hawaye she cant believe abunda kunnuwanta suka juyo mata, adda matar ya muhammd ce? Auren yarjejeniya sukayi saboda ta samu katin kasa ta kawosu kusa da ita? Sulale wa tayi anan wajen ta fara hawaye, daman ya Muhammad yace she will regret it idan taji abunda ta jefa kanta a ciki saboda su, kamar wadda aka tsugula ta miqe ta wuce cikin dakin amra, amra dake kukan zuci dana fili bataji kararbude kofar da salima tayi ba sai ganinta da tayi akanta, kura mata idanu amra tayi don tadan tsorata da ganinta tana hawaye,
‘’adda what did I just hear? Auren yarjejeniya kikayi saboda mu?’’
Salima ta fada tana kallonta, kauda kai amra tayi tace ‘’ian kikaji wannan’’
Zama salima tayi gefenta kanta akasa don wani irin nauyin amra ta fara ji tace ‘’adda im so sorry im sorry for blaming you’’
Kuka ne ya kufce mata ta cigaba ‘’wallahi adda ban taba tunani kema kin shiga wani hali ba saboda mu, im so srry addaa’’
Janyota amra tayi a jikinta tana hawaye tace ‘’salima ya za ayi na manta daku, daku nake kwana daku nake tshi, na shiga babban tashin hankali lokacin da kika kirani, don har lokacin nayi niyar dawowa saidai nayi laakari da idan na dawo komai zai iya wargajewa don daddy yace karna sake na dawo ba tare da na biyashi kudinshi ba bayan wannan ma banida wani option daya wuce na san aynda zanyi na kawo ku kusa dani har allah ya hada ni da ya muhammad’’
It was an emotional moment for amra and salima a wannan lokacin, kuka dai har suka gaji babu wanda ya iya hana dan uwanshi suna rungume da juna, saida suka gaji dan kansu suka rarrashi kansu kafin salima tace ‘’adda, ina neman wata alfarma a wajenki, bansan irin zaman da kukayi da ya Muhammad ba but bana jin akwai abunda shida ammah zasu nema a wajen mu muqiyi masu, adda mutanen nan basu san ba sun karbe mu hannubibiyu, ya muhammd yayi mana abunda iyayenmu ne kadai zasu iya yi mana don yayi mana gatan da waenda ya kamat suyi mana basuyi mana ba,shi ya biya mana kudin aikin da akayi mana lokacin da muka kusa mutuwa shine yayi protecting dinmu lokacin da aka watsar damu akan titi, shine wanda dora mu kan ilimin da aka hanamu yi aka tauye mana, shi ya samu a school nida salim ba tareda yasan asalin mu ta sanadiyarki, ke karan kanki bakisan yayi hakan ba,adda babu abunda zasu nema a wajen mu da zamu gagara yi masu shi har karshe nunfashin mu don komai zamuyi masu bazamu taba biyansu da abunda sukayi mana ba’’ hannunta salima
ta rike looking very very serious tace ‘’adda rokeki da allah, karki rabu da muhammd don lalurar shi, yau ko bashi da kafa nasan zaki zauna dashi adda, idan har kinason haihuwar ma ni idan nayi aure zan baki duka yayana kyauta, kimin alqawarin bazaki taba barinshi ba adda promise me’’
Amra na hawaye take bin salima da idanu, shes so speechless, wannan yanxu kanwarta ce, salima tayi hankalin da ayau ko bta raye zata kula da kanta da kaninta sannan tasan me ake nufi da halacci,
Murmushi amra tayi danyi tare da yar dariya ta kalleta ‘’basai kin roke ni ba salima, yau koda ace baya iya amfani da jikinshi zan zauna dashi, har abada bazan taba complain ba’’
Saurin rungumeta salima tayi tace ‘’tahnk you adda na, ni zan baki duka yaya na idan nayi aure’’
Kallonta amra tayi tace ‘’soyayya kikeyi ko? Har kinsan wani idan aure zaki bani yaya’’
Dariya salima tayi tace ‘’kaii add aim 19 years fa yanxu’’
Bugu amra takai mata tace ‘’karya kike youre 18 ay a lissafe yake akaina, next month’’
Dariya itama salima tayi tace ‘’wow ni harna manta fah, kuma next month ma graduation dina’’
Hira suka sha sosai ta kewar juna har suka shagala, kiran sallar magrib ne yasa salima fucewa ta barta a daki, murmushi amra tayu sai taji 50% din damuwarta ta raguwa, nauyin da zuciyarta keyi ma duk ya ragu.
