Rabin awa tana abu daya harta samu ta saka pant da pad, wandon Ma Kasa mai dashi tayi Sai towel ta nada a kugunta , dakyar ta rarrafo ta futo dakin ta ta zauna bakin gado sai hawaye wiwi, fuskanta yayi jaaa alamun jin jiki sosai, ahankali ahankali nunfashinta ya soma neman daukewa kamar mai asma, mikewa tayi don zuwa toilet ta kwata Ma kanta ruwa don intaji irin haka Toh da suka ne kawai zatayi baya iya tsaida kafafunta ba taji sun Kasa daukanta,wata Kara ta kwala da karfi kafin ta fadi Kasa warr, Amar dake shirin wucewa dakin dake kusa da nata sanye cikin kayan gyming ya jiyo karar tata, kallon dakin nata yayi don tantance ko daga nan ne karar ta fito kamar bazai takaba ya daki handle din dakin da yake shirin shiga ya bude natan, duhu ya soma gani a dakin saidai dan hasken dake lekowa daga window, laluben switch yayi kafin ya Danna, ganinta a yashe kasa ya sashi saurin takowa gabanta yama rasa mai zaiyi, tsugunnawa yayi gabanta yace “ke ke,”
Jin alamun bata motsi yaji gabanshi ya fadi ya sake tabo ta yace “ke ayshaaaa”
Shi kanshi yanda ya furta sunan nata Sai ya sake mashi kamar baqon suna, kamar zai zauce ya sake taba ta, kokarin cicibarta somayi towel dinta ya sake kasa, baima san towel din yayi hanyarshi ba ya kwantar da ita kan gado a natse ya wuce bathroom dinta, ruwa ya deba a cikin bowl yazo gabanta ya soma shafa mata cikin kulawa kamar baya so, doguwan nunfashi taja tare da bude idanunta
saidai yake ciki ta ya soma murdawa ta kwala wata karar ta suke, ganin haka ya sashi saurin taba aljihun gajeran wandonshi ya janyo wayanshi ya soma dialing number da ya fara cin karo dashi
“Morning sir,”
Bai tsaya amsawa ba yace “I need doctors now, it’s emergency”
Hankali tashe asad yace “doctor kuma waye bashi da lpy ko Ammah ne tunda daga ji dai nasan kai lafiyanka kalau”
Cikin dan fada yace “just get me a f**cking doctor now”
“Okay”
Yayi saurin katse wayan.
Ruwan ya sake shafa mata saidai wannan Karin doguwar suma tayi don babu yanda baiyi ba don ya dawo da ita hayyacinta.
Yana nan zaune yaji karar bell da sauri ya fito daga dakin ya tsaya bakin wajen stairs don Ana iya hango wanda ke qasa,bai tsaya sauraran Nadine dake shirin mashi bayani ba yace “let him in”
Cikin sauri ta koma ta shigo da doctor, Nadine ce ta jagoran ce shi har gaban Amar kafin ta juya.
Hannu Amar ya miqa mashi suka yi musabaha kafin ya jagoranceshi gaba, yana bude kofar bai kaiga shiga ba ya hango ya yanda ya barta don sa a lokacin shima ya Lura da yanayi ya don dazun baya cikin hayyacinshi shima, saurin juyawa yayi don doctor na gab da karasowa, daka yar dashi yayi ta hanyar ce mashi “wait a minute” ya bude kofar tare da saurin rufous ya karaso gabanta tunda ya tsaya ya kare mata kallo Har ya kusa shagala da kallon nata kamar wanda aka tsikara yayi saurin janyo duvet dinta ya rufa mata gaba daya ya rage iya fuskanta kafin yace “come in”
Shugowa doctor yayi kai tsaye ya karaso inda yake tsaye kafin ya maida idanunshi kanta.
