where saika fada min dalilin kaini asibiti da kayi”
Azafafe ya miqe yayo kanta yace “who d hell do you think you are da Zance kiyi abu ki qiyi huh” ya fada jikinshi na karkarwa alamun yana cikin bacin rai, take taji tsoronshi na durar mata tayi saurin dakewa tana jaa da baya tace “I’m going nowhere saika fada min dalilin da yasa ka kaini asibiti?“ ta karashe tana sauke nunfashi da karfi don a tsorace take dashi, bata gama shiga furgici ba saida ya damke hannunta kamar zai balla yace “don’t act dumb, I don’t have to tell you the reason why I take you to the hospital,”
Hawayen dake maqale a idanunta ne suka sauko don tana jin zafin riqon da yayi mata, “inkinsan what has been going throug my head, and my mind bazaki yi gangancin zuwa inda nake ba,this is my last hope my only last hope, shikenan, and you have to guts to stand in front of me trying to question me? Are you insane”
Yanda yake magana gaba daya kamar bashi ba ya gama futa hayyacinshi, jikinshi na rawa kamar wani zaki,kuka ne yaci karfinta don yanda ya damke hannunta kamar yana venting anger dinshi a wajen, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun ta fara furtawa, flower vase din dake gefensu ya wurga gefe da karfi da kafanshi Har kafan ya soma fidda jini,damko ta ya sakeyi ya hadata da bango kamar wani marayan zaki ya daka mata tsawa da ya kusa sata fitsari anan tsaye, yace “why did you even enter my life why??????, idan nasan this will cause me so much pain da banyi raising hopes dina ba harna yarda na aureki”
Yanda yake magana da yanda fuskanshi ta karashe ta janza dole ya baka tausayi, don fada yake out of anger da hidden pain, ya kwallafa rai sosai, he wants to have his own blood, idan ya tuna da ammah sai yaji he’s like a disappointment, tana son ganin Jininshi yanxu shikenan bazai taba haihuwa ba, runtse idanunshi trying to vent his anger somewhere don yasan yanda yake da zuciya shiyasa ya koreta taqi fita, bai gama tunani ba yaji ta rungumeshi tsam
tana kuka, Sai a Lokacin ya Lura da yanda ta furgice sosai, Har ta fishi shiga furgici da tashin hankali,kasa motsi yayi don kamar ta cire mashi damuwa haka yaji,runtse idanunshi yayi trying to calm him self, sun dauka kusan 10mins a haka kafin yace “Aisha!!!” In a calming tone, cikin sheshekar kuka ta dago ta kalleshi, kallon juna suka fara yi na kusan minti biyu kafin yace “let go”
Shuru ta danyi saida yace “get your hands of me”
Da sauri ta cire hannunta don kwata kwata bata cikin natsuwarta, kamar me layi haka ya Taka Har zuwa gadonshi ya zauna tare da dafe kanshi, kafin ya dago yace “amfanin ki ya kare a wajena, so I will free you”
Gabanta ne ya bada damm, Sai a lokacin ta tabbatar da abunda yake zargi, ya aureta ne saboda ta dauka cikinshi ta haifa mashi ya saketa, wani irin takaici bakin ciki ya tsaya mata arai, bata taba jin zafin da take ji kamar yanxu ba ko alokacin da ya kusanceta abun bai tsaya mata ba Sai yanxu,saurin share hawaye ta tayi ba tace “Wallhi ko zaka kashe ni I have to say this, you’re so selfish, ka aure ji ne daman saboda kamin ciki na haifa maka ka dauke?,”kuka ne ya kufce mata tayi saurin fucewa daga dakin, binta yayi da idanu harta fuce, tsaki yayi ya dafe kanshi don shi wannan ba matsalarshi bace yanzu.
