da sales din company gaba daya, ranshi yayi mugun baci ganin barnan da akayi,da slush fund din da aka samu, wanda an Kasa gani inda kudin ya tafi, nan take ya saka ayi investigation mai tsanani, hankalin kowa ya gama Tashi waenda ke aiki tsakani da Allah najin dadi zuwanshi waenda basa yi taakani da Allah kuma na tsinke mashi dukda babu wanda ya isa ya Taka kasar daya Taka saidai a yi surutun daga nesa nesa.
Nan take kowa ya gane waye ya shigo cikin company, mai gayya mai aiki mai gado, General Muhammad yunus Taura, da daya tilo ga marigayi alhaji yunus taura.
Baibar company ba sai wajen karfe hudu, again ya ya dawo, saidai yaji dadin zuwanshi sbd achievement din daya samu tare da mamakin abubuwan daya tarar achan, sai a yanxu yake danasanin sakin ragamar komai hannun dady da useless danshi wato Aman.
Ko gida bai wuce ba ya tafi gidansa dake lariccs,Nadine ce ta bude mashi kofa kafin ta gaishesa, kallonta yayi yace “where’s she?”
Sanin wa yake nufi yasa ta cewa “she’s upstairs”
Saman ya wuce direct, yana zuwa daidai kofar ta ya dan tsaya yayi knocking ya bude kofar ba tare da tunanin komai ba, a zaune ya sameta ta doka uban tagumi, tunanin duniya yayi mata yawa,batama ji shugowan shi ba sai kamshinsa daya iso cikin dakin, saurin miqewa tayi jikin ta nadan bari tace “san….nu da dawo…wa”
Gaba daya ta gama furgita ta gigice, ahankali ya bude bakinshi in a calming tone yace “calm down kinga dodone”
Da sauri ta dago tace “kayi hkuri”
Dan runtse idanunshi yayi ya bude yace “zo nan”
Da sauri ta dago tace “naam”
“I hate….”
Da sauri ta gareshi Ashgabat hawaye na shirin zubo mata tace “Allah.. banji me kace ba”
Dariya taso bashi yayi saurin gimtsewa yace “zo”
Harda dan gudunta jiki na bari ta karaso Har gabanshi, gaba daya kuruciyarta yake gani sosai tunanin Anya zata iya Bearing mashi child dinshi yake, dan nesa dashi ta karaso gani, baya son yawan magana don haka ya tako taku biyu ya karaso gabanta yana ganin yanda kirjinta ke sama da kasa a cikin rigar dake jikinta,hannunshi yasa ya janyo waist dinta gab dashi sosai, a tsorace ta dago zatayi magana ya sanya hannunshi kan lips dinta yace “shiiiiii”
Tsit kamar an janye mata ruwan jikinta tayi, gabanta na lugude ahankali kamar mai rada yace “maysa kike rashin kunya?”
Kamar doluwa haka ta dawo Sai girgiza kai da take yi, tambayarta ya sake yana dan duqo da kanshi dede wuyanta zuwa kunnenta yace “uhm..speak”
Rasa abun cewa tayi don yanda yake mata magana ahankali da yanda yake sauke mata nunfashi yasata…….
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 116
Update!!
Unedited page
15/05/2023
Rasa abun cewa tayi don yanda yake mata magana ahankali da yanda yake sauke mata nunfashi yasa tsikar jikinta Tashi at the same time tana jin tsoronshi na ninkuwa, tanason zame jikinta daga nashi saidai tana tsoron abunda zai biyo baya,babu zato ba tsammani taji tambayarshi “how many days those it take?”
Dan dagowa tayi ta kalleshi don bata gane me yake nufi ba, nuni ya mata da idanunshi mararta, nan take ta dago abunda yake nufi, wani irin kunya ne ya durar mata, saurin kai da kanta tayi chan kasan maqoshinta tace “5days”
Dan matsa wa yayi baya yayi ya tabe baki yace “okay”
Yana kaiwa nan ya juya zai fuce tayi saurin tsaida shi ta hanyar cewa “dan….Allah”
Dan dakatawa yayi ya juyo ya daga kaya fita daya fuskanshi na nan yanda yake babu yabi ba fallasa, saurin sauke idanunta tayi don ta gagara kallon cikin idanunshi, tsaki ya danyi Har zai juya “dan Allah ka barni na tafi,”
Tsuke fuskanshi yayi tam yace “Ina?”
