Allah ya kaimu” ammah ta fada tana godiya ga Allah a cikin zuciyarta
Futa amra tayi zuwa dakin ta don agajiye yake sosai dukda batayi wani abun gajiyan ba, abun yanxu ya daina bata mamaki kwata kwata, yawan barci, da mood swings ga changes da yake gani a jikinta, bata kawo komai aranta ba sai maybe stress din jigilar asibiti da suka dunga yi wanda tana tunanin idan ta samu ta tsaida natsuwarta guri daya komai zai daidata.
Tana shiga daki ta rage kayan jikinta ta shige bathroom ta watso ruwa mai dumi kafin ta fito daure da towel, gaban dresser ta tsaya tana son shafa mai saboda skin dinta dake zama dry sosai cikin kwanakin saidai kuma qiwar yin hakan na cinta sosai, lumshe idanunta tayi jin barcin na neman fuskaganta “wannan wani irin yawan barci ne haka nake yi”
Ta fada tana Mirza idanunta da hannu, kallon kanta tayi a jikin mirror, yau kusan sati biyu kenan rabon da ta kalli kanta a mirror haka, ta dan kara qiba kadan don cukowar tafi futowa akan fuskanta fuskanta ma yadan kumbura kadan, shafa face din nata tayi kafin ta juya ta nufi kan gadon, zama ta fara yin tana tunanin abubuwa da dama, sauke idanunta tayi akan feet dinta Ganin kamar sun dan kumburo kadan, bata kawo komai aranta ba ta basar da komai tabi lafiyar gado cikin mintina kadan barci ya fusgeta.
Bayan futarta ammah ta kalli nurse fuskanta dauke da murmushi tace “is it obvious?”
Kallonta nurse din tayi tana kokari balle magungunan da ya kamata ta sha yanxu kafin yamma tayi, “yea ma”
Nurse ta amsa ta tana murmushi, murmusawa itama ammah tayi tana kara godiya ga Allah.
Tun bayan yabar dakin ammah dakinshi ya wuce direct, gaba daya agajiye yake don kana Ganin fuskanshi kasan he’s stressed, gajiya ne sosai a tattare dashi, yana shugowa dakinshi ya wuce bakin gadonshi ya aje keys dinshi kafin ya fara kokari cire wrist watch din hannunshi, yana cire ya ajiye gefen gado tare da wayarshi kafin ya wuce closet room, cikin natsuwa ya bude kofar ya shige ciki ya soma rage kayan jikinshi saida ya rage daga shi Sai shorts dinshi kafun ya futo, yana fitowa toilet ya shige hannunshi sanye cikin gashinta yana hautsina Ganin nasa,cikin shower ya tsaya ya sauke shorts din nashi kasa ya kunna tab din ya rike kugunshi, ruwa na sauka akanshi yana tunanin maganganun ammah,bazai taba take zancen ta ba don haka dole yayi abunda yake so don ya faranta mata,na farko yanxu zai fara settling case din daddy ya cireshi daga
hannunsa yabarma su asad don daman niyarshi ya tafi dashi chan dubai don ya hukunta shi achan don anan bazai iya hukuntashi ba saboda bashida wannan right din don ba Nigeria yake ma aiki, chan dubai kuwa babu wanda zai hanashi hukuntashi, shiyasa ya nemi asad ya karba mashi approval ko kuma ya karba da kanshi hannun president don abu ne mai sauki a wajen shi, kira daya zaiyi mr president zai sa abashi approval saidai baya son bin wannan hanyar don kamar ya karba ne ta inda dole abashi ba saida approval din military din Nigeria ba don case din na hannun su shiyasa asad ya dage akan ya bari ya karba mashi da kanshi idan sunyi approving.
Shampoo dinshi ya dauka ya latsa a hannunshi ya goga a gashinsa dake sheki, ya dauka kusan awa guda yana gida chan yana wanke chan,Har shaving gashin bakinsa saida yayi yana gamawa ya futo feeling refreshed, don kwata kwata tun bayan admitting ammah da akayi a asibiti bai samu time din yin komai ba musamman kula da kanshi daya saba yi koda yaushe, anatse ya fito qugunshi daure da towel harya karaso gaban dresser dinshi, Yan shafe shafen shi yayi ya feshe ko’ina na jikinsa da body mist dinshi kafin ya wuce cikin closet room.