Bayan sallar ishai salima tazo ta kirata don suci dinner, tare suka sauko gwanin ban shaawa, anra sanye take da doguwar rigar material da amma tasa akayi mata na bubu, suna karasowa suka tadda ammah da salim akan dining, da murmushi ta tarbesu ganin yanda suka rike hannu suka karso, har kasa amra ta tsugunna tagaishe da amma kafin ta samu waje ta zauna, su hudu kawai sukayi dinner don amar da aman basu dawo ba.
Karfe tara daidai amra ta fito daga dakinta sanye da hijab, cikin natsuwa ta tako zuwa part din da take tunanin na ammah ne don yafita daban a saman, da sallama ta shiga part din, babu kowa a sitting room don haka ta kara kwada sallama, daga ciki ammah tace ‘’bislillah’’ anatse amra ta tako har cikin dakin bakinta dauke da sallama, kanta a kasa ta shigo amma na ganinta tace ‘’daughter shugo mana ya kika tsaya kamar bakuwa daga kofa’’
Anaste amra ta karaso ta tsugunna har kasa ta gaishet kafin ta samu waje ta zauna tsakiyan carpet, ammah na ganin haka tace ‘’haba daughter ki zauna kan gado mana’’
Kai akasa amra tace ‘’nan ma yayi ammah’’
Murmushi amma tayi ta kalleta, kai akasa amra ta soma Magana cikin kunya ‘’uhm daman….’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’kinason ki fada min shawarar da kika yanke ne’’
Kai a kasa amra ta girgiza mata kai tace ‘’ehhh’’
‘’okay inajinki daughter, duk abunda kika yanke haka za ayi’’
Dan nunfasawa amra tayi tace ‘’ammah bana son ya sake ni’’
Runtse idanu ammah tayi cikin farin ciki da jin dadi tace ‘’are you sure daughter, karkiyi deciding kodan abunda yayi maku keda kannenki, inason kibi abunda zuciyarki ta raya maki kinji’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’badan haka bane, babu abunda zan iyayi da zan saka mashi da wannan saidai na roki allah ya biyaku da aljanna, kune gatanmu, duk duniya babu abunda zai chanza wannan’’ ta karashe tana hawaye, kanta ammah ta shafa tace ‘’thank you so much daughter, allah ya maki albarka, allah ya baku zuriyya dayyaba, inda rai akwai rabo, allah mai jin qan bayinshi ne, insha allah zaku dawwama cikin farin ciki har abada’’
Wani irin dadi ne ya ziyarci amra jin kalamin da ammah tayi da adduó ta.
Bata dade ba tayi ma ammah saida safe ta wuce dakin su salima, a zaune ta tadda salima tana zane while salim nab arci, karasowa amra tayi fuskanta dauke da murmushi tace ‘’har yanxu kina zanen’’
Juyowa salima tayi cikin murnar ganinta tace ‘’addaaaaa naa, yau tare zamu kwana ko’’
Kallon book din hannunta amra tayi ta ga zanen nata, kafin tace ‘’kin tuna min da abba, allah ya jikanshi da rahama da mami’’
Hira suka sha sosai kafin su kwanta tare……
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 131
UPDATE
Uendited…
The next morning…
Amra ce ta fara tashi, agurguce ta shege bathroom dinsu salima ta dauro alwala don gari ya soma yin haske, tana fito ta karaso gaban gado ta kurama su salima idanu tana jin dadin reuninting da qannenta, shagala tayi da kallon su, dukkansu sun chanza sosai sunyi kyau, fatarsu fresh hutu ya zauna ajikinsu, bin daki nasu ta soma yi da kallo, babu abunda babu a cikin dakin na yayan gatan,wani irin dadi ne ya ziyarce ta lokaci guda,acikin ranta babu abunda take sai godiya ga allah daya saka su hannun mutane na gari.
