mutsuke idanunta sosai kafin ta uwar kara nan take aka taho da sauri aka ririke ta, da sauri ya karasa gabanta yana “umiy hu hadha ant (ammi is that you)” cikin kuka ya cigaba “umiy , 'ant ealaa qayd alhaya (ummi you’re alive)” sosai ya rungumeta abun mamaki itama rungume shi tayi a jikin ta tace “dana,yarona kaine”
Ta fada cikin larabci
Saida suka gama kokekoken su kowa mamaki yake yanda ta shafe shekaru yana hauka lokaci guda memory dinta ya dawo,
Nan take ya soma mata bayani “bayan na dawo daga training abbu ya shaida min mutuwarki na shiga damuwa, amma maysa na ganki annan dama baki mutu ba”
“Ban mutu ba Hammam saidai zabin da aka bani yafi min na zauna a haka don bazan taba bari ka salwanta ba, Sai gashi allah ya kawo ranarda Zan hana ka shiga hadarin da tun farko aka yaudaremu batare da saninmu ba”
“Bayan tafiyarka na gano manufar alif shuraim aka ka na amfani dakai don biyan buqatunshi, babu tsoro na tunkareshi kuma ya tabbatar min da haka saidai na nuna mashi bama buqatar taimakon nashi zamu bar bashi gidanshi, nan take yayi threatening dina akan dole na nisanceka inba haka ba zai kasheni, nan ya bani zabi biyu ta hanyar bani kwaya ko kuma ya kasheni a wajen ganin banida Mafuta na karbi kwayar tundaga lokacin bansamu kaina ba Sai yanxu, I’m so sorry son na barka cikin wannan rayuwa Kara amfani”
Wani irin zafi da daci zuciyar Hammam keyi, Sai yanxu komai ya warware mashi idanunshi sun bude sosai, nan take yayi alqawarin saiya kawo karshen alif kuma zai taimaki amar, abokinshi na arzki saidai yana jin kunga da takaicin rufewar idanunshi wajen taimakon mugaye.
Nan ya barta bayan ya shaida mata komai akan abunda ke faruwa
“ ka tafi ka barni anan Allah yana tare daku hammam Addu’a ta Ma tana tare daku, idan Har ya gane cewa ka gani gaskia zai iya lahantaka, ya kamata mu boye komai”
Da wannan sukayi sallama kafin ya tabbatar da tana under care din nurses din wajen.
Amar kuwa Yana zuwa asibiti babu wani bata lokaci yanemi ganin likitanshi, nan take ya buqata likitansa da yayi unfreezing sperm dinshi, babu wani bata lokaci suka shiga operation room cikin Yan mintuna suka gama don ba wani dadewa akeyi ba wajen unfreezing din, magunguna doctor ya rubuta mashi kafin ya soma mashi bayani “thankfully kazo anyi unfreezing don daka Kara
wasu kwanaki I’m sorry to say za a samu matsala, anyway for now bazaka samu erection, don’t worry Duk cikin side effect din freezing dinne, but kana samun hutu da kulawa sosai komai zai dawo daidai, normally wasu in just 2days komai yake dawowa normal wasu kuma it takes a month ma,I’m sure you’re ready by now ko?”
Ya tambaya yana kallon amar
“Uhm” kawai ya iya ce mashi kafin doc din ya cigaba
“One of the side effects also is for waenda basu taba sex ba it will be a long journey, don zai saka feelings sosai and idan ka samu mace for the first time especially virgin zaka wahala sosai don zaka Kasa controlling kanka, but anyways waennan magungunan will help out sosai”
Tunda ya Lauda kanshi gege yana sauraron doc din bai kallo shi ba har saida ya gama mashi bayani sukayi sallama ya fito.
