Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   40 / 94

117K to 120K   out of 279.4K words

tunanin da zatayi don bata gama yarda da abunda idanunta ke nuna mata ba, saida ta fito daga office din health team wadda take supervision dinsu ta wuce office ta zauna, kallon certificate din ta sakeyi ahankali wani irin hawaye na sauko wa daga fuskanta, she can believe what her eyes are seeing, daga paper tayi da kyau ta kalli sunanta Baro Baro, sauke idanunta tayi wajen da yayi signing da sunanshi a kasa, she can’t believe it, haifa ce ta shigo office din da sauri ta goge hawayen dake zarya akan fuskanta, da sauri haifa ta karaso don ta hango yanda yake hawaye ke zarya a fuskanta,”babe is everything okay?”

Kallon certificate don haifa Tayi Ganin yanda amra ta kwakume, karba yayi ya sama karantawa, itama tayi mamaki sosai don bashine yayi signing nata ba, saidai itama an bata permanent license, murmushi kawai tayi tace “why are you crying babes?”

“Ba komai I just can’t believe it babe”

Murmushi haifa Tayi mata tace “nima nayi mamaki sosai, actually he’s not that bad, “ ta fada tana dariya, dan duka ta amra tayi tace “ay ko duniyar nan ya hada ya bani bazai taba compensating abunda ya karba daga wajena ba” 

Sanin abunda yake nufi yasa haifa saurin kauda zancen don yanxu sai emotions yasa su fara Koke koke gashi bata son suyi ruining wannan moment din na gama aikin su lafiya,kallonta haifa tayi tace “gobe fah zamuje yawo, get black ready card din abuh zaiji jiki gobe”

Dariya amra tayi tace “kai babes ki bar card din abu ya huta don Allah”

Dariya haifa Tayi tana jin kaunar amra aranta tace “ke kinsan bazan hakura ba, anyways Ay Duk Nawa ne cos I’m the heir so I’m spending it to my satisfaction”

Murmushi kawai amra tayi tace “Yanxu shikenan daga yau mun gama housemanship dinnan oh ya Allah”

“Yea babes saura graduation kuma in 3 months time” haifa ta fada

“Hmm Ay saidai naga hotunan ku,” amra ta fada fuskanta dauke da damuwa

Haifa ce Tayi saurin cewa “babes why?, bazaki zo graduation ba”

“Nop, wa zai biya min na dawo, dole na taci wajen kannena”

“So you’re leaving this opportunity behind kenan? Zuwan ki is not a problem babe, I can work on that kinga yanxu jin samu katin kasa (citizenship) na kasar nan, zansa abuh yayi sponsoring trip dinku keda qannenki”

Murmushi kawai amra tayi tana jin qaunar haifa don kawa ce ta gari wanda zata iya mata komai a duniyar nan saidai she’s not that selfish, bazata taba daura ma wani nauyin ta ba da qannenta, ita gaba daya ma zaman kasar ne yanxu bata so komai ya fuce aranta Har gwanda ta koma tayi amfani da certificate achan dukda tasan ba wani kudin kirki maaikantan lafiya ke samu ba anan Nigeria, she will manage that tayanda zata kula da qannenta, hannun haifa ta kamar ta fusknaceta tace “I will always be thankful to Allah for having you as a friend, but just a friend but a sister from another mother, but let’s not talk about it now”

Rike hannunta itama haifa Tayi tace “please think about it, Wallahi idan kika tafi bansan ya zanyi ba, kin zama wani chapter na cikin rayuwata da nake so ki kasance aciki har abada, I want us to grow old as best of friends,”

Hawaye ne ya gangaro kan fuskar haifa ita amra already hawayen take yi na rabuwa da aminiyar Tata, sun dade a haka babu ne rarrashin wani Har lokacin tashinsu yayi, haifa ce ta fara yin gaba saboda Kiran da ummi tayi mata.