Zama amra tayi gefen gadon ta soma tashin su, ‘’salima…salim.. ku tashi lokacin sallah yayi karmu makara’’ amra ta fada tana kokarin tashin su, salima
ce ta fara bude idanunta kafin tayi miqa tace ‘’adda harkin tashi,?’’ murmushi amra tayi mata tace ‘’yanxu nima na tashi, mun Makara sallan asuba’’
Mikewa amra tayi tace ‘’zoki bani sallaya da hijab’’
Gaban closet salima ta bude, juyowa amra tayi ta karema closet din nasu kallo, kaya ne shake aciki tamm, murmushi kawai amra tayi don lokacin da suke hannun uncle basu samu wannan gatan ba kwata kwata.
Mika mata hijab din salima tayi tare da shumfida mata sallaya tace ‘’bari nima nayi alwala, wanchan shemamman nayin barcin nan nasa bazai say a tashi ba’’ tana kaiwa nan ta wuce bathroom, amra kuwa murmushi kawai tayi ta zura hijab din ta tada sallah, tana idarwa salima ta fito daga bathroom, itama shimfida sallaya tayi gefen amra ta zura hijab ta tada kabbara, sun dade sosai azaune suna addu’a, musamman amra data daga hannunta sama tana yima ammah da amar addua’a sosai, hr salima ta mike tana nan zaune tana addua hawaye na yawo akan fusknata, gaban lafiyayyan gadon su salima ta tsaya ta karema salim kallo tare da bugun hannunshi tace ‘’kaiii, tashi da allah, kai wallahi wannan barcin naka saikace na mutuwa’’
Anatse ya bude idanu ya galla mata harra kafin ya miqe, shima bathroom din ya wuce ya dauro alwala kafin ya fito, kusa da amra inda salima ta shimfida nata sallayan ya tsaya ya tada kabbara yana idarwa ya kafama amra idanu, kallonshi itama tayi tace ‘’salima ta takura maka ko?’’ girgiza mata kai yayi ya watsa ma salima harara, tana ganin haka kuwa tace ‘’mara kunya, gwara da bakinka ya tsuke dan allah kadai yasan irin kunyar da zakayi ma mutane’’, dariya amra ta soma yi tana jin dadin ganin kannen nata.
Kallon salima amra tayi tace ‘’yau zakuje school?’’
‘’yes akwai, yau zamu gama mid term test ma, zasu bamu hutun 2 weeks,’’ salima ta fada tana shirin shiga bathroom, bata dade ba ta fito salim ma ya shige bathroom din yayi wanka, agaggauce suka gama shirin school duk akan idanun amra, babu abunda take sai murmushi har suka gama, atare suka fito sukayi mata sallama kafin ta wuce dakin ta, tana shiga daki ttabi lafiyar gado don barcin bai gama sakinta ba.
