Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   28 / 94

81K to 84K   out of 279.4K words

saidai yanada girma sosai Sai mutane dake ciki da baza su wuce goma ba fuskokinsu a rufe”

Saurin Mika mashi wani cup din tayi tace “wow mugani”

Karban laptop din tayi kafin ta kalleshi ta gefen idanu ganin ya rufe idanu yasa tayi saurin bude connecting da wayan ta ta tura ta airdrp don Mac book ce laptop din, tana turawa tayi saurin shiga wasu files din nanma ta tura wasu kam basu shiga ba irin files din kudadeden dake cikin accounts, Harda hotuna saida ta tura duka. Tana gamawa tayi saurin kashe laptop din ta maida cikin drawer din ta dawo kan gadon ta tattara kayan data tube ta maida ta kafin ta zafi wayarta da jakarta, da gudu ta sauko kasa don anytime zai iya Tashi don gaba daya abun baya wuce minti talatin yake sakin mutane.

Driver dake zaune cikin mota ya hango

Fitowa ta a furgice bai ce komai

Ba don oga ya gargade shi akan komi ya gani ya nuna bai gani ba.

Alh Kabiru kuwa tun bayan fitarta bai dawo hayyacinshi ba Sai bayan minti talatin, da kyar ya Tashi don wani irin matsanancin ciwon kai ne ya taso mashi, gaba daya ya manta Duk abunda ya faru, abu daya ne ya iya tunawa shine lokacin data sauko daga bene da maganganun da sukayi anan qasa sai giyar daya bashi yasha bayan wannan ya kasa tuna komai, toilet ya wuce don tunanin maybe tana ciki yana shiga yaga wayam babu ita,shuru ya danyi don ya fara suspecting, kamar wanda ya tuna wani abu ya bude wardrop dinshi nan take yaga babu laptop dinshi da yake aje important documents a ciki, saurin bude dayar drawer yayi nan take yaga laptop din, hankali tashe ya tsaya kyam don tabbas a Dayan side of drower yake aje laptop, me hakan ke nufi kenan? Yar leken asiri ce? Ya bama kanshi ansa, da sauri ya maida kayanshi da wandonshi ya fuce daga dakin, tundaga nesa driver ya hango tashin hankali a fuskan alhaji, don haka yana karasowa ya bude mashi kofa ya shiga ya jasu suka fice suna fita alhaji ya fara balbaleshi “kai dan ubanka kaga sanda yarinyar nan ta fita”

“Eh, minti talatin da suka wuce ta fita”

“Toh dan ubanka shine baka tsaidata ba”

Shuru driver yayi don kamar akanshi ake shirin huce takaici “

Guest house dinshi suka wuce, nan take ya fara kiraye kirayen yaranshi ya baza su don a fara nemanta aduk inda take, nan take ma ya bada umarnin a kwasheta Idan an ganta ma.

Hameeda dai ranar taga tashin hankali don mai gadin gidanta ya kirata ya shida anzo neman ta, kuma daga gani ba mutanen arziki bane nan take ta gane cewa Ana farautar ranta, wanda ta tabbatar alhaji kabiru ne, abunda yafi tayar mata da hankali shine Kiran data dunga yima Amar baya shiga kwata kwata, kuka ne kawai ya kubce mata hankali tace kawarta ta kalleta tace “meeda kukan nan na menene”

“Baby dan Allah ki boyeni sugar faraytar rayuwata yake” da sauri wadda ta kira da baby tace 

“Ban gane ba?”

“Baby bazaki gane ba, nidai Duk wanda zaizo kice baki san inda nake ba please”

“Gaskia bazan iya boyeki ba bansan wace masifar kika kwaso ba karki janyo a hada dani, kinga Tashi ki bar jin gida”

Kuka sosai meeda tayi tace “lallai baby ashe daman ba zaman tsakani da Allah kikeyi dani ba, Toh babu ni babu ke har abada”

Tana kaiwa nan ta zura hijab dinta da niqab data zo dashi ta fuce, tana futa ta wuce tasha, bata dade da futa ba wasu gardama suka zo gidan baby, har duka saida sukayi mata don su ce Idan bata fada masu inda take ba zasu kashe ta karshe dai ta shaida masu bata dade da fita ba, don batafi minti goma ba da fita suka shugo.