Da sauri ta dago tace “gidan mu”
“Nan ba gida bane? Ko daji ne”
Da sauri ta tari nunfashinsa tace “ba haka nake nufi ba”
Hawaye ne ya gangaro a fuskanta tace “inason zuwa wajen Yan uwana, dan Allah ka barni na tafi zamana anan bashida wani amfani”
Hade rai yayi sosai ya kalleta da kyau yace “ and who told you zamanki bashi da amfani?,look the next time kika Kara maganar nan ranki zai baci I’m I clear”
Da dan fada ya karashe Har tana ja da baya sosai tace “yes”
Azafafe ya fuce daga dakin Har ya sauko kasa yana cire buttons din suit din jikinshi ya fuce daga gidan, yana futa ta fashe da matsanancin kuka kamar ta daura hannu aka ta kwala qara haka takeji, dole ta bar gidan komai zai faru, bazata iya zama ba.
Yana karasawa gida kamar koda yaushe babu kowa a parlor sai hasken fitilu daya haske ko ina bauuu, dakinsa ya wuce ya rage kayan jikinshi kafin ya wuce toilet ya watsa ruwa,yana fitowa ya sauya kaya zuwa jallabiya fara qal,futowa yayi daga dakin ammah, yana gab da hawa stairs yaci karo da Aman,baibi ta kanshi ba ya kauda kanshi gefe, ganin ya tsaya akan hanyar yaqi matsawa yasa Amar dagowa ya zuba mashi idanunshi babu alamun wasa, shima aman din kallonshi yake saidai chan cikin zuciyanshi yana mamakin yanda yake shakkar sa da tukarar sa akan wasu abubuwa, bai gama tunanin ba Amar yace “do I have to say excuse me?”
Hade rai shima Aman yayi yana dakewa yace “what do you think of your self?”
Dago da jajayen idanunshi yayi ya kalleshi shima kamar bazaice komai ba chan kuma ya bude bakinshi kamar zaiyi magana Sai ya tuna tsayawa ya maida mashi magan Ma bata lokaci ne don haka ya hade rai tamm kamar shine babba akan aman din yace“get out of the way”
Babu kudi aman ya matsa mashi ya wuce bai kaiga shiga dakin amma ba aman yace “Ina tausayin ka”
Dan juyowa yayi shima yace “pity your self first, cause it looks like your life is already miserable”
Yana kaiwa nan yasa kai ya wuce dakin ammah, wani irin takaici da zafi aman yaji, ranshi ya sosu da maganar daya fada mashi,wato shine dan iska shi kuma holy holy,yar kwafa yayi ya fuce daga parlor.
Shiko yana shiga dakin ammah ranshi fess kamar bashi ya gama bata rai ba,hira sukayi shida ammah kafin su fito tare Har kasa.
Da kanta ta zuba mashi abunci ta kawo mashi nan sitting room ta aje mashi gefenta, kasa ya sauka daidai kafarta kan carpet ya soma cin abuncin da ta dafa domin shi, Duk duniya babu wanda yake respecting sama da mahaifiyarshi, idan kaga kan Amar a kasa Toh ammah ce.
Bai wani ci da yawa ba ya aje spoon, kallon plate din patten accan ammah tayi tace “don kodai baiyi maka dadi bane naga baka ci da yawa ba”
Da sauri ya dago ya kalleta yace “ay babu abincin da zai dafu da hannunki yaqi dadi ammah”
Dariya tayi tace “babana da zolaya”
Shima dariyar yayi yace nayi lunch dazu so baba jin yunwa yanxu sai zuwa anjima”
“Lantana lantana!!!”
Ammah ta soma kira, da sauri lantana ta fito tace “gani hajiya,barka da dawowa yallabai”
Daga mata kai kawai yayi ya mike tsaye dan nesa dasu ya ansa wayar ganin hammam ne ya kira.
