nata ya dan bata slow peck kafin ya zare bakin shi “mai bakin rashin kunya” ya karashe yana sauke wani lausasan murmushi wanda ya Kara ma fuskanshi mahaukacin kyau sosai kamar bashi ba, lumshe idanunshi yayi har barci ya sauke shi mai dadi sosai.
Salima na gama yankan fruit ta wuce sama don takai mata, tana hawa sama taga wayam, bakin toilet dinta ta tsaya tace “adda??? Kina toilet ne? Ga fruits din”
Jin shuru yasa ta cewa “adda!” Still babu response, da sauri ta Bude kofar nan ma wayam, haka nan ta juya ta sauko kasa ta wuce kitchen, ammah dake sauke tukunya tana ganin ta shugo hannunta dauke da bowl din fruit din data futa dashi tace “ah ah ya kika dawo dashi ko bata so ne?”
“Ammah naje ban ganta ba, na duba ko’ina”
Dan shuru ammah tayi kafin ta dan murmusa tace “ajiye mata a fridge zata sha anjima”
Gaban fridge salima ta bude ta saka bowl din don itama sai a lokacin ta tuna taje wajen ya Muhammad, dariyar keta ta danyi kafun ta dan basar saboda ammah na wajen.
Suna cikin shirya abuncin warmer Aman ya shugo kitchen din yana hamma, da sallama ya karaso ya gaishe da ammah kafun yace “ammah!!! meysa kika shugo kitchen ya kamata ace kina hutawa ne saboda baki gama recovering ba”
Murmusa ammah tayi ta kalleshi cikin kulawa tace “son na samu sauki fah, kuna shagaltani da yawa shiyasa naqi biye muku kaida son, Ay gwara na fito saboda na dunga exercising jikina, bayan wannan ma my baby tana buqatar helping hand tunda ku bakwa taimaka mata”
Ta karashe tana kallon salima dake smiling kamar mimi kafin ta kalleshi ta watsa amshi harara, shima hararar ta yayi, ammah na kallonsu tana murmushin jin dadi sosai, “wannan mara kunyan babu wanda zai taimaka mata”
Ya fada yana kallon salima yana zabga mata harara
Turo baki salima tayi ta rike kugu ta kalleshi “niba Mara kunya bace yaushe nayi maka rashin kunya ?”
“Bani kika yima ba, baby na kikayima” wani irin maqoqon baqin ciki ne ya turnike ta Har batasan lokacin datace “ah ba baby ba Ka manta feeder ce”
Kallonsu ammah tayi kamar tohm and jerry yanda suke ma junansu, “nidai aurar daku zanyi na huta inkunje chan saiku karata ba a gida ba”
Tabe baki Aman yayi ya bude fridge ya dauko ruwa yana shirin balle karfin yace “chapp ammah dawa zaki hadani? Wannan ? Badai niba ni inada wadda Zan aura”
A harzuke salima ta kalleshi da idanunta da suka kawo ruwa tace “nima inada wanda nake so,”
“Toh ya isa haka nan, kowa Zan bashi wanda yakeso tunda bakwa son juna,”
Ammah ta fada fuskanta na nuni da she’s serious, kallonta Aman yayi kafin ya dan sauke murya yace “nifa ba Yanxu zanyi auren bafa ammah”
“Meysa ba yanzu ba ga dan uwana nan da matanshi, kaima aurar dakai zanyi very soon acikin shekarar nan ka fadama babyn taka anytime za a turo”
Dan jim yayi kafin ya dan dago idanunshi nan take ammah ta kashe mashi ido daya,nan ya hasko abunda take shirin yi, dan murmusawa yayi ya soma magana trying to go along, “Toh shikenan ammah Zan mata magana, sai aje ayi tambaya ma kawai” ya karashe ba tare da ya kalli inda salima ke tsaye ba,
Salima dai kafafunta gagarar daukanta sukayi don haka Tayi saurin fucewa tana hawayen takaici.