Ba ita ta farka ba sai wajen karfe goma, agurguje ta shiga bathroom tayi wanka kafin ta fito daure da towel, anatse ta shirya cikin kayan da ammah ta kawo mata, material ne na bubu milk color, kayan sunyi mata kyau don sun haska fuskanta, anaste ta gama saka kayan ta feshe jikinta da turare mai sanyin kamshi kafin ta fuce daga dakin, part din ammah ta fara zuwa, daga sitting ta fara sallama, jin shuru yasa ta fuce daga part din, kasa ta fara sauko wa nan taci karo da lanatana dake shirin haurowa saman, tana ganinta tace ‘’ina kwana anty’’
Kunya amra taji datace mata anty saboda lantana ta girmeta sosai, kanta akasa tace ‘’ina kwana, mun tashi lafiya?’’ ta maida mata fuskanta dauke da murmushi, lanatana ma murmushi tayi mata tana yaba kyawu irin nata kafin tace ‘’daman hajiya ce tace nazo na duba ko kin tashi’’
‘’oh!! Ayya na tashi ina ammah in? amra ta fada tana kallon lanatana,
‘’tana kasa’’ tana kaiwa nan ta sauka kasan amra na biye da ita,
Nuni da hanyar dining lanatana tayi mata tace ‘’tana cikin dining’’
Murmushi amra tayi ta karasa wajen dining din, da sallama ta karasa kafin ta tsaya chak, idanunta ne suka sauka akan shi, lokaci guda suka hada idanu, samun kanta tayi da kasa dauke idanunta akanshi saida ya kauda nash kafin ta sauke nata wani irin kunya na lullubeta, ammah dai murmushi kawai take don taga yanda suka kafe juna da idanu, wani irin dadi takeji aranta sosai, miqewa ammah tayi ta tako har inda take ta janyo hannunta zuwa dining din tace ‘’daughter kin tashi ashe’’
Da sauri amra ta danyi kasa tace ‘’ina kwana ammah’’
Da murmushi ammah ta tarota tace ‘’no bendings dear, how was your night’’ ammah ta fada fuskanta dauke da fara’a, dan dagowa amar yayi ya zuba masu idanu, don ammah na ganinta t aaje serving dinshi da takeyi ta wuce wajen amra, tabe baki kawai yayi yana mamakin yanda ammah ke nuna kulawa agareta sosai, hannunta ammah taja har kusa da seat din ammah kafin ta zaunar da ita
Da sallama aman shima ya shugo dining din ya karaso inda suke zaune yace ‘’good morning’’ ammah ne ta dago fuskanta dauke da murmushin daya qi barin fuskanta don murna tace ‘’morning son how was your night’’
‘’alhamdulillah’’ ya bata amsa kafin ya maida kallonshi kan amra yace ‘’good morning sister inlaw’’ sunkuyar dakai amra tayi don kunya tace ‘’ina kwana’’
Ataqaice ya amsa kafin ya maida kanshi kana mar daya turnpike fuska kamar hadarin kaji, ammah ce ta juya ta kalleshi gannin yanda ya hade rai tace ‘’sorry son, what where yous saying me za’a zuba maka’’
Ba tare da ya dago kanshi ba murya a kasa ayce ‘’anything’’
Kallonshi ammah tayi kafin ta maida dubanta ga amra tace ‘’daughter bismillah, kiyi serving dinshi’’
Dago da idanunshi yayi ya kalli ammah kafin ya maida dubanshi ga amra dake shirin miqewa, wani irin kallo ya watsa mata mai wuyar fassara daya sata tsorasata sosai kafin ta kauda kanta gefe, duk wannan kallon da yake mata akan idanun ammah, batace komai ba ta zuba msu idanu tana karantar relation din tsakanin su da yanda suke treating juna, cikin ranta tace ‘’waiii akwai gyara,’’
Jiki amace amra ta miqe ta soma serving din ammah, saida ta zuba mata kafin ta matso wajen da yake, tunda ta karaso kusa dashi kamshinta ya shige hancinsa, hade rai ya sake ya kauda kanshi gefe hart agama serving dinshi, tana gamawa ta karaso kusa da aman tace ‘’mey za a saka maka?’’ dagowa amar yayi ya bita da idanu da wanda take ma Magana, take ranshi ya baci jin ta tambayi wani chan daban shi dake ta rainashi bata tambayi abunda yake buqata ba,lallai zai gyara mata zama, wani irin tsaki ya buga wanda yasa duk suka juyo suka kafa mashi idanu harda ammah, amra dai wani iri tashi don tasan saboda ita yake wannan abun, aman kuwa girgiza kai kawai yayi yace ‘’thank you sister zanyi serving kaina’’ yana kaiwa nan ya janyo plate ya deba yanda zai isheshi, tana ganin haka ta koma seat dinta ta janyo plate ta deba kadan kafin ta fara ci anatse, duk ta zama so unconfortable gaba daya, ta chan kasa ta soma jin kafarta
