Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   35 / 94

102K to 105K   out of 279.4K words

mata ataqaice, juyawa yayi zai wuce tace “ya Muhammad akawo maka dinner?”

Kamar bazai juya ba chan kuma yace “me aka dafa”

“Tuwo ne da miyan kubewa” ta amsa mashi

“Bring me just coffee” 

Da saurin ta tace “okay tohm”

Daki ya wuce ya zauna cikin Yan mintuna qalilan saigata hannunta riqe da mug da saucer, aje mashi tayi gefen Center stool tace “ya coffe din ya Muhammad”

Bai dago ba idanunshi nakan wayanshi yace “thanks”

Fucewa tayi yabi bayanta da kallo kafin ya maida idanunshi kan wayar yana karanta message da aka tura mashi da hidden number kamar haka “you cannot afford to miss what I have for you, 100million if you’re interested call this line”

Mamakin irin messages dinnan yake dan kusan kullum sai an tura mashi,bai kawo komai a ranshi ba ya aje wayar ya fara sipping coffee dinshi.

Alhaji kabiru’s hideouts….

Alhaji kabiru ne zaune tare da wasu mutane biyar a gefenshi, kallonsu daya bayan daya yayi kafin ya maida idanunshi akan wani jigegegen murdaddan saurayin dake miqa mashi waya, kallon wayar yayi yace “if I can remember na fada maka kazo min da yarinyar nan da rai ko babu”

Mikewa alhaj yayi azafafe ya wanke fuskar saurayin da mari, “you’re useless, waya zaka kawo? Me zanyi da waya?”

Daya daga makarraban Alhaji ne yayi saurin cewa “shugaba calm down,”

Juyowa alh yayi yace “calm down fah kace? A wannan situation din kake expecting nayi calming? Are you insane”

Sanin halinshi yasa kowa yayi shuru, juyawa alaji yayi ya dauka juice sun dake hannunshi ya juya shi kafin ya fuskanceshi saurayin yace “drink”

Kallonshi saurayin yayi don baiyi tsammanin hakan ba, karban glass din yayi ya rike kafin ya kafa baki yasha, shuru ne ya karade ko’ina, alhaji kabiru ne ya kalli agogon dake hannunshi kafun  yace “ku fitar min da gawan nan..” arazane kowa ya dago yana kallon inda Alhaji ke nunawa 

Bai gama fada ba saurayin ya fadi kasa a mace, nan take kowa yasha Jinin jikinshi,

“Useless fellow, just a simple job kun kasa komai, da kwaya daya nayi amfani nunfashinsa ya dauke”

Maida idanunshi yayi kan sauran mutanen gayen don sune yake bama dirty work suna mashi irin su kashe kashe, “basai na maimaita kaina ba, kuyi abunda ya face in a haka ba” ya nuna ogansu dake kwance ya cigaba “kuma haka ne karshen ku,”

Da sauri suka hada baki wajen cewa an gama yallabai, kallon wayar dake yashe a kasa alhj kabiru yayi kafin wani tunanin yazo mashi kafin yasa a miqo mashi, jujuya wayar yayi ya kafin ya kunnata, kallon mutanen wajen yayi yace “this can be useful also”

Bude wayar yayi ganin babu pin yasa ya fara bunciken wayar, saida ya shiga call log ya fara duba last call da tayi, da messages, kallon last message dinta yayi inda take cewa “sir Ka taimake ni……”

Kwata kwata babu suna a jikin number kuma number ne ta qira last don haka ya tabbatar da ba ita kadai take aiki ba, Akwai waenda take ma aiki, agurguje yasa aka kira hacker dinshi dake mashi Duk wani ayki daya shafi digital yayi buncike akan number,hacker ya dauka mintina sosai kafin ya gano mai number, nan take ya shaida ma Alhaji kabiru kan cewa yayi iya kokarin da zaiyi ya kasa samun information din mai line din don special line ne ba kowa ke using dinshi ba sai manyan mutane.

Afadace Alhaji yace “dukkan ku are useless, do something about this, Duk yanda za ayi ka dubo min koma waye behind this contact”

Shuru Alhaji yayi yana nazari tare da kallon number, hankalin shi atashe ya kalli yaranshi yace “Duk yanda zakuyi kuyi na baku 24 hours ku nemo min yarinyarnan”

“Okay shugaba suka fada tare da fucewa.