Da idanu Amar ya mashi nuni da ita dake kwance hannayenshi nade a kirjinshi dake sanye da rigar under armor na gym, babbake wajen yayi wanda yasa doctor din zuba mashi idanu shima shi yake kallo fuskannan babu yabi ba fallasa, takowa doc din yyi kusa dashi sosai kafin yadan matsa mashi gefe
“meke damunta”
“Idan nasan abunda ke damunta Zan kiraka ne”
Ya fada Adan kausashe don yaga lokacin da doc din ya zubama fuskanta idanu wanda hakan baiyi mashi ba sam
Dan murmushi doc din yayi ganin Duk ji da kanshi da kudi da yake dashi ya hadu da wanda ya fishi
“Na tambaya ne don na samu damar duba ta yanda ya kamata”
Maida idanunshi doc din yayi kanta ya kai hannunshi wajen fuskanta da duvet yadan rufe sosai sbd yanda ya janyo bargon, Amar na ganin haka ya runtse ido a dan fada yace “don’t…..”
“Just check her”
“I can’t check her just by looking at her face, I have to touch her to feel her pulse tunda naga kamar bata nunfashi”
Tamke fuska ya sake kafin yadan kauda kanshi gefe ya tsaya akansu.
Dan sauke duvet din doc din yayi kafin ya kare mata kallo sosai, shagala yayi da kallonta saida Amar yayi Gyaran murya kafin ya soma taba wuya ta don jin pulse dinta, jin pulse din is so weak yasa shi saurin bude dan box dinshi ya fara mata taimakon gaggawa saida ya kammala komai ya saka mata ruwan nunfashinta ya sauka da karfi alamun ta farfado Sai bacci kuma, dagowa doc din yayi yace “she’s stable now, yanda naga tana nuqurqusar na tabbatar da monthly cramps ne da mata keyi, Banda awa biyu zata ji sauki”
Tattara kayan aikinshi yayi gyara tsayuwar glass dinshi kafin yace “taba da aure ne”
Dan dago idanu Amar yayi ya kalle shi yace “no why”
“Daman yawanci yafi bama yanmata wahala musamman waenda basu taba Sadiya da namiji ba, Akwai magungunan da zata sha harta gama, Zan dawo anjima don na duba ta”
Wani irin kallo mai wuya fasaara Amar ya mashi kafin ya kauda kai gefe yace “thanks, asad will handle your payment”
Cije lebe gayen yayi kafin ya juya ya fuce.
Yana futa ya daga wayanshi ya Danna kira Ana dagawa cikin dan fada yace “are you sure wannan certified doc ne, send someone I don’t like perverts”
Shuru asad yayi don ya Kasa gane me Amar din ke nufi da inda ya dosa, don wannan Loki tan babban Lokita ne shike kula da family dinshi saidai baya iya jayyay dashi yace “okay sir”
Dakin ya koma ya zauna gefenta ganin lokaci guda ta sauya sosai, kauda kanshi yayi gefe ya dauka kusan awa a zaune kafin ya miqe ya turo Nadine don ta tsaya da ita.
Tunda ya koma dakinshi ya Kasa natsuwa saida ya shigo dakin yafi sau uku cikin awa guda, ta dade bata fara ba don saida ta kai kusan awa hudu don allurar nada karfi sosai, wajen asr ta farka, babu kowa dakin lumshe idanunta tayi ta zauna dakyar,tunawa da yanayin da take ciki yasata dan mikewa don tasan yanda take rushing tsoronta karya bata beddings din, tana mikewa kuwa jiri ya debeta alokacin shi kuma ya sako kai cikin dakin, da Santala santalan cinyoyinta ya soma cin karo bai kaiga sama ba ya runtse idanunshi, itakuwa tama manta da jiran daya debeta tayi saurin janyo towel ta daure kugunta, tana taku daya kuwa ta kwala Kara don kiris ya rage ta zube, da taku biyu ya cimmata kafin Adan fada ce yace “get your head straight tunda kinga bazaki iyaba Ay saiki zauna”
Shuru ta danyi don azabar da take cinta yafi surutanshi zafi, zauna da ita yayi tare da ficewa ya turo nadine, tun daga Safiya zuwa yamma Nadine ke mamakinshi, ashe yanada zuciyar tausayi.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 108
Tun bayan zuwan da yayi bayan ta farka bai sake lekowa ba Nadine ce ke kula da ita sosai ganin tana Shan wahala sosai, gashi ta Kasa cin komi Sai ruwan tea, karshe Ma dai saida Nadine ta taimaketa wajen jika mata towel a cikin ruwan zafi tana gasa wajen a kwance.
