ba, “dan Allah ka futa ma…”
Bata gama fada ba salima ta sake dawowa ta karbi Hamad da Hamid,
Kallon salima amar yayi don yana tsaye daga gefe ya hade hannunshi a kirjinshi, ganin tana wani murmushi yasa ya daga mata hannu daya shima yana murmushi kafin ta fuce, tana futa amra ta fara kokarin gyara bathroom din, bath din ta fara dauraye bata gama daurayewan ba ya tsugunno inda take ya karbi hand faucet sin da take kokarin daurayewan dashi ya fara daurayewa da kanshi, dan baya tayi ta zuba mashi idanu, gaba daya ya gama sau yawa mata, yanxu he’s so gentle, calm and sweet at the same time, dan tabe baki tayi ta juya zata fuce tace “hmm kamar da gaske,”
Bata gama rufe baki ba ya juyo da faucet din ya feshe ta ta ruwa, nan take ta taaya chak ta juyo zatayi masifa, “mey hakan dan Allah, what’s…”
Bata karasa ba taji ya sake feshe ta da wani ruwa tundaga sama ta zuwa kasanta saida yayi mata jagab ya sauke faucet din Yana dariya, bunshi ta soma yi da idanu, Anya shine kuwa, itama Har lokacin bata yarda ya chanza ba gani take kamar wani baqon mutun ne daban ba Amar ba, kallon cute face dinshi da yake dariya har yana tafawa ya dan rike cikinshi tayi, zuciya ta ne ta fara bugu Fatt fatt fatt kamar zata futo, nan take taji kamar an bugu zuciyarta an wanke ta tass tayi haske, samun kanta tayi da shagala wajen kallonshi tana admiring how handsome he is, zata iya rantsuwa yau taga ainahin kyawu da Allah yayi ma kyakyawar fuskanshi saboda annurin da ta hango a tattare dashi, Har ya tako gabanta bata Ankara ba saida ya cicibeta gaba dayanta ya daga ta sama ya fara juyata sama Har lokacin dariya yake kana ganin fuskanshi kasan gaba daya ya mace a sonta sosai, “maimaita abunda kikace” ya fada yana dariya yana juya ta,
Dariya ce itama taso kubce mata don abun sai ya zamana kamar masu wasan Yan yara, irin na kamaki dinnan, “dan Allah ka saukeni na fara jin hajijiya” ta fada a shagwabe
“Naki din saikin maimaita abunda kikace”
“Haba jiqani da kayi” ta bashi amsa kai tsaye tana kunshe abunda ke tunkarota
Yanda ta umarta hakan akayi don sauke tan yayi kasa yace “Ina na jiqakin nunamin”
Nan ta fara mashi nuni da kirjinta tace “ba gashi ba”
Bin wajen ya soma yi da idanu kamar wani maye, tana Ganin haka tasan wayo ya mata daman yayi hakan ne don ya kalli jikinta, gashi bata saka bra bama akan cotton rigar dake jikinta, saurin juya mashi baya tayi ta dafe kirjinta ta fuce daga toilet din afusace.
Tana futa ya girgiza kai Har lokacin murmuahi yake yana tunanin abunda asad ya fada mashi lokacin da yake tambayarshi yanda ake yin soyayya,
“Oga dole Ka saukar da kanka fa, Ka dawo kamar shekarunku daya d ita, ka riritata sosai, mata Akwai son Suga Ana binsu Ana lallaba su”
Murmushi kawai Amar yayi bayan ya gama tunanin kafin ahakali ya soma furta “Ki gama guje gujen ki zaki shugo hannu ne stubborn wifey”
Wifey word dinma dariya yake bashi don da kyar ya iya tattara courage dinshi ya koyi fada, tunawa da yanda ya shagala a dubai ya dunga koyan yanda ake soyayya yayi da yanda ake nuna ma mace so, wanna ma kanshi idan ya tuna dariya yakeyi yana mamakin kanshi.