Direct apartment dinshi ya wuce don daukan laptop dinshi a hajiya yake sbd haka yana shiga bai tsaya komai ba ya dauka laptop dinshi juyawa yyi zai fita nan idanunshi suka sauka akan kayan data tube Harda bra dinga garin sauri gama manta dasu bata kwashe ba, tsungunnawa yayi ya kwashe mata su, gaban closet ya karasa zai saka a ciki, Chan kuma ya tsaya kallon bra don nata yayi yana ayyana girman albarkatun kirji da Allah ya bata, nan take yaji wani abu na taso mashi, da sauri ya aje bra don ya juya ya fuce zuwa sitting room, gaba daya sai apartment din ya mashi girma sbd rashin ta a ciki, tabe baki yayi kafin yace “ fitina girl”
Dan murmushi ne ya ku ce mashi kafin yasa kai ya fuce daga apartment.
Direct penthouse dinshi m5 ya sauke shi kafin ya wuce sama direct bayan Pablo ya gaishesa, wanka yayi kafin yayi sallah magrib da isha’I ya sauko Kasa sanya da Riga da gajeran wando bakake na under armor, sunyi matukar amsarsa sosai, dining ya wuce bai wani ci abunci sosai ba ya koma sama wajen gaming dinshi don ya kwana biyu baiyi ba, Sai wajen karfe goma ya fito daga gym ya wuce daki ya watsa hot shower
A jikinshi don yana buqata kafin yabi lafiyan gado.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 107
Update……
Washe gari ya kusa makara sallan asuba don Sai wajen karfe bakwai ya tashi, toilet ya wuce direct ya watsa hot bath da body wash dinshi masu shegen tsada da kyau, cikin natsuwa da kamewa ya futo, bai tsaya wani shafe shafe ba ya shingida sallaya ya fada kabbarar sallah yana idarwa ya fara shirin tafiya, normally yana aje travel box dinshi da Duk abubuwan buqatanshi daya Tashi tafiya kaya kawai zai deba wanda zasu ishesa tsawon kwanakin da zaiyi, wani lokacin kuma pablo ke hada mashi sanin yawanci kayan daga jallabiya sai kananun kaya karasa nauyi wanda yawanci yafi buqatansu musamman idan zaiyi tafiya Kasashen da ake yawan zafi sosai, yana gama hada box din nashi ya fidda kayanda zai saka, farrar Riga ya jawo ta brand din Ralph Lauren wanda ke cikin manyan collection din kayansa, sanin yanayi weather na nigeria a lokaci yasa ya dauko dogon wandon army ya saka, kafin ya feshe jikinshi da hadaddun turarukanshi masu da yin kamshi da tsada, laptop bag dinshi kawai ya jawo da wayoyinshi kafin ya sauka kasa, bai tsaya ko Ina ba Sai dining area, bai wani tsaya cin abunci da yawa ba, coffee kawai ya buqaci pablo yayi serving dinshi da english breakfast, cikin natsuwa ya gama cin breakfast daidai nan m5 ya shigo, saida ya gaishesa ya shaida mashi komai is ready kafin su fito tare m5 na gaba ya bude mashi bayan katuwar jeep dinshi da tasha zanen army a jiki kana ganin motar kasan ta manya ce, Pablo ne ya fito dauke da baggage dinshi, da mugun speed suka fuce daga penthouse dinshi, tafiyan 20 mins sukayi suka iso uae international airport, lokacin da suka iso kusan sauran 30mins suyi taking off, yana zaune hakimce kamar bazai fito daga motar ba idanunshi a lumshe yana tunanin abubuwa da dama wanda suke mashi yawo, saida ya dauka kusan minti goma kafin m5 ya bude mashi kofar ya sanyo kyakyawar fatar kafafunshi waje, wayanshi kawai ya rike a hannunshi yayi gaba m5 ya rufe kofan tare da janyi baggage dinshi ya bi sahunsa, bai tsaya ko Ina ba sai first class lounge, ya hakimce tareda daura kafanshi daya kan daya, turarenshi ne yayi ma mutanen dake zazzaune akan kujerun wajen sallama,nan kallo ya koma kanshi, wayanshi ya soma latsa wa ba tare da ya kalli kowa dake wajen ba don basuda wani yawa Ma a wajen don Sai yayan wane da wane ne a wajen.
