message”
Kai Tsaye mutumin yace “eh nine, nasan ba lallai Ka gane koni waye ba, amma Ina tabbatar maka inada abunda kake buqata saidai”
Dan dago da jajayen idanunshi yayi ya Dora akan mutumin yace “Ina jinka”
“Kwanaki ka bawa Alhaji sammani offer kudi miliyan hamsin”
Nan take Amar ya dago inda ya nufa don harya manta da Alhaji sammani ma saidai Har lokacin bai gane koma waye ba”
Katse mashi tunani mutumin yayi yace “nasan mana tunanin koma waye ni saidai wannan bashi da amfani”
“Wannan offer din tana nan…”
runtse idanunu amar yayi ya katseshi yace “100m” ya fada fuskanshi babu wasa, murmushi mutumin yayi ya jawo wayanshi ya tura mashi wani audio sannan yace “na tura maka”
Amar ne ya kalli wayarshi yaga audio, na tare da bata lokaci ba yayi playing kasa motsawa yayi jin muryar Alhaji kabiru radau yana magana shida Alhaji sammani,gabanshi ne ya bada damm jin abunda Alhaji kabiru yace “akan asirina ya tonu n kashe rayuwa da dana ciki kuwa Harda dan uwana jina na”
Sammani ne yace “kaii kabiru baka da dama, yanxu kashesa kayi saboda me?”
“Saboda shine mutun na farko dayayi min shigigi a almarina, kai bama shi kadai ba Harda matata ta farko”
Kece wa sukayi da dariya dip video ya tsaya, amar dai hannunshi Har karkarwa yake tsabar tashin hankali, ya kasa motsawa idanunshi kyami jaa, tunda yake bai taba shiga tashin hankali ba, jikinshi Har mazari yake, kallonshi mutumin yayi yace “Akwai video yallabai amma”
Azafafe Amar ya shako wuyanshi yace “kudi kake so kudi??? Zan baka miliyan dari biyar a take anan” ya karashe idanunshi sunyi jaaa, da kyar mutumin ya banbare wuyanshi daga rokon dayayi masa yace “zaka kashe ni yallabai”
Sakinsa mar yayi yana sauke wani wahalallaen nunfashi jijiyoyin kanshi sun firfito Rudu rudu, wayarshi ya bude yace bani account details dinka, nan take Amar ya tura mashi 500 million, yana kaiwa nan ya shige mota, shikuwa mutumin yana jin alert ya doka tsalle cikin hanzari ya tura mashi video, amar
dake zaune dakyar ya iya daga wayarshi ya bude video, saurin runtse idanunshi yayi ya wurgar da wayar yana karanto innalillahi, da sauri ya sake kallon wayar Ganin dada shi a zaune yana jikinshi kamar wanda wanda akayi paralysing, Alhaji kabiru na kallonshi yana dariya yace “haba yaya, ban taba tunanin hannuna zasu taba jinina ba saidai kayi gangancin yin Buncike akaina harka gano sirrina da babu wanda ya sani duk duniya, I’m sorry but dole na kasheka yaya don nasan bazaka rufa jin asiri ba”
Dada dake zaune helpless ya kasa cewa komi idanunshi na rufewa, bakinshi harya soma karkacewa, Alhaji kabiru ne ya miqe tare da daukan sauran juice daya zuba kwayar a ciki yace “yaya guda biyar kawai na saka maka wannan kwayar tawa as a sample don kaji yanda take, normally guda daya ake shaa ahankali zata kashe Duk wani kwayar dake kare lafiyar jikinka and you’ll die silently and peacefully”
Yana fadin haka ya kece da dariya nan video ya tsaya dipp, wata irin Kara amar ya yi tare da bugun glass din window motarshi nan take ya fashe gaba daya har yana tsaga mashi fatar fuskanshi hannunshi kam ya fashe sai jini, ahankli wasu irin ruwan hawaye ya kwanta cikin idanunshi ya qi barin su sauko kan fuskanshi,girgiza kai kawai yake yana innalillahi wa inna ilahi rajiun,
Alhaji kabiru shine ya kashe dada…..
