Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   61 / 94

180K to 183K   out of 279.4K words

sameta don shes his everything, itace rayuwar shi gaba daya.

Jikinshi na kyarma ya tallabo kanta, bakinsa na karkarwa ya kasa motsawa gaba daya, hannunshi na karkarwa ya soma jijjiga ta, ‘’am..mah..ammahh…innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ammah please wake up, ammah karki tafi ki barni yanda dada ya tafiya, ammah plaes’’ gaba daya y agama rikidewa ya chanza kamar ba general ba, amra dake gefenshi dasu salima babu abunda sukeyi sai kuka, tun yana Magana ahankali harya soma ihu idanunshi yayi jaaa, kana ganinshi kasan an tabo weak point dinshi‘’somebody should fucking call the ambulance’’

Cikin sauri aman ya miqe tsaye ya wuce cikin gida ya domin ya dauko car keys dinshi, yana gudu yana tuntube harya shige dakinsa agigice ya dauko car keys.

Yana futowa motar karar motar ambulance ta karade anguwar hade da motocin su asad, cikin sauri securities suka bude gate, nan take suka fara shigowa aguje, motar ambulance din na parking emergency health team suka fito da gadon marasa lafiya daga motar, shima asad sunayin parking suka sauko shida yaransa kowannen su hannunshi dauke da bindigu,

Aguje suka firfitowa gaba dayan su sukayo kan lantana dake ayashe kamar babu rai, haka suka dibeta kamar wulaqantattun kayan wanki suka watsa a cikin

mota, ammah ma dakyar aka banbareta daga hannun amar don gaba daya ya susuce don gani yake kamar ana rabata da jikinshi mutuwa zatayi,dakyar aka samu asad ya dagashi suka samu akasa ammah a cikin mota.

Aman na ganin haka ya fiddo da tashi motar shima, janyo amar asad yayi ya turashi cikin motar aman din, baima lura dasu salima da amra ba da suke tsaye, saida suka shige motar amra tace ‘’dan allah ku tafi damu ya aman’’

Wata uwar kara amar ya yi ya kalli aman yace ‘’give me the car keys’’ da kyar asad ya karaso inda yake yace ‘’oga bazaka iya tuki a wannan condition dinba ka bari shi tuka.

Kallonsu amra asad yayi yace ‘’ku shiga’’

Shigewa sukayi gaba dayansu bayan motar cikin gaggawa kafin aman yabi bayan motar ambulance din da matsiyacin gudu har saida suka kamo motar ambulance din, har suka karaso cikin asibitin amar dai tunda ya zauna cikin motar ya dafe kanshi hankali atashe, suna isowa ko parking aman bai gama yiba amar ya futo daga motar acikin hanzari ya shige cikin asibitin don already an shiga da ammah, hankali atashe aman yayi parking ya bude motar duk suka fito duk hankalinsu atashe, bin bayanshi duk sukayi kowannen su hankali atashe.

Yana shiga cikin emergency ward din ya wuce wajen emergency room da gudu, yana zuwa daidai kofar ya tsaya saboda family doctor su daya fito daga cikin ward din a hargitse, amar na ganinshi yayi saurin karasowa gabanshi cikin fada yace ‘’whats going on aciki? Hows ammah?’’

Yanda ya zubama doctor idanu haka shima ya zuba mashi jiki na bari ya kasa cewa komai, kana ganinshi kaga mara gaskia, amar na ganin haka ya daka mashi tsawa ‘’don’t just fucking shut your mouth,Talk to me whats going on there meyya samu mahaifita’’

Saurin tattara natsuwa doctor yayi ya kalleshi yace ‘’we are trying our best don mu gano meke damunta, excuse me’’

Yana fadin haka ya bi wata hanya kamar wani ward din ya fuce, amar dai wani irin tangadi ya soma yi, da sauri aman ya taro shi ya jashi wajen waiting chairs ya zaunar dashi don gaba daya y agama chanza kamar bashi ba, abunda yake tsoro yana neman faruwa,

