dan duqawa kadan.

Har inda take ya tako ya tsaya dan nesa kadan kafin yace “get up”

“Adan furgice ta jiyo ta ganshi don batayi tsammanin ganinshi ba din Duk tunaninta ya wuce sama, miqewa ta soma yi ahankali kafin ta daga kafa daya ta kwala yar kara, tabe baki yayi don ganin kamar Ma abun nata da raki da shagwaba baiyi wata wata ba ya sungumeta gaba daya, Sai jinta tayi a sama, tsoron dauka. Da yayi mata bazata ya sata saurin kankameshi sosai wanda hakan saida ya sashi dan tsaya jimm jin lafiyarshi ta motsa, daidai ya natsuwarshi yayi kafin ya haifa saman da ita, Har bakin gadon ta ya sauketa bai tsaya kallonta ba ya juya ya fuce daga dakin, yana futa kuwa ta sauke wata ijjiyar zuciyar, cikin Yan mintuna kadan Sai gashi da babban mug daban, karasowa yayi gabanta ya miqa mata, bai ce komai ba ita ma tana ganin yana miqa mata ta karba tare da cewa “thank you!”

Ganin ya tsaya bai motsa ba Sai nannade hannayenshi dayayi a kirjinshi gashi ya zuba mayun idanunshi dake sata jin wani iri ya sata kauda kai gefe ta soma kwankwadar ruwan batama jin zafin ruwan harta shanye tass ta sauke nunfashi  still hannunta nakan kirjinta tana kokarin rufe kirjinta, shi mamaki Ma yake tana da kananun shekaru take da jiki haka, tsaki yayi ganin yanda take kare kare kafin yace “what are you hiding?,” ya fada yana hade rai tamau 

Saurin dagowa tayi ta zuba mashi idanu chan kuma ta sauke still hannunta na kan wajen, “babu komi”

Wani irin kallo ya zagba mata mai Wayar fassara wanda ya sata daburcewa ganin yanda ya bata rai sosai.

Kamar wata munafuka haka ta sauke hannun ta kadan ta kare wajen yanda bazai gani ba.

Oga dai gyara tsayuwanshi yayi yace “Ina kike jin ciwon”

“Kasan mara ne” ta fada Adan shagwabe don tama manta dawa take magana, abunka da mara lafiya da neman attention

Kamar ya karanenceta kuwa ya sake tambaya “wajen Ina ne let me see”

Kamar doluwa haka ta mike tama manta da kare Karen kirji da take ta tako gabanshi tana turo baki a shagwabe ta daura hannunta kasan shafaffen cikinta wajen mararta ta sunkwi da kai tace “nan kasan”

Tunda ta mike ta dunfaro gabanshi kamshinta ya bugeshi sosai Har cikin hancinshi, Dukda da yar tazara tsakanin su saida ya tako gab da ita sosai, itako da kanta ke Kasa tana kokarin nuna mashi Sai jin nunfashinsa tayi daidai fuskanta yadan duko gabanta sosai ya sauke mata lafiyayyen nunfashinsa mai zafi akan fuskanta, abunda yafi tada mata hankali shine jin saukan lausansan tafun hannun shi akan mararta dake cikin yaloluwar rigar da ita da babu Duk daya, da sauri ta ragi idanunta tare da sauke wa ka shi, nan take tayi arba da Tashi fuskarta daidai tata Har hancinsa na neman gogar nata, tuni nunfashinta ya tafi wucun gadi, don kamewa tayi kyam ta Kasa motsi, hannunshi kam yana nan kan mararta shima ya Kasa daukewa don wani irin shock yaji ya durar mashi take ya gane cewa lafiyar ta dawo inma bata gama dawowa ba kiris ya rage, shafa wajen daya danyi ne ya maidota hayyacinta da kuma muryarshi dake dauke da kamshin mint daga bakinshi 

“Daidai nan ne?”