Kallon lantana amma tayi tace “kwashe wannan, a daura ruwan tuwo, a fiddo da mama da ganda dasu hanta”
Da sauri ta duqa tace “Toh hajiya”
Tana shirin daukan plate din sallamar labaran ta katse su, tunda ya shigo amar ya kafa mashi idanu yana wani tunani, jin shirin da yayi yasa Hammam dake jiran amsarshi daga waya cewa “hello!!”
Da sauri ya kauda kanshi yace “are you sure we can trust him?, you need to be very careful, I’m sure they have eyes and ears everywhere,”
Da sauri Hammam yace “yes I’m very sure sir, as soon as I receive all the information I will send it directly to your email”
“Thanks dude”
Juyowa yayi ya koma gefen wajen one seater ya zauna yana kallon ammah dake magana da labaran, tabbas ya taba ganinshi a gidan nan saidai bai damu ya tambayi koshi waye ba,
Amma ce ta katseshi da cewa
“Malam labaran, ga mutanen dubai fa”
Da sauri labaran ya maida idanunshi kan amar yace “ay Mun gaisa jiya da safe saidai bai sheda ni ba, Ina wuni yallabai an iso lpy”
Dan duka kai kasa amar yayi yace “Alhamdulillah!!”
“Allah ya taimaka” malam labaran ya sake magana
Amar baice komai ba saima miqe da yayi yace “Bari nadan Huta ammah”
Murmushi tayi tace “okay son”
Dakinshi ya wuce zauna bakin gado, kamar wanda aka tsugula ya shiga bude wasu emails dinshi, ganin bai samu abunda yake nema ba yasa ya aje wayan, ko minti biyar baiyi ba da aje wayar asad ta shigo, yana daga wa asad yace “oga barka da warhaka”
“Thanks” ya amsa mashi kafin yace “any update”
Da sauri yace “yaron da kace kana buqatar gani, yana da cases da yawa a boye na daya Mun samu rape cases da yawa akanshi,
Azafafe Amar yace “lock him up, make sure he regrets having his that stick under his pants”
Jinjina kai asad yayi jin yanda Amar ya dauko zafi sosai, tabbas Akwai abunda wannan yaron wahab ya mashi, bai damu da ya sani ba saboda kobaiyi Ma Amar komai ba Sai yaci ubanshi saboda case din shi da fito, da sauri asad ya nunfasa yace “yea sir”
Har zai kashe wayan asad yace “maganar Alhaji, a binciken da nayi bai bar kasar nan ba yana nan, sannan yana da tight security sosai don na saka private investigation akan shi da wuraren da yake zuwa, bai fiya zama a guest house dinshi ba,,“
Shuru Aman yayi yana wani tunani kafin yace “keep digging on him”
Sallama sukayi kafin ya kashe wayar gaba daya,kiraye kiyrayen sallah da ake ne yasa shi wucewa toilet ya dauro alwala kafin ya fuce zuwa masallaci,tare sukayi sallah harda su labaran da baba mai gadi don sauran securities din ba musulmai bane,tare suka fito dashi daga asibitin,mutane da yawa suna mamakin yanda yake hulda masu gadi da mutane Ma baki daya, don Har gaggaisawa yayi da jama’ar wajen, mutane da yawa suna mamakin koshi waye don gaba daya rayuwar shi a uae yayi ta tun daga girmanshi Har zuwa yanxu.
Tun akan hanya ya soma Yan maganganu da baba mai gadi don labaran yayi masu sallama ya wuce.
Baba mai gadi babban mutun ne don baza ace mashi tsoho ba don zaiyi kusan sa a da kai gidan,don haka Amar me girmamashi do tun yana karami yake tare dasu anan gidan tun farko farkon taura estate.