Amra dai tunda taga yanda ya lokaci guda ya chanza kamar baa mar din data sani ba, wani irin tausayinsa na yawo a jininta, tsakanin daaa da uwa sai allah, tabbas su zasu shiada kaunar dake tsakaninshi da ammah, bama shi kadai ba, har suma don babu wanda zai kallesu bazai hango tsantsan tashin hankali atare dasu ba, sai hawaye sukeyi, sun dauka kusan minti biyu saiga wata nurse ta fito daga emergency din hankali atashe ta, bata dade ba ta dawo tare da doctors biyu suka shige cikin emergency room din, amar dai tunda yaga suna shige da fuce gaba daya jikinsa yam utu, babu abunda yake furtawa sai innalillahi wa inna ialihi rajiun, don idanda za a gwada jinin a wannan lokacin toh tabbas ya je high sosai, tunda ya dafe kirjinshi ya kasa motsawa, bakinsa ne kawai ke motsawa, adduar ma da yakeyi baya futa kwata kwata daga bakinshi, su amra da salima da salim dai suna tsaye sun kasa zama kowannanesu babu abunda yake sai hawaye,

aman ma yana tsaye yana sassarfa tsakanin walk way din, kowannen su yayi jigum hankali atashe, cikin mintuna talatin saiga daya daga cikin doctors din ya fito, amar na ganin futowarshi yayi saurin mikewa ya karaso inda yake tsaye aman na biye dashi suka zagaye doctor, kowannensu idanun shi yayi jaa sosai jijiyoyin wuyansu ya fito sosai, kokarin calming dinsu ya fara baima karasa magana baa mar ya katse shi ‘’how my mother? Meke faruwa da ita? Whys she bleeding’’ amar ya fada yana kafeshi da idanu

 ‘’I’m so sorry to say this but…’’ dan jim yayi yama rasa ta yanda zai mashi bayani

‘’why are you silent? Kun kasa aikin ku ne? wallahi idan wani abu ya same ta sainayi suiing aisbitin nan’’ cikin sauri aman ya dafashi yace ‘’calm down, ka tsaya muji me zaice’’

Kallonsu doctor ya sakeyi yace ‘’shes in danger rn, zuciyarta na gab da bugawa saboda tayi damaging ta tsaya chak dalilin pumping jini da batayi kwata kwata, mun yi iya kokarin mu don mu gano abunda ya toshe hanyar mun kasa ganowa saidai, dole zamuyi mata operation, and we only have 10% chance zata rayu idan anyi operation din Kenan idan baayi ba cikin gaggawa kuma, im so sorry to say this she cannot make it, and right now shes in coma’’,

Hannu aka salima ta dora tana ‘’innalillahi mun shiga uku’’

Amar dai gaba daya komai nashi tsaywa yayi chak, babu abunda yake sai innalillahi wa inna ialiahi rajiun, idanunshi yayi jaa sosai kamar garwashi, jijiyoyin kanshi sun firfito sosai, da sauri ya damko rigar doctor hankalinshi y agama gushewa gaba daya ‘’are you insane? Wannan wani irin maganar banza kakeyi, shes perfectly fine dazu yanxu kuma zaka cemin zuciyarta ya buga kai mahaukaci ne’’ kakarin amai doctor ya soma yi saida aman ya taimaka mashi ya kwaci kanshi a hannun amar, ya tura shi baya, da sauri amra ta taro amar ta riko shit ace ‘’yaya please calm down, ka kwantar da hankalinka babu abunda zai samu ammah insha allah she will be fine’’ bai dago ba haka zalika bai kalleta ba jikinshi dai sai bari yake kamar mazari, gaba daya kana ganinshi kasan hes weak, asuna nan tsaye nurse ta fito hannunta rike da report ta kalli doctor ‘’sir ga scan ga result din scan’’

Karban file din doctor yayi ya bude ya karanta tsaf yana gamawa ya dago ya kalli aman don amar ya futa hayyacinshi gaba daya yace ‘’dole ayi mata opration yanxu don komai zai iya faruwa, and dole zamu buqaci jini don blood type dinta babu a blood bank so I suggest kuje a diba jini as much as possible saboda shi tafi buaqata ayanxu’’ yana kaiwa nan ya juya ya shige emergency room don ya shaku sosai.