Tana nan kwance wani doctor ya shigo saidai wannan babban mutun ne sosai, lokacin da yazo Nadine ta je dakin general don shaida mashi zuwan doctor, nan take yacemata ta kaishi dakin ya dubata, nan ta koma ta shigo da doctor din tare da mashi jagora zuwa dakin amra koda yazo tana zaune Duk ta galabaice sosai ta ji jiki ba kadan ba don haka ya samu damar tambyanta yanda take jin jikinta, nan take ya shima ya gano menstrual pain ne na mata saidai yayi mamaki yanda ta mashi bayani yanda yake Shan wahala Harda suma ,duban ruwan da aka sa mata yayi ganin harya kare, magunguna ya bata tare da nuna mata yanda zata sha kafin yace ta samu ta watsa ruwa mai zafi sosai zataji dadin jikinta sosai don alamu sun nuna she’s weak, saida ya tabbatar she’s stable kafin yayi masu sallama ya tafi.
Da kyau Nadine ta yaye mata bargon dake lulling a jikinta da Harya soma dan baci ta taimaka mata zuwa toilet, ruwan mai dumi sosai ta tara mata a cikin bath kafin ta futa don gyaran dakin, a daddafe ta karasa gaban wc ta zauna tayi tsarki kafin ta shiga cikin hoth bath din, da dan dade sosai kafin ta futo ta sake watsa ruwa mai zafi sosai, da taimakon Nadine ta dawo dakin daure da towel, lokacin har Nadine ta gyara ko”Ina Harda kan gado, ta cire duvet din da Zan in gadon ta sauya zuwa wasu sabbi ta kunna diffuser da oils masu kamshi sosai.
Ganin mikewa Ma dakyar takeyi yasa Nadine bude closet ta janyo mata wata rigar bacci daidai gwiwanta mai santsi pink color, hannun rigar bashida kauri dan siriri rigarma ba lallai takai kasan gwiwa ba, saida ta shafa mata turarenta dake kan dresser data gani kafin ta aje mata a gefenta, ganin ta dafe kanta alamun yana mata ciwo yasa Nadine cewa “sannnu ma, ga kaya nan ki saka bari ba kawo maki tea ki samu Kisha tunda kin Kasa cin abunci.”
Dagawa tayi idanunta sunyi luhu luhu sunyi ja dakyar ta iya furta “thanks Nadine”
Nadine na futa ta janyo rigar ta saka, kamar Nadine tasan bata son kaya masu nauyi idan tana period, tafison ta dunga kinga freely babu takura.
Koda Nadine ta dawo hannunta dauke da tea sun saida ta zuba mata idanu, ganin wani extra ordinary kyau da yake dashi, tana da irin kyau din da Duk kyan fuskanta jikinta yafi daukan hankali. Karasowa tayi tare da mata sannu ta bata tea din da zafin sa, bata wani sha da yawa ba kadan tasha jin amai na zuwan mata yasata ajewa.
Wajen karfe sha biyu na dare ganin bacci ya kwasheta yasa nadine rufa mata bargo ta rage mata gudun ac tare da rage hasken fitilar dakin ta rufe mata kofan ta wuce daki don ta samu ta huta itama, don wuni ranar tana tare da ita a dakin wasu daga cikin ayyukanta ma bata samu ta karashe ba donma babu wani ayyuka masu yawa, yawanci abunci ne yawanci basu fiye ci ba saidai idan anyi in ba a ciba a abaima securities Sai kuma dan gyare gyare wanda tajeyi safe da yamma, Allah ga taimaka tayi na safen na yamma ne bata samu tayi ba dalilin rashin lpy madam wanda takema kallon kanwa a wajen oga don alamu basu nuna matarshi ce ba.