Shima Alhaji fitowa yayi ya shiga mota suka wuce gida.

Sai wajen karfe daya kabiru ya shugo cikin gidan, bai tsaya ko Ina ba ya wuce dakin ammah, daman da safe kafin ya futa sun samu sabani, yana mamakin yanda ta chanza sosai musamman yanda take damuwa akan alamuranshi da yawan tambayoyi da take akan aman da ayyukan da yake saka shi.shiga dakin yayi ganin wayam yasa ya fuce ba tare da ya damu da rashin ganinta a dakin ba daidai lokacin.

Akan idanun Amar Alhaji ya dawo gida don baiyi barci ba kwata kwata, idanu sosai ya saka akan Alhaji kabiru don this time around ya fara sensing matsaloli da yake tsoro daga gida musamman dayaga yanda alhaji yake movement dinshi don saida yaga yanda aka kusa kashe yaron nan da aka samu wayar meeda atare dashi nan tabbatar da Alhaji zai iya yin komai don Kar asiri shi ya tonu, yanxu tashun hankalinshi biyu ne, na farko ammah, bayason wani abu ya sameta kwata kwata, na biyu kuma meeda don yana jin idan abu ya sameta bazai yafe ma kanshi ba. Don haka ya yanke shawarar  gaggawar kawo karshen Alhaji kabiru, koda hakan zai sa ya rasa ransa, he will do anything for his family to protect them.

Washe gari da sassafe asad ya kirashi kan yaron ya farfado saidai baya iya magana, agaggauce ya shirya saida ya fara zuwa wajen ammah, ya duba lafiyarta, dadi yaji sosai Ganin yanda take recovering sosai, saida ya dade a wajenta kafin ya mata sallama tare da neman adduarta.

Karfe goma daidai ya iso kauyen fatakum, asad ne ya fito, suna gaisawa suka shige cikin asibitin, daidai gaban gadon yaron suka tsaya, kallonshi Amar yayi kamar yanda shima yaron yake kallonshi kamar dolo, ahanakli amar ya tako Har inda yake hannunshi cikin aljihun wandonshi yace “ya jikinka?”

Shuru yaron yayi ya zuba mashi idanu,ganin haka yasa asad cewa “oga tun daxu muke tambayarshi babu response”

Zama kan gadon Amar yayi ya fuskanceshi yace “nasan mana jina, bazamuyi maka dole akan saikayi magana ba, amma Ka sani cewa idan Har baka fada mana inda Ka samu wayar nan ba rayuwar na cikin hadari, mu kuma taimakonka zamuyi”

Kamar daga sama sukaji yaron yace “ku suwaye? Kuma kasheni zakuyi?”

Ba karamin dadin su asad sukaji ba Ganin ya soma magana, kallonshi Amar yayi yace 

“Mu ma aykatan kariya ne ga alumma, inason Ka fada min ind aka samu wannan waya”

Shuru yaron yayi chan kuma yace “agurin iliya mai chargy na saya, ni Wallahi banma iya amfani da ita ba karambani na yakaini na siya gashi na jefa rayuwata a hadari”

Kallon juna Amar shida asad sukayi kafin asad yace “Ina ne shagon iliya din?”

Kai tsaye yaron yace “bakin kasuwa mai ci”

Da sauri Amar yace “zaka iya kaimu chan?”

“Eh amma…”

Dafashi asad yayi yace “karka damu babu abunda zai faru dakai kaji”

Futowa sukayi su uku suka shige motar su asad kafin su gangara zuwa kasuwa, suna fita motar yaran alh kabiru na isowa cikin asibitin, suna shiga suka fara duba yaron babu shi, karshe da sukayi tambaya nan aka shiada masu wasu mutane ne suka tafi dashi, hankali a tashe yaran kabiru suka kira suka shaida mashi, nan ya basu umarnin su bunciko inda suka tafi da yaron don yana tsammanin mutanen dake aiki da meeda ne.

