Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   44 / 94

129K to 132K   out of 279.4K words

dake dan bugun ta,tana nan tsaye wani mutumi yazo ta gabanta yayi mata sallama, Adan tsorace ta amsa 

“Hajiya tun dazu nake jiran isowarki”

Shuru ta danyi tana kallonshi don bata gane abunda yake nufi ba, ganin haka ya bude wayarshi ya nuna mata hotonta yace “oga ne yace azo a daukeki”

Tana jin haka ta matse fuska tace “malam inaga kayi mistake ne”

Kallonta ya sakeyi kafin ya dubi wayarshi yace “hajiya kece, ga hoton daya bayar nan”

Azafafe ta dago tace “Wai waye”

Baice mata komi ba ya Danna ma Amar kira, yana dauka ya miqa mata wayar, karba tayi tasa wayan a kunnenta, muryarshi ne ya daki kunnenta “get in the car,”

Shuru ta danyi kafin ta hade rai yace “Ina zai kaini?”

“I hate repeating my self, just get in the car” cire wayar tayi daga kunenta jin yanda yake magana afadace gashi da alamu kamar yana cikin mutane, itama Adan fada ce tace “no babu inda zani,”

Tana kaiwa nan ta katse wayar, ta miqa mutumin tace “malam kaje kawai”

Kallonta sosai mutumin yayi yan yaba kyawun irin nata kafin ya sake wani tunani amar ya kira wayar, yana dagawa yace “don’t let her move, I’m coming now”

“Okay sir” mutumin ya amsa, juyawa tayi zata tafi yace “hajiya dan Allah kiyi hkuri ki tsaya, ba a samun taxi anan, bari na nemo maki ko nayi maki bolt”

Shuru tayi tadan jingina da motar gefe, ranta a hade don tayi alqawarin wannan Karan bazai sake yi mata wayo ba.

Amar dake meeting da shareholders din taura company wayar driver daya tura ya daukota ya shugo wayarshi, yana Ganin call din yasan cewa tayi gardama kenan,daukan wayar yayi ya saurari abunda driver ya fada mashi kafin ya buqaci ya bashi ita, take ranshi ya baci yanda yana mata magana tana maida mashi kai tsaye, kallon shareholders din yayi da suke ta surutai wasu na cewa

saidai a saida company din sbd imaging company din ya rigada ya fadi so babu wani hope,kallonsu yayi daya bayan daya miqe ba tare da yace masu komai ba ya fuce suka bishi da idanu,daya daga cikin mutanen ne yace “mu za a mayar Yan iska”

Juyowa Amar yayi don Har yana gab da kofar ya kalli mutumin yace “Nawa ne share dinka a company dinnan?”

Cikin tsagali mutumin yace “5%”

Wani irin banzan kallo Amar yayi mashi cikin isa yace yace “you’re out of this company, Ka tura account details dinka to the finance, kudinka zai shugo account dinka” nan take kowa yayi tsit sanin me hakan ke nufi, hankali atashe mutun ya miqe cikin borin kunya yace “so what, a biya I hakina bazan zauna ba, companies da yawa suna buqatar shareholders kamar ni basu samu ba”

Kallon Amar ya sakeyi ya danyi murmushi ta gefen baki yace “send your accounts zasu tura maka kudin 10% share, company nan baya buqatar mutane irinka” yana kaiwa nan ya fuce, lift ya shiga zuwa kasa, bai tsaya komai ba ya shige cikin g-wag dinshi ya bama motar wuta.

Cikin minti goma ya isa airport, gaban wajen arrival parking space yayi parking motar shi,kafin ya kira driver din, jikin Yan mintuna kadan saiga driver din tana biye a bayanshi don cemata yayi ya samo mata bolt din da yayi mata order ya iso, kallon motar tayi da kyau kafin ta kalli mutumin, bata kawo komai aranta ba don normally a dubai zaka iya requesting mota irin haka saidai kudinka ne zaiji jiki, a matse take data bar wajen don haka ba tare da wani tunani ba ta bude bayan motar ta kalli driver din tace “nagode malam”

Murmushi kawai mutumin yayi ya rufe mata baya motar, yana rufewa Amar ya figi motar suka bar wajen, kanta a kasa tace “malam dan Allah moto park zaka kaini”

Banza yayi da ita saida ta sake maimaita wa,kiii ya Taka burgi da karfi Har tana buge kanta da seat din gaba, dan dagawa tayi karaf idanunta suka sauka akan na Amar ta cikin mirror, hankali atashe ta gwalo idanunta waje, ranshi a mugun bace don yawanci 70% of abunda ke damunshi Duk akanta ne, rai abace babu wasa afuskanshi yace “get out, waye driver ki?”