Kamar wawuya ta bude baki tace “uhm”

Kara dan matsa wajen yayi yace “uhmmmm”

Jikinta ne ya soma kyarma 

Da sauri ta danyi Kara tace “zafi tare da saurin yin baya ta koma ta tsaya sauraron yanda zuciya ta ke racing sosai, tabe baki yayi Harda yar guntun tsuka yace “go back to sleep”

Batayi wata wata ba ta hau kan gado ya bita da idanu harta janyo duvet ta rufa, jin alamun bai motsa ba yasata bude kanta tace “good night yaya”

Bai tsaya amsata ba ya juya tare da janyo kofar ya rufe mata 

Yana futa ta sauke ijjiyar zuciya sosai tana mamakin yanda ya sauko yau, saidai bata sama kanta hope sun haka zasu dinga tafiya ba don baka gane mashi kwata kwata.

Dakyar barci barawi ya kwasheta dukda idan ciwon ya nuqurquso ta farkawa take idan ya lafa kuma ta koma.

Shima gogan yana shiga daki ya hau kan gadonshi ba tare da tunanin komai ba yayi kwanciyarshi saidai barcin baizo mashi ba Sai gab da sallar asuba tunani iri iri na yawo a kwakwalwarshi saidai yanda yake da dakewa yasashi kawar da komai kamar ba komai ba.

Washe gari Monday da sassafe ya fuce daga gidan saboda wani urgent investigation da zasuyi shida lieutenant asad, koda ya fuce Nadine ma bata fito ba,

Ahankali ta soma bude idanunta da sukayi mata nauyi sakamakon baccin data samu gab da sallah asuba, Mika tayi tare da addua Tashi daga bacci, ayanxu ciwon cikin nata ya dan ragi don sama sama take jinshi, gashi maganin datasha ya sata jin kwarin jikinta, kafafunta ta sauke kasa ta wuce toilet, ba tsaya komai ba ta fara watsa  ma jikinta hot bath, tana gamawa a gurgurguje tayi brush ta fito don yunwa takeyi sosai, Riga mara nauyi ta zaro doguwa daga cikin kayanta tare da set din bra da pant dinta ta shirya tsaf,saida ta feshe jikinta da turarenta bata tsaya shafa mai ba ta nannade gashunta ta tura cikin hula ta fuce daga dakin, Kasa ta sauka ganin Nadine bata parlor yasata wucewa kitchen direct, tana shiga kuwa ta hangota tsaye tana goge gogen gas da alamu bata dade da amfani dashi ba, cikin girmamawa suka gaisa kafin ta tambaya jikin ta.

“ how are feeling now ma?”

“Alhamdulillah Nadine naji sauki”

“Na gama breakfast yana dining, daman na bari na gama ayyuka ne Saina duba ko kin Tashi don dazu wajen 7 bayan sir ya futa na leko don naga ko jin Tashi sainaga baki Tashi ba”

Nunfasa tayi kamar bazatace komai ba chan kuma tace “uhm shi ya karya ne?”

“No bai karya ba, lokacin daya futa ma ban dade da futowa ba, nima ban sameshi ba don saida naje kaima security da driver abunci naji sun futa shida driver da sassafe.

“Oh okay,Yau me kika dafa mana nadine”

Murmushi Nadine tayi tace “ma, asual dai chips ne Sai egg sauce da chicken pepper soup”

Shuru amra tayi kafin tace “Bari naje dining din, sannu da aiki”

Tana kaiwa nan tasa kai ta fuce nadine ta bita da ido tana murmushi tace “wannan yarinya badai kyauba ga fara’a saidai shi yayan nata baida fara’a kamar ita”

Zama tayi  ta zuba chicken pepper soup din daidai cikinta kafin ta hada tea mai zafi, laifi taci da dan yawa, kafin ta sha tea din  don shi tafi buqata, tana gamawa tayi hand aka ta goge bakinta ta wuce sama, magungunan da doctor ya bata ta ballo tasha zauna gefen gado ta janyo wayanta, line din haifa ta soma

kira, baya shiga tun last time da sukayi waya ta daina samunta, haka zata kira dinga kira amma baya tafiya kwata kwata.