Hamieda dai kauye ta nufa don buya don tabbas ta gane Ma kanta masifa akan kudi.

Amar kuwa kamar yasan zata iya nemanshi ya turama asad number dinta yace ya kirata kafin ya dawo.

Amra….

Kwance take kan doguwar kujera tana kallon tv, sanye take da doguwar Riga har kasa pink mai dan gajeran hannu cikin set of maddd kayan da haifa ta sayo mata su jiya, kayan kala goma sha biyu ne, sunyi mugun haduwa sosai don basu da nauyi gashi tana jin dadinsu, kanta yasha gyara sosai yayi coily, har wani shining yake, fatarta ta Kara kyau don tasha gyara a cikin kwanakin wanda haifa ta dage da kaita kusan kullum, fuskarta babu komi Sai dan kohl data goga a kasan idanunta da suka Kara mata kyau, Bakinta Ma ya danyi pink dalilin wani scrub da haifa ta kawo mata tana scrubing lips din dashi,jikinta babu gashi ko daya wanda ya fidda asalin kyawu na fatarta da hutu a bayyane, jikinta wani irin sohirtaccen kamshi ke fitarwa wanda haifa ta amso mata wajen ummi, aranta tana matukar jin dadin yanda mutanen kirki suke around her, duniyar tunani ta fada wanda yasa ta dan lumshe idanunta, gaba daya ta fada wani yanayi Mara misaltuwa don yanxu Duk wani damuwa ta ragu aranta sai karfin gwiwa da take samu wajen haifa da nadine, yanxu babu abunda yake budi face ta gama makaranta ta koma wajen Yan uwanta.

Bude kofa akayi kai tsaye, ahankali kunnuwanta suka soma jiyo mata takun tafiya wanda yake jin takun har cikin zuciyarta, kamshinsa ne ya biyo baya wanda yasa ta tuna da shi lokaci guda don gaba daya tunda ta dawo kusan wata guda kenan ta manta da Duk wani alamarinshi wanda ta sanadiyar haifa da taimakon Nadine ta samu karfin gwiwa, sanye yake da kayan da ya taho

Airport dashi Riga da wando na herms sai jacket dinshi daya daura ta akan kafadarshi, takowa yayi har cikin sitting room din hannushi zube cikin wandon nashi, tun daga nesa ya hango tudun ass dinta don rubda ciki tayi ta kwanta, saida ya dan tsaya na Yan mintuna kafin ya tako Har zuwa sitting room din ya tsaya daga can nesa bayan kujeran yana kare mata kallo anan tsaye, take yaji

Wani yarr a jikinshi kallonta kawai da yayi, ta Kara kyau da cika sosai a idanunshi, skin dinta Sai kyalli yake yi, ya kwasa kusan minti biyar yana nan tsaye ba tare da saninta ba, gyara tsayuwan shi yayi baice komai ba still bai daina kallonta ba kamar mai tunanin wani abu, nadine data hangoshi tana shirin karasowa hannunta rike da bowl na popcorn tayi saurin karasowa tace “welcome sir”

Gaban amra ne ya bada damm,idanunta alumshe, wato hancinta ba karya ya mata ba shi din ne a tsaye don tunda ya fara takowa taji gabanta na faduwa,

Gaishesa nadine tayi kafin ta aje Mata popcorn din a kasa tadan zunguri kafarta alamu ta miqe kafin ta wuce ciki tana fatan amran tayi abun arziki, don tasan sarai idanunta biyu lokaci data taci kitchen kuma bata wani dade ba ta Juyo zuwa parlor din daman pablo ya daina kwana a gidan sai maid itama tana chan part dinta a baya.