Amra kuwa tana shiga dakinta ta rufe kofar ta zauna nan bakin kofar tana kuka mai cin rai, yanxu ta gama concluding komai, shiyasa bai fada mata dalilinshi na aurenta ba, daman abunda ya shirya kenan, don ya dirka mata ciki ta haifa mashi ya saketa sannan ya rabata da abunda ta haife, how could he be this selfish”
Saida tayi kuka mai isarsa ta kira haifa ta shiada mata komai, ba karamin tashin hankali haifa itama ta shiga ba, da kyar ta lallabata ta sakko kafin sukayi sallama akan zatazo saisu zauna don sun tattauna don wannan babbar magana ce.
Duk wannan abun da amra keyi bata kawo dalilinshi na yin haka ba, abunda ke damunta kawai shine abunda yayi mata wanda ta dauki hakan as selfishness.
Nigeria….
Kwanan meeda biyar a kauyansu, wajen kakannin ta kullum tana kunshe a gida hankalinta a tashe ta kashe wayanta don tasan za a iya traking dinta gashi bata san yanda zatayi ba, haka Duk dare zata fita bakin layi wajen masu chargy ta karbi Aron waya don tayi kira, gashi kauyan babu atm card sai an fita wajen gari, a cikin kwanakin nan meeda taga ainahin rayuwa ta chanza ta koma kamar wata jaka, fatarta Duk ta sauya saboda babu cream da take dan gogawa, hatta cimarta ta chanza.
Babu abunda yafi tayar mata da hankali kamar layin Amar da baya shiga Idan ta kira,kullum ta zauna saidai tayi kuka ta godema Allah don ta saka rayuwarta shikin hadari garin taimako.
Asad Ma yayi kiran line dinta yafi sau Nawa kullum a kashe,karshe dai ya fara sensing wani abu, ba tare da ya shaida Ma Amar ba ya fara buncike akanta, nan
ya gano ganinta na karshe da akayi tare da alhaji kabiru ne kafin ta gudu wanda hakan ya tabbatar mashi da guduwa tayi kuma ta samu wani abun dan gane dashi alh kabiru, da kyar ya samu wannan information daga wajen kawarta da itama guduwa tayi don mutanen alh kabiru sun mata illa sosai don saida ya basu umarni su mata duka saboda ita kadai ce kawar meeda da aka sansu tare kuma yana zargin tasan inda take don haka ta tattara ta gudu itama don Idan ta zauna zazu kashe ta a banza.
Hankalin alhaji kabiru ba a karamin tashe yake ba,don Idan asirin shi ya tonu a duniya Akwai matsala babba, abunda yafi tayar mashi da hankali shine a binciken da yayi shima na mutanen da tayi muamala dasu cikin kwanakim ya gano ta hadu da amar da wani babban soja wanda abun yayi mugun bashi mamaki kuma ya daure mashi kai, yasan Amar baya neman mata balle yayi tunanin ko neman ta yake don ita a cikin bariki take, bai kawo Amar na zargi shi ba ko yana kokarin amfani da ita don sanin wani abu don babu wani alamu da amar ya nuna yana zarginshi, abu daya ne ke tayar mashi da hankali, wato tunanin Kar tarihi ya maimaita kanshi don haka ya dauki damarar duk abunda zai biyo baya a shirye yake da Duk wani abu dazai tunkaro shi alhaji kabiru hatsabibi ne mai yana aikin shi ta karkashin kasa ba tare da kowa ya zargeshi ba,abunda yafi damunshi yanxu shine abokin harkallar sa wato alif da baya samun shi kwata kwata,saida ya tuna da alif yayi wani tunani kafin ya danyi murmushi yace “yaro yaro ne, yaro kana wasa da wuta”
Drivern shi dake gefenshi ya zuba mashi idanu don gani yake kamar oganshi na gab da zaucewa don suna cikin mota yake wannan surutan nashi.
Taura estate…
Driver na parking yayi saurin fitowa ya budewa alhaji kabiru kofa, yana fitowa ya rufe kofar ya zubama alhaji kabiru idanu don yayi gaba, murmushi kawai yayi ya juya wajen masu gadi ya zauna.