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 125
Update
Unedited
Arana irin tayau ta kasance rana mafi bakin ciki agareshi, zuciyarshi ta gama dishewa, babu abunda yake sai kukan zuci, ya dauka kusan awa daya a cikin motar kanshi nakan steering motarshi, ya kasa koda motsawa,aduniya babu mafi soyuwa a gareshi kamar iyayenshi,wayarshi daya wulla gefe ce ta soma ringing, dago da kanshi yayi ya kalli inda wayar take, hannunshi na karkarwa ya dauka wayar kamar zata subuce daga hannunsa, dakyar ya dauka ba tare da sanin wanda ya kira ba ya dauka yasa a kunnenshi, “oga Ka isa abuja ne? I have a good news, na samu wannan yarinyar”
Shuru Amar fuskanshi dauke da damuwa,it’s hard to understand him don kwata kwata baka gane yanayinsa saidai yau mana ganinshi kasan he’s not his normal self, kasa cewa komi yayi saida asad yace “hello oga are you there?”
Runtse idanunshi yayi ya budesu bakinshi na karkarwa yace “can’t…talk..right..now” ya fada ararrabe, asad ne hankalinshi yayi mugun faduwa jin yanda yake magana don sun rabu lapiya, hankali atashe yace “oga is everything okay? Kana Ina?“
Kasa cewa komai Amar yayi sai sauke wani irin nauyayyan nunfashi da yayi yace “please kazo Ka daukeni”
Yana kaiwa nan ya kashe wayar, don dakyar wayar ke zama a hannunshi, dafe zuciyar shi yayi da yake mashi wani irin zafii, kasa motsawa yayi idanunshi sun zama kamar garwashi.
Asad da hankalinshi shima ya gama Tashi yayi saurin shiga wani app a wayarshi yayi tracking din layin Amar, cikin gaggawa ya fito daga asibitin federal medical Center, kallon yaranshi yayi ya basu command din guarding din meeda kafin ya fuce daga cikin asibitin gaba daya, sojoji biyar ne ke guarding gaba da bayan dakin nata, da kyar asad ya gano inda Amar yake inda yayi mamakin wajen sosai don wajen gaba daya is not safe, yana shiga cikin uncompleted building sun ya hango motar amar, da sauri ya fito daga motar shi don ko parking dinma bai gama ba hankali a tashe ya karasa inda yake, tundaga kan glass din dake fashe a kasa yabi da kallo, da sauri ya bude motar Ganin Amar ya kafa kanshi jikin steer, “oga meya faru anan? Attacking dinka akayi?”
Da kyar ya daga idanunshi ya sauke akan asad, da sauri asad ya bude kofar hankali tashe don sanin inda matsalar ta faro,
“Please take me home” amar ya fada hannunshi dafe a zuciyarshi,
Da taimakon asad ya fito daga motar suka shiga tashi, saida asad ya fara kiran wani yaranshi kan yazo ya dauki motar Amar kafin su fuce daga wajen.
Tun akan hanya asad yaso ya tambayeshi abunda ya sameshi saidai Ganin gaba daya baya cikin natsuwarshi yasa ya barshi, ahankali asa ya fara lura da kamar Ana binsu a baya, don haka ya dauki wayarshi akayi connecting dinshi da research team dinsu, nan ya basu plate number dake binsu sannan ya bada umarnin buncike akan plate number,gangarawa yayi gefe da motar, kafin ya futo, yana futowa yaga motar ta tsaya daga chan gefe,hannunshi ya saka a bayan aljihun shi ya rike bundigarsa, yana zuwa kusa da motar suka jaa motar a guje suka bar wajen, nan take yayi suspecting dinsu don hakan ya bada umarnin a tare hanyar da suka bulla, amar dai baisan meke faruwa ba don tunda ya shiga motar ya dafe kirjinshi ya bai dago ba, addua ya soma yi ahankal don neman sauqin abunda yakeji, don ayanda yake jin kanshi yanxu idan zaiga Alhaji kabiru zai iya kashesa mercilessly yanda ya kashe mashi mahaifi, babu abunda yafi azaba da masifa kamar akashe mutun yana ji yana gani helplessly,asad ne ya dawo ya bude kofar ya tada motar suka bar wajen, cikin mintuna qalilan suka iso daidai taura estate, horn asad yayi securities suka zo gaban motar, ganin Amar a zaune yasa sukayi saurin bude kofar sanin koshi waye, suna bude gate din asad ya yo parking tare da cewa “oga mun iso,”
Amar kasa cewa komai yayi ya daga hannunshi ya bude kofar ya fito da kyar kamar wanda yayi maye,asad dai da idanu ya bi shi don tabbas wani abu ya faru,
Hanyar entrance Amar yabi ya Danna door bell,lanatana na bude kofar tayi baya don yanda ta ganshi ta razana sosai,asad na Ganin shigewar shi ya ja motarshi yabar gidan don zuwa asibiti, don lokacin daya fito meeda bata farfado ba.