Daidai kantin iliya mai chargy suka tsaya, atare suka fito Harda yaron, da sallama suka karasa gefen shagon Ganin mutane a zaune, asad ne ya fara magana yace “waye iliya mai chargy anan”

Da sauri iliya ya fito daga wajen chargy yace “ni ne iliya”

Asad ne ya sake tambayarsa “Kasan yaron nan?” Ya nuna yaron

“Eh na sanshi”

“Ka sugar mashi da wayar zamani shekaran jiya anyi haka?”

Zaro idanu iliya yayi jin tambayoyin da akeyi mashi don babu abunda ya fadi aranshi sai qila wayar sata ce aka kawo mashi ya saya ya sayar, cikin tsoro yace “lpy dai yallabai?”

Asad ne ya kalleshi ya sake cewa “lpy, kawai Muna son sanin yanda Ka samu wayar”

Da sauri iliya yace “ni Wallahi yallabai a wajen wani almajiri na saya,”

“Kasan inda zamu samu almajirin?” Amar ya tambaya

Shuru iliya yayi yana nazari yace “yallabai sayar wayar yayi ne?”

Atsawace Amar daya kosa yace “ba shi muka tambayeka ba,”

A tsorace iliya yace “daga cikin Karka suke zuwa  almajiranci, yaran malam inuwa ne mai zaure”

Ba tare da bata lokaci ba ya nemi idan iliya zai iya rakasu cikin garin, yana neman yi masu gardama asad yace “Nawa kake ciniki arana, za  a ninka maka kudin"

Baki a washe iliya yace to muje, akafa suka wuce Har cikin garin fatakum dan bashida nisa sosai daga kasuwa, har gaban gidan almajirai suka karasa, saida sukayi sallama kafin malam ya fito, agurguje suka gaisa tare da neman almajirin nan malam ya tambayi koda matsala, asad ne ya shaida mashi babu wata matsala tambayarshi kawai za ayi, suna cikin magana saiga almajirin ya shugo,cikin sauri iliya yace”ga yaron nan ma”

Malam ne ya kirashi yaron ya karaso ya, asad ne ya kalleshi yace “kaine Ka sayar da waya a wajen iliya?” Ba tare da tsoron komai ba yace 

“Eh nine”

Kallonshi ya sake yi yace “Ina Ka samu wayar?”

“Aikena akayi na sayar” ya basu amsa

“Waye ya aikeka?” Asad ya Kara tambayarshi 

“Ranar naje bara gidan mai zogale shine ta bani naje na sayar,”

Amar daya gama komawa da zancen yace “let’s go please, zaman nan da muke ma bata lokaci mukeyi”

Mikewa sukayi Harda almajirin yayi masu jagora Har gidan mai zogale, suna zuwa gidan suka sa almajirin yayi sallama da mutanen gidan, kamar meeda dake zaune tana kuka ta miqe jin sallama, yaron ne yace Ana sallama a wajen don haka ta janyo tsohon mayafinta ta fito

Gaisheta asad yayi din shi Amar ya koma gefe takaicin komai ma ya mashi yawa, he’s so exhausted bai saba da wannan wahale ba, asad ne ya soma tambayarta “baba wannan yaron yace kin bashi waya ya sayar anyi haka?”

Kalllonshi tayi nan take ta tuna da maganganun meeda da take cewa bibiyarta akeyi ko anzo nemanta tace bata sani ba, 

Adaburce yar tsohuuwa tace “lafiya dai batun Allah?”

Murmushin yaqe asad yayi yace “lpy kalau Muna tambaya ne, dan Allah Ina kika samu wayar baba?”

“Tsinta nayi “ ta bashi amsa, Amar najin haka ya juya rai abace tare da naushin iska, godiya asad yayi mata ya juya ya sallami su iliya kafin ya wuce wajen asad, kallon Amar yayi yace “oga calm down, zamu nemo ta Insha Allah..”

Amar baice komai ba nufi hanyar da suka aje motar ya shige cikin motar, shima asad ya shige suka ba.

Asibiti suka dawo inda Amar ya aje motar shi,futa yayi daga motar asad ya shige Tashi suka bar wajen.