Tana futa amma ta kalleshi, “ son!! Kaifa yanxu ba yaro bane, basai an fada maka yanda yarinyar kirki ke sonka ba, man up and stop all this childish act Ka daina wahalar min da yarinya, seat her down and talk to her in a cool manner, okay??””
Kanshi a kasa ya amsata “Insha Allah ammah na”
“Masha Allah, Allah yyi maku albarka baki daya”
“Ameen” ya yi saurin amsata kafun ya taimaka mata suka fito da warmers zuwa dining.
Salima na hawa sama tasha kukanta tana dana sanin shegen Jan aji data dunga yi mashi gashi yanxu ya kubce mata, son da take mashi bata jin yayi mata irin shi, “Wallahi yaya bazaka auri kowa ba saini” ta fada tana hawayen takaici.
Bangaren su amra Basu farka ba sai wajen karfe uku na rana, shine ya fara bude idanunshi ya sauke su akanta, gaba daya ta nannadoshi kamar mage ta kudundune shi, saida ya dauka kusan minti biyar yana kallonta, kumatunta daya kara zama fluffy yajaa kadan kafun ya kauda kanshi ya soma kokarin zame jikin shi daga nata ahankali.
Kokarin riko towel dinshi yayi saidai yanda ta kwanta a jikinshi dole saidai ya bar towel din, haka kuwa yayi ya akai towel sun don baya son tashin ta,juyawa yayi ya dan tsaya yayi miqa jikinshi na murdewa sosai, ahankali ya soma tafiya majestically, daidai nan ta bude idanunta da sukayi luhu luhu karaf ta sauke su akan naked bodynshi daga bayanshi zuwa ga structure dinshi, da sauri ta runtse idanunta don batayi expecting Ganin haka ba daga tashinta daga barci, kamar munafuka haka ta soma bude idanunta akaro na biyu ta sauke akanshi lokacin har yakai wajen kofar bathroom zai shige, kasa sauke idanunta tayi daga kallon jikinshi, he’s so hot, skin dinshi fari tass babu tabo, ga kirarshi so sexy, saida ya shige bathroom ya dawo hayyacinta ta sauke ijiyar zuciya kafin Tayi saurin mikewa ta gyara towel dinta dake neman zamewa ta janyo hijab dinta ta zura shi ta fuce daga dakin cikin sassarfa don wata irin yunwa ce ta tashe ta daga barcin.
Cikin sassarfa ta hau sama don bata son amah ta ganta, saida ta shiga cikin daki ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya tana haki kamar wadda za a kama, toilet ta wuce direct ta dauro alwala don an kira sallar la’asar.
Bangaren salima saida ta shaqi kukanta son ranta kafin tayi wanka, tana futowa agurguje ta sauya kaya tayi sallah ta fito kasan jiki a mace, idanunta sun kumbura sosai alamun kukan datayi sosai,
Kasa ta sauko ahankali tana tafiya tunaninta ya gushe harta shiga kitchen , ganin ko’ina tsaf yasa taji wani iri don tama manta aiki sukeyi ita da amah ta gudu sama saboda takaicin aman, fridge ta bude ta janyo pack daya na hollandia bata ma san shi ta dauka ba don tunaninta ya gushe, damuwar da soyayyar aman na burkita mata lissafi harta fito daga kitchen din ba tareda tana kallon gabanta ba, hanyar stair ta nufa tana tafiya kanta a kasa, buge kafarta tayi da karfen handrail, da sauri tayi baya ‘’wash allah na’’ ta furta ahankali, dan dukawa tayi tana kokarin duban kafar tata,
‘’dan allah ayi min Magana da hajiya’’ labaran dake zaune tun bayan saukowanta ya hangota daga nesa harta shige kitchen ta fito, daman ya dade a zaune yana jiran wanda zai sauko dan yayi fada ma hajiya yazo, har cikin kwanyarta taji muryarshi, anatse ta soma dagowa, tana shirin waigawa inda taji muryar aman ya sha gabanta, yanda ta ganshi a gabanta ba zato ba tsammani yasa gabanta faduwa cikin tsiwa tace ‘’meye haka kuma,’’
Yanda suka saba cikin kwanakin idan suka hada hanya yawanci harara ce ke biyo baya saidai yanxu taga akasin haka don murmushi yake mata, sauke kanta kasa tayi tana tausayin kanta don ya maidata as a joke, don haka ta nemi giftawa ta gefenshi, hannunta ya rike in a calming tone ya soma Magana ‘’sorry for what I said earlia idan ya bata maki rai’’
Dan dagowa tayi ganin yanda ya marairaice, kauda kanta ta sakeyi tare da zame hannayenta tace ‘’bakayi min komai ba’’
Hannun nata ya sake kamawa ya bude tafin hannunta ya dora mata leda akai kafin ya juya ya wuce dakinshi, kallon ledar tayi kafin ta wuce sama itama, labaran dake zaune yana kallon ikon allah harsuka bar wajen.