Cikin Yan mintuna kalilan sai gashi ya futo a shirye cikin kananun kaya da sukayi mashi kyau, Riga da wando, rigar ta kamashi sosai musamman wajen damtsen hannunshi gashi tabi lafiyar fatar jikinshi don six packs dinshi sun fito ta cikin rigar, agurguje ya janyon wrist watch dinshi ya saka kafin ya janyo wayarshi da car keys dinshi.
Anatse ya futo daga part dinshi ya tsaya ya karema gidan kallo, gidan is so big yanxu tunanin yanda zaiyi da help din da zata dunga taimakawa wajen Gyaran gidan yake don Yan matan gidan kadai bazasu iya ba,gashi dalilin abunda ya faru yasa baya jin zai iya trusting wata house help ayanxu, harma da professionals helps dukkansu baya jin zai iya yarda da kowannensu ayanxu.
Kauda kanshi gefe kawai yayi ya fuce daga cikin parlor zuwa motarshi, yana shiga motarshi ya kunnata yayi reversing kafin ya fuce daga gidan gaba daya.
Salima dake tsaye a kitchen tana kiciniyar dora lunch a kitchen ita kadai don kafin ta sauko saida ta Leqa dakin amra Ganin tana barci yasa ta sauko kasa kawai don bata son tashinta don alamu sun nuna agajiye take yanda take yin barcin a wahale,
Sanye take da simple doguwar riga mata nauyi hannun rigar ma karami ne sosai,gaba daya kana ganinta kasan tana cikin walwala saboda ammah, Bude freezer tayi ta fiddo Jan mama da kayan miya, naman ta fara sarrafawa kafin ta bude fridge ta fiddo veggies ta fara yankawa anatse cikin kwarewa, jin alamun shugowa mutun cikin kitchen din yasa ta dan juyo, idanun su ne ya sarke dana juna, kallon kallo suka fara na kusan minti biyu don Har wukar hannunta na neman gifcewa daga hannunta harta gives ya fadi kan kafarta, “ahhh wayyo Allah na “
Ta danyi Kara tana duban kafarta, da sauri ya karaso inda take tsaye tana kokarin dukawa, da sauri ya duka ya fara duban kafar nata yana dan fada “why are you careless sai jin jika kanki ciwo jin tsaya kina kallo na kamar zaki cinyeni”
Saurin fusge kafarta tayi ta kalleshi “yaushe na kalleka?”
Dagowa yayi tsaye ya mata kallon ko in kula yace “yanxu mana,”
“Saidai in kaine ke kallo na” ta bashi amsa tana kauda kanta gefe, matsawa baya shima yayi ya tabe baki yace “why are you denying bayan na kama ki?”