A parlor ya tadda su salima suna kallo, yana isowa suka duqa Har kasa suka gaishesa kallo su yayi fuskanshi Adan sake yace “kunyi sallan”
Da sauri salima tace “munyi ya muhammad”
Murmushi kawai yayi ya wuce dakinsa don wani iri yake jinshi, da farko ya dauka stress ne saidaga baya ya gane lafiyarshi ce ta dan motsa, Kasa yin komi yayi ya kwanta kan gado,ya dauka kusan awa biyu a kwance bai cire jallabiyan ba, knocking din dakinshi akayi kafin ya bada umarnin shugowa, da sallama ta shigo tace “ya muhammad ammah tace dinner is ready”
runtse Idanunshi yayi da sukayi jaa sosai, muryarta exactly irin na yar uwarta, nan take yaji duniyar shi ta sauya don muryarta ta sanya shi tunanin da baya son yayi, da kyar ya dan bude bakinsa yace “okay ina zuwa”
Tana jin haka ta fice, da aman taci karo don yana gab da shiga nashi part din dake gefen na amar, zuba mata idanu yayi, take yaji wani abu ya daki zuciyarshi, ganin ammah a wajen dining ya sashi taho wa a zafafe ya janyo hannunta zuwa part dinshi dake dan nesa kadan dana amar, ya a bude kofar ya wurga ta gefe yace “ke dan Ubanki kame kika je yi dakin shi?”
Dago da idanunta tayi ta watsa mashi harara cikin tsiwa tace “abunda ake zuwa yi”
Take idanunshi sukayi jaa kamar ya Shaketa cikin daga murya yace “don ubanki ni kike cema abunda ake zuwa yi? Menene tsakanin ki dashi, idan baki yi magana ba Zan babbalaki anan”
Itama afadace cikin tsiwa tace” an fada maka kowa irinka ne?”
Baki ya bude, ya kasa ce mata komai, Sai binta ya dunga yi da idanu yana kallon yanda take surfa masifa, tsit yayi ya Kasa cewa Kala, “you’re unbelievable mtewww”
Ta fada da karfi kafin ta dauki mayafinta daya fadi kasa dalilin turota da yayi ta wuce, saurin bude baki yayi yace “sal” da sauri ta juyo ranta a bace, wato ya chanza mata suna zuwa na Yan iska, rai abace tace “idan bazaka ce salima ba karka Kara kirana da wani sal miye wani sal”
Tana fadin haka ta banko mashi kofar a zafafe, tana fitowa ta tsaida natsuwar ta tare da saurin tsayawa wajen sitting room ganin ya Muhammad ya fito, kallonta yayi ganin yanayinta kafin ya kauda kai ya wuce dining, itama dining din ta nufa ta zauna kusa da Salim dake kusa da ammah don Har sun fara cin abunci,kallonshi ammah tayi tace “me za ah zuba maka son” dago da idanunshi da sukayi jaa yayi yace “anything ammah” kokarin kauda idanunshi yake daga kallon ammah don yasan tana ganin shi zata san yana cikin damuwa don ita kadai ce ke karantar shi, uwa kenan,hakan take kuwa ta bangaren ta don tunda ya tunkaro hanyar dining din ta hango yanda yanayinshi ya sauya, sanin basu kadai bane yasa ta kauda zancen don Aman ma ya karaso ya zauna opposite kujeran da sal dinshi ke zaune.
Dakyar amar ya tsakuri lomar tuwon guda biyar ya mike kallonshi ammah tayi tace “are you okay son?,”
“Yea ammah”
Yana kaiwa nan ya wuce dakinshi, yana shiga ya dafe kanshi, toilet ya wuce ya tube jallabiyan da shorts sun dake jikinshi ya tsaya gaban shower ya sakarma kanshi ruwan zafi, tunanin ya fara yanda yake Shan wahala, shi wannan ba sauqi ya samu ba na cire abunda ke cikin marar shi da yayi saima ingiza shi da yayi, babu dare babu rana yake jinshi a buqace, bayason sama kanshi cewa buqatar yake saidai jikinshi yaki bashi hadin kai don kamar pressure ake Kara mashi kullum, he’s trying so hard for keeping what he promise not to do”
Wannan ruwa dake sauka jikinshi ji yayi kamar Kara mashi azaba suke don garin Akwai sanyi sosai gashi ruwan zanyi ne, fitowa yayi daure da towel ya zauna gefen gado ya runtse idanunshi, wani tunanin ne yazo ranshi yayi saurin miqewa ya shige cikin closet ya nemi kaya matasa nauyi ya zaro key dinshi da wayanshi ya fito daga dakinsa, lokacin daya fito Duk sun hau sama Sai lantana dake kwashe kwanukan da suka gama amfani dashi, fucewa yayi daga gidan gaba daya.