M5 ne ya mashi Duk wani necessary arrangements, ya karba boarding pass dinshi, kafin ya wuce lounge din, cikin girmamawa ya aje mashi laptop bag dinshi gefen shi tare da su boarding pass dinshi da passport dinshi kafin ya mashi sallama ya fuce daga cikin airport din.
“Meeda kinga wani Hadadden guy kuwa, ya Allah ya hadu harta gaji da haduwa”
Wadda aka kira da meeda ce ta dago ta kalli inda ta gefenta ke nuna mata, wani irin maybe kallo ta Bishi dashi kamar zata hadu ya shi, nan take taji wata Kibiyar sonshi ta daki zuciyarta, da sauri ta hadiye wani irin Miyau ta juya tareda kallon kawar Tata tace “kam bala’i, zabgi wallahil azeem gayen nan ya hadu, kura bata ganin nama ta kauce”
Dariya wadda aka kira da baby akay kafin ta juya ganin inda kawar Tata take tunkarowa, gaban shi ta isa lokacin ya mike don lokacin tashin jirgi yayi, kamar an wullota ya hanya gabanshi, dago idanunshi yayi da suka kusan saka ta suman tsaye dukda babu alamun dariya ko annuri a fuskanshi hakan bai hanata hango
Sirrin kyau da yake dashi ba, gaba daya saida ta karaso gabanshi ya tafi da imanin ta, cikin yanga da iyayi irin na Yan mata da sukaji duniya, ta soma magana “assalam handsome”
Tsayuwanta a gabanshiya bashi daman yi mata kallo daya don ya fita tsayi sosai, kananun kaya ne a jikinta wanda ya fidda surar ta sosai, batada wani kyawun jiki don komai ya gama yin lanqwasa nan take ya soma jin kyankyamin ta, kauda sexy eyes dinshi yayi gefe ba tareda ya sake mata kallo daya ba ta sake magana “sunana hameeda idan babu damuwa inason na san sunanka harma dakai din gaba daya” ta karashe tare da juya idanuwanta wanda shi baida lura da hakan ba, wani irin disgusting kallo ya mata tare da giftawa gefenta ya wuce, kamshinsa ne ya daki hancinta nan take ta lumshe idanu ba tare da ta damu da dizgata da kallon da yayi mata ba, kawar ya kuwa dake zaune ne zatayi Banda dariya harta juyo ta dawo inda suke zaune, “ke meeda daman wannan Ay yafi karfinki nesa ba kusa ba, kidai lallaba da sugar daddies dinki dake baki kudi suna biya maki jirgi kina zuwa hutawa”
“ hmm baby bazaki gane ba, wallahil azeem ban taba ganin hadadden gaye wanda kina ganin shi kinsan ya juqu da kudi ba kamar wannan,”
Kallonta baby tayi yanda ta lumshe idanu tana smiling hakan ya tabbatar mata da abunda ta hango a idanunwan kawar tata
“ Toh mayya, kedai ako Ina Sai kin nuna zalama, irin wannan Mazan dai kinsan basa daukan raini,don mugun wulaqanci ne dasu,”
Ganin kamar bata sauraronta yasa tace “malama saiki Tashi kamu tafi ay tunda kinaji an kira flight din namu”
Kallonta meeda tayi tareda daukan wayanta tace “Toh tsaya muyi hotunan posting mana”
Karban Wayar baby tayi tace “ aikin banza, dama dai rayuwar karyarki da kika saba kika bawa himma da zalama ba irin wadannan Samarin ba”
Hotuna zafafa suka dauka, kafin su wuce cikin jirgi, suna shiga kuwa direct first class area suka wuce, tattara idanuwa meeda ta soma yi ko zata ganshi saidai bata samu damar hakan ba akayi announcing take off, daman seat dinsu ba roll daya bane da baby don haka bata damu da wanda ke gefenta ba da yake a rufe ba, baka ganin wanda ke ciki ta zauna, wayanta ta fidda ta soma zafafan hotuna Harda tsaida wata crew ta sakata yi mata hotuna, cikin qanqanin lokaci jirginsu ya daga.