Shi Duk a tunaninshi ma barci take don yasan Idan Har tasan yana tsaye zatayi saurin mikewa, m5 ne ya bude kofar shima hannunshi rike da trolly dinsa da kayan amfaninsa ke ciki, tun kafun ya karaso wajen ya maida idanunshi kan hanyar ya mashi nuni da ya aje ya tafi anan, ajewa kawai m5 yayi ya juya, jin alamun shuru yasa ta dan gyara kwanciyarta da yasa ass dinta dan muskutawa, take ya hadiye wani abu daya tsaya mashi a makogaro, itako tasan yana tsaye tsoronshi ya gama cikata, tana son yin abunda Nadine ta fada mata saidai tana tsoronshi sosai, tunawa da kalaman nadine da take cewa “whenever you feel like you can’t do it, just think about the pain and the lies he cost you”

Take taji wani irin abu ya daki zuciyarta tunawa da abubuwan da yake mata, kamar wanda aka tsugula ta Tashi zaune still Gabanta na faduwa ta daga hannunta sama tare da yin miqa ta buntsuru kirjinta gaba in a calming tone tace “ashhhhh”

Idanunshi Har wani qif qif yakeyi yanda ko kiftawa baya yi, popcorn din ta dauka takai bakinta nan take ya gane ashe ba barci take ba, hade rai yayi sosai don baya son raini, wato tasan da zuwanshi, yana shirin magana kenan kamar wadda tasan zaiyi hakan ta dan juyo ta kalleshi da idanunta da suka qanqance, samun kanshi yayi da Kasa cewa komi Sai binta da yayi da ido yanda danunta suke sheki, saurin kauda nata idanun tayi kafin ta sake maidashi kansa tayi kokarin fidda surprise expression tace “laaa ya…yaa, sannu da dawowa”

Ta fada tana miqewa ta tako Har inda yake jikinta na girgiza, Kasa motsi yayi don ji yayi wani iri yanda tace mashi “yaa…yaa”

To his surprise tana karasowa majestically ta bude hannayenta ta rungumeshi very tight chan beneath her breath tace “sannu da dawowa”

Nan take yaji kamar Ana tsikararshi, he can feel her chest around him, hannayenta na nade da kugunshi ta rike gam ta lumshe idanu, dake ya fita tsayi sosai yana hango tsakiyan kanta da coily gashinta dake fidda wnai kamshin mai dadi, katse mashi tunani tayi tace “Bari na barka ka huta ko,”

Ta karashe tare da zame jikinta ahankali, take yaji kamar karta fita daga jikinshi, saurin runtse idanu yayi yanaso ya bar wajen ya kasa don idanunshi ne sukayi

capturing sculpture ass dinta dake cikin rigar tana tafiya kamar me cat walking ahankali harta fara hawa sama, dan juyowa tayi ta kalleshi ta sauke mashi wani lausassan smile da yasa shi jin wani iri, bazaka taba gane shi ba kwata kwata, fuskanshi na nan yanda take saidai ita tayi nasarar hango wani abu a cikin idanunshi, tana karasawa daki ta sauke wani ajiyar zuciya, tace “ya Allah… ashe Zan iya wayyo Allah naaa, meysa nake tsoro shi ne haka kamar naga malaika,” murmushi kawai tayi tace “hmm this is just the beginning, kai amma nayi mamaki, ya kasa cewa komi”

Chan kuma tsoro yadan durar mata tace “what if…” saurin kauda zancen tayi ta karasa cikin dakin ta kwanta tayi rub da ciki, har lokacin tana jin giant kirjinshi dake dauke da kamshinsa a jikinta, saurin runtse idanunta tayi tana jin wani Sabon feeling.

General ko mamaki ya hanashi cewa komai don gani yake kamar ba ita bace, har cikin idanunshi ta kalla, he can’t believe it, Toh kodai shi shock din daya sa zuciya ta ya kusa harbawa ya taba brain dinta, rasa wani tunani ma zaiyi,kamar wanda aka toshe Ma baki karshe Ma dai dakyar ya wuce sama don kamshinta har cikin kwakwalwarsa kamar Ana connecting dinshi zuwa gareta at the same time kamar an rufe mashi baki, tsaki kawai yayi ya wuce daki.