Tunda alh ya shugo cikin parlor amma dake zaune ta zuba mashi idanu,ganin yana magana da kanshi, kallonshi tayi tace “barka da dawowa, ka shugo babu sallama hope dai lafiya”
Wani irin kallo ya watsa mata yace “lafiyarce ta kawo haka”
Ganin haka yasa ta jaa Bakinta tayi shiru don wannan ne karo na farko data ganshi a hargitse sama ya wuce tabi bayanshi don daman tana jiran dawowan shi don jin lafiyar aman don kusan kwana biyar kenan rabonta dashi kuma last time da sukayi magana yace mata zaije wajen dady, tana shiga dakin ta taddashi tsaye yana safa da marwa, kallonshi tayi ta sauke murya tace “alhaji is something wrong? Wani abun na damunka ne”
Bai kula ta ba saida ta sake cewa “dan Allah kamin bayani ko wani abun na damunka”
Juyowa yayi azafafe yace “woman please stop asking me silly questions, tunda kika ganni haka kisan bana cikin kwanciyar hankali so stop asking questions, ki fadi abunda ya kawo ki”
Shuru ta danyi kafin tace “daman Zan maka maganar Aman ne yau kwana biyar kenan rabon shi da gida kuma wayarshi baya shiga, jiya na maka magana kace zai kira yau,dan Allah ka fada min inda ka tura shi”
Kallonta yayi babu was a fuskanshi yace “menene matsalarki da da inda yake? Why do you care? Ko isarsa data haifesa sai haka, bari kiji nine ubansa kuma Nike iko dashi, yau ko bangon duniya na kaishi Na aje ba damuwar ki bane don haka kiji da abubuwan da gantalallan danki keyi acahn wata kasa daban da kike ganin babu wanda ya kaishi natsuwa kafin ki damu da ta dana”
Mamakin abunda yake fada ta soma yi, saidai bata kawo komai ba don tasan Idan yana cikin fushi babu irin maganar da baya yaba wa don haka cikin fada itama tace “da aman da amar Duk yaya ne, babu banbanci kuma dole na damu da su duka,and inason ka sani ada chan Idan kana aibata amar bana cewa komi, yanxu kuma abun ya fara yawa, ka dunga gyara harsheka”
Wata yar bazawarar dariya yayi yace “saboda Nace gantalalllan dan iskan danki shine kike tada jiniyoyin wuya Maryama? Kinyi trusting dinshi da yawa shiyasa bazaki san komai b
Yana kaiwa nan ya wuce bathroom ya barta tsaye cikin mamakin Kalamanshi akan amar.
Dakinta ta wuce tana nazarin abubuwa da dama,bata taba zargin amar ba ko sau daya saboda tasan irin tarbiyar datayi mashi dukda yawanshi Rabin rayuwarshi a dubai yayi ta ba akan idanunta ba, saidai kalaman alh kabiru sun tsaya mata sosai arai,tunani ta fara yi take ta tuno lokacin da taji kuryar mace lokacin da suke waya, bata son zarginshi saidai zuciyarta Raya mata wani abu, Toh kodai amar ya fara bin mata ne? Da sauri ta kauda zancen don tasan ba abu ne mai yuwu ba, zuciyarta ce ta fara mata wasi wasi da tunanin daban daban, na farko kalaman daddy don wannan ne first time da yayi magana akan amar makamancin wannan na biyu kuma muryar mace da taji a wayan Amar na uku tunawa da yanda baya son Idan tana mashi maganar aure da yaya, innalillahi kawai take furtawa, bata son zarginshi da komai saidai dole ta tambayeshi kodan zuciyarta zata samu peace, Kiran line dinshi ta fara yi harta katse bai dauka ba, sake kira tayi nan ba shuru aje wayar tayi don tasan tabbas inyaga call din zai kira, haka nan ammah ta wuni cikin damuwar Aman da amar, dukda na amar yafi damunta don this is the first time ta kirashi bai kirata back ba komi dare, washe gari Ma haka ta dunga zuba idanu shuru bai kira ba nan take hankalinta ya sake tashi, line dinshi ta sake kira still
Ba ayi picking ba kusan missed call biyar harta hakura ta Har wayan ta barma Allah komi saidai abun yayi mugun daure mata kai sosai.
