masjid, a zaune ya tadda amra tana bama little madara feeder, da sallama ya shigo, tana mashi kallo daya ta dauka idanunta, karasowa yayi har bakin gado ya kalleta ita da little yace “morning our mommy, and good morning to my little princess” ya fada yana kaima little peck, yana gamawa ya daga yayi pecking go shin amra, da mamaki amra ta dago ta kalleshi “mey hakan kuma”
Sauke muryarshi yayi kasa Ganin ammah na shirin fitowa daga bathroom “it’s a morning kiss for my little and my wifey”
Tabe baki amra tayi ta mashi wani irin mugun kallo tace “sabon salo, that’s not going to work on me”
Murmusawa ya danyi ya shafa fuskanta anan tsaye da yake “we shall see mummny triplet”
Wani irin mugun kallo ta mashi tana jin haushinsa da takaicinsa tana son ture hannunshi babu damar hakan saboda duka hannayenta tana amfani dasu wajen bama little kulawa.
Saida ammah ta futo ya gaisheta ya fuce daga dakin.
Girgiza kai kawai ammah tayi ta hau kan sallaya saidai deep down tana jin wani irin dadi sosai.
Bayan ya dawo daga masjid ma saida ya shiga dakin lokacin sun shiga wankan safe don haka ya tsaya yayi kissing babies dinsa ya dunga masu magana shi kadai kafin su ammah su futo daga bathroom, ammah ce ta fara futowa don ta barta tayi wankan sabulu, ammah na futowa kuwa ya fara mita “ammah adaina barinsu su kadai please, Zan turo salima ta zauna dasu kafin ku gama”
Tana kaiwa nan ya fuce zuwa dakin salima, haka ya taso ta ya tura dakin bayan yayi mata kashaidin kula mashi da triplets dinshi kafin ya wuce dakinshi.
A cikin kwana abubuwa da dama sun faru, inda ta bangaren daddy triplet da mummy triplet sai babu sauyi don gasa mashi aya take a hannu, kwata kwata
taqi sake mashi shikuwa babu abunda yake sai chusa akanshi don idan har taci galaba akanshi to tabbas yasan za a samu matsala don ammah zatabi bayanta ne, ayanxu in kukaga general kamar bashi ba, ya sauke wannan ego din yayi laushi, yanda yake nan nan da amra kuwa abun Har mamaki yake bata kuma yayi mata wani banbarakwai cos ba haka ta sanshi ba a sanin da tayi mashi he’s so tough., donko dariyanshi wahalar gani take mata achan baya saidai yanxu yanda ya suke kanshi abun Har daure mata kai yakeyi sosai.
Gata kuwa babu irin wanda triplet basa sha a wajen mahaifinsu da ammmah, kullum cikin order kayan wasa kayan jarirai da abubuwan amfaninsu dana mahaifiyarsu suke kamar basa jin zafin kudi.
After 6days…..
Gobe suna don haka yayi kokarin bin yanda sunna ta gindaya, da kanshi yake ya sayo shanaye guda uku da raguna uku da kayan abuncin da za ayi sadaka a raba saboda babu wani shagali da zasuyi don yace bayason wani taro, dukda ammah taso ayi saboda saidai yaqi yarda da hakan , tunda ya fita sai dare ya dawo agajiye, yana shugowa sitting room ya tadda ammah a zaune da Salim a gefenta yana kallon little princess dake kuka, da sallama ya shigo ya zauna kusa da ammah, yana gaisheta ya amshi diyarshi, ammah dai babu abunda yake sai murmushi saida ya gana yi mata kisses din daya saba kafin ya mika ma ammah ita ya wuce part dinshi.
Yana shiga ya wuce bathroom yayi wanka ya futo ya sauya kaya, yana gama shiri ya futo sitting room, kusan karfe Tara Ganin basa nan yasa ya wuce sama direct don yanzu hawa chan baya mashi wahala.
Da sallama ya shige bedroom din, amra ne zaune sai ammah a gefenta tana mika mata wani hadin kunu na musamman don har yanxu ruwan Nono bai zoba.