 

Takowa aman yayi inda amar ke tsaye yace ‘’bamuda wani option yanxu, dole we have to accept duk abunda suka ce’’

Afusace amar ya kalleshi yace ‘’waennan basu san komai ba, I will be transferring her now to dubai, I want to confirm abunda suke cewa’’

Wani irin kallo aman ya mashi kana ganin kasan hes very serious ‘’wai bakaji abunda suka fada bane?, shes in danger dole ayi mata operation yanxu, ayanxu da kake cewa zakayi mata transfer to wata kasar how sure are you zatakai har lokacin’’

Kallonshi amar yayi, gaba daya jikinshi yam utu he cant believe abunda kunenshi ya jiyo mashi, katseshi amar yayi yace ‘’yes nida kai munsan komai, wannan duk aykin daddy ne, so we have no other option dole muyi abunda doctors sukace kafin mu gano komai’’

Dafe kai amar yayi yana ambaton allah, lallai abunda suke zargi haka ne, da farko ya dauka sun tsirar da ammah na kokarin gano lantana, saidai abunda basu sani ba shine dalilin bugawar zuciyarta.

 

Nurse din data kawo report ce ta jagorancesu zuwa lap gaba dayansu, suna gab da shiga aman ya waigo wajen su amra yace ‘’ku jira anan’’

Yana kaiwa nan yabi bayan amar don ya shige ciki already cikin gaggawa, jininshi aka fara diba don ayi blood test kafin a diba na aman, ana gamawa suka fito waiting room suka tsaya don jiran report, cikin mintuna qalilan saiga doctor ya fito cikin kayan operation, yana futowa suka miqe su duka suka tsaya gabanshi har ya soma Magana ‘’sir jininku baiyi daidai da nata ba, I mean bazaku iya bata jininku ba, gaba dayan ku blood group din ku AB ne, ita kuma universal donor ce dole sai universal donor irin ta ne zai iya bata,’’

Hannu amar ya daga ya shafa kanshi kafin ya kaima bango naushi, nan take hannunshi ya fara fidda jini, gaba daya duk saida suka tsorata dashi sosai,

‘’im a universal donor’’ duk waigowa sukayi suka zubama amra idanu datayi Magana harda amar, takowa tayi har gaban doctor din tace ‘’im o negative’’

Kallonta doctor yayi shes so young gashi da yawa ake buqatan jinin don haka yace ‘’that’s perfect, saidai jinin da za mu buqata yaan da yawa sosai’’

Saurin katseshi tayi tace ‘’ba damuwa a diba,’’

Kallon nurse doctor yayi yace ‘’kuje blood bank a diba sample kuyi running blood group test kawai cikin gaggawar ko bag biyu ne for now’’

‘’okay sir’’ nurse din ta fada tana bin hanyar lap din amra na biye da ita har suka shige cikin lap din.

Babu abunda aman keyi sai hamdala, gaba daya fatansu allah yasa a dace.

 

Bangaren asad tun bayan fitarsu amar shima ya shige motarshi da yaransa suka wuce asibitin dake cikin nigerian army head quarter saboda abama lantana taimakon gaggawa don gaba daya kamar ta daina nunfashi, suna zuwa aka karbeta akayi treating ciwukanta, kowa saida yayi mamakin yanda ta karairaye kamar wadda tayi accident, don anyi mata gyaran karaya biyar a jikinta, tasha azaba kuwa hannunta an daureshi da ankwa a jikin gadon asibitin.

 

Saida asad ya tabbatar ta dawo hayyacinta ya fara buncike akanta tundaga kan rayuwarta har zuwa abubuwan da takeyi da mutanen da take mu’amala dasu.

 

Amra….

Bayan sun shiga lap nurse ta deba sample din jininta, cikin yan mintuna kalilan tayi running test nan taga jinin amra yayi matching da amma don haka tayi saurin bata gado anan cikin lap don kafin ta ta fara kokarin diban jininta.