Bangaren Amar aranar dai bai samu natsuwa ba don Har zazzabi saida ya rufe shi, tunda ya kwanta a daki, saida ya wahala sosai kafin ya kira m5 ya kawo mashi doctor ya dubashi.
Washe gari Ma haka ya wuni sukuku babu natsuwa yayi kokarin danne wa don Duk a tunaninshi abun zaizo mashi da sauki saidai hakan bai samu ba.
Wayarshi kam tunda ya aje ta gefe lokacin da zazzabin ya dameshi bai sake bi takanta ba.
Bangaren amra kuwa damuwa ta saka aranta da ya janyo mata ciwon kai sosai, kuka dai kamar ruwan jikinta zai kare don bata rabo dashi don kukan Ma Harda Mara dalili takeyi saidai Idan ta tuna abunda ya mata saita godema Allah da yasa babu cikinshi a jikinta don bata san ya zatayi ba Idan da ace ta dauka cikin nashi, nan tayi alqawarin fita daga alamuranshi Har ta samu ya saketa tabar mashi rayuwarshi,aranar dai ko fitowa daga daki batayi ba abunci Ma saida nadine tazo dubota ta kawo mata yanda ta barshi kuwa haka ta dawo ta daukeshi.
Washe gari haka ta shirya ta sakko ta wuce aiki don yanxu tayi alkawarin maida hankalinta wajen abubuwan daya shafi abunda ya kawo ta kasar.
After 2days…
Da sassafe ya Tashi ya shirya cikin kaki baima tsaya yin breakfast ba ya fuce daga gidan, m5 ne ke tuka shi yana mashi bayanin yanda abubuwa ke tafiya anan headquarters don an mama alif cikin sirri ba tare da sanin kowa ba harta hammam, tun akan hanya ya soma bin missed calls dake kan wayarshi, a hankali idanunshi ya sauka kan “sweet mum”
Runtse idanunshi yayi tunawa da abubuwan dake faruwa around him, he’s feeling so sad musamman Idan ya tuna da ita da yanda ta kwallafa rai akan son ganin jininshi saidia kana naka Allah na nashi sai mai tawakkali, tunawa da maganar aure da yake mashi yayi shi baima taba kawo matsalarshi zaisa babu macen da zata zauna dashi ba.
Saida ya shiga office ya zauna kafin ya danyi shuru kamar mai tunanin wani abu yayi dialing number ammah, ringing biyu ta dauka tayi shuru, shima shuru yayi ya kasa ce mata komi ahankli ya tattaro natsuwar shi yace “good morning ammah na”
“Muhammad lafiya dai? Ka tayar min da hankali, is there something that I need to know Muhammad?are you hiding something?”
Shuru ya danyi tare da runtse idanunshi yana jin wani irin zafi aranshi yace “ammah babu komi, I’m just sick ne kwana biyu, so sorry for worrying you”
Muryanta babu wasa tace “I will Not ask you again Muhammad ni mahaifiyarshi ce if you’re hiding something from me ka fada min”
Dan shuru yayi yana sauraron tone din datayi magana dashi yace “babu komi ammah Zan dawo very soon nanda 2-3days Insha Allah Idan na gama abunda nake yi anan”
Shuru ta danyi tace “Allah ya kaimu” kafin ta kashe wayan.
Wani iri yaji don harga Allah yaso ya fada mata tun farko saidai kuma yana jin kunyar yin haka don uwace ita bazai iya ce mata ga matsalar ba ta ospermia dake damunshi shiyasa yayi komai cikin sirri ba tare da saninta ba, don daman ya bari Idan Har cikin ya samu sai ya mata bayani daga baya.