Da idanu yabi amra da kallo, kanta babu dankwali gashinta ya sauko Har kasa saboda a jike yake sai sheki takeyi abunta.
Sanye take da wata Riga mai sirin hannu, tunda ta mashi kallo daya ta duake kanta Har yazo ya zauna, yana zama ammah ta mike ta fuce don ta basu waje.
Ammah na fita ya hade rai ya daura kafa daya kan daya, ya soma magana cikin kame wa, “ajiye wannan abun”
yanda yayi mata magana sounding very serious yasa ta ajiye ta hade rai, nuni yayi mata da baby number one yace “kawo shi nan”
Mikewa amra tayi ta duaka babyn ta tako Har Inda yake nan ya dunga binta da idanu harta karaso kafin ta ajiye amshi babyn a hannunshi.
Tana ajiye babyn ya gyara zamanshi ya dago babyn ya daidiaci kunenshi yayi mashi addua kafin yayi mahai huduba yana gamawa ya mika mata shi, nan taje ta ajiye shi ta dauko babyn number two nan ma hudubar yayi mashi kafin ya mika mata, yana Mika mata ta dauko amshi little, karban ta itama yayi ya mata huduba yana gamawa ya sumbaceta ya mika mata ita, tana karban ta ta wuce kan gadon ta ajiyeta, tana dagowa taji ya rungumeta ta baya yayi kissing
bayanta, “Masha Allah wifey, mun samu Yunus(hamad) badaru (hamid)and maryama, bar maki saiki zama mata nickname daya dace da ita”
Dan juyo da ita yayi ya daga hannunta daya tare da nashi yayi nuni da baby number one yace “wannan shine yunus takwaran dada kenan Allah yayi mahai rahama, wannan kuma mahaifinki ne shima Allah yayi mashi rahama, sannan ga little princess dina nan ammi na, Allah ya Raya mana su”
Saurin runtse idanu amra tayi hawaye na saukowa akan fuskanta intace bataji zuciya ta yayi sanyi ba tayi karya, hawaye takeyi sosai Har yana diga akan hannunshi, yana jin haka ya juyo da ita ya share mata hawayen “Allah ya masu rahama, stop crying wifey”
Idanunta a rufe tana jinshi yana ta maganganunshi, babu zato taji lipa dinshi akan Bakinta, wani irin passionate kiss yake mata wanda bai taba yi mata shi ba, idan tace bataji saqin da yake aika mata ba tayi karya, kukan Hamad ne ya dawo dasu daga yanayin da suka shiga don haka Tayi sauri kwace jikinta ya wuce bathroom tana hawaye.
Ammah ne ta shugo dakin jin kukan yayi yawa tana zuwa yayi kata albishir da sunan daya sanya ma yaran, guda sosai ammah tayi tana murna tare da masu addua.
Bai wani dade ba yayi mata sallama ya fuce don Har lokacin amra bata futo ba.
Washe gari yara sukaci sunayensu bayan anyi masu yanka, tunda safe babu wanda ya runtsa a gidan, ammah na tsaye akan abuncin sadaka da akayi na kusan mutane Dari Harda kudi aka dunga rabawa mutane, lowkey suna sukayi anan cikin gida inda ammah ta dage kan dole sai sunyi hotuna, at that minute Aman yayi booking wani mai hoto abunka da harkar kudi nan take sukazo babban company ne inda suke service na komai daga kan makeup zuwa photoshoot, suna zuwa aka zarara ma mai jego kwalliya sosai, hannunta tasha red henna wanda salima ta goga mata asuba a yatsunta sai yayi jaa sosai yayi ma cute fingers dinta kyau aranar kuwa Madina ta dura a nigeria ko zama batayi ba ta taho nan gidan aka fara shagali da ita.
Sunsha hotuna sosai inda baban twins bai shugo bama ya fuce daga gidan tun safe.