Amar…

Tunda ya karaso Nigerian army headquarters ya wuce direct office din lieutenant asad, tundaga gate kowa yasan anyi babban baqo,Duk zuwan da zaiyi Sai an zuba manyan securities wanda baya don haka sbd ba official zuwa yyi ba don cikin sirri suke yin aiki da taimakon asad saidai in Har zai shiga headquarters na sojoji dole Sai Ansan da zuwan shi, shiyasa yawanci idan zasuyi meeting akan investigation da sukeyi yake saka lieutenant asad ya nema masu waje mai sirri, wannan zuwan Ma da yayi zuwan gaggawa ne kuma dole ya shigo cikin headquarters don abun ya shafesu.

Yana iso wa ya wuce direct office din asad, yana shiga kuwa ya miqe suka gaisa cikin girmamawa kamar yanda suka saba, shima office dinshi babba ne kamar ko wani office saidai kuma bazai taba Kamo na general gabaki daya ba lols.

Tunda ya fara ma asad bayani, baiyi wani mamaki ba don abunda yafi haka Ma za a samu anan nigeria, gashi sunada report dayawa akan child trafficking da akeyi da yawan futar haramtarciyar kwaya wanda an Kasa gano daga inda take, gashi tana kisa musamman wa kauyuka sbd yawanci waste din drugs din rafi ake kaiwa ayi dumping inda baza ayi tsammanin ,mutanen kauye kuwa basu damu da  chan ruwan rafin sukeyi wanda daga karshe su dinga cututukan da ba a gano ta yanda suka samu.

“Oga nifa bazanyi mamaki ba,we have thousands of report akan child trafficking, yanxu haka da nake maka magana Akwai badge of yaranda went missing, Mun Kasa gano komai, amma yanxu ka kirashi muji idan zai samu turo mana evidence koda hoton yaranda aka tafi dasu tunda yace maka ya tabbatar Yan nigeria ne Sai muyi comparing mu gani daga nan zamu damar tracking ta inda yaran suka bace”

Shuru Amar yayi kafin ya dauka wayanshi ya soma dialing number hammam..

Ringing daya biyu ya dauka 

“ hey dude”

“I’m so surprised ka kira, bansan da wani baki zan baka hakuri ba, I’m so sorry dude”

Nunfasawa Amar yayi kafin ya saka wayan a speaker 

“It’s okay dude, naji dadi da kayi uniting da mahaifiyarka”

Murmushi hammam yayi yace “all thanks to you, ta dalilinka na gano komai and I promise you yanda na fada maka I will make sure Mun kawo karshe azaluman nan”

“Insha Allah” Amar yayi saurin maida mashi kafin ya cigaba 

“Now I need your help, naga email din da kayimin akan abubuwan daka gano”

“Oh yes, jiya an kawo yara wajen alif, nan tambaya shi ba don normally idan naga an kawo mutane gidanshi bana magana,don baya son yawan tambayoyi, saidai bayan an aje su ah gidan I sense something very fishy, I had to dress like one of the workers dake gidan, na shiga inda ake aje mutane a nan gidanshi kafin a kwashesu zuwa wata Kasa, dude I was so surprised with what I see, yaranda na gansu an shigo dasu lafiya kalau Saina gansu sun zama mahaukata, Akwai mutun daya da naga yanata kuka, yaron is about 17 years i rush to him na tambayeshi, nan ya shaida min an shigo an basu wata kwaya, shi dai yaji tsoro bai sha ba yace zaije toilet bayan an bashi bai hadiye ba, yana zuwa toilet ya boye a wandonshi, I quickly ask him su sunsha, nan ya shaida min sunsha suka haukace after few hours don gaba daya daga zuwansu bayan an aje su a daki aka basu,”

Da sauri Amar yace 

“Zaka iya tuna lokacin da aka kawo su da lokacin da aka bama yaran kwayar”

Shuru Hammam yayi kafin ya cigaba “yea about 5hours”