Amar na wucewa dakin shi ya zube kan couch din dake facing gadonshi,gaba daya komai ya taaya mashi chak, ya shiga tashin hankali sosai, tattaro kuzarin shi yayi ya dauka wayar Tashi tare da playing video din, gabanshi na bugu fat fat fat, saurin runtse idanunshi yayi sosai, ahankali hawaye suka fara gangarowa a fuskanshi, hannu ya saka ya taba fuskanshi, zai iya cewa wannan ne first time ya taba hawaye tun bayan girmanshi, don ko lokacin da dada ya mutu baiyi kuka ba, saidai dalilin mutuwar dada ayanxu, kallon hannunshi ya dunga yi, he can’t believe it, for over many yeara zarginshi da yake yi ya tabbata, Duk zamanshi da daddy duk rashin jituwarshi dashi bai taba kawo zai kashe wani ba balle dan uwan shi kuma jinin shi wanda yayi mashi komai a duniya akan abun duniya, abun duniya mai karewa, wani irin ihu yayi ya buga wayar a kasa take ta fashe tass, dafe kanshi yayi trying to pour the bitterness in his Heart, alhaji kabiru azzalumi ne macucine, shine ake kira da makashinka na tare da kai ba tare da saninka ba, ahankali ya furta “ya Allah…why? Whyyyyyyy”
Har kusan karfe hudu Amar na zaune ya kasa koda motsawa, kanshi na mugun Sara mashi, he’s so weak, bai taba sanin weakness dinshi family dinshi bane ba sai yanxu,kiraye kiraye sallah da akeyi ne ya sashi tattaro sauran kuzarin shi ya shige toilet yayi wanka ya dauro alwala, anan dakinshi ya shimfide sallaya ya gabatar da salloli da ake binshi don ko sallar dhuhur baiyi ba, ya dade yana kai kukanshi wajen Allah don neman sassaucin abunda yake ji tare da nemar wa mahaifinshi rahamar Allah, ya dade sosai yana yima dada addua Har barci ya soma dibarshi anan zaune.
Wannan barci da yayi ba karamin rahama ya saukar mashi ba don yaji kusan Rabin abunda yakeji ya sauka, toilet ya shige ya sake wani wankan ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin kayanta marasa nauyi ya dauka wani car key cikin keys dinshi na motocinsa kafin ya fito, yana shirin fitowa su salima na dawowa daga islamiyya, gaishesa suka fara yi, fuskanshi kamar koda yaushe babu walwala ya amsa kafin ya fuce daga gidan.
Yana futa su salima suka hau sama, kaya ta fara ta chanzawa zuwa marasa nauyi tayi sallah don salima already ya wuce masallaci don bashida nisa daga gida, kasa ta sauko ta wuce kitchen, lantana ta hango tana tuka tuwo, da sauri ta karasa inda take tace “anty lantana sannu da aiki”
“Kin dawo ashe, waye ya bude maki kofa?” Lanatana ta tambaya
“Ya Muhammad ne ya bude shima yazo fucewa” salima ta fada
Kallonta lanatana tayi tace “nidai kwana biyu gidan nan gaba daya babu dadi, hajiya babu lafiya,Allah yasa dai lafiya ba jikin nata bane ya motsa ba don dazu daya dawo kamar yana cikin damuwa sosai”
Shuru salima tayi tana bare mata ledar da take zuba tuwon tace “nima dazu dana ganshi naga kamar da damuwa a tattare dashi, dazu dai driver daya daukomu yace daga asibitin yake yakai abunci, na tambayeshi jikinta yace taji sauqi sosai gobe za a sallameta ma”
Salima ta fada tana kallon lantana
“Toh Allah yasa kaffara ne”
“Ameen” salima ta fada,
Tare suka gama tuwon suka diba wanda zasuci kafin su zubowa wanda za a kai asibiti.