Sai wajen yamma ya dawo gidan, yana dawowa kuwa ammah ta jawo shi akayi hotunan dashi inda akayi mashi shida yaranshi, amra dai qin yarda tayi a daukada ita don yana zuwa wajen ta wuce sama abunta.
Agajiya kowa ya kwanta aranar inda amra kuwa ta kwana a zaune don aranar tasan motherhood is not an easy job donma ammah na gefenta tana taimaka mata.
Washe gari sai wajen karfe sha daya kowa ya Tashi a gidan, amra dai na zaune a daki tayi wanka ta shirya zasuje first week immunization na triplets, tana nan zaune salima ta shigo itama a shirye take don tare zasuje saboda ammah zata zauna ta huta saboda bp dinta, tana shugowa ta dauki princess a hannunta “adda ya Muhammad yace ki sauko”
“Gani nan dan Allah” amra ta amsa ta
Fucewa salima tayi tana rike da baby hamra.
Ammah ne ta fara saukowa daga stairs fuskanta dauke da murmushi, harta karaso parlor, malam labaran dake zaune akan kujera Amar na gefe shima a zaune bayan sun gaisa yayi mashi barka.
Karasowa ammah tayi “ah ah malam labaran kaine da Safiya haka”
Har kasa ya duka “hajiya ina kwana ashe an samu karuwa Allah ya Raya”
Zama ammah tayi “lpy Lau malam labaran mun samu Yan uku”
Dariya labaran yayi yace “Masha Allah Allah ubangiji ya Raya su yasa su zama mahaddatan alqur ani”
“Ameen ya Allah” ammah ta amsa
“Basu sauko bane son?” Ammah ta tambayi amar
“Uhm “ kawai yace mata ya cigaba da latsa waya Yana kokarin Kiran bata daukan wayan, ranshi yadan sosu
Kamshin turare ta ne ya fara kawo masu ziyara parlor inda ammah ta dago ta hangosu yana saukowa ita da salima, tana gaba ta rike su Hamad da hamid a hannun ta while salima ta rike hamra a hannunta, karasowa suka farayi inda ammah tace “Masha Allah malam labaran ga mai jegon nan ma saiku gaisa”
Dagawa malam labaran yayi a daidai nan salim dake shugowa cikin gidan don tare suka futa da aman zuwa gyaran handle din game dinshi , yana sauke shi ya wuce office shi kuma ya shugo gidan har ya karaso sitting room din babu wanda ya kura dashi kwata kwata, idanunshi babu inda suka sauka sai akan labaran take ya kwalla kara wanda yasa gaba daya suka dago suka kalli inda yake tsaye, amra ce kadai bata kalli inda yake tsaye ba idanu ta ya sauka akan labaran, wani irin jiri jiri ne ya soma dibanta tayi baya cikin sauri Amar ya mike ya taro ta saboda kiris ya rage ta fadi ga yara a hannunta, Salim dai tunda ya kwala karar nan ya sume a kasa…..
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 149
Update
Unedited page
Cikin sauri ammah ta miqe tsaye tana tunkarar inda Salim ke kwance a sume tana fadin “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”
Dagawa salima tayi don Ganin abunda ke faruwa, kwata kwata batama Lura da labaran dake zaune ba shima hankali a tashe ya miqe, arazane tayi baya kiris ya rage bata fadi ba ta dafe gefen kujera, nunfashinta ne ya soma yin sama sama ta qame kamar gunki, she can’t believe abunda yake gani agabanta, amra dai kamar kurma haka ta dawo jikinta na bari kamar mazari, hannunta ma dake rike da Hamad da Hamid ma karkarwa yake, cikin sauri Amar ya karbe yaranshi don kwata kwata bai ganema abunda take ma rawar jiki ba.
Malam labaran shima daya kafesu da idanu ya kasa cewa komai, yanda suke Binshi da ido haka shima yake binsu da idanu gabanshi na faduwa kamar zuciyar shi zata buga, at the same time kanshi yana sarawa kamar an buga mashi guduma.