Karshe dai shine ya karasa Gyaran bathroom din ya futo, salima ne kawai a dakin ta gama shirya triplet Harta kwantar da Hamid da Hamad, princess ce dai ta rage batayi barci ba itama madara take so don haka ta zauna tana bata kafin ta fuce daga dakin,
Kallonta amar yayi har lokacin tana murmushi tace “yaaayaaaan mu…”
Ta karashe da shakiyanci tana mashi dariya, hannu ya sake daga mata yace “aikinki nayin kyau sister inlaw”
Dariya salima tayi don yanxu wani irin good relationship ne tsakaninta dashi don wani sa’in ita yake kira daga dubai yana tambayarta yanda amra take da abubuwa da take so da Abubuwan da bataso, kusan kullum ma ita ce ke aika mashi da report akan amra, da abunda taci wani sa’in ma Har hotunan amra take dauka ba tare da saninta ba saita nuna mashi.
…..
washe gari ammah tasa yar chad ta zo daga chad aranar, abunka da harkar masu kudi da sassafe akayi ma yar chad booking ta taho Nigeria, tana isowa babu wani bata lokacin ammah tayi mata bayanin komai akan komawar amra gidan mijinta, already a shirye daman yar chad tazo don haka babu wani bata lokaci ta fara dirzarta da kayan gyara masu kyau sosai, a cikin package sun datayi mata
Harda wankan madara wanda sai yar gata akeyi ma wannan daman ammah ce ta hana ayi mata a kwanakin baya sai idan lokacin tarewar ta yazo, saida ta fara waxing jikinta tasa kafun tayi mata wankan madara Harda gashi, ranar dai amra taga ikon Allah don ta dirzu iya diezuwa fatarta Har tayi jaaa sosai kamar jini zai fita daga ciki, private part dinta kuwa yasha turirin herbs daga chad masu shegen kyau bayan wannan ma haka ta dunga durka mata wani sirrin magungunan su wanda tun bayan datasha da Yan mintuna ta fara jin yanayi ta ya sauya, dropping takeyi madly down there,
Basu gama Gyaran ba sai wajen yamma don sun dauka kusan awa uku sunayi, suna gamawa ammah tasa tayi mata henna dinsu, nan ta Zane ta da henna hannu da kafa, ko awa baiyi ya fara maroon yayi ma ta fun hannunta kyau sosai, daman Akwai ta kyawun yatsu dogaye,
Suna gama lalle yar chad ta mata turarruka masu kamshi sosai wanda zatayi amfani dasu idan yana kusa, amra dai girgiza mata kai kawai takeyi tana sauraronta saidai bata jin ma Akwai abunda zaisa ta bari yazo kusa da ita balle turaren ya shige shi Har ya susu ce mata.
Sanin tana son waist beads yasa yar chad ta taho mata dashi, wannan kam amra taji dadin karbanshi don tana bata tayi mata godiya sosai don tana son kyale kyale irin wannan…
Aranar yar chad ta koma chad don a ranar aka sakeyi mata wani booking din tabi flight na dare ta koma bayan ta shaida ma ammah kan cewa Kar amra ta yawaita futa saboda sirrikan dake jikinta na Gyaran jikin masu karfi ne sosai.
Washe gari ammah ta hana amra saukowa kwata kwata don ko breakfast ma kaimata salima tayi sama inda ta dunga zuzuta Kyan data karayi cikin kwana daya tal, amra dai babu abunda yake sai tabe baki don bataga amfanin wannan gyara Gyaran ba saidai ta wani bangaren tana jin dadi aranta saboda koba komai ita tasan cewa ita cikakkiyar macece mai ji da kyau da sura wanda tana Ganin da wannan kadai zata Rama abubuwan da yayi mata don tana sane da komawa gidan nashi daya buqaci hakan.
Ahaka ta wuni a daki taqi futowa, inda Amar kuwa ya dunga zuba idanu ko zai ganta, karshe ma dai dakinta yayi kokarin zuwa don duba ko dai lafiya, nan ammah ta dakatar dashi don lokacin daya hau saman tana kokarin shiga dakin amra itama, tana ganinshi kuwa babu wani corner corner ta koreshi, bai kawo komai aranshi ba don haka ya wuce bedroom din babies dinshi don kusan kullum sai ya shiga dakinsu yayi spending some quality time with them kafin ya wuce dakinshi ya kwanta.