Bangaren Amar tunda ya fito ya shige cikin Range Rover dinshi ya fuce daga compound din gidan da mugun speed.
Yana karasowa asibiti yayi parking ya futo, take ya soma jin gabanshi na faduwa don sai a lokacin ya fara tunanin yanxu idan ammah taji wannan baqin labari how would she feel, yasan she will shattered, abun saiyafi taba ta don itake auren Alhaji kabiru ba tare da samun shine ya kashe mijinta ba gashi tana da weak heart, runtse idanunshi yayi ya furta “ya Allah ka shiga lamurana,I can’t let her know any of this not until she recovers,”
Shuru yayi yana tunanin yanayin daya shiga lokacin daya gano gaskiyar, shima kenan ya shiga cikin damuwa dukda he’s strong balle ita dake da ciwon zuciya, dole he has to do something,he can’t afford to loose to her, dole yayi protecting dinta bazai taba bari any harm yazo kusa da ita ba musamman yanxu daya ganoi komai.
Futowa yayi daga motarshi ya shige asibitin dakinta ya wuce kai tsaye, a zaune ya taddata kan gadon marasa lafiya hannunta rike da charbi da alamu tana lazimi, yana sallama Tayi saurin dagowa ta kalleshi, takowa yayi har gaban gadon ya zauna gefenta ya fara kokarin danne Duk wata damuwar shi, kallonshi tayi kafin ta shafa adua tace “barka da zuwa son”
Kallonta yayi ya danyi murmushi yace “Ina wuni ammah na? Ya jikinki?, me kikeji yanxu do you need anything?”
Ajere ya watso mata tambayoyin, kallonshi tayi tare da kamo hannunshi cikin so da kaunar dan nata tace “wannan tambayoyi haka son? Alhamdlh I’m feeling much better, ni dama kace su sallameni yau mu tafi gida na gaji da zaman nan haka”
Murmushi ya mata shima ya rike hannunta gam cikin nashi yana jin kaunarta na ninkuwa a ranshi yace “ no ammah na saikin ji sauqi sosai, I will talk to doctor first, Saina tabbatar kina cikin koshin lafiya”
Dariya tayi tace “babana I’m so happy to have you as a son, Allah yayi maka albarka ya baka zuri’a ta gari, wanda ko bayan raina bazakayi maraici ba”
Shuru yayi ya sauke kanshi yana jin wani iri. “Ammah na ba yanxu zaki mutu ba, I will grow old with you”
Dan tire hannunshi tayi cikin wasa tace “grow old with me kuma? Saidai with your future wife”
Dariya yayi suka shiga hirar da da uwa.
Ya dauka kusan awa biyu yana tare da ita, kwata kwata bai yarda ta fahimci da damuwa aranshi ba kuma baiyi yunqurin fada mata komai game da abunda ya gano ba.