Dakin ta na masu aiki wanda zaka rantse dakin baqi ne, daki ne babba da gado Harda carpet da wardrobe sai toilet shima dayasha abubuwan zamani, koda ta koma daki kwanciyarta tayi.
Karfe daya daidai ya aje laptop dake kan cinyanshi tare da janye duvet din daya rufe kafafunshi dasu, mikewa tayi tsaye tare da yin miqa, ciki natsuwa ya zura bedroom slippers dinshi tare da gyara riganshi da buttons din suka bude, fitowa yayi daga dakin cikin kamewa ya sauka kasa, tunda ya sauko second floor ya rasa dalilin saukowan nashi, maida idanunshi yayi ga kofar dakin ta kafin ya juya ya sauka kasa, hanyar kitchen ya nufa wanda ya zamo mashi rana ta farko daya tako ya shigo kitchen din, ko ina tsaf tsaf babu kazanta, sai kamshin freshner dake Tashi harma da dan sanyi sanyin ac dake kune a cikin kitchen din, kunna duka lights din kitchen din yayi don guda daya ne a kunne, bin ko’ina ya soma yi da kallo, kafin ya tako gaban katon fridge freezer dake a hade ya cinye kusan Rabin bango daya, budewa yayi kafin idanunshi su sauka kan bottle water masu sanyi, janyo daya yayi kafin ya rufe fridge din ya balle marfin ya kafafunta bakinshi, yanda yake Shan ruwan Ma a gayance da natsuwa kamar basarake, yanda ruwan ke sauka daga makoshinsa Har wani dan zufa ke sauka daga wuyanshi wanda yake looking so sexy a tsaye, amra dake saukowa kamar wadda aka zare Ma laka fuskanta gwanin ban tausayi lokaci guda Duk ta dan fada kadan fuskanta fayau, tun bayan futar Nadine bata wani dade ba ta farka jin ciwon na shirin dawowa, saukowan datayi Ma tazo neman ruwan dimi ne don tasha ko zata ji dan dama dama,tun daga bakin stair ta fara jin kamshinsa saidai bata kawo zata ruskeshi ba a wannan lokaci, koda ta karaso cikin kitchen kanta na kasa, karaf kamar ance ta dago idanunta suka sauka akan fuskanshi zuwa makoshinsa, yanda yake Shan ruwan Ma ya shagaltar da ita don mamakin ganinsa a kitchen din ta soma, jin murdawan cikin ta ne ya sata damke kasan marar tata tare da dan dafe kan mable din kitchen island tayi yar Kara “arhhhhhshhh”
Yana nan tsaye bottle din na bakinshin ya sauke idanunshi kanta jin karar datayi don baiji shugowarta ba, kyam idanunshi suka sauka kan nipple dinta da suka mashi hello daga nesa don sosai suka fito daga cikin rigar tata nan take ruwan
daya sauka makoshinsa ya soma sarqe mashi a maqoshi Har idanunshi nayin jaa fuskarma ta soma jaa abunka da farin fata, sauke bottle din yayi ya kauda kanshi gefe kafin ya maida bottle din bakinshi ya shanye sauran with just a sip, shida kesha a natse Sai gashi natsuwar ta kufce ya kwankwade gaba daya lokaci guda ya rufe bottle din, tare da dan sauke nunfashi da huci mai zafi, cikin ranshi ya soma magana “uhmm damnnn”
Juyowa yayi azafafe ya zuba mata idanunshi kamar yaga abunci na farko yanason karantar asalin ciwon nata saidai bai gane ba koda doc yace mashi monthly menstruation da mata keyi takeyi, Yadai san period da mata keyi Duk wata saidai cramps dinne ya Kasa gane daga Ina yake, ta wani bangaren yake,da wannan yake kokarin son hana zuciyarci tunanin da take shirin bijiro mashi don tun kallon farko da yayi mata gabanshi yayi mugun bugu lokaci guda kamar wanda ake fusga ya tako zuwa gabanta dan nesa da ita kadan ya tsaya tare nade hannayenshi a kirjinshi dake a bude don rigar a bude take, kallonta yayi tsaf irin kallon kurulla dinnan, tundaga kanta da babu hula, curly gashinta a bayyane sun kwanta lub lub sun nannade, gaban goshinta da edges din gashinta sun kwanta sakamakon zufa data tsatsafowa mata saboda jin zafin ciwon marar nata,