“Hmm da wani idon kasan Ina kallonka in kaima ba kallo na kake ba” ta bashi amsa tana kokarin dora carrot daya akan chopping board ta fara yankawa aqule, don maganar shi ta kona mata rai sosai, bai sake kulata ba ya bude fridge ya janyo hallandia yogurt, duban kitchen din ya soma yi yana neman glass cup don baisan inda suke ajiye wa, tana Lura dashi don jefi jefi take kallon side dinshi kafin ta kauda idanunta don karya kamata, ganin duban nashi yaqi karewa gashi cups din na drawer da yake tsaye, runtse idanunta tayi kafin ta bude su ta ajiye knife din ta karaso gabanshi, yana Ganin yanda ta taho ya danyi baya ya jingina da gefen cupboard din drawers din, matsawa tayi daf dashi sosai don nunfashinsa na gogan juna ba tare da ta kalli fuskanshi ba ta zura hannayenta ttsakanin shi ta janyo drawer ta fidda glass cup kafin ta rufe drawer ta danyi baya, kallonshi tayi ta miqa mashi cup din ba tare da tace mashi qala ba, kallonta yayi kafin ya maida idanunshi kan cup din, karba yayi atsanake ya hada da hannunta, wani irin shock tayi saidai bata nuna hakan ba saima zame hannunta datayi ta danyi baya ta koma inda take tsaye tana yankan veggies don, “thank you!” Ya fada ahankali yana kokarin bude cover din pack din, saida yasha ya koshi ya maida sauran kafin ya koma Inda take tsaye daga gefenta “meysa kike gaba dani, is it because…”
Saurin ajiye knife din salima tayi ta kalleshi “baba gaba dakai, babu dalilin da zaisa nayi gaba dakai,”
Katseta yayi saurin yi yana matsawa kusa da ita “then why are you ignoring me?nine ya kamata nayi ignoring dinki saboda ni kika yima breaking heart tho I’ve moved on” ya karashe yana daga mata kira, kallonshi tayi kafun ta kauda kanta gefe “ni bana gaba dakai kaine de…” ta fada tana jin yanda zuciyarta ke pounding,
Murmushi kawai yayi ya miqa mata hannu fuskanshi dauke da murmushi “friends”
Kallon hannun nashi tayi hawaye na shirin zubo mata Tayi saurin dannewa tace “no”
“Please!!!!!” Ya fada yana Jan word din kamar mai riko
Kauda kanta gefe tayi tana jin zafin shi sosai Wai friends may yake nufi da ita kenan,
“Kinyi shuru friend” ya sake magana
Wani irin maqoqon bakin ciki ne ya turniketa yana ganin haka, wata irin dariya ce ke ciyo bai Ganin yanda yake take reacting ba tare da saninta
A harzuke tace “okay but don’t call me frind call
Me with the name you usually call me”
“You mean baby sal? Or sal? Or salima”
Y tambayeta yana kallon cikin idanunta, saurin kauda nata idanun tayi da suka kawo ruwa “anyone” ta bashi amsa tana kokarin slicing green pepper, maganar da yayi ne ya Dakar mata zuciya “okay but banda baby sal, sabod ayanxu baby daya gareni kinga bai kamata na dunga hadata da kowa ba ko sal?”
Rai abace ta dago ta kalleshi “just call me with salima, and please kaje kana distracting dina idan Ka gama abunda kakeyi” tana kaiwa nan ta juya mashi baya ta wuce wajen sink ta fara wanke veggies sun hawaye na sauka akan idanunta tana gogewa, sarai yaga yanda yake goge hawayen tana basar wa, baice komai ba ya danyi dariya ta gefen baki kafin ya tabe baki “au harda korata salima?“ yanda ya karashe maganar da suna ta kamar an buga mata mashi a zuciya, saurin runtse idanunta tayi ba tare da da tace mashi Tak ba, “daman Zan taimaka maki da wasu ayyukan ne but tunda an koreni bari nayi tafiya na”
Yana shirin juyawa call ya shugo wayanshi, saurin muting call din yayi ya kai wayar kunnenshi kamar ya amsa yace “hello baby na how are you today?Kinci abunci kuwa?”
Ya fada yana fucewa daga kitchen din, wani maqoqon bakin ciki ne ya turnike salima ta juyo ta bishi da harara “Allah ya isa Wallahi, shegiya koma wacece bazaki taba samunshi ba”
Ta fada ahankali tana goge hawaye kafin ta maida hankalinta wajen girkinta, Aman da ya dan labe a hanyar kitchen din sarai yaji abunda tace don Har darawa saida yayi “zanyi maganin ki ne” ya fada yana dariya shi kadai kamar wani zautacce, wayar hannunshi ce ta sake yin ruri, kallon wayar yayi ganin Amar na kira don shine ya kira dazu ma, saurin dagawa yayi ya kafa wayan a kunnenshi, magana Amar yayi daga chan bangaren kafin ya soma amsawashi “Bari na duba dakin nata, yanxu nake shirin haura wa saman ma”
“Okay thanka, idan kaje Ka kirani zanyi amra magana” Amar ya fada yana kokarin kashe wayar
“Okay” Aman ya amsashi kafin ya wuce sama.