Allah ya tashe mu lafiya guys

Yau amra anyi abun arziki

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 121

Update!!

20/05/2023

Unedited

The next morning….

Wani irin barci tayi na kwanciyar hankali, tun bayan sallar asuba bata Tashi ba sai wajen karfe goma, agurguje tayi wanka wanda saida ta dauka kusan minti talatin tana skincare, fitowa tayi daure da towel, kamshin body wash dinda aka jera mata a toilet datayi amfani dashi na fita daga lausansan jikinta,cikin natsuwa ta shafa body cream dake cikin set din da aka jera shi kan dressing mirror, mayukan kanshi tasan na kudi ne sosai, don ko haifa data zo kwanaki saida tace masu tsada ne sosai.

Agurguje ta shirya cikin wata doguwar riga wanda ta dan kamata sosai, rigar kamar rubber take Sai tayi lapping da jikinta sosai, turarukan nadir kan dresser din ta feshe jikinta dashi don kafin ta nannade gashinta cikin mayafin doguwar rigar, kallon kanta ta tsaya yi kafin ta janyo wayarta don wata irin yunwa ce ke

nuqurqusarta, cikin natsuwa ta fito, tunda ta Tashi take cikin rashin walwala, stairs ta fara saukowa kafanta sanye da bedroom sleepers da shima yake cikin abubuwan da m5 ya sayo, ahankali take takowa Har takai sitting room din kasan, dago kanta tayi don nufa hanyar dining ta hango Nadine na shirin fitowa daga kitchen, 

A hankali ta soma karasowa wajen dining din tace “hey good morning Nadine”

Da sauri Nadine ta amsa ta da “good morning ma’am”

“yau kece a kitchen”

“Yes ma’am the other chef yayi handing over responsibilities din ayyukan gidan a hannuna including abinci da anything daya dangancin cikin gida”

Dan shuru amra tayi tana nazari ta kafin tace “okay”

Karasawa tayi wajen dining din saida tazo dab da wajen ta ji kamshin turaren sa, saurin dakatawa tayi don harga Allah ta manta ya dawo, gabanta ne ya soma bugu dab dab, Har Nadine ta wuce ta domin aje warmer dake rike a hannunta, Nadine ce ta karaso inda yake don already tayi serving dinshi breakfast tace “sir do you anything”

Bai kalleta ba hannunshi rike da cup of coffee yace “no thanks” 

Maganar ce ta maido ta daga tunanin data shiga, ji tayi kamar ta juya saidai babu damar hakan don haka tayi saurin tattara kuzari ta ta karaso gefen kujeran da yake zaune ta janyo fuskanta fayau ta zauna ta dan kalleshi kafin ta kauda kai gefe tace “good morning yaaa..ya”

Saida ya dauka kusan minti biyu kafin ya dago idanunshi dake kashe Duk wani kuzarin mace ya mata kallo daya kafin ya kauda idanunshi yace “morning”

Tabe baki tayi don wannan yana daya daga cikin abunda yake bata haushi game dashi, zaka dage ka gaishesa ta ya sha kamshi kafin ya amsa, Nadine ce ta karaso inda take tace “Ma what would you like to have”

Dan murmushi tayi Ma Nadine tace “thanks Nadine zanyi serving kaina”

Juyawa Nadine tayi zata tafi tayi saurin cewa “bazaki zo muci ba”

Da sauri Nadine ta kalli bangarenshi fuskanshi na nan yanda take a hade, amra kuwa bata damu da kallon inda yake ba, da sauri Nadine tace “I’m sorry ma’am, na rigada naci abunci”

Tana kaiwa nan tayi saurin wucewa, Nadine na tafiya ta mike tare da janyo plate tayi serving kanta liver sauce da chips agefe? Tana gamawa ta mike, tunda ta zauna bai kalli inda take ba saida ta mike, tana shirin tafiya akausashe yace “go back to your seat”