Cikin Yaran alhaji da suke cikin mota suna ganin motar data shugo a asibitin tambarin sojoji a gaban motar yasa suka labe, Amar na fitowa daga motar kuwa suka fara daukan hotonshi Harda motar daya fito daga ciki, amar da asad na fita da motocinsu yaran kabiru sukayi saurin fitowa suka tsaya wajen wani nurse daya fito daga asibitin, tambayarshi sukayi ko masu motocin da suka fita likitoci ne nan ya shaida masu, sunzo ne wajen wani yaro Har anma sallami yaron, nan take suka gano sune waenda akace sun tafi da yaron, saurin Kiran number Alhaji kabiru sukayi da yake zaune a secret hideout dinshi, nan suka shaida mashi sun gano waenda suka tafi da yaron don Har hoton daya daga cikinsu sun dauka, take ya umarci da su tura mashi kuma su cigaba da bincike akan yaron.

Hacker din dake zaune gefen Alhaji ne yace “yes I got it sir”

Kallonshi kabiru yayi yace “ka gano information din number ne”

“Eh na samu sunan mai number saidai babu address ko hoto a jikin profile din number”

 Tsaki kabiru yayi yace “dan uwarka get something important ba suna kadai ba, you’re useless”

“Sorry sir” ya fada yana maida hankalinshi 

Message din daya shugo cikin wayar Alhaji kabiru ya duba, da sauri ya fara loading don Ganin abunda yaranshi suka turo, picture din na budewa ya bude idanu ba tare da kiftawa ba runtse idanu alh kabiru yayi ya sake budewa don tabbatar don tabbatar da abunda ya gani, miqewa yayi  tsaye hankali a tashe yace “me nake gani”

Hannunshi na tawa kamar wayar zata fadi ya kalli hacker dinshi dake zaune yace kai “menene sunan mai number daka nemo?

Da sauri yaron yace “Muhammad Yunus”

Sakin wayar Alhaji kabiru yayi yace “shikenan, tarihi ya maimaita kansa”

Wata irin dairiya Alhaji ya kece dashi kamar mahaukaci, surutai ya fara kamar mahaukaci yace “yaro baka san wuta ba ka taka, zaka bai sahun…”

Shuru ya yi ya sake kece wa da wata dariya ya fuce daga gidan gaba daya.

Tun akan hanya amar yake tsaki, komai ya tsaya mashi chak ya rasa tunanin da zaiyi, wayanshi dake ringing ya kalla, ganin unknown caller yasa yayi rejecting wayar ya maida hankalinshi kan driving da yake,call dinne ya dunga shugowa babu kakkautawa don haka rai abace ya dauka wayar yakai kunenshi, jin anyi shuru yasa yayi tsaki, yana shirin aje wayar akace “haba yallabai, kaida Zan taimaka saika…”

Saurin katseshi amar yayi ta hanyar kashe wayar, sake kira mutumin ya yi constantly azafafe ya dauka rai abace yana shirin yin magana mutumin yace “zakaso kasan waye ya kashe mahaifinka Alhaji Yunus taura”

Amar najin bai ya Taka burki kiiii, kiri a ya rage ya buge motar gabanshi, shuru yayi ya kasa cewa komai chan kuma yace “who are you?”

Dariya mutumin yayi yace “yanxu zaka saurareni kenan?”

Yana kaiwa nan shima ya kashe wayan, rasa abunyi Amar yayi don bazai iya kiran unknown caller dinba don haka ya fara kokarin kiran asad, message ne ya shugo wayanshi da wata number, hanunshi na bari ya bude message din “meet me at this location” kallon message din yayi har asad ya dauka wayar yanata hello baima sani ba, jikinshi ne Ya soma bari, ahankali ya furta “daada”

Dafe kanshi yayi dake Sara mashi, saida ya dauka kusan minti talatin kafin yaja motar da mugun speed.