Ay kamar jira take ta bude bayan motar ta fito waje, zuge glass din gaba yayi babu wasa a fuskanshi ya kalleta yace “get in” banza tayi dashi ta kauda kanta gefen, Ganin ta tsaya gefe guda ta kame, kuma sarai yasan ta jishi ranshi a mugun bace yake da wannan sabon attitude din nata “Aisha!!!!!!”

Ya daka mata tsawa da yasa Tayi saurin kofar gaba ta shige, bata gama rufe kofar bama ya figi motarshi ba tare da ya kalleta ba Har tana dan buge kafarta da motar, 

Shuru ne ya biyo ba sai kawai ta fashe mashi da kuka, quluwa dai ya gama quluwa da attitude dinta sosai don kamar ya buge Bakinta haka yake ji, murya asanyaye don gaba daya yama gaji da hayaniya don tunda yazo Nigeria yake hayani yace “shut up”

Kamar wadda ruwa yaci kuwa tayi tsit batace komi ba,gabanta na faduwa, kauda kanta gefe tayi tana kallon yanayin garin daya hade kamar za ayi ruwa lokaci guda, tunda suka shigo cikin layin gabanta ya soma faduwa, anguwan is so peaceful and serene, kallonshi ta danyi kamar baza tayi magana tace “Ina zaka kaini?”

Banza yayi da ita hankalinshi nakan Yukon da yake saida ta sake fashe mashi da kuka tace “Wai meysa kake min haka ne dan Allah?,ni na gaji da wannan rayuwa, Ka sake ni kaki, Nace maka I’m done bana…”

Juyowa yayi ya kura mata jajayen idanunshi rai abace yace “you don’t have to worry your self, yau yau dinnan Zan sakeyi babu kari, having you in my life was a mistake, mara Konya”

Tunda ya fadi haka ta danji wani dadi aranta, chan kasan zuciyanta kuma tana jin wani iri don yana sakinta shikenan ta zama bazawara, saurin kauda zancen kawai tayi har yayi horn a gaban estate din gidan, bude idanu tayi tana kallon tsarin gidan, ya hadu sosai ba kadan ba don kamar ba a Nigeria ba, komai a tsare tun daga bakin gate, shigarda motar yayi cikin estate din, direct ya wuce hanyar babban apartment din daya fita daban daga sauran gidajen estate din, nan ma saida yayi horn aka bude gate din kafin yasa kai da motar, bin ko’ina ta soma yi har inda yayi parking gaban entrance sun gidan, bai kashe motar ba ya juyo ya kalleta yace “sauka kije ciki”

Juyowa tayi tana buqatan jin karin bayani,ganin ko kallon inda yake baiyi ba yasa ta bude motarshi gabanta na faduwa, hannunta maqale da Jakarta ya juyar da motar ya fuce daga apartment din, ahankali ta soma takowa jiki a mace cikin tsoro ta karaso gaban entrance door din, hannunta Har karkarwa yake ta Danna door bell din,saida ta Danna Sau biyu kafin a bude kofar, kallonta lantana tayi daga sama Har kasa Ganin zankwadediyar budurwa yasa Tayi saurin cewa “bismillah!!”

Matsawa tayi ta bata hanya don tasan daga gani qila cikin yan matan aman ne da yake kawowa Duk sanda yaga dama, Har gaban sitting room lanatan ta rakota kafin ta nuna mata wajen zama “bismillah, wurin wa kika zo?”