Salima na haurowa sama har zata wuce daki ta tuna da maganar mutumin dake zaune a kasa, dakin amah ta wuce ta sanar mata da wani yazo yana kasa kafin ta futo ta wuce dakinta ta bude ledar daya bata, bunch of chocolate ne a cikin ladar hade da apology card a ciki, dukda taji dadin kyautar hakan baisa ta tabe baki ba tana tausaya ma kanta.
Saukowa kasan amah tayi cikin mutunci, anatse ta karaso har cikin sitting room din ‘’lale maraba, malam labaran sannu da zuwa’’
Zama tayi kan kujera tana fuskantarshi, yana zaune akasa ya dukar da kanshi ‘’ina wuni hajiya, ya karfin jiki, ashe bakiji dadi ba, nazo shekaran jiya ay baba mai gadi yake fada min, allah yasa kaffara ne’’
‘’ameen ya allah malam labaran, ay naji sauqi sosai, ya noma? Kwana biyu baka zoba’’ amah ta fada tana kallonshi
‘’wallahi nayi rashin lafiya ne tsawon wata guda hajiya shiyasa na kwana biyu ban zo ba’’ malam labaran ya fada cikin girmamawa
‘’subhanallahi shine baka kira ka fad aba labaran’’ amah ta fada in a concerning way.
‘’ay naji sauqi sosai hajiya, allah ya kara arziki da lafiya’’
‘’ameen ya allah’’ amah ta amsashi
‘’kun gaisa da mutan gidan kuwa?’’ amah ta tambayeshi tana kallon gefensa
‘’eh mun gaisa da yallabai na dubai,don tare mukayi sallah a masallaci ma, dan uwansa ne dai bai lura dani ba lokacin daya shugo’’
Malam labaran ya karashe yana sunnar dakai
‘’madallah, ay kwanaki inataso na fada maka yayi aure ma’’ amah ta fada tana murmsuhi
Cikin fara a malam labaran yace ‘’masha allah , allah ya sanya albarka, ya kade fitina’’
‘’ameen ya allah ya aikin gona’’ amah ta tambayehsu anatse
‘’ay sai godiyar allah hajiya, tun shekaran jiya naso na kawo kwasar wannan shekarar, an samu buhu talatin na shinkafa, buhu ashirin na masara’’
‘’ahhh madallah, allah yasa albarka, akai kasuwa kawai’’
‘’toh shiknan hajiya’’
Sun danyi hira kafin yayi mata sallama ya wuce bayan ya kara yi mata godiya akan abubuwan datayi mashi.
The next day…
Da sassafe amah ta wuce dakin amra don ta shigo da asuba ta sanar mata da wuri zasuje asubiti don bata son amar ya sani saboda zai iya suspecting wani abun ko yace zai bisu don haka ta shaida mata da wuri zasu fita.