Karfe hudu daidai itama amra ta fito cikin natsuwa, ganin m5 a tsaye yasa ta dan sauke shi yar zuciya ta fara takowa saida tazo dab da shiga motar ta juyo ta karema wajen kallo for the last time, abubuwa da dama na running through her mind, so This is the last time dazata Kara saka kafanta a wajen kamar haka, she has lots of memories anan,saurin janyo wayarta tayi ta kalli m5 tace “can you please take a picture of me”

“Yes ma’am” ya amsa tare da karban wayar, gaban tsakiyar compound din ta tsaya, hawaye na gangarowa a fuskanta haka ta goge tayi smiling ya dauka kusan guda uku,  yana gamawa ta juya gefe tana kallon tambarin uae armed forces headquarters a zaman buliding din, m5 na Ganin haka ya janyo wayarshi yayi airdropping hoton nata kafin ta juyo, karasowa tayi ta karbi wayar daga hannunshi tace “thank you” kafin ga shige cikin motar,shima bai tsaya komai ba ya shige ya ja su zuwa gida.

Suna isa ta fito hannunta rike da laptop da handbag dinta ta wuce ciki, tana fucewa yabita da kallo kafin ya maida idanunshi kan hotunan da yayi mata guda uku, daya ta su ku yar da kanta daya tana kallon camera daya kuma tana goge

hawayen daya zubi mata, she look so breathtaking an cute at the same time, saurin kauda abund ake ranshi yayi ya tura ma general pictures din nata.

Amar na office din asad message din m5 ya shugo wayar, relaxing bayanshi yayi kan kujera ya bude message din, ganin pictures yasa yayi saurin budewa nan take hotunan ta suka bayyana, tayi masifar kyau fuskanta babu kwalliya sai dan kohl, lips dinta yayi pink yarrr, gaba daya he’s lost baya ma jin abunda asad ke fada, Ganin tana kuka yasa ya fara wondering kukan me takeyi, asad dake ta faman Kiran “oga” ganin yanda Amar ya kafa ma waya idanu yasa ya tako ya zagayo bayanshi ya tsaya don Ganin abunda yake kallo,shima idanu ya zuba mata don bai taba ganin budurwar da is captivating and attractive at the same time kamar ta ba, ya kasa dauke idanunshi akan hoton shima, saida ya gaji da tsayuwar yace “ahh lallai oga dole Ka kasa bani amsa, Ka tafi chan wata duniya, by d way wace wannan damsel din?”

Wani irin kallo Amar ya watsa mashi tare da kashe wayar yace “tun yaushe kake tsaye a kaina”

Da wasa asad yace “about an hour ago”

Ya fada yana dariya, matse fuska Amar yayi yace “what where you saying?”

“Ni harna manta mema zance maka saboda wannan picture ya tafi da tunanin Nawa”

Wani irin kallo Amar ya watsa mashi daya sashi cewa “wooo calm down oga, daga gani Ka kamu da yawa, dan Allah wacece wannan?”

Banza Amar ya mashi karshe ma daya dameshi fita yayi daga office din don take yaji wani irin haushin sa.

The next day..

Saturday morning, da sassafe haifa ta kirata a waya, cikin barci ta dauka tare da cewa “hellowww…”

“Get up sleepy head, we have a lot to do, kinsan daga yanxu komai ya chanza, no more work no more readings, daman I’m sick and tired of studies da komai ma, now get up”

Dariya amra tayi cikin barci tace “Allah ya shirya ki babe”