Dakin ammah ya wuce direct, da sallama ya bude kofar,budurwar nurse din dake kula da ammah ce a tsaye hannunta rike da wayanta, kallonshi tayi fiskanta duake da murmushi, shima kallonta yayi, black beauty ce ga ido ga diri saidai gajeriya ce sosai don sai ya zamana dirin nata ya dunkufe, kallonta Aman yayi yana karasowa inda ammah ke kwance tana barci saboda maganin da aka bata wanda kesa barci sosai sannan yana hana jin yunwa sosai, “welcome sir” nurse din ta fada anatse tana kallonshi tana lankwashe murya don tunda ta shugo gidan tasan gidan masu hannu da shuri ne, don haka taci alwashin cusa kanta itama, kallon gefenta yayi fuskanshi duake da murmushi yace “thanks, tasha magani ne?”
“Yes sir, maganin yana aka barci but zata Tashi in 2hours” ta bashi amsa tana kallonshi da manya manyan idanunta kamar na mujiya, juyawa kawai tayi ba
tare da yace mata komai ba ya fuce daga dakin ya sauko kasa, dialing number Amar ya fara yi ya shiada mashi tana barci don daman ya kirata ne bai sameta ba don yanason yaji ya lafiyar jikinta sannan yana son ya shaida mata ya futa sai yamma zai dawo “na shiga yanxu tana barci saboda magani data sha, she will be up in the next 2 hours, will call you zuwa lokacin”daga chan bangaren Amar yace “thanks, please let me know idan wani abun ya faru”
“Don’t worry I will watch over” Aman ya bashi amsa kafin ya dauke wayan daga kunnenshi ya wuce dakin shi.
Aman na kashe waya shima ya aje wayarshi ya maida hankalinshi kan tukin da yakeyi anatse, tafiyar minti goma ta maqoshi Nigerian military headquarters, anatse ya shige da motarshi kamar koda yaushe, yana parking ya dauki wayarshi dake kan dashboard ya futo daga motar kafin ya rufe ta ya nufi hanyar shiga cikin headquarters din, bai tsaya ko’ina ba sai office din asad, da sallama ya bude office din yasa kai ya shige ciki.
Asad ne zaune kan kujeran office dinshi, sanye yake da kakin sojoji, saurin miqewa yayi, nan Amar ya tako inda yake ya miqa mashi hannu, musabaha sukayi kafin amar ya zauna, shin zama yayi fuskanshi dauke da murmushi yace “ya jikin hajiya? Allah yasa kaffara ne”
“Alhamdulillah,taji sauqi mun dawo gida ma”
Amar ya bashi amsa yana kokarin duban wayarshi
Kallonshi asad yayi ya tura mashi file din gabanshi yace “Masha Allah Zan shugo yau da daddare, Allah ya bata lafiya”
“Ameen” Amar ya amsa shi a taqaice
Kallon file din yayi kafin ya soma budewa, “oga ga approval ta iso, you have the right to take him zuwa uae,“
Kallon file din Amar yayi saida ya gama karantawa gaba daya ya rufe file din ya tura gaban asad, kallonshi asad tayi tana neman Karin bayani,
“No need for that anymore, Zan barshi anan kuyi mashi hukunci daidai da abunda yayi,”
Da mamaki asad ya dago ya kalleshi don yasan saboda wannan abun ne ya kasa komawa bakin aikin sa acahn uae saboda yana son ya tafi dashi don a hukuntashi achan, “but oga..”
“No but, lieutenant asad, saidai Ina rokonka don Allah karka bani kunya,”
Amar ya fada yana kallonshi fuskanshi a hade tauuu kamar baiso hakan ta kasance ba,
“Yes sir, justice will served”
Asad ya fada yana Sara mashi, fuskanshi a hade ya cigaba “suma ku hukuntasu gaba dayansu, nabar komai a hannunta nasan bazaka bani kunya ba?”
“Insha Allah sir,but oga…why did you suddenly change your mind” asad ya tambaya yana kallonshi don gaba daya he’s confused, yayi mamaki sosai don yasan idan Amar yace zaiyi abu sai yayi babu wanda zai hanashi haka zalika
daya nemi abashi kabiru koda military ta hanashi zaiyi using power shi ya karbeshi ta karfi da yaji, saidai yanxu dayaga akasin haka yayi mamaki.