Tunda amra ta kwanta babu abunda take sai hawaye, gaba daya she’s weak, alokacin babu abunda take fata sai samun lafiyar ammah, tunda ta kwanta idanunta akan celing tana jin yanda jinin ke fita daga jikinta har aka diba 1st bag, ita kadai tasan abunda take ji ajikinta, saida aka gaam diban seconb bag ta soma jin jiri, lokaci guda tayi passing out, nurse na ganin haka ta tsagaita daman tasan dole hakan zata faru don haka tayi mata taimakon gaggawa ta mata alluran bacci.

 

Bangaren su amar tun bayan tafiyar amra kowannensu na zaune a gaban emergency room suna cikin zullumi, gaba dayansu hankalinsu a tashe yake sallah ce kawai ke fidda su amar da aman da salim, suna nan zaune har nurse tazo ta wuce da bag of jinin da aka diba na amra, tana fitowa ta sanar dasu amra tayi passing out har an bata daki, tashin hankali biyu, ga amra ga ammah, salima dai kamar zata haukace haka take ji, gashi basuji komai daga bangaren ammah ba, haka suka dunguma itada aman suka wuce dakin da aka kwantar da amra suka bar amar da salim a emergency, da sallama salima ta bude kofar, a kwance suka taddata, fuskanta yayi pale sosai, kana ganinta kasan she’s not okay kwata kwata, tausayinta duk suka fara ji gaba dayansu salima dai babu abunda take sai hawaye.

Basu wani dade wajen amra ba suka koma emergency ganin tana barci, koda suka koma chan ma haka salima ta zauna ta doka uban tagumi.

Suna nan zaune saiga amra ta zama wata abar tausayi, salima na hangota daga nesa tayi saurin miqewa ta taho da ita don da kyar take dingisawa, suna karasowa ta kalli su aman tace ‘’yaya ya jikin nata? An gama operation din’’ ta tambaya tana kokarin zama, kallonta yayi yana jin tausayinta sosai aranshi yace ‘’basu fito ba tukunna how are you feeling now? Meysa kika fito ki koma karki fadi’’

‘’ah ah ya aman, zan zauna anan har su fito’’

Tunda suka fara Magana amar bai dago ba, idanunshi a lumshe yana addua aranshi, kana ganinshi zai baka tausayi fuskanshi tayi jaa sosai.

Suna nan zaune nurse ta sake futowa hankali atashe, suna ganin futowarta suka miqe gaba dayan su,tana kokarin wucewa ta hango amra, ‘’alhamdullah daman dakin da kike zanje, ana buqatar wani jinin saidai ina tsoron zaki iya samun matsala kema’’

Saurin katse amra tayi tace ‘’ku diba kawai,’’

Shuru nurse din tayi tana kallonta dakyau tana son sensing wani abun, don tabbas kana ganinta kaga lafiyayyiya saidai diban jini ba abu bane mai sauqi dole zataji a jikinta,

Wata nurse dinta ta sake fitowa tace ‘’nurse t what are you waiting for, ana buqatar jini yanxu, jinin ta yayi kasa, we can lost her at any time’’

Saurin runtse idanu amar yayi gabanshi na faduwa, hankali atashe amra tace ‘’dan allah ki diba kawai, babu abunda zai sameni,’’

Wadda aka kira da nurse t tanajin haka tace ‘’amma…’’

‘’dan allah ku diba kawai nace maku im okay’’ amra ta katseta

Dayar nurse dince ta shiga emergency room ta debo abubuwan da zasu diba jinin dashi, anan zaune ta saka mata canula ta soma diban jinin, babu abunda amra keyi sai runtse idanu tana hawaye, yanda takeji kamar ana zare mata rai, ana diban half nurse t ta kalleta tace ‘’ko zaki tashi ki dunga zagayawa saboda naga baya futa sosai’’

 

Girgiza mata kai akwai amra tayi ta mike salima dake gefenta itama ta miqe, ahankali ta daga kafarta tayi taku daya biyu harta kusa gifta inda amar yake kafin ta yanke jiki, amar da idanunshi ke rufe yayi saurin budesu ya tarota da sauri, abubuwa da daman a yawo aranshi, cikin muryanshi da baya futowa sosai yace ‘’ku cire mata please’’