“Ameen get up” haifa ta amsa ta kafin ta kashe wayar, kallon screen din wayar amra tayi Ganin karfe takwas da rabi, miqewa tayi ta wuce toilet tayi wanka, ganin pad dinta saura daya yasa tayi planning sayan da yawa don ta tafi dashi chan Nigeria don babu irin su anan Nigeria gashi suna da dadin amfani sosai, fitowa tayi ta shiga closet tsaya, tana tunani, oh Wai yanxu ita amra itace tayi luxurious rayuwa haka? Rayuwar da bata taba tsammanin zatayi irin ta ba a Doran kasa, saurin kauda tunanin tayi aranta don yanxu komai sata kuka yakeyi, cikin natsuwa ta shirya cikin wata luxury abaya wanda kana ganinta kasan ta jiqu da kudi sosai, bata tana saka abayar ba don ta Gansu ajere kusan guda goma bata taba attempting sakawa ba don sunfi karfin ta nesa ba kusa ba, and tana managing level dinta gudun magana,yau dinma zata saka ne saboda ita going to

be the last days da zatayi living in luxury, a tsanake ta shirya fess ta feshe jikinta da turarrukan dake shaqe akan dressed dinta, tana gamawa ta mike ta koma closet ta jawo wata gucci chain bag,lokacin dataga jakar ta shiga ranta sosai don kana Ganin jakar kaga kudi hakan yasa ta duba kudi ta don ta saya irinta, kudin jakar nan ya bata mamaki sosai don jakace that is worth a million, Har ta haura miliyan daya da rabi, Ay tana Ganin haka Tayi saurin fita daga cikin official site gucci don Ina ita Ina jakar kusan miliyan biyu,kallon jakar tayi kamar karta dauka chan kuma ta janyo ta kawai ta fito, box sun jakar ta bude nan take taga Harda takalmin jakar shima kudinshi daban don a kalla gaba daya sunkai kusan miliyan uku gaba daya, takalmin hills ne ta kasanshi anyi ado da diamond, sakawa tayi chip ya zauna daidai a kyakyawar kafarta, wani irin murmushi ne ya kufce mata, fitowa tayi ta tsaya ta goga jam baki matte dayayi ma oval lip dinta kyau sosai, kohl dinda bata rabo dashi koda yaushe ta saka Harda eye liner, fadin irin kyau da amra tayi arana irin ta yau ma bata lokaci ne, karfe sha daya daidai haifa ta iso, bata shigo gidan ba ta kirata, tana gama waya da haifa ta kalli kanta, ahankali ta furta “Masha Allah”

Murmushi ne ya kufce mata kafin ta fuce daga dakin, tundaga kan stairs kamshinta ya hade ko’ina, kallon inda take saukowa Nadine tayi, nan take ta yar da cup din hannunta ya fashe tasss, dagowa amra tayi tace “ya Allah, be careful”

Galala Nadine ta daki baki tana kallonta tace “wowwww ma’am you…you loook so beautiful”

Dariya amra tayi tace “thank you Nadine”

Ganin tana shirin fita yasa Nadine cewa “break fast is ready?”

Juyowa amra tayi tace “I’m going out with haifa, zamuyi breakfast tare”

Tana kaiwa nan ta fuce daga parlor Nadine ta bita da idanu tana mamakin yanda general ya kasa Ganin irin sirrin kyau da Allah yayi ma amra, lallai wannan yarinya ita ake cema allura cikin ruwa mai rabo kan dauka, indai Har ya bari ta kubce mashi he’ll surely regret it one day”

Amra na fita ta hango m5, shima dai kasa dauke idanunshi yayi akanta saida tazo wucewa inda yake yace “good morning”

Da mamaki shi yau smiling tayi mashi Harda cewa “morning sir”

shiga motar haifa Tayi nan ma bata barta ba babu irin hype din da haifa batayi mata ba karshe dai cewa tayi “Zan koma fa idan bazaki kunna mu tafi ba”