Shuru amra tayi don gaba daya tsoro ma take ji, rasa abun cewa tayi tayi gum da Bakinta, ganin haka yasa lanatana cewa bari na kawo maki abunsha, baya nan ya fita”kallonta amra tayi don bata gane kan zancen ba lantana kuwa Duk a tunaninta cikin yan matan Aman ne dake biyoshi Har gida, tabe baki tayi ta shiga kitchen, kallonta salima tayi tace “ya Muhammad ne ya dawo?”

“Bashi bane ba, wata baqi wa ce inaga cikin Yan matan yallabai ne”

Juyowa salima tayi ta kalleta yace “waye kenan?”

“Wa kika sani Banda wannan bugaggen dan Alhaji”

Hade rai salima tayi ta kauda kai jin abunda lantana ta fada, kafin ta cigaba da yankan carrot ba tare da ta sake tanka mata ba don kalamanta na karshe basu mata dadi ba

Bude fridge lantana tayi ta dauko ruwa da juice ta saka a tray tace “dan Allah kikai mata Zan wanke rice din naga ruwan ya tafasa”

Fuska Adan sake salima ta aje yankan carrot din ta karba plate din ta juya zuwa parlor, kanta a kasa ta soma takowa Har cikin sitting room ba tare da ta kalli inda bakuwar ke zaune ba don tunda lanata tace mata cikin Yan matan aman ne tazo taji wani irin bacin rai.

Amra ma bata Lura da ita ba don kanta a kasa yake ta takure don taji motsin su a kitchen, gashi bata san gidan waye ya kawotaba bayan wannan ma batasan yanda zatayi introducing kanta ba,aje tray din salima tayi agabanta kafin ta dago, jin alamun faduwar abu yasa salima juyowa ga bakin kofar, salim ne a tsaye daga bakin kofa game handle din hannunshi a fashe a kasa, idanunshi kyam akan su, salima na Ganin haka tace “kai lafiyarka kalau kuwa, kalli yanda Ka fada game handle din” takowa tayi har inda yake ta dauki handle din tana dubawa ko ya fasa.

Amra da taji muryar da bazata taba mantawa da ita ba Har karshen nunfashinta Tayi saurin dagowa karaf idanunta ga sauka akan salim daya kara tsayi sosai don Har ya kusa kamo salima, gefenshi kuwa wata budurwa ce ta juya mata baya don bata Ganin fuskanta, mikewa tayi tsaye zumbur Bakinta na karkarwa haka zalika jikinta ya soma kyarma, salim ma cikin tsoro yake kallonta gashi babu bakin magana, dagowa salima tayi tana mashi fada kan ya fasa, Ganin yanda ya kafa ma parlor idanu babu ko kyaftawa saidai mana ganinshi kaga he’s shocked sosai,juyowa salima ta soma yi don Ganin abunda yake kallo, karaf idanunta ya sauka kan amra babu zato babu tsammani, baya ta soma yi kamar zata fadi Salim ya taro ta, idanunta ne ya soma yaro hawaye, saurin goge idanunta tayi don tabbatar da abunda idanunta ke gane mata, ahanakli kamar mai koyon magana tace “addaaaaa!!!!”

Amra dai tuni ta fara tagal tangal kamar zata fadi don ma Allah ya taimaka da kujera a bayanta, hawaye na bin kuncinta tace “salima????? Salim??? Kune kodai mafarki nake? Kodai ido na ne ke mani gizo? Innalillahi wa inna”

Take ta fashe da kuka, amma dake shirin saukowa dan duban girkin da sukeyi ta taaya kyam itama surprisingly take kallonsu duka, musamman amra data taaya chak kamar wadda aka zare ma ruhi,jikinta na rawa, da gudu salim ya tako Har gaban amra ya tsaya bakinshi na rawa ya kasa magana, hannunta ya kama ya fara shafawa dan tabbatar da idanunshi daidai suke Ganin mashi,a furgice ya koma wajen salima ya jawo hannunta Har gaban amra dake hawayen farin jiki na ganinsu, “adda kece?” Salima ta sake tambayarta hawaye na zubowa a fuskanta, ammah dai kallonsu ta fara yi kamar tv don kana gani su kasan Yan uwa ne, don kamaninsu harya baci sosai, cikin saurin amra tace “salima!!! Salima kune??”