“Damnnnn” Amar ya bugi table da yasa asad saurin dagowa, ganin yanda idanunshi sukayi jaaa Har jiniyoyin wuyanshi na futowa yasa asad bude fridge din gefenshi ya zaro ruwa ya bashi, yana karba ya mashi kwankwada daya ya wurga bottle din ya cigaba 

“Dude send me the picture of the drug,I just need to confirm it, and also I need the picture of the boy, and some of his information tunda kace dan nigeria ne”

“Okay dude”

Cikin qanqanin lokaci kuwa saiga hoton drugs din harda hoton yaron ta email, yana budewa ya bugi table din yace “ka gani ko, those bastards,I will Make sure they pays all they have been doing” 

Da kyar asad ya tausasa shi don dan maza yayi mugun baci saida yadan dawo daidai kafin ya sake Kiran hammam don wayan ya yanke, yana dagawa kuwa ya fara bashi command don gaba daya ya rikide ya juye ya koma asalin general. Babu fara’a a kausashe ya soma magana da karfi

“ officer Hammam shuraim”

Jin haka yasa Hammam saurin cewa “yes sir, officer Hammam on the line waiting for you Command!!!!!!!”

“ I command you, with your power to investigate throughly on alif shuraim, don’t leave even his finger tip during this investigation,most importantly I need his private account, that will be the link of his business, I want to crush every single one of them”

“Yes sir!!!!!”

Kashe wayan yayi Yan fudda nunfashi mai zafi, 

“Calm down oga”

Mugun kallo ya zabgawa asad “how can I calm down Ana wannan ta addancin huh, yanxu dai tunda Mun gani link din kwayar da trafficking da akeyi, abu na

gaba inason kayi min bincike akan wannan mutumin,dagowa asad yayi ya kalli hoton da yake nuna mashi, Alhaji Mustapha, inason na tabbatar idan yana cikinsu, cos yaronshi na hannunmu yanxu kusan sati biyu kenan, he’s under investigation, yaso fita da kwayar daga Nigeria zuwaga Egypt saidai kasan saiyayi transit a dubai so anan aka kamashi, dalilin dayasa na gano Akwai hannun Nigeria a cikin case din.

“Okay ba damuwa ka turamin hotonshi gobe zakaji bayani,”

Runtse idanu Amar yayi kafin ya bude idanunshi yace “Akwai wani dan Iskan danshi wahab, ko me zakayi kayi inason na ganshi anan nigeria, I have to deal with him for trying to touch what doesn’t belong to him, I will make sure he never use what he tries to use to rap….”

Shuru ya danyi ganin yanda asad ya kura mashi idanu yanason Karin bayani, fuzgewa yayi yace “I will forward hoton wannan 17 year old yaron, check his profile a cikin data base dinshi gobe Sai muje wajen iyayen shi don muji when last suka ganshi”

Bai samu futowa daga wajen asad ba Sai wajen karfe goma na dare, gaba daya ya gama chanzawa rana daya ya dauko zafi sosai, don mutun ne shi mai kushin kasar sa da defending kasarsa akoda yaushe, yawanci akan ce masu zuwa suna serving wata kasar basa kishin tasu, shi dai yana cikin masu protecting kasarshi da kuma ganin ta samu cigaba.

Hammam….

Tun bayan wayanshi da Amar ya cigaba da harkokinshi kamar koda yaushe, don shima yasan aikinda zaiyi Akwai risk a ciki don yana tare da mugayen ne baki daya, kullum yakan zuwa wajen mahaifiyarshi wadda kw Kara karfafa mashi akan ya kasance me adalci da yin aikin daya dace, yawanci da safe yake zuwa ganinta kafin ya wuce aiki saidai ya sauya akalar zuwan nashi sbd Akwai ranar da alif ya zo don dubata ko tana cikin haukan don kwayar tana iya sakin mutane after few years,Allah ya taimaka yana fitowa daga cikin old age house din ya boye don Shiya fara ganin alif din yana shirin shugo wa saura kiris alif ya ganshi ya kubce mashi, tun daga wannan lokaci ya rage zuwa da safe, Sai idan dare yayi yake samun zuwa ganinta,magungunanta kuwa gudun Kar alif yayi bribing wasu daga cikin ma’aikata don a dunga bata kwayar ba tare da saninta ba yasa ya hanata shan ko wane irin magani tunda lafiyar garau.