Koda ya koma dakinshi kamar koda yaushe wanka ya fara yin ya sauya kaya zuwa pjs dinshi kafin ya janyo laptop dinshi ya hau kan gadonsa, aiki yake yi
but zumudin dake cinshi ya hanashi focusing, shi kadai yasan abunda ke cikin rashi, da haka Har barci ya daukeshi baima gama aikin ba.
Washe gari da sassafe ya shirya ya fuce daga gidan, bai tsaya ko Ina ba sai inda suka shirya haduwa shida asad, sun dade sosai inda suka dan Tattauna akan wasu abubuwan daya shafi tsaron a Nigeria kafin suyi sallama.
Daga wajen asad gidanshi na larrics ya wuce don duba yanayin gidan don tun last time bayan an gama aikin daya zo bai sake zuwa ba, gidan yayi kyau sosai sai san barka, yaji kayan alatu na zamani wanda sukaci uwar na da, babu abunda aka sauya daya dangancin Ganin gidan sai refurnishing da yasa wasu interior designers sukayi,
Sama ya wuce direct, nan ma saida ya taaya yabi dakinshi da kallo abubuwa da dama na dawo mashi, memories din lokacin tarayyarshi da amra ne ya dawo mashi, it was crazy and erotic that day don baya tunanin zai taba iya mantawa da wannan lokacin,
Murmushi kawai yayi ya soma rage kayan jikinshi yana Yan wake kafun ya wuce bathroom, bai wani jimaba sai gashi ya futo…..
Amra dai yau da faduwa gaba ta tashi, tana kunshe a daki taqi futowa tunda tayi wanka, don sai shugowa su salima sukayi da su Hamid, suna shugowa dakin nata kuwa Tayi saurin karbansu tana jera masu kisses, suna nan zaune ammah ta shugo dakin ta kawo mata wani warm milk, karba tayi ta mata godiya, “ammah nima baza a san min ba”
Bugu amra ta kai mata Tayi saurin kaucewa tana dariya
Murmusawa ammah tayi kafin tace “kema lokacin ki zaizo sai a baki”
Dan tabe baki salima tayi “Ay shikenan nidai wannan warayyar da akeyi mana bana jin dadin ta wallahi.”
Dariya ammah tayi “Allah ya shirya ki my dear, zanzo na aurar dake na huta, yauwa Abban ku yace zaizo yau ko?”
“Eh yace zaizo kafin su adda su wuce”
Wata mutuwar harara amra ta kai mata, saida ammah ta fuce daga dakin tace “ke wai meysa bakida kunya ne?”
Turo baki salima tayi tace “Toh me nayi?”
Tsaki kawai amra tayi ta ajiye Hamad a gefenta ta shanye warm milk din.
“Ina princess ne?”
“Tana dakin ammah tana barci”
Dan girgiza kai amra tayi alamun gamasuwa kafin ta juya wajen Hamad ta fara mashi wasa……
Yamma nayi wajen karfe shida saiga abbansu yazo, tarba ta mutunci ammah tayi mashi sosai anan sitting room don Har abunci saida salima ta ajiye mashi da lemuka agabanshi bayan sun gaisa da ammah.
In kunga babansu amra kamar bashi ba yayi qiba sosai kamar ba labaran ba, sai yanxu nake Ganin girmanshi ya fito sosai, kudi sun zauna mashi, Har lokacin idan zai gaisa da ammah saiya dan dukar da kanshi koyaya ne.
Gaba daya saukowa sukayi suka gaisa dashi Banda amra dake kwance a daki saboda ciwon kai data wuni dashi, bata ma san yazo ba,
A parlor kuwa gaba daya suna zaune a sitting room Harda Aman wanda yanxu ya daina biye kanshi, don bayan sunyi magana da salima haka ya fada courage dinshi yaje Har gidan gona ya nemi Afuwan Abban su akan abubuwan da yayi mashi, tashun farko labaran ya nuna mashi Ay komai ya wuce daman bai rikeshi da komai, Aman yaji dadin haka sosai don baiyi tunanin haka abban nasu keda sauqin kai ba.