Yanda ya fada babu wasa yasa ta dan turo baki wanda akan idanunshi tayi hakan kafin ta zauna, dan dole haka ta fara tura abuncin a bakinta, tsit kake ji sai sound din karar spoon da take kaiwa bakinta, ko rabi bata ci ba ta ture abuncin gefe, yana sane da ita, Har saida ya gama kafin ya miqe yace “meet me upstairs”

Gabanta ne ya bada damm don bata san me zaiyi mata achan dinba, harya fice Ma ganinta tana tunanin maganar shi, saurin miqewa tayi ta wuce kitchen, Nadine dake gyaran cooker ta juyo ta kalleta, da sauri ta karaso gaban Nadine Har jikinta na bari tace “Nadine ni tsoro nake ji”

Kallon yanda jikinta ke bari Nadine tayi tace “meke baki tsoro?”

Kallonta tayi idanunta har sun danyi jaa tace “yace I should meet him upstairs, ni gaskia tsoron kebewa nake dashi, Wallahi bazan yarda wani abun ya sake shiga tsakanina dashi ba”

Hannunta Nadine ta jawo gefe tace “ma calm down,kin manta maganar da mukayi dake?, dole saikin cire tsoro nan zaki samu ki kwato yancinki,kije dakin nashi kiji mai zaice mashi qila Ma abunda kike buqata zai baki”

Tunaninta danyi kafin tace “okay bari naje, amma tsoro nake ji wallahi”

Murmushi Nadine tayi mata tace “remember abunda na fada maki? Duk sanda kikaji tsoron shi ki tuna abunda ya maki chan baya,”

Jikinta ya gama sanyi haka Nadine ta bata karfin gwiwa ta fuce daga kitchen din, jiya da ya dawo harta tunkareshi ta dauka abun zaizo da sauki saidai yanxu d more yana existing around her the more take jin tsoron shi, tana cikin wannan tunanin ta hau 3rd floor, kofa daya ce a wajen, saida tayi knocking jin shuru yasa tayi tunanin maybe yana cikin bedroom, bude kofar tayi ganin duhu yasa gabanta faduwa don haka ta danyi baya kadan, haske ne ya bade dakin sanadiyar censor light din dakin, mamaki ta tsaya yi ganin gyming equipment, shiga ciki tayi ta karema wajen kallo, girman wajen haryafi wani wajen gyming din, babu abunda babu a ciki, takowa tayi Har gaban wajen curtains da ya rufe glass din daya zagaye dakin, tana karaso wajen shima curtains din ya bude da kanshi, sanin haka duka gidan yake yasa bata tsorata ba ta tsaya kallon view din wajen, saida ta dan zagaya ko’ina Har wajen shower dake wajen shima glass yadan rufeshi ta gefe, kallon ko ina tayi tana mamakin irin kudi ta aka zuba a wajen, gaba daya gidan kamar wata aljannar duniya Duk inda ka shiga saika kusa yin kauyanci , murmushi ta danyi tace “daman akwai wajen gym a gidan hmm, allah kayi mana arziki”

ta juya ta rufe kofar, ganin babu wata kofar anan yasa ta shiga lift ta Danna 4th floor don shi kadai ne ya rage a wajen madannan lift din, tana dannawa cikin Yan seconds kofar lift din ya bude, rarraba idanu ta farayi don nanma kofa daya ce, saidai wannan kofar ta glass ce gaba dayanta, daga waje baka ganin komi ta ciki kuma zaka

Iya ganin wanda ke tsaye a wajen, tunda ta karaso gaban kofar gabanta ke faduwa, hannunta sa Danna handle din kofar karfi ya bude, nanma censor light din ne don haka ta dan kutsa kanta ciki take hasken ya bade ko’ina, ahankali ta furta “wowww tana bin ko’ina da kallo”

Parlor ne tafkeke sosai wanda ya kawatu da kaya marasa yawa, set of kujeru sai resting chair daga gefe wadda tasha pillow, harda fireplace daga gefe sai katuwar tv kamar cinema, parlorn is so cold don haka ta dan kalli ko’ina da kyau, shima glass ne ko’ina sosai Sai view na waje da ruwa, nan ta gane ashe bayan

28 / 94