Waigowa ammah tayi bayan ta tsugunna inda Salim ke kwance a sume ta tallaboshi zuwa jikinta tace “ku bani ruwa”
Kyam ko wannen su ya tsaya babu wanda ya motsa, Amar dai kasa daina kallon amra yake Ganin tana kuka, sheshekar kukan salima ne yasa ya maida kallonshi gareta itama, gaba Dayan su waje daya suka kurama ma idanu jikinsu na bari kamar sunga dodo “babu wanda zai iya bani ruwa ne?” ammah ta daka masu tsawa hankalinta a tashe, jiki na bari salima ta miqe ta miqa ma amra angel har lokacin idanunta na kan labaran kwakwalwarta ta kasa aiki kwata kwata, wucewa kitchen din tayi ta dauka ruwan bottle ta dawo kitchen din, Har lokacin jikinta na Rawa tana kallon inda labaran yake tsaye kikam ya kasa motsawa shima, yana jin kamar ya sansu a wani wajen ko kuma suna da alaqa da past rayuwanshi, don yanda kirjinshi ke bugu ya gane tabbas yana da wani babban attachment’ da yaran, saidai abu daga ne bai gane ba, kwata kwata babu wani memory dunsu akanshi.
Salima na miqa ma ammah ruwa ta tsaya daga gefe, ruwan ammah ta yayyafa ma Salim Har sau biyu kafun ya ja nunfashi, yana Jan nunfashi ya kankameta sosai jikinshi na bari sosai.
Abunda ya razanar dasu su duka Har hankalinsu ya dawo garesu shine first furucin da Salim yayi tsawon shekarun nan, “un…cle ne Wallahi un..cle ne ya kashesu, ammah kice ma ghost din abba ya tafi Wallahi uncle ne”
Rike shi sosai ammah tayi Ganin kamar yana neman zaucewa kafin ta fara karanto mashi addua, malam labaran ne ya mike tsaye yana kokarin takowa inda suke salima ma tayi baya Har tana neman faduwa kansu ammah jikinta na bari tace “innalillahi,Wallahi fatalwan abba ne”
Kallon ta ammah tayi Ganin tana nuni da labaran gashi itama tana shirin neman zaucewa yasa ammah cewa “Ina fatalwan yake?”
Nuni tayi mata da labaran tace “Wallahi fatalwan Abban mu ne,“
Chak labaran ya tsaya yana mamaki, saida ya zo dan dasu ne yaji wata hajijiya akanshi, nan take ya runtse idanunshi yana dafe kanshi yayi baya zai fadi shima,
cikin sauri amra ta miqe tsaye ta nufeshi, tana karasowa gabanshi ta tsugunna kasa sai hawaye, “abba kaine? Daman kana raye baka mutu ba? Kodai idanuna ne ke min gizau, yaya dan Allah duba min kina Ganin mutun a wajen nan ko fatalwar ne nima nake gani”
Hannunta ta sanya ta rike na labaran nan take ta razana tayi baya,sai hawaye, Amar dai kasa motsawa yayi yana kallon ikon Allah sai a yanxu komai ke dawo mashi, bazai manta ba ranar da yasa akayi mashi investigation akan amra da iyayenta tabbas ba ayi declaring mutuwar baban su ba saboda gawa daya ce ta kone a cikin motar, da farko yaso yayi buncike akan haka saidai kuma daga baya ya bar binciken saboda da Bakinta tace baban su ya rasu, bayan wannan he can recal first time daya ga labaran, tabbas yaga kamannin shi da yaran gaba dayansu, don turawa na cewa blood is thicker than water, tabbas jini baya karya ko a Ina ne, bayan wannan ma yasan ta yanda ammah ta kawo labaran gidan don ta kanta ta bashi labarin yanda suka tsinceshi akan hanya,harta taimakeshi da memory dinshi dayayi loosing, nan take ya gama harharda puzzle din gaba daya, shi kadai ne ya samu courage din daga kafafunshi ya karaso sitting room din ya kwantar da baby Hamad da baby Hamid akan kujera kafun ya karaso inda malam labaran ke zaune, anatse ya maatso ya taimaka mashi ya mike tsaye suka wuce wajen kujrar ya zauna, kallon inda ammah take Amar yayi yace “ammah ku dawo nan sitting room”
Mikewa ammah tayi Salim na maqale da ita kamar za a kwaceshi daga wajen ta kafin su karaso cikin sitting room din suka zauna nan ma saida ya kankameta, suna zama Amar ya kalli inda amra ke zaune tayi zaman dirshen ta hade jikin ta waje daya sai salima dake gefe itama tayi Tsuru tana hawaye “ku taso kuzo nan”
Dan dagoda jajayen idanunta tayi ta dawo ta mike tsaye a hankali Har lokacin jikinta na mazari salima na biye da ita kamar munafukai suka zaunaa kasa kowannen su kana ganinsu kasa a furgice suke.