Bai amsashi ba ya mike tare da miqa mashi hannun “thank you so much for your help”
Jinjina kai asad yayi “nine da godiya oga fir trusting me on this case”
Fucewa sukayi atare daga office sun suka wuce criminal room inda aka aje Alhaji kabiru, gaba daya nan bangaren babu wuta kwata kwata don cikin duhu ake ajiye criminals Ana Kiran wajen ma da dark room don azabar da ake gamawa a ciki, asad ne ya bata umarnin aka kunna wutar wajen nan take haske ya hade ko”ina, dakunan ne aqalla zasu kai kusan goma sha biyar Kowanne da manya manyan criminals a ciki gefen su kuma na kananun criminal ne da ake kamawa suma Ana ajiye su, cikin dakin da aka ajiye Alhaji kabiru suka shiga
Kallon inda Alhaji kabiru ke maqure amar yayi, an kulle hannayenshi da karafuna gaba daya ya sauya fasali ya yanqwane ya zama kamar tsumma, ahaka ma in aka barshi ya gama lalacewa gaba daya, takowa Har gabanshi amar yayi ya tsugunna ya kalleshi “yanxu menene ribarka na abubuwan da kayi? Ka cuci kanka kuma muka Ka cucemu”
Dagawa kabiru yayi ya kalleshi dakyar don idanunshi a kumbure suke, yana gane amar ne ya babbake da dariya, kamar mahaukaci “finally!!!! Burina ya cika yanxu, you’re miserable, yanxu saika kashe ni ko?”
Alhaji kabiru ya fada yana dariya, murmushi amar yayi sai yanxu ya gane abunda ammah ta fada mashi jiya, ganin yana murmushi yasa Alhaji kabiru tsagaita dariyar shi ya kafa mashi idanu kamar mahaukaci, kallonshi amar yayi kallon ina tausaya maka “in kashe Ka saboda na zama kamar kai ko? Haka kake so?” Nunfasawa amar yayi ya cigaba “bazan taba zama kamar kai ba, kuma bazan kashe ka ba, Zan barka kasha azabar duniya da hakkin waenda ka salwantar da rayuwarsu, shi kadai ma ya isheka, “
Mikewa Amar yayi bai sake kallonshi ba ya juya ya fuce daga cikin dakin, Alhaji kabiru dai ba haka yaso ba, don haka ya dunga ihu yana surfa ashariya, “ Wallahi saika kashe ku kasheni dan Allah na gaji da wannan masifar na shiga uku”
Kallonshi asad yayi don shima sai alokacin ya gano dalili da yasa amar ya fasa tafiya dashi chan “ay mutuwa ba yanzu zakayita ba sai lokacin Ka yayi bayan munci ubanka”
Asad ya karashe yana Kiran yaranshi don zuci ubansa.
Futowa yayi ya tadda amar a tsaye kafin su wuce dakin mata da aka ajiye lantana, bude dakin asad yayi kafin amar yabi bayanshi, a zaune take a kasa kan cement don ko leda babu a cikin dakin, dago da idanunta da sukayi jaa tayi, da sauri tayi baya Ganin Amar a tsaye, gaba daya furgicewa tayi kamar mahaukaciya don bazata taba mantawa da dukan da yayi mata ba din taji kamshin lahira, kallonta Amar yayi daga nesa, ta rame sosai ta koma kamar
wata mai kanjamau saboda rashin abuncin kirki, hawaye ta soma yi jikinta na bari “dan darajar Allah ku yafe min, dan Allah yallabai Wallahi sharrin shaidan ne”
Takowa Inda take Amar yayi idanunshi sunyi jaa, aduniya babu wadda ya tsana kamar lantana dukda yana kokarin dannewa saboda itace ta kusa sanadin rabashi da farin cikin sa wato mahaifiyarsa, “dan Allah yallabai ku yafemin l, hajiya ta yafemin Wallahi sharrin shaidan ne”
“Ba sharrin shaidan bane, da saninki cewa abunda