Tafiyar minti ashirin ta kawoshi larrics cikin mintuna goma don wani irin mahaukacin gudu yakeyi, yana isowa yayi parking,saida ya dauka kusan minti ashirin yana sake sake a cikin motar, duban agogon dake screen din motar yayi, ganin kusan karfe goma da rabi yasa ya futo ya kulle motar ya shige cikin gidan,Nadine ce ta bude mashi kofa don suna zaune kamar kullum, tunda ya shigo ya kafa mata idanu, yanda take gyangyadi a zaune, at the same time tana hana kanta barcin, maganar Nadine ce ta fargar da ita jin tana gaishesa, gabanta ne ya bada dammm, saurin danne wa tayi ta gyara zaman rigarta a jikinta, takowa yayi ya zauna gefen da yake zaune don raqubewa tayi daga chan karshe doguwar kujerar, Nadine kam wucewa tayi bata tsaya ba.
Adan tsorace murya chan kasa ta dago tace “Ina yini” chan kasan makoshi ya amsa da lapiya don ko kallon inda yake baiyi ba, itako zaman nan da yayi kusa da ita kamar ya watsa mata garwashi haka take ji,waigowa tayi ko zata ga Nadine taga wayam,tana son mikewa saidai tana tsoronshi don haka ta danne abunda ke mata zafi ta maida idanunta kan tv, Allah Allah take a gama movie din ta samu ta wuce sama, cikin ikon Allah kuwa aka gama movie din, shi dai ba kallon yake ba don gaba daya zaman nan da yayi hatta saukan nunfashinta a cikin xuciyarshi yake ji, ya rasa tunanin da zaiyi, ya Tamke fuskanshi tsam bai ce qala ba saima kwantar da kanshi da yayi a baya, tana ganin an gama kuwa ta miqe tsaye ta Kasa motsawa, chan kasan maqoshi kamar wadda aka zarema soul tace “saida safe”
Jin yayi shuru yasa ta fara tafiya, difff light din gidan ya dauke gaba daya sakamakon dan spark da wani line yayi, hankali tashe ta fara zuba idanu ganin ko ina duhu, gashi tabar wayan ta asama ta saka charge, ita bama tsoron duhun take ba don wani tsoron ma mantawa kake dashi Idan wanda yafishi yana gabanka, laluben kujerun ta fara don samu access to hanyar dazai sadaka da sama, karaf taji hannunta kan wani thick abu, da sauri ta dauke hannun bata gama ba daukewa ba ya damke hannun nata da ta daura kan lap dinshi ba tare da saninta ba, nan take ta zama mai in’ina, shock din abunda ta dafa da hannunshi daya damke ta yasa gabanta mugun faduwa, kamar Mara gaskia ta sauke murya tace “dan Allah kayi hakuri nan san na…”
Fizgota yayi gaba dayanta kan jikinshi, saurin runtse idanunta tayi jinta a jikinshi, kamshin nufashinsa dake fita da kamshin mint ya tabbatar mata a jikinshi take, a daburce ta gwale idanu hankali a tashe ta fara kokarin Tashi, idanunshi na nan lumshe yana jin yanda yake kokarin Tashi, kasala ta hanashi yin komai, matsoda da ita yayi sosai kan kirjinshi ya lalubo fuskanta zuwa wuyanta, ahankali ya matso da fuskanshi wajen wuyan nata yadanyi relaxing jaw dinshi a wajen, gashin sajenshi na gogar wuyanta, ahankali ya soma magana kamar ba Shiba “shiiii relax”
take ta runtse idanu jin wani abu na yawo tun daga yatsunta, Har wani zafi zafi take ji, nunfashinsa yana sauke mata wani alamari mai wuyar fassara