Asad dai tunda suka kama hanya bai gamsu da maganar tsohuwar nan ba don yaga tsoro karara a fuskanta,dan haka yayi deciding ya koma gidan, yana karasawa yaga a kulle gidan da kwado, nan take ya tabbatar Akwai wani abun a kasa,mutanen dake zaune gefen gidan ya tambayi ko tsohuwar tayi tafiya ne,

mutanen kauye da hadin kai don haka sukace basu sani ba, ganin haka yasa yace masu shi jikanta ne yazo wajenta, sanin taohuwar bata da jika sai yar budurwa dake zaune  da ita yasa sukace, “haba malam, kowa yasan mai zogale bata da jika da namiji sai budurwar yarinyar nan dake zuwa daga burni wajenta, don haka bamu san inda take ba bazakaji komai a bakinmu ba, kaje wajen mai gari”

“Jika, daga burni” asad ya maimaita aranshi, wani tunani yayi nan take ya juyo ya kallesu hankali tashe ya zaro kudi daga aljihunshi yace “ga wannan ayi cefane”

Suna Ganin kudi kuwa daya daga cikin su ya washe baki yace “au au toh madallah, dan nan Ay bamusan kai jikanta bane, wannan yarinyar ce kawai muka sani”

Murmushi asad yayi don daman yasan kudi sune bakin mutun don haka ya sake jefa masu tambaya yace “dan Allah inason nasan inda suke”

Daya daga cikin mutanen ne yace “ay yarinyar ce take rashin lafiya suka tafi asibiti,amalanken daya dauke su bai dade da tafiya bama”

Tambayar sunan asibitin yayi nan suka shaida mashi asibitin bakin kasuwa don nan ne kadai asibiti a cikin garin,godiya ya masu kafin ya juya…

Asibitin ya koma, gabanshi na faduwa yana adduar Allah yasa abunda yake hasashen ne, wani nurse ya tsayar tare da tambayarshi ko Akwai tsohuwar daga kawo yarinya budurwa nan asibiti, 

“Kai nidai yau nasha tambaya, Wai ni lafiya kuwa ake mana zarya a cikin asibitin nan?”

Asad bai damu ba ya zaro card dinshi ya gabatar da kanshi as a soja, hankali a tashe nurse din yace “yallabai Ay bansan aikin Ka kake yi, ayi min afuwa”

Murmushi kawai asad yayi ba tare da yace komi ba, 

“Akwai yarinyar da wata tsohuwa ta kawo dazu saidai bansan ko ita bace,suna daga bakin kofar dakin marasa lafiya don babu gado ma anan kasa ake Kara mata ruwa” nurse din ya fada yana yin gaba asad biye dashi Har inda mai zogale take rike da meeda ta ta gama fita hayyacinta saboda ruwan jikinta daya kare, karasowa asad yayi mai zogale na ganinshi tace “na shiga uku ni mai zogale daman yarinyar tace bibiyarta akeyi, dan allah bawan allah ne tayi maki kuke bibyarta”

Saurin karasawa asad yayi ya kurama meeda idanu, bai gane ta ba saida ya bude wayanshi ya duba profile dinta da yake dashi a wayanshi lokacin dayayi buncike akanta, nan take ya ganeta, kallon tsohuwar yayi yace “baba ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru da ita”

Kallon nurse din yayi yace “menene condition dinta”

Nan nurse din ya mashi bayanin komai,nan take asad yasa aka bata special care, kudi ya zuba sosai karshe dai ya roki mai zogale ta a wuce da ita babban asibiti don ta samu taimkon gaggawa, da kyar mai zogale ta yarda aka fito da Meeda aka sakata a asad tare da ita suka wuce.

Amar na isowa cikin abuja ya fara tunanin what if setting dinshi up ake son yi, nan take ya yanke shawarar zuwa kawai don baya tsoron komai, laluben location din da aka tura mashi yayi ya karya Kwanan motarshi.

Tunda ya shawo corner wajen ya fara raba idanu, ahanakli ya fara karantar wajen don wajen looks suspicious don waje wajen gari ne, gaban wani uncompleted building ya tsaya, fitowa yayi daga motar shi ya tsaya daga nesa, ya dauka kusan minti goma yana nan tsaye yana duban wayanshi don bai san yanda zaiyi communicating da anonymous mutumin da yayi mashi message ba dan dashi idanunshi yayi daga nesan ya fara hango wani mutumin kasa gane koma waye yayi saida yazo dan dashi, kallonshi Amar yayi tundaga sama Har kasa, bai gane koma waye shi ba don haka yace “kaine wanda ya tura min

35 / 94