Aiki ya soma yin underground yanda babu wanda zai ganoshi musamman mutanen alif dake tare dashi, bayan wannan Ma yana samun nasarar samun abunda yake bincike akai sbd idan ya nema dalilin saninshi da akayi a matsayin alif babu wanda ke kawo komai ko tunanin zai ci amanar alif, yasha wahala sosai wajen shawo kan daya daga cikin masu managing secret account din alif, wanda saida yayi abusing power dinshi ya samu gayen zai bashi duk

information da transaction dake gudana a cikin account din alif wanda babu wanda yasan da account din Sai top management na bank din, shima gayen yana daya daga cikin maaikata dake karka shin tops din, da farko ya buqaci maqudan kudade don yasan idan gaskia ta fito za a koreshi don haka Hammam yayi sorting dinshi don shima yana da kudade da yawa wanda yake kaso da yake samu daga babanshi dalilin ayyukan da yake mashi a cikin headquarters.

Yanxu hankali shi ya koma ga haifa wadda tayi moving on da rayuwarta gama manta dashi, lokacin daya mata message tayi mamaki sosai saidai bata jin zata iya dawowa gareshi don ya bata tabonda zaiyi wuya ya gogu nan kusa, yayi roko yayi magiya karshe Ma idan ya kira kashewa takeyi, daga baya ya bata tausayi sosai ta soma dan kula shi sama sama saidai tace babu soyayya tsakaninsu 

Yaji dadi sosai daya samu take kulashi don yayi alqawarin bazaiyi giving up ba, he will fight for her love,because Sai daga baya ya gane haifa itace rayuwarshi bayan mahaifiyarshi.

Bangaren hafiza tunda taji batun suspending din Amar gaba daya alif ya cireta daga mutanenshi don bayan ya gama amfani da ita ya sallameta, saidai ko kadan hakan maimakon ya sake mata abun farin ciki sai ya sake mata bakin ciki don tun bayan tafiyar Amar ta shiga tashin hankali sosai sitar sonshi ta Rufus zuciyarta wanda babu zaro babu tsammani ta shigeta tashin farko, ada chan baya sha’awarshi take yi Yanxu kuwa daga baya ta gane mahaukacin sonshi takeyi, gaba daya ta mutu akanshi ita dake cewa saita ga ya zama miserable,Sai gashi ba ayi nisa ba ita ta lalace, Akwai wata kawar ta wadda sukazo dubai tare daga eygypt itama yar asalin chan ce, saidai ita halayyansu ba daya yake dana hafiza ba, barta dai da shanye shaye, ganin halinda hafiza ta shiga yasa ta mata introducing abubuwan da take sha, hafiza kuwa dake neman sauki ta karba ta soma hawa network, kan kace ne Duk ta lalace, babu aiki babu komi, Har takaiga rent apartment dinsu kawar ta ke biya, ganin abubuwa sun fara mata yawa itama kawar, na sayan kayan shaye shayen Ma na neman gagara yasa ta Tilasta dole hafiza itama ta tunda kawo kudin rent inba haka ba ta koreta, hafiza kuwa da kudinta ya kare lag Har wanda ta samu wajen alif na aiki data masu na nemo masu evidence da aka kori general, ganin abubuwa sun sauya hatta kudinda zata saya abubuwan amfaninta sun yanke yasa kawarta bata gurguwar shawara, dayake idanunta a rufe suke nan take ya amince, daman ciki ne zata dauka na wasu Sai a biyata maqudan kudi, da farko komai ya tafi daidai don Har cikin ya shiga saidai ba a kaiga ko ina ba ta fara cuta sosai  har yayi affecting cikin mutanen wanda larabawa ne asalin Yan uae

8 / 94