Da sallama amah ta bude dakin, a kwance take cikin shiri don saida tayi wanka ta shirya barcin nata yazo mata, takowa har inda tae amah tayi tana murmushi, ‘’wannan jika nawa akwai barci’’ amah ta fada tana murmsuhi,
Dafata amah tayi ‘’daughter, tashi muje ko’’
Bude jajayen idanunta tayi ta sauke su akan amah kafin ta miqe da kyar ‘’good morning amah, harkin futo’’
‘’yes dear muje kar muyi latti’’
Atare suka sauko amah naga ba amra na biye da ita, sanye suke da abaya gaba dayansu, tasha stone tundaga sama har kasa, sai colors din daya banbanta, amah na rike da wata haddaiyar handbag mai shegen tsada ta manyan mata, fuskanta da farin glass mai kara kwarin idanu tayi masifar kyau, hausawa sunce lafiya uwar jiki kana ganinta kasan ta samu sauyi sosai a rayuwarta compare to lokacin da take yawan rashin lafiya, ramar datayi ma kara mata kyau tayi sosai, inka ganta bazakace ta haifi amar ba kwata kwata, skin dinta sai glowing yake daman ga haske ga kyau duk ta hada don a jikinta amar yayi gadon komai, amra dake gefenta ma tayi kyau sosai dukda gama daya kana ganinta kasan tana jin jiki.
Inka gansu yanda suka fito atare cikin abaya zaka dauka sisters ne saboda amra nada jikin girma sosai fuskanta ne kawai ke nuna kankantar shekarunta, sai kuma amah in ka kalli fuskanta ta zaka ga ta manyanta dukda manyancen nata bai futo sosai ba, she’s looking so beautiful and young kamar ba ammah ba, bata da damuwar komai ayanxu sai ta iyalinta don yanxu ita kadai ta rage masu gaba dayansu.
Duban agogon dake maqale a hannun ta tayi ganin kusan bakwai da rabi yasa tace ‘’daughter ay bazamu jira driver bama ni zanyi driving dinmu’’
Murmushi amra tayi tace ‘’toh ammah’’ kafin tabi bayanta har suka karaso inda motoci suke, da sauri baba mai gadi yazo ya gaishesu gaba daya kafin amah ta bada umarnin ya cire car cover din motarta don it has been long tayi driving tun bayan rashin lafiya data farayi,
Baba mai gadi na bude cover motar amah saida na kalla na sake kalla, wata bugaggiyar range rover ce rr2023 white color, fadin irin haduwar motar bata lokaci ne da alamu ma sabuwa don kamar ba a shiganta,
Motar ma gaba daya smart car ce, don bata danna key din motar ba kofar ta bude ta, amra dake biye da ita ma tana tsayuwa motar ta bude da kanta, anatse ta shige gaban motar ta zauna.
Saida amah tayi warming motar kafin tayi revarse ta juya, nan securities suka bude gate suma suna kwasar gaisuwa kafun su fuce daga gidan.
International specialist hospital…
Daidai wani haddadden asibiti amah tayi parking, amra na kwance tana barci batama san sun iso basaida amah ta tasheta, bin asibitin ta sma yi da kallo, ya hadu sosai har yafi wanda aka kwantar da amah.
Atare suka fito amah ta taimaka mata wajen rike mata hannu don she looks pale and weak,har suka shiga cikin asibitin .
Suna shiga amah ta barta anan reception ta wuce wajen receptionist ta bude mata file, cikin yan mintuna kalilan ta gama yi mata komai har tayi booking appointment.
Tana gamawa ta dawo ta taimaka mata ta mike suka wuce wajen vips don anan zataga doctor, idan lokacin appointment dinsu yayi daman by 8am dctor zaizo.
Zama suka danyi har doctor yazo, nan ma saida amah ta taimaka mata suka shiga har office din doctor, fadin irin haduwar wajen ma bata lokaci ne don ya fita daban a cikin asibiti, don ana kiran wajen da presidential root lol, zama sukayi inda doctor yayi welcoming dinsu kafin amah ta soma mashi bayani, a bayanin da amah tayi mashi saida ya tsaya y agama sauraron ta kafin ya soma Magana ‘’well hajiya ance komai na allah ne inda rai akwai rabo, we have a lot of patients muma anan nigerai waenda sukeda ospermia kamar aynda kikayi explain mujinta nadashi, kuma cikin ikon allah zakiga basu da kwayayan haihuwar cikin ikon allah zakiga allah ya akwo wata hikima allah ya basu haihuwar, yanxu ayanda kikayi bayanin yanayinta it obvious shes preg, but zamu mata blood test baya daukan 10mins result ke fitowa don munyi upgrading facilities dinmu na nan, sannan zanyi mata scanning yanxu so that we can know how far she has gone then after that sai muyi tunanin wani irin medication zamu daurata.