Da kyar amra ta bude idanunta ta sauke akanshi, tsantsar damuwa ne akan fuskanshi sosai,saurin runtse idanunta tayi tace ‘’no karku cire min dan allah, ammah needs it more’’

Binta yayi da jajayen idanunshi kafin ya dauketa gaba dayanta da hannunshi ya kalli nurse din ya nufi hanyar dakin da aka bata, yana gab da shiga dakin ya dan rankwafo daidai kunenta’’ why are you stubborn, youre not okay bari acire maki’’

Wasu siraraen hawaye ne suka zubo mata muryanta baya futa sosai tace ‘’ah ah yaya, dan allah kar a cire, ammah..’’ bata kaarsa ba ta sake passing out, saurin kwantar da ita yayi akan gadon ya kalli nurse din dake biye dashi yace ‘’ku cire mata, zanje na nemo wani ji

Yana kaiwa nan ya fuce daga dakin hankali atashe, har wani tangadi yakeyi kamar zai fadi, yanxu ina zaije ya nemo jini ya tambayi kanshi, wajen emergency ya koma ya dan tsaya, yanajin kamar idan ya tafi shikenan bazai sake ganin ammah ba har abada.

 

After 3 hours of successful operation, sai wajen karfe biyar doctors suka fito daga cikin operating room, amar dake shirin barin wajen yayi saurin tsayawa ganin green light a jikin kofar emergency din which means an gama operation Kenan, gabanshi ne ya bada dammm, shikenan babu abunda yazo ranshi sai qila ta mutu ne, saurin rintse idanunshi yayi lokacin da doctor yake ma aman bayani kan zuje office dinshi.

 

Doctor na juyawa aman yabi bayanshi, amar shima dai haka ya daga kafarshi da kyar yabi bayansu zuwa office din doctor, suna shiga office din suka zauna suka kafama doctor idanu kamar tv, kallonsu shima yayi ya soma Magana

‘’alhamdullahi, dole mu gode ma allah, we have a successful operation, saidai shes still in coma’’

Wata irin ajiyar zuciya suka sauke atare suna hamdala, amar kuwa saida yayi sujudul shukur,

Kallonsu doctor ya sake yi yace ‘’abunda ya bamu mamaki shine shes very strong shes a fighter don ko lokacin da muka shiga operating room bamu taba tunanin zata rayu ba, saboda chance din kadan ne, sannan operation din anyi shi cikin gaggawa wanda hakan ma saboda ikon allah ne muka samu komai ya daidaita,’’

Kallon doc aman yayi yace ‘’thank you so much thank you but munason komai game da rashin lafiyar nata, meya kawo mata wannan heart damage din?’’

Nunfasawa doctor yayi ya bude file din gabanshi ya tura amsu gabansu kafin ya danyi yan danne danne akan screen din desktop dake gabanshi ya juya masu screen din ya soma bayani ‘’wannan scan din zuciyarta ne,wannan hole din shine yake pumping blood zuwa ga zuciya, case irin nata bamu taba samu ba saboda yawanci masu heart attack da wuya ka samu wanda heart dinshi yayi blocking gaba daya daga jan jini, saboda kwayoyin hallita da suke kare lafiyar jikin dana adam,abunda yafi bamu mamaki shine kwayoyin hallitar jikinta duk sun mutu kadan suka rage wanda sune suka taimaketa har take raye saboda jinin ta nada karfi sosai, and bayan wannan a buncikena da mukayi akwai wani substance a jikinta wanda shine ya kashe mata kwayoyin haliitar kare lafiya na jikinta wanda buncike ya nuna yana bin jininta ne bayan wannan munyi buncike akan substance din and it looks like drug ne mai karfi don drug ne mai karfi ke kashe waennan kwayoyin.

Acikin file dinta naga ta taba samun heart attark, shima duk ta dalilin substance dinne don ahankali ya fara cinta harya nemi hanyar

61 / 94