Suna zama shima Amar ya samu waje ya zauna kafin ya soma magana, kallon inda malam labaran yake zaune yayi, cikin kamewa yace “malam labaran kasan su ne?” Ya tambayeshi don son jin daga gareshi
Dan dagowa labaran yayi ya kalli inda amra take, yana yi mata kallo daya ya runtse idanunshi kanshi na Sara mashi kafin ya maida kallonshi ga Amar bayan ya dafe kanshi yace “yallabai ban sansu ba saidai….”
Kasa karasawa yayi saboda wani moment da yayi mashi flashing akanshi , gashi ga amra a a zaune a wani garden tana nuna mashi assignment dinta na school suna dariya.
Saida memory din ya bace mashi yayi saurin dagowa ya kalleta, ga kamannin nan sosai da yarinyar da memory dinta yayi mashi flashing saidai ita waccar bata kai haka girma ba, kura mata idanu ya dungayi har saida Amar ya sake mashi tambaya, nan ma shuru yayi ya kasa cewa komai, “ya Muhammad don Allah waye wannan mai kama da baban mu?” Salima ta fada tana karkarwa, kallon inda take labaran yayi nan take wani memory din ya sake mahai flashing,
gaba daya ya zama so confused, kamar daga sama sukaji yace “sunanki aisha? “ ya fada yana kallon amra, cikin sauri ta girgiza mashi kai tana hawaye, maida kallonshi yayi ga salima bakinshi na karkarwa yana son yin hawaye ammah ya danne yace “sunanki salima?,”
Itama girgiza mashi kai tayi tana hawaye, “kuna da qani Salim ?”
Atare suka girgiza mashi kai nan take salima ta miqe tayi kanshi ta rungumeshi a jikinta , “Wallahi abba ne wannan Abban mu ne wannan”
Gaba daya baki suka bude galala musamman ammah daga zama speechless, ya za ayi ace labaran ne babansu? How ya tambayi kanta, tana nazari, Amar ne yayi saurin breaking silence din yace “yes I think mahaifinku ne wannan, kuma bai mutu ba”
Ammah ce Tayi saurin katsesu tace “ku min bayani dalla dalla karku barni a duhu mana”
Shuru gaba daya sukayi kafin amra ta tattaro courage dinta ta soma bayani.
Yau shekara takwas kenan da rasuwar iyayenmu inda sukayi accident alokacin da suka dawo daga umra, Abban mu da mami, a ranar ne uncle ya shaida mana sun mutu kuma sun kone don ko gawarsu bamu gani ba, Salim ne kawai ya gani saboda tare sukace da daddy inda abun ya faru.
Fashe wa Salim ya farayi da kuka kamar ranshi zai fita yana shesheka, hankalin ammah ya gama Tashi gaba daya ganin Duk sun burkice.
“A kwai lokacin dana saka ayi min investigation akan aisha, a buncikenn danayi na gani cewa ba ayi declaring mutuwar iyayensu ba, saidai an rubuta sun kone saboda accident da sukayi shekaru takwas da suka wuce kenan”Amar ya fada yana kallon inda ammah ke zaune
Kallon shi ammah tayi tana son Karin bayani kafin ta maida duban ta ga