na kaikayi, da sauri ta zura hannunta kasa don tabo wajen, da sauri amar ya dago jin saurkar hannunta kan kafanshi, kasa hadiye abuncin bakinshi yayi ya kalleta akausashe yace ‘’whats the meaning of that?’’ dagowa duka sukayi daga ammah har aman suka zuba mashi idanu don sanin abunda ya sashi Magana,da sauri amra kuwa ta cire hannun don bata san kan kafanshi hannun nata zai sauka ba, tsaki kawai yayi ya miqe tsaye ya fuce daga dining din, amra dai jikinta har bari ya soma yi don tsoro, yana fuce wa ammah tace ‘’daughte is everything okay?’’ kasa dagowa amra tayi sai girgiza ai da tayi, abuncin ma baifi loma uku kawai ta iya kaiwa bakinta ba har suka gama ta soma kwashe plates din zuwa kitchen, da sallama ta shiga ganin lantana a tsaye, bin kitchen din ta soma yi da idanu, kitchen din ya hadu sosai don babba ne kamar daki, babu abunda babu acikin kitchen din na amfani, lanatana na hangota tayi saurin juyowa tana gyrara zaninta adan fugice tace ‘’laa ay da kin barshi yanxu zan zo na kwashe’’ kallonta amra tayi bata kawo komai aranta ba don haka tace ‘’ba komai zan iya ay’’ tana kawai nan ta karasa gaban sink ta ajiye, kafin ta koma dining din, ammah dake shirin fucewa daga dining din ta kalleta tace ‘’daughter barshi lanatana will take care of that, zo muje sitting room muyi fira’’
Yanda ammah keyi mata kamar ba surukarta ba, janta take kokarin yi sosai a jikinta don kwata kwata bata dauke ta amatsayin surkulle ba saidai ya kamar yanda ta dauki amar a matsayin da.
Sitting room suka zauna ammah ta janyo mata album dake cikin kasan tv unit, karasowa ammah tayi kusa da ita ta zauna tace ‘’zo daughter na nuna maki hotunan tarihi’’ cikin zumudi amra ta matso kusa da ita ta zauna, album din ammah ta bude ta soma mata bayani, kallon cute picture din amar ammah tayi don hoton ne a farkon album din kafin tace ‘’wannan mijinki ne, bazan manta ba ranar da aka dauki hoton nan, awanshi biyu a duniya, he was a very calm baby baya kuka kwata kwata, but idan ya fara kukan yunwa saikinyi mamaki, baya jurar yunwa’’ dariya amra tayi ammahma dariya tayi sosai kafin ta cigaba,’’shiyasa yanxu nake mamakinsa sosai yanda baya son cin abunci yanxu, dear saikin dage sosai fah’’
Kasa dakai amra tay I don taji kunyar maganar ammah, wuce hoton ammh tayi kafin tace ‘’wannan shine mahaifin muhammd, kinga kammanin su ko? Mutane suna cewa wai sunfi kama’’
Dariya amma tayi ta kurama hoton idanu kafin tace ‘’ammah yafi kama dake gaskia’’
Murmusawa ammah tayi ganin ta dan fara sake yi kafin tace ‘’ahh toh nima dai haka nace, ni kwashe min kyawu na ma yayi’’
Dariya sosai amra tayi don shes enjoying the conversation sosai, gashi daman yanxu ta samu experience din laraba na saurin sakewa da mutane, haka ammah ta dunga bude album din tana mata bayani, duk wajen da ya bata dariya kuwa haka zata kyakyace da dariya, suna nan zaune amar ya fito, basu ma ji tsayuwanshi ba a bayansu ya kafa masu idanu, yanda suke hira suna daiya sosai sai abun ya bashi mamaki sosai, daga dan nesa chan yace ‘’ehmm’’
Waigowa sukayi gaba daya su suka zuba mashi idanu, ‘’son harka fito’’ ammah ta fada tana kallonshi, anatse ya soma Magana ‘’eh, ammah please kisa agyara min bedroom dina’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’okay son, kwana biyu nina hana lantana shiga dakin naka saboda youre now a married man’’ ta karashe tana kallonshi tana murmushi, hade rai kawai yayi yace ‘’saina dawo’’
Kafin ya fuce, nunfasawa ammah kafin ta maida dubanta ga amra tace ‘’daughter jiya na tambayeki