Gyaran murya Abban nasu tayi yace “muhammd baya nan ne? Banga sirikinsa Nawa ba?”
Ammah ce ta dan murmusa tace “Ay yau tun safe ya futa bai wuni a gidan bama”
Sallamar salima ce ta katse su, hannunta rike da Hamad da Hamid, tana karasowa ta mikama Abban su, fuskanshi duake da murmushi ya karbe yace “Masha Allah Yan dugul dugul an fara girma Allah ya Raya”
Gaba daya amsawa sukayi da Ameen.
Salim ne ya matso inda yake yace “abba yau Zan bika”
Sunkuyar dakai labaran yayi yace “Ay bani zaka tambaya ba malam”
Sallamar Amar ce ta katse su, anatse yake tafiya cikin kamewa har ya karaso parlorn, yana karasowa ya duka ya gaishe da malam labaran,
Cikin fara’a ya amsa shi inda yake tambayarshi ya aiki da hidimar iyali.
Basu wani jima ba aka kira sallar magrib don haka suka wuce masjid gaba dayansu achan ma sukayi alwala sukayi sallar isha’i
Ammah ma sama ta wuce zuwa nata bedroom din tayi sallar kafin ta futo sanye da hijab ta wuce dakin amra, da sallama ta bude dakin ta shige hannunta rike da wata katuwar paper bag.
A zaune ta taddata kan sallaya tana lazimi, karasowa ammah tayi bakin gado saida ta idar kafin ta nannade sallaya ta mike jiki a mace ta karaso bakin gado ta dan duka tace “barka da dare ammah”
“Barka dai my dear,zauna”
Zama amra tayi tana fuskantarta, “daughter naga Duk kinyi sanyi yau dinnan Akwai abund ake damunki ne? Ko baki son komawa chan ne?”
Saurin girgiza kai amra tayi kanta a kasa “ah ah ba haka bake kaina ne kawai ke min ciwo”
“Toh Allah ya sawaqa,”
Kanta a kasa ta amsa ammah da “Ameen”
Shuru ne ya biyo baya kafin ammah ta janyo paper bag din ta bude, wani box ta fara fiddowa ta ajiye akan cinyar amra “daughter ga wannan, kyauta ce dana so na baki tun watannin baya da suka wuce,“
Kallon box din amra tayi kafin ta dago kanta murya ta chan ciki tace “ammah….”
“Karki ce komai daughter kyauta ce kawai nayi maki okay?”
Girgiza mata kai amra tayi kafin ta sauke kanta kasa “thank you so much ammah Allah ya Kara arziki da budi”
Ammah bata amsa ta ba ta fidda wani hadadden laffaya orange color wanda yasha stones sosai, kana Ganin lafayan kasan ba anan akayi shi ba, designer ne mai Kyan gaske,
Ajiye mata shi ammah ta gafenta tace “ki shiga ki wanka saiki saka wannan ki sauko Abban ku yazo yana jiranki”
Ammah na kaiwa nan ta mike tsaye, “ki hanzarta”
“Tohm ammah” amra ta fada jiki a mace, ammah na fita tabi lafa yuan da kallo, hannunta dayasha red henna ta daura akan lafayyan, kafin ta maida hannun nata kan box din, kamar wadda ke jin tsoro haka ta soma bude box din, idanunta ne ya sauka akan tapkekiyar sarkar gold da dan kunne awarwaro Harda zobe dake ta faman sheki, wato idanu tayi waje taba kallon sarkar, wani irin dadi ne ya ziyarceta, babu abunda take a cikin zuciyarta sai godiyar Allah daya azurtata da sury Ka ta gari mai so da kaunarta ada ita ba kowan kowa bace sai gashi lokaci guda Allah ya sauya mata rayuwa.