Saida tafiyan tayi nisa har aka fara zuwa rabon wine da juice harda starter ga masu buqatan Ana zuwa wajensu kuwa matar ta tambayeta abunda yake buqata, ba tare da bata lokaci ba tace red wine, nan take matar ta zuba mata, kallon gefenshi matar tayi tare da zagayowa gefenshi tace “sir would you like to have anything, juice,water,wine”
Cikin dakakkiyar muryarshi kamar na zaiyi magana ba yace “no thanks”
Jin daddadar muryarshi yasa hameeda sako kanta don ganin mai maganar, nan take idanunta suka sauka akanshi, cikin sauri ta koma ta zauna tana wani murmushi mai ma’anoni daban daban, kallon matar tayi tace “can I get something else please”
Sauya wine din tayi zuwa juice, tunda ta tabbatar shine ta Kasa sukuni, fatan ganinshi kawai takeyi don gaba daya bangarenshi a rufe yake, goga kuwa bai Ma san tanayi ba don tunda tazo gabanshi dazu kallo daya ya mata yaji kyankyamin ta a gabanshi yasa manta da ita nan take, don bashi da time din irin wannan matan.
Saidai yayi mamakin jin bahaushiya dake kusa dashi wanda ta buqaci a bata giya saidai shiga hurumin da ba nashi ba baya cikin tsarinsa don bai fiye bama mutane attention ba.
Tana nan zaune aka soma kawo abunci nan take ya bada order abunda take so still tana fatan ya zuge nash bangarenshi saidai bata samu daman hakan ba, kofa suka tambayi abunda yake buqata, juice kawai yake su kawo mashi nan take kuwa aka kawo mashi hadadden juice tare da glass cup, matar na kokarin zuba mashi takalmin kafar ta yayi slippering ta zuba mashi juice din akan jacket din daya daura kan farar rigarshi, Allah ya taimaka bai zuba a jikin white Riganshi ba, hankalin matar ne ya Tashi ta soma bashi hakuri, kai kawai ya girgiza mata ya miqe zuwa toilet ba tare da kallon gefenshi ba, gyaran wajen data bata mashi crew din tayi karfin ta koma don kawo mashi sabon juice din,yana shiga toilet din ya Gyara jikinshi kafin ya futo, meeda kuwa da taga wucewanshi toilet cikin sauri ta bi bayanshi, yana bude kofar kuwa zai fito ta kame hanyar ta zuba mashi idanu kamar mayya tace “do you need any help?”
This time around tsayawa yayi ya mata kallo tsab take ya gano itace ta buqaci wine, mamakin yanda yayan musulmai suka lalace yakeyi qira qira yasan tayin wani abun yake mashi daban saidai bata san cewa shi ba irin mazan nan bane ba, Karon farko ya bude bakinshi dake kamshin mint yace “you’re so disgusting,get the hell out my way”
Ya fada idanunshi sun nuna babu wasa a cikin zancen nasa, a burkice ta matsa mashi baya dinta tsorata da yanayinshi tana nan tsaye wata crew tazo wucewa yace “get me head of Crew staffs now!!!!”
Wucewa yayi nan kuwa meeda ta tsaya kyam don Duk ihun nan dayayi akan idanun mutanen dake zaune kusa da toilet dinne, kunya yasa ta komawa cikin toilet din ta rufe kanta a ciki.
Goga kuwa ya shaka sosai, don haka head of staff na zuwa babu bata lokaci ya buqaci roll guda ba tare da kowa ba, Allah yaso kuwa Akwai roll din da babu
passengers nan take ya sauya zuwa chan don baya buqatan hayaniya dukda Sai ya biya kudin roll din gaba daya wannan ba damuwa shi bane don kudi kam Akwai su.
Ganin zaman cikin toilet bazai amfane ta da komai ba sum sum ta fitowa wuce wajen mazauninta, baby kuwa da take Yan gaba gaba me zatayi Banda dariya don akan idanunta akayi drama din. Kwafa tayi tace “shegiya kai taurin kai da zalama, maganinki kenan, nan gaba bakya kara tunkarar irin wadannan yan girman kan ba”
Meeda kuwa tana komawa seat dinta ta kame, ganin baya wajen yasa ta jin wani iri, saidai tayi alkawarin koma waye shi saita nemo shi kuma ta nema abunda take buqata.