Da sauri ta hada su su duka ta rungumesu tana kuka, wani irin kuka suka fashe dashi at the same time, kankankameta sukayi kamar za a kwace masu ita

“Adda daman kina raye? Shine kika barmu muka shiga qangun rayuwa?, why adda why?,”

Babu abunda amra ke cewa sai “I’m sorry ku yafe min, rashinku yamin babbar illa arayuwa”

Kasa sakinta sukayi suna kuka sosai sun dauka kusan minti goma a haka….

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 129

Update 

Unedited

Karasowa tsakiyan parlor ammah tayi,cikin mamaki tace “salima???what’s going on here”

Muryar ammah ne ta dawo dasu daga koke koken da suke, cikin sauri salima ta janye jikinta daga na amra tare da komawa gefen ammah tana hawaye, Ganin yanda take kuka yasa hankalin ammah Tashi tace “whats going on speak up?” 

Kasa magana dukansu sukayi, amra dai tunda ta tsaya a tsaye babu abunda take sai kukan zuci dana fili kanta a kasa jikinta na bari don bata ma Lura da ammah ba, Salim dake gefenta shima matsawa yayi daga jikinta ya koma wajen ammah.

Ganin haka yasa ammah kallon amra don kwata kwata bataga kamannin sani a tattare da ita ba,

Cikin natsuwa ammah ta kalleta sounding calmly tace “baiwar Allah daga wurin wa kika zo?”

Dan dagowa amra tayi ta kalli ammah, kafin ta sauke kanta kasa, don tana ganinta ta gane cewa mahaifiyarshi ce don kamanni su daya fito sosai, gaba daya kanta ya gama qullewa, meya kawo su salima gidan nan? How? Waye ya kawo su? Maysa ya kawota nan gidan? Wadannan sune tambayoyin da ta fara yima kanta, jiri ne ya fara dibanta tayi baya kamar zata fadi, da sauri ammah ta karaso kusa da ita ta rike hannunta cikin kulawa tace “are you okay?”

Kanta a kasa ta girgiza kai, kallon inda salima ke tsaye ammah tayi tace “dear jeki kawo glass of water”

Juyawa salima tayi ta wuce kitchen kafin ta fito da glass cup a hannu, gaban ammah ta tsaya ta miqa mata kafin ta koma gefe ta tsaya,mikama amra ruwan ammah tayi, saida taga ta samu natsuwa kafin ta kalleta tace “sannu, wurin wa kikazo?”

Ammah tayi tambayar tana kallonta don itama Duk a tunaninta maybe cikin Yan matan aman ne da suke zuwa,saidai tayi mamakin Ganin yanda ta rungume su salima tana kuka, itama salima dalilin da yasa ta kasa cewa komi kuwa shine saboda Duk zamansu da ammah bata taba zancen amra, and Duk sanda akayi masu tambaya a school ne cewa take Salim ne kawai sibling dinta, don ta cire amra daga rayuwar su gaba daya.

Kallonsu ammah tayi Ganin Duk sunyi shuru kafin tadan murmusa tace “salima come and seat” ta fada tana nuni da kujeran dake gefenta, karasowa salima tayi ta zauna ta kalleta, hannunta ammah ta rike tace “dear kin Santa ne?”

Sunquyar dakai salima tayi don kunyar fada ma ammah ma take ji don bata taba fada mata cewa suna da babbar ya ba.

 

Sallamar Amar ce ta katse su su duka, dawowa yayi don saida ya kawo hakan zai faru aranshi, “wa alaikum salam” ammah ta fada tana kallon hanyar da yake karasowa, sanye yake da suit din daxu, yayi kyau sosai, kwarjini da qimarshi ta futo fili sosai.