Gaban wani floral eatery suka tsaya sukayi wani haddaden breakfast kafin su fito atare, Duk wand ayagansu yasan yayan masu hannu da shuri ne, bare ma amra wadda tafi haifa cika da komai ba, daga nan flower garden suka fara zuwa suka sha hotuna nan haifa take tuna mata lokacin da suka fara haduwa da Amar, amra dai bata ce komai ba don that was not the first time suka hadu don abun ma kamar destiny, daga nan desert safari suka wuce nan ma sun sha hotuna sunfi sunsha, amra dai ta samu memories dinda she will forever cherish dukda tasan dis will be the last time, daga safari mall suka wuce, nan amra taga abunda

ya daure mata kai, haifa was spending on her and her siblings kamar babu gobe, kaya ne , kayan ciye ciye, babu abunda bata saya ba, amra dai karshe Harda dan kukanta don babu yanda batayi ba akan haifa ta bari haka ta qiya, daga kan jaka takalma skincare dinta Duk wani abu da zata mora har kannenta su mora saida ta saya mata , abaya da kuwa ta saya yakai kusan guda talatin kuka designers, amra dai da kyar ta tsaida kukan tace “I can’t accept it ki daina daukowa please”

Murmushi kawai haifa Tayi tace “no, dole sai kinyi accepting dis isn’t from me, this is from abu and ummi,”

Wani kukan amra ta sake fashe wa dashi Har Ana kallonsu, saida suka gama haifa Tayi payment , lokacin da amra taji payment din saida gabanta ya fadi 50,000 dirham, that’s about 6m kenan, kasa cewa komi tayi har suka fito da kaya niki niki,suna shiga cikin mota gida suka wuce babu wanda yace da wani qala don fushi sosai amra take da haifa akan sayayyar da tayi,don bata jin  zata karbi kayan, suna zuwa gida amra ta fara kokarin fita, kallonta haifa tayi tace “babe ki saurare ni please” zama amra tayi hawaye na sulalo a fuskanta “babe kinyi karfin wannan awaje na da wajen su abuh, kinsan how special you are to me? You changed my life you changed the old brat haifa, ke haskece a rayuwata babes pleas karki qi karban Duk wani abu da nayi maki, you deserve it”

Da sauri amra ta rungumeta ita tana kuka tace “I’m speechless babe, kinyi min abunda nan taba tunanin Zan samu ba a duniya, lna rokon Allah ya biyaki da iyayen ki a aljanna”

Share mata hawaye haifa Tayi kafin ta zaro wani dan box a bayan mata tace “don’t say no

Please, this is from me”

Kallon box din amra tayi kafin ta karba, ta soma budewa, kataon frame din hitonsu ta fara cin karo dashi, murmushi amra tayi kafin ta Kara bude wani karamin box din, idanunta ne ya sauka kan sarkar diamond da aka rubuta bestie a jiki, runtse idanu amra tayi ta rungume haifa tace “thank you so much, I’m out of words,”

Saida suka gama koke koken su kafun suyi sallama.

Amra dai wannan rana ta zamo mata one the best days of her life, data kalli kayan da haifa ta jibgo mata sai hawaye, dakyar ta samu barci ma ya kwasheta.

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 127

Washe gari sunday, sai wajen karfe sha biyu ta Tashi da wani matsanancin ciwon kai, dakyar ta samu ta Tashi daga kan gado ta wuce toilet ta watsa ruwa kafin ta fito, bin dakin nata tayi da kallo, packaging din kayan da haifa ta saya

ajere a kasan wajen, mikewa tayi ta kwaso su ta wuce dasu cikin closet ta ajesu, Riga da wando ta jawo daga cikin closet ta saka, rigar takai Har gwuiwarta, wandon ma yanada fadi sosai don bai kamata ba saidai ya zauna daidai a jikinta,fitowa tayi ta wuce kasa wajen Nadine.