Alhaji kabiru dake ta daman sintiri a cikin guest house dinshi ya kasa natsuwa kwata kwata, yanada power yana da kudi da zai iya yin komai saidai yana tsoron Amar sosai don babu wanda zai fada mashi ko wanene amar da mukamin da yake rike dashi a uae government, he’s powerful
Har anan Nigerian,don gudun irin shiga wannan yanayin yasa yayi employing alif cikin business dinshi wanda hakan ya mugun Samar mashi dama mai girma ta hanyar jin Duk wani motsin amar, bayan wannan ma alif na cikin top members dinshi da suka bunqasa business dinshi, don shine yayi introducing human trafficking da sukeyi don already dirty work din da yake yi anan dubai kenan, lokacin da alh kabiru ya zamo alif komai is under control musamman lokacin dayayi adopting danshi daya kasance amini a wajen Amar sai abun yazo mashi da sauqi sosai don ta hanyar suke sanin Duk wani movement da achievement din Amar harma da ayyukan da yakeyi da bunciken da yakeyi, amar is very tough, mutun ne shi mai aiki da kwakwalwa, Duk abunda zaiyi saiyayi calculating, sannan yana da kwazo sosai musamman idan yasaka kanshi akan abu, da farko lokacin da suka gano yana digging akan business dinsu shida alif alhaj kabiru ya shiga tashin hankali sosai don komai was moving smoothly saidaga baya sukayi amfani da power da suke dashi suka danne Duk wani hanyar da zai tona asirin su, yanxu abunda yafi damunahi shine rashin samun alif da yayi wanda hakan ya tabbatar mashi da Akwai babbar matsala ko matsalar na shirin faruwa saidai bai tabbatar da hakan ba sai yanxu da komai is falling into places musamman daya gano Amar ne wanda yake aiki da meeda which means yana suspecting dinshi.
Yanxu abunda yafi tayar mashi da hankali shine meeda, don baisan amount of abubuwan data sani ba ko ta dauka na sirrin shi, don a cikin wayarta recordings kawai ya samu wanda sukayi magana shida ita alokacin datayi drugging dinshi da maganin dake saka mutun yana fadin maganganu, karar wayarshi ne ya dawo dashi daga tunanin daya shiga yayi saurin dauka yakai kunnenshi, yace “hope kasan cewa na fada maka this is the last time da zaka kirani indai ba kamata kukayi ba?”
“Oga mun gano inda take saidai Akwai matsala fah”
Da sauri Alhaji ya tari nunfashinsa yace “wace matsala kenan? Akwai matsalar da baku magance ta?”
“Mun gano tana asibitin fmc Yanxu haka bata cikin hayyacinta, daya daga cikin mutanen da takeyi ma aiki ne ya kawota”
Da sauri Alhaji yace “yanxu tana asibitin ne kuka gagara kasheta?”
“Oga Akwai sojoji dake gadin….”
Da karfi cikin ihu Alhaji kabiru katseshi yace “kai Jan idoo,na baku awa daya Duk abunda zakuyi kuyi ku kasheta, banason ta Kara koda rabin awa ne araye inba haka ba Saina kasheku duka”
Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya jefata gefe yana hucin masifa idanunshi sunyi jaaa don gani yake idan har suka bari ta Kara awanni zata iya tona mashi asiri.
Kallon hoton asad yayi da suka tura mashi, tunda suka turo hoton hankalinshi ya tashi don sai alokacin suka tabbatar mashi da shine dayan mutumin da yake ma aiki, don Har hotonsu tare da amar suka dauka lokacin da suka bi motar su abaya, yanda suka gano admsad shine dayan kuwa shine bayan tafiyar su daga asibiti nan suma yaran kabiru suka fara nasu binciken har suka gano inda meeda wata boye wato gidan kakarta amai zogale, lokacin da suka iso asad bai dade da barin wajen ba don haka suma suka tambayi inda matar gidan take wato kakar meeda mai zogale don Har lokacin gidan akwai kwado da aka kulle, mutanen dake zaune gefen gidan kuwa Ganin banza ta samu suka fada masu don sunyi tunanin suma kudi zasu basu kamar yanda asad ya basu, cikin hanzari yaran Alhaji suka koma asibiti nan suka samu lokacin da ake shigar da ita cikin motar asad, tundaga lokacin suke bin motar asad Har zuwa asibiti, basu samu sunyi komai ba don sojojin dake zagaye da asibitin wanda asad ya zuba su don kareta.
Hankali tashe Jan ido ya kalli abokin aikin da yace “kai mazaaa wannan Tsohon fah yana neman sakamu a matsala,ya zamuyi kenan?”
Shuru Dayan yayi yana nazari kafin yace “inada shawara,Akwai wata