Kauda kai gefe ammah tayi tunawa da abunda ya faru jiyan, kallon su yayi duka Har ammah da yanayin ya chanza da ya shigo,samun waje yayi dan nesa dasu ya zauna akan 1seater dake facing dinsu su duka,salima ce ta dago tace “Ina wuni ya Muhammad”

Ta fada kanta a qasa, amra dai bata daga ba saidai kamshinsa ya tabbatar mata da shi dinne ya shugo sai kuma sallamarsa data doki kunnenta.

Kallon gefen ammah yayi yace “ina wuni ammah na”

Ba tare da ta kalleshi ba tace “lafiya!!”

Shuru ne ya biyo baya, ganin Duk sunyi gum yasa ammah kallonsu su gaba daya, idanunta ne ya sauka kan amar dake kallon amra shima ya kasa cewa komai, ganin haka ya tabbatar mata da sun san juna gaba daya su, rai Adan bace tace “cikin ku babu wanda zaiyi min explanation ne?”

Dan dagowa amar yayi ya kalli fuskanta yanda yaga ranta yadan baci yasa yayi gyaran murya ya kalli salima yace “kun san wannan?”

Dan waigowa salima tayi ta kalli inda yake masu nuni da amra kafin ta sunkuyar da kanta qasa tace “eh”

Nunfasawa yayi yace “who’s she?”

Kanta a kasa tace “addan mu ce, she’s our elder sister”

Da idanu ammah ta bisu su duka tana buqatar bayani, katse mata tunani yayi ta hanyar cewa “ammah,kwanakin baya banyi maki bayani akan yarannan ba saboda rana irin ta yau,“

Nuna salima da Salim yayi yace “waennan yaran ba yaran aboki na bane,marayu ne hasalima ban sansu ba kwata kwata saita dalilin yar uwarsu”

Ya karashe yana kallon amra, gaba daya suka juyo suka kalli amra da kanta ke kasa, tana hawaye,kafin su maida kallonsu kanshi, salima was so surprised da jin zancen nasa,Nunfasawa yayi ya cigaba “ranar da aka kawo su gidannan nina saka private investigator dina dayake min buncike akan su ya kawosu daga kano ,saboda……. ” nan ya kwashe duk yanda akayi da buncike a daya saka akayi akansu Har kawosu gidan da akayi, saidai bai fadi dalilin kawosu da yayi ba kwata kwata”

Wani irin kuka amra ta fashe dashi jin irin ukubar rayuwar da qannenta suka shiga, babu abunda take sai sheshekar kuka jin yanda uncle ya wulaqanta rayuwarsu,salima da Salim ma kukan sukeyi sosai don sai Yanxu suka gane komai.jikin su duk yayi sanyi,musamman salima da Duk a tunaninta amra ta manta dasu gaba daya ashe ta dalilinta suke zaune a gidan,

Kallon su salima ya sakeyi yace “kuje dakinku keda salim”

Mikewa sukayi suka wuce sama, suna wucewa amar ya kalli ammah ta gefen ido Ganin tana mashi kallon neman Karin bayani, cikin natsuwa yace  “she’s the one ammah”

Binshi da kallo ammah tayi sosai don kwata kwata bata dago zancen nashi ba saidai,

Ganin haka ya sashi Sunkuyar da kanshi don kunyar abunda ke shirin futowa daga bakinshi yake “she’s the lady that I got married to”

 Cike da mamaki ammah ke kallon bakinshi, sai a lokacin ta dago zancen, amra dai babu abun da takeyi sai hawaye ta rasa tunanin da zatayi a ranta.

Kasa magana ammah tayi saidai idanunta na kanshi don jin Karin bayani, nan take ya labarta mata tundaga lokacin da sukayi yarjejeniyar aure inda ya amince da aurendon ta samu katin kasar don ta kawo kannenta kasar saidai baice komai game da nashi dalilin auren ba wanda ya hasala ammah sosai,saida ya gama labarta mata kaff kafin yace “wannan ne dalilin da yasa ban fada maki ba, ki gafarce ni ammah, wannan auren ba komai bane, it’s just a contract marriage, daman na bari ta karasa karatunta Saina sallameta don na hadata da Yan uwanta”

Yana kaiwa nan ya kalli amra kafin ya kauda kanshi gefe,amra dai bata dago ba Har ya gama bayin

44 / 94