Tunda ta dago ta mashi kallo daya bayan sun hada idanu ya kauda nashi gefe bata sake gigin dagowa ba don kallonshi, saidai har yazo gabanta tana jin takunshi har cikin xuciyar ta, runtse idanunta tayi gam lokacin da ya tsaya dan nesa da ita tana jin yanda idanunshi ke yawo a jikinta, lokaci guda taji gaba daya she’s so uncomfortable don jikinta is expose gashi babu bra kwata kwata a jikinta,rigar ma is not helping the matter don tana da santsi sosai wanda ya sanya nipples dinta fitowa kyam sosai don shatinsu a bayyane yake sosai, Dayan hannunta dake gefe tayi saurin daurawa wajen kirjinta Dayan dake dafe kan island kuwa kamar zata fasa marble din donta damqe shi sosai, taku daya yayi ya karaso gabanta saidai da dan tazara sosai tsakaninsu, dake wa yayi ya soma magana fuskannan dai bazaka taba tantance ta,
“How are you feeling now?”
Babu zafi taji tambayan nashi, don haka ta Kasa dagowa don gaba daya kunya ta gama lullubeta dukda rashin lafiyan da takeji hakan bai hanata jin kunyarba, don tana da kunyar jikinta sosai,
Kanta a Kasa muryanta ma baya futa sosai tace “Alhamdulillah!!”
“Raise your head”
Dan daburcewa tayi don kusan bata gane me yake nufi ba still kanta na kasa
“ I don’t want to repeat my self”
Yadan fada azafafe
Kungukuni ta soma,fuskanta adan shagwabe ta dago ta kalli gefe,hakan kuwa kamar ta ingizashi ya sake magana a kausashe
“Heyyyy look up here”
Ya sake fada still hannunshi na nade a kirjinshi.
Kamar mai maye haka ta maido da fuskanta kanshi tana dan kunkuni don bata son hada idanu dashi, ganin yana shirin magana yasata saurin kallon idanunshi saidai ko second batayi ba idanunshi suka rinjayi nata don gaba daya wani irin kwarjini yake mata sosai. Kokarin sauke nata idanu tayi saidai irin kallo daya zabga mata ya sata sallama mashi ta tsaida idanun akanshi, tunda ta zuba mashi manyan idanunta da ke nan kamar mai jin barci Har wani lumshesu takeyi tana budewa eyelashes din na kwanciya sun dan jike dalilin kukan datayi, take yaji tsayuwansa ma na neman gazawa, da sauri ya dauke nashi idanun daga kanta ya gyara tsayuwanshi kafun yace “me kika futo yi”
Da sauri kamar wadda ke jira take “ruwa nazo dauka”
“Dan tabe baki yayi kafin ya raba ta gefenta ya fuce daga kitchen din cikin kamewa.
Yana futa kuwa ta sauke nauyyayiyar ijiyar zuciya wadda saida ya jiyota kafin ya bar kitchen din gaba daya.
Saida ta dauka kusan minti biyu kafin ta daidata natsuwarta ta wuce wajen aje mugs, ruwan zafi ta deba daga diapenser dake jikin fridge din kafin ta fito ahankali jin yanda murdawan keyin gaba sosai, bata tsaya duban sitting room din kasan ba don ko ina a kashe yake babu haske Saina wajen entrance dake hasko parlor kadan, stair din ta fara takawa bata kaiga taku biyu ba taji ciki ta ya Kara murda, cikin saurin ta dafe handle din stair din tare da da yar Kara don yanda ta razana dajin zafin ya sa ruwan mug din ya dan fantsala akan skin din hannunta, Amar dake tsaye nesa da ita don yana zaune a sitting room din harta fito yana hangota saidai ita bata ganinshi, harta hau stairs da tsayuwan datayi Duk