Murmushi amah tayi tace ‘’okay tohm’’
Kiran wata nurse doctor yayi don ita zata taimaka mashi tana shugowa office din ta ajiye abubuwa test data dauko daga mini lap dinshi dake cikin office din, nuni yayi mata da amra yace ‘’overall blood test za ayi mata yanxu but ina buqatan pregnancy test immidiately’’
‘’okay sir, it will be ready in 5 mins;’’
‘’okay thank’’ ya amsa nurse din, gaban amra ta karasa ta soma diban jininta tana gamawa ta ta wuce general vip lap don tayi running test din daya buqata, cikin mintuna biyar saigata da result har biyu, karba doctor yayi, tunda doctor yak araba gaban amra ya soma bugawa pat pat, ammh kuwa babu abunda take
sai murmushii tana godema allah don tasan ma mai zai buyo baya, bayan doctor ya gama karantawa ya kalli amah fuskanshi dauke da murmushi yace ‘’hajiya congratulations, shes 5 months and 3weeks pregnant, by next week zata shiga 6months zata fara zuwa antenatal, sannan akwai magungunan da ya kamata ta dunga sha don jininta is very low shiyasa take zama weak,’’
Tunda ya fara Magana amra kebin bakinshi da kallo gabanta na faduwa, yanxu itane ake cewa tana da ciki? Cikin ya muhammd?
Bangaren ammah kuwa Fadin irin murna da farin cikin da take ciki a wannan lokacin bata lokaci ne karshe ma bude Jakarta tayi ta zaro bundle din kudi yan dudu dubu guda uku ta ajiye akan table din doc tace ‘’wannan tukwicinka ne for this good news, I’m sure idanda agaban mijinta kayi breaking wannan news din abunda zai baka saiyafi wannan ma, but ayi managing wannan’’
‘’no hajiya ia cant take it’’
Kaste amah tayi ‘’I insist,’’
ta karshe tana hamdala, hannun amra ta rike tana kallonta ta fara zabgo mata albarka,’’allah ya shi maki albarka daughter, allah ya saukeki lafiya, allah ya biyaki da gidan duniya kin gama yimana komai, youre a blessing to us dear thank you so much’’ hawaye ne suka soma zubowa akan fuskan amah itama kukan takeyi sosai tana rungume amah, saida sukayi mai isarsu shiko doctor don farin ciki shima yak washi kudin da aka bashi ya ajiye a locker shi.
Saida komai yadan lafa doctor yace ‘’yanxu scan zamuyi ko? At this time zaku iya sanin gender of the baby ma’’
‘’no doctor, bazamuyi ma allah shishigi ba kuyi scanning din kawai it’s a gift from allah so we want to keep it basai munsan komai ba ta hanyar yima allah shishigi’’
Dariya doctor yayi yace ‘’toh shikenan hajiya, zan duba lafiyan babyn kawai’’
Mikewa yayi ya nuna ma amra kan gadon da zata zauna anan office din nashi kafin ya janyo scanning machine, anatse ya soma observing cikin nata saida ya dauka kusan minti goma kafin ya mike ya dawo saet dinshi, amra ma mikewa tayi dakyar don tana jin kamar karta tashi ta kwanta tayi barcinta.
yan rubuce rubuce yayi a laptop ammah dai na zaune tana kallonshi, saida ya gama ya dago a kallesu su duka,’’she is having a healthy baby, the breathings are nomal, babyn yana inda ya kamata,’’
‘’toh likita banga bumps ba? Kuma naji kace ta kusa wata shida’’ amah ta tambaya
‘’yes that is not a problem yanayin jikinta Kenan, baya nuna bumps din, mostly matan yanxu haka suka fi so saboda basa son suyi teba da stretvh marks but intakai 8 months definitely she will be very very heavy