Karfe takwas daidai jirgi su na emirate ya sauka ah Nnamdi azikiwe international airport abuja, saida kowa ya tsaya akayi clearing ko ina kafin ya sauko cikin isa da kasaita, nan fa kowa ya soma kallon isa da harkar manya cikin Yan kallo kuwa Harda meeda wadda yanxu kam ta cire rai don taga fin karfi nesa ba kusa ba, gaban jirgin motoci manya manya kusan guda biyar a jere hade da sojoji suka zo tarbanshi, dan wannan official zuwa ne ba normal zuwa da yake yi ba na visiting Ammahn shi,Sara mashi aka soma hi kafin a bude mashi katuwar lexus baqa tinted, sauko wa yayi hannunshi rike da jacket dinshi Dayan kuma ya zuba cikin aljihun wandonshi, direct gaban Lexus din mai plate number hade da sunan TAURA a kasan da manyan harufa ya tsaya sojojin suka soma Sara mashi irin gaisuwar su ta sojoji, kamewa yayi bayan motar kafin a rufe mashi suka juya harsuka fuce gaba daya da tawagar datazo tarbanshi.
Ranar kuwa abuja ta shaida babban sojan uae ya iso nigeria, wanda basu san da zaman shi bama su san da zamanshi ba sun sani saidai kuma babu wanda yasan fuskanshi.
Bude laptop bag dinshi yayi ya fidda da wallet dinshi da yake zuba Duk wasu sims dinshi na kasashe daban daban, Ciro din din Nigeria yayi na mtn ya bude wayanshi ya musansa ya aje na uae, yana kunna wayan ya soma dialing wata number ya kara kunanshi Ana dagawa daga chan akace “oga harka iso kenan”
“Wannan mutanen fa daka hadoni dasu, kasan fa bana son hayaniya, infact bana son Adam na shigo kasar nan Ma sbd aiki ne zamuyi cikin sirri”
“Toh ka fa dawo kenan, anyway na turo su ne sbd bazan samu zuwa tarbanka ba”
“ please call them, bana buqata su”
“Okay, anyway gida zaka wuce yanxu? Zan shigo anjima daman nasan ni mai laifi rabona da Ammah tun bayan rasuwar dada,”
“No karka damu ba gida Zan wuce ba, heading somewhere else, zamu hadu gobe kawai”
“Yes ranka ya dade sir”
Ya fada yana dariya kafin ya aje wayan.
General asad Abdullah kenan da ga abokin Alhaji taura kuma babban aminin sa tun tasowarsu, shima mahaifin sa ya rasu saidai zumuncinsu bai dauke ba tsakanin yayansu dukda ba wani kusanci suke dashi sosai ba, asad shima soja ne mai rike da babban mukami na chief of army staff anan Nigeria(lieutenant asad Abdullah) ya girmi Amar sosai saidai yanda Amar keda kwarjini zaka dauka zai fishi ma.
Kallon sojan driver yayi bayan ya gama wayan yace “to larrics estate”
“Yea sir” yayi saurin amsawa
Maida kanshi yyi bayan kujeran ya lumshe idanunshi Har wani bacci baccin gajiya ne ke neman fuzganshi.
Horn din da driver yayi ne ya tabbatar mashi da sun iso, drivern yana parking yayi saurin bude mashi bayan motar futo cikin kamewar shi, tunda ya sanya kafafunshi kasa yake jin wani irin niima na saukar mashi, kamshin kasa da bushiyoyi tare da sanyin dake kadawa ne ya bade ko’ina, lumshe idanunshi yayi kafin ya soma takawa gaban entrance din, cikin sauri driver ya karaso gabanshi ya Danna door bell din tare da janyi baggage dinshi, bude kofar da akayi ne ya sashi dago kanshi, Nadine data bude kofar saida tadanyi baya, sauke kanta Kasa tayi kafin tace “welcome sir”
Don Duk kwarjininshiya cika