Saidai jin yanda take maimaita mashi ya fada mata Idan yana da matsala yasa yaji wani iri aranshi.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 123
Haka nan ya karashe wunin ranar babu walwala, ga tarin ayyuka dake gabanshi da suka mashi yawa,ya kosa komai yazo karshe ya samu yayi freeing kanshi daga wannan dilemma din tunawa da ita yasa ya dafe kanshi, Sai yanxu Yake jin kamar maganganunta gaskia ne, he’s selfish saidai shi mutun ne shi mai magana kai tsaye don haka ya kauda tunaninta don yaji zafin yanda yarinya kamarta zata tsaya agabanshi ta fada mashi magana kamar haka, he don’t blame her anymore kanshi yake blaming don haka yayi deciding freeing dinta sannan alqawarin da yayi akanta da plans dinshi suma bazai janye ba zai hadata da kannenta.
Bai fito daga office ba Sai wajen karfe biyar, kasa ya sauko ya wuce inda m5 yayi parking kafin su wuce, tunda ya shiga mota ya dafe kanshi tunani iri iri na yawo akanshi musamman akan abubuwan dake revolving around, kamar wanda aka tsugula yayi saurin bude idanunshi, wayanshi ya zaro yayi dialing number asad, ringing saya ya dauka, gaisawa suka farayi kafin yace “any update kuwa? Did you call that lady?”
“Yes sir daman Ina ta son kiranta, I’ve lost track of her, a iya binciken da nayi ina ganin she has got something, and ta gudu because Ana bibiyarta, agurguje dai her life is in danger”. Asad ya karashe
Shuru amar yayi yana dafe kanshi dake mashi sara mashi sosai, bazai so wani abu ya sameta ba dukda don kudi Tayi hakan, bayan wannan bai gaba tsammanin daddy is this ruthless and dangerous ba,
“Lieutenant asad, please kayi kokari ka nemo ta before he gets his hands on her, Insha Allah I will be back on Thursday, kayi iya kokarinka, zanyi rounding up case din nan, before then”
Sallama ya mashi kafin ya kashe wayan ya dafe kanshi, kallonshi m5 yayi ta jikin mirror yace “sir are you okay? Or do you need to see a doctor”
Dago da rinannaun idanunshi yayi yace “no need for that”…. Resting kanshi yayi abubuwa da dama na yawo akanshi.
Suna isa gida ya wuce sama zuwa dakinshi.
Bangaren Amra tun bayan abunda ya faru ta cire komai aranta, dukda idan ta tuna da abun Sai Tayi kuka, kullum zata je aiki tana dawowa zata wuce daki, sai kuma washe gari,baya yarda kwata kwata ta hada hanya dashi, kullum yana kunshe a daki, nadine ce ke kawo Mata Duk wani abu da take buqata, wani lokacin idan ta shigo dakin zata taddata yana kuka, baya taba tambayarta dalilin kukan ba saidai ta baya hakuri ta tausasa ta, kwana uku kenan rabon data sashi a idanunta wanda hakan ba karamin relieve ya kawo mata ba.
Kullum Sai wannan number yayi mata message tun bata reply Har ta fara replying don sanin koma waye, bai boye mata koshi waye ba ya fada mata shine wanda Tayi treating dinshi a asibiti, Da farko bata gane shi ba saida yace mata shine wanda yace mata she’s beautiful, nan take ta gani shi, bata kawo komai ranta ba don tunaninta maybe ya nemi number ne concerning health dinshi maybe, da tafiya Tayi tafiya ta gano intentions dinshi daban yake da abunda Tayi zato, don babu boye boye ya nuna he wants to be friends with her, batada da wulaqanci don haka ta amince da tayin sa.
Tuesday morning…
Fitowa Tayi