 

Gaba daya gidan is so boring, tunda ta zauna a parlor ta kunna tv ta rasa abunda zatayi,kamar wadda aka tsugula janyo wayarta ta shiga camera ta daidaici fiskanta dauke da murmushi har attractive dimple dinta na futowa ta dauki hoton kanta, murmushi tayi tana kallon kanta, ta chanza sosai tayi kyau, hutu ya zauna a jikinta, cikin Instagram ta shiga tayi posting iyakacin fuskanta don babu hula akanta, tayi mugun kyau sosai, dukda bata da followers da yawa a account din nata, fita tayi daga app din ta shiga whatapp nan taga hotunan da sukayi haifa ta turo mata, ita kanta mamakin yanda ta chanza tayi don ta saje da larabawa,murmushi kawai tayi ta daura hotonsu da sukayi ita da haifa rungume da juna a profile dinta, Harda Instagram.

Nigeria…

Alamarin daddy dai sai gaba suke yi,don kullum threat daban daban yake yima Amar ta bayan fage, karshe dai amar yayi deciding ya dauke su daga gidan, dukda yana tsoron tambayar dalilin hakan da ammah zatayi, bayan wannan ma baya son tasan komai dukda dole saiya fada mata wata rana but not now, baya jin zai iya tunkararta da maganar yanxu cause her heart is weak gashi tana da ciwon zuciya, abu qalilin ne zai saka mata heart attack, don doctor yayi warning akan damuwan da take sama kanta shike affecting din zuciyarta.

Ba tare da wani bata lokaci ba yasa ayi masu visa, su salima ma da kanshi ya dauke su ya kaisu akayi masu passport cikin mintuna, komai was moving smoothly kamar yanda ya tsara don baya son kowa yasan zai daukesu daga gidan,tunda suka dawo ammah taso tambayanshi inda suka je, saidai yana saukesu ya wuce office din asad, su salima na shiga gidan a kitchen suka samu ammah, da sauri salima ta karaso inda yake ta karbi plate din hannunta tace “ammahh please ki daina shugowa kitchen, nida anty lantana ma mun isa muyi komai, kinga doctor yace ki dunga hutawa saboda health dinki”

Murmushi ammah tayi tace “Toh Ay naga yau kun fuce yawon ku kuda ya Muhammad din naku shiyasa na shigo don na taimaka wa lantana”

Cikin zumudi alima tayi tace “laa ba yawo mukaje ba fah ammah,wani waje ne mukaje akayi mana hoto”

Shuru ammah tayi tana dan nazari kafin tace “hoto kuma?wani irin hoto?”

Saukar da kai salima tayi tace “eh, ni bansan wajen ba amma naga an rubuta Nigerian immigration service”

Nazari ammah ta soma yi don tasan me hakan ke nufi, Toh kodai maida yaran zaiyi wajen mahaifinsu, ta tambayi kanta, ganin babu wanda zai bata amsa yasa tabar zancen kawai saiya dawo taji bayani daga bakinshi.

Bangaren amar bayan ya sauke su salima office din asad ya wuce direct, yana zuwa ya mashi bayanin plan din yake shirin shi, kallonshi asad yayi yace “oga Ay saida na fada maka tun wuri kasan yanda zakayi saboda safety dinsu,mu kuma saimuji dashi daga baya, yanxu ina zaka tura su?”

Kai tsaye Amar yace “dubai, yau za ah tura min visa dinsu zuwa gobe nasan passport din yaran will ready”

“Okay Allah ya kaimu”

“Ameen, yanxu menene on the ground? Ya bunciken ku?” Amar ya tambaya 

“Kamar yanda na fada maka ya toshe Duk wata kofa da za a zargesa ko a kama shi da wani laifi, Duk inda muka saka kai bama samun komai. Don Har accounts dinshi mun bincike Duk wani transactions dinshi na kamfanin ne, komai under taura yake,abunda mafi zargi shine yana amfani da 2identity wanda daya musanshi dayan kuma babu damar sani, but trust us oga, Insha Allah something will definitely come out”

Shuru kawai Amar yayi don yasan hakan ne zata kasance, Yanxu idan ya biye masu haka za aita surutu babu

40 / 94