Jiki a mace ta mike ta wuce bathroom tayi wanka a gaggauce Har ta fito daga wankan jikinta a mace yake kamar Ana tura ta,
Bata tsaya wani kyale kyale ba ta bude wardrob dinta ta janyo wata atamfar super wax Riga da skirt sai set of bra da pants da under skirt,
tana daukowa ta ajiye akan gado ta wuce gaban dresser ta dan goga mai kadan a jikinta, tana gogawa ta wuce gaban gadonta ta soma shirya wa, cikin Yan mintuna qalilan ta gama shirya wa ta Dora lafayan akan atamfar nata, gashinta dake a kwance lub ta kwance ta tattare shi baya kafin ta daura dankwalin atamfar, tana gamawa ta bude box din sarkar da ammah ta bata ta saka sarkar da dan kunnen,
Tana gamawa ta rufe box din ta Adana shi cikin bedside drawer kafin ta wuce gaban dresser ta kurama kanta kallo, tayi masifar kyau sosai dukda batayi wani
kwalliya ba a fuskanta ba don ko kohl babu a idanu ta, ko a jikinta tana jin rana irin ta yau ta fita daban, sai a yanxu take jin wani iri, Anya zata bishi kuwa? Maysa ma zata bishi?, she’s happy zamanta haka nan daga ita sai yaran ta da ammah babu wnai stress dinshi saidai bazatayi jayyya da maganar ammah ba don haka ta dan fesa ma kanta turare mai sanyin kamshi, tana nan tsaye Salim ya shugo dakin “adda abba yace kizo”
“Gani nan” ta amsa shi tana ajiye kohl din data dauka ta dan goga a fuskanta, kafin ta juya ta zura bedroom slippers dinta ta nufi hanyar futa daga dakin nata,
Anatse take saukowa kasan harta karaso sitting room, babu kowa a parlorn sai abbansu don haka tana karasowa ta dan duka domin gaishesa, fuskanshi duake da murmushi ya kalleta ya mata nuni da gefen da yake zaune kan kujera, hankali ta tako tazo ta zauna nan gefen nashi kanta a kasa don lokaci guda taji wani irin sauyi a tattare da ita, “Alhamdulillah!!! Godiya ta tabbata ga Allah daya kaddara mana yanda rayuwar mu zata kasance, Aisha!!” Ya kirata anatse,
Dan dagowa amra tayi idanu ta Har ya dan fara jaa tace “naam abba!”
“Aisha kiji tsoron Allah kina da ilimin addini dana Boko daidai gwargwado, Ina jin takaicin shekarun da akayi mana iyaka dashi, wanda yasa banga tasowarku ba ammah Ina alfahari dake da macen da kika zama, ayanxu ke uwace ga yara har uku wanda suka zama kamar kyautar allah, aisha kiji taoron allah kiyi ma mijinki biyayya karki bani kunya, aljannar ki na kafarshi Wallahi aisha idan kika kuntata mashi bazan iya yafe maki ba, wannan bawan Allahu da mahaifiyarshi sun gama yi mana komai a duniya, maganar da kikayi min kwanaki ta girgiza ni don idan har kika tafi da wannan kudi don a ranki to tabbas kinyi butulci, allah ya rufa maki asiri ya Baki miji na gari ya Baki sirikarta ta gari da bakinki kince min yanda yake kula dake kamar ita ta tsugunna ta haifeki,don haka nake fatan ki faranta ma danta ki mashi biyayya, ki zama madafar da zata sanya mashi nutauwa ki kawo mashi kwanciyar hankali a rayuwarshi don da haka ne kawai zaki saka ma hajiya da abunda tayi mana, I trust you my daughter and I’m proud of you, Ina fatan allah ya baku zaman lafiya ya kore maku Duk wata futina kinji ko?”
Amra dake kuka shabe shabe don ba karamin dukan zuciyarta kalamanshi sukayi ba sosai,
Hannu abbansu yasa ya goge mata hawayen ya cigaba “kibi mijinki ki mashi biyayya sannan kiyi hkuri a Duk yanda kika tsinci kanki kiji?”
Girgiza mai amra tayi tana hawaye Bakinta na karkarwa tama rasa me zata ce mashi,
Salima ce ta sauko kasan hannunta rike da