Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   86 / 94

255K to 258K   out of 279.4K words

ba saboda lokaci na baiyi ba,”

“Wallahi fatalwa ne, akan idona nasa a kashe shi, karya ne “

Yanda yake magana ma kwata kwata ba a cikin hayyacinshi yake ba.

Kallon inda kareema ammah tayi tace “ko zaki bamu wajen zama sai muyi magana?”

Katseta labaran yayi yace “hajiya karna yo hanzarin katse maki magana, ammah ba zama mukazo ba, babu wata magana data rage da zamuyi, mu wuce sasan inna kawai”

Sai alokacin kareema ta tabbatar da gaske ne don haka ta fara kokarin dukawa tace “dan Allah ku tsaya hajiya,”

Kallonshi ammah tayi tace “baban amra kayi hakuri mu zauna ayi magana”

Runtse idanu kawai labaran yayi baya son jayayya da ammah don haka yayi shuru kawai, kallon inda asmaa ke tsaye da sandarta kareema tayi tace “ke chogala jeki dauko tabarma a uwar daka”

“Wace tabarmar zata dauko? Daman Akwai wata tabarmar ne bayan wannan wadda kuke zaune?” Khady ta fada babu alamu respect kwata kwata a kalamanta, 

A burkice karima tace 

“Auu laa haka ne, kuyi hakuri bari mu Tashi sai ku zauna akan tabarmar, 

Amar ne yayi saurin katsesu don bayajin zai bari amra ta Kara taku daya  da yaranshi zuwa wajen nan, gaba daya Kuda ya gama bade wajen ga wani ruwan yauqi na ciwo dake fita daga jikin daddy,”kuyi zamanku anan babu damuwa zamu tsaya daga nan”

Ya karashe ranshi abace don gaba daya haushinsu yake ji idan ya tuna da sune suka wulaqanta mashi matar shi, yanxu ko ba a fada masu ba su san cewa rayuwa ta juya masu baya babu arziki babu takamar balle ayi wulaqancin, daman ance inka Shuka alkairi zakaga alkairi inka shuka sharri kuwa shi zaka girba bayan wannan ma ga hakki, hakkima ba daya ba hakkin mutane Har hudu, na marayu dana ubansu da sukayi kokarin kashewa.

Saukar dakai kasa kareema tayi don gaba manta yanxu basuda matsayin da zasu wani saukar da baki a waje mai kyau, don koda Amar yace mata basai sun zauna ba tasan abunda hakan ke nufi, 

Ammah dai kasa cewa komai tayi don mai duka yayi magana batada jayyayya don itama kanta bazata so jikokinta suzo wajen ba, daga nan tsaye ta soma magana “nasan kinsan waennan ko?”

“Eh na sansu, yayana ne don yayan suke a wajen kanin mijina  gashi nan” ta karashe tana nuni da daddy, 

Wata irin bazawarar dariya khady tayi tace “chap ikon Allah, yau kikasan yayanki ne ? Kai mummy jin shiga uku,hmm”

Wani irin kallon Amar ya wurga mata don ta juyo tana kallonshi aranta tana yaba kyawun d a yake dashi Har tana jin ina yace yana sonta.

“To tabbas wannan mahaifinsu ne kuma bai rasu ba yana nan raye,” ammah ta fada

“Toh ya akayi hakan ta faru? Hajiya Kar nayi katsalandan menene alaqarku da su?”

Nuni ammah tayi mata da amra tace “wannan diyata ce matar dana Muhammad kuma marikin qannenta”

Ammah ta fada tana nuni dasu, hannu aka kareema ta daura tace “na shiga uku ni kareema, don Allah ku yafe min yayan nan ashe zubar daku danasa ayi sautin rayuwa ya kawo maku”

Yanda kareema ke magana ba karamin qular da Amar Yayi ba harma da ammah, don kwata kwata babu wani sign of nadama a tattare da ita saima wasu surutai da takeyi marasa kan gado,

“Hajiya dan Allah kiyi min afuwa Zan wuce ciki bazan iya tsayuwa anan ba” labaran ya fada yana kaiwa nan ya nufi hanyar bangaren innarsa “baba badaru Ay inna ta rasu” asma ta fada tana daga tsaye don Har lokacin basu yarda shi mutun bane kallon kamar fatalwa suke yi mashi, chak ya tsaya ya juyo yana kallonta kafin ya runtse idanunshi, amra ce Tayi karfin halin cewa “inna ta rasu? Yaushe ta rasu?” Ta karashe hawaye na yawo akan fuskanta,

“Tun watan bara lokacin da muka dawo nan da zama ma bamu taddata ba” asma ta amsa mata fuskanta gwanin ban tausayi,

Gaba daya wajen dauka yayi da innalillahi wa inna ilaihi rajiun, juyowa babansu amra yayi ya nufi hanyar futa nan take daddy ya tsaidashi “Wai da gaske ne daman baka mutu ba? Wannan wace irin masifa ce?na shiga uku ni mustapha,”

Juyowa labaran yayi rai abace yace “Ada banso nayi magana ba saidai yanxu bazan iya jurewa ba, allah ya isa tsakanina dakai, Ka cuceni Ka cuci yayana na barka da allah, ahaka ma kaga yanda karshen Ka ya kasance”

Labaran na kaiwa nan ya juya ya fuce daddy na faman kiranshi “laa da gaske bai mutuba, kai badaru baka mutu ba ashe”

Yanda yake magana da yanda zugin azabar jinyar da yake fama dashi ke rudashi yasa yake sambatu baima san yanayi ba, labaran na fuce wa Amar yace “muje ko ammah”

Khady ce Tayi saurin cewa “anty amra don Allah ku tafi dani Wallahi bama cin abuncin kirki, kullum wahala muke sha kinga wannan ma gwanjo ne nake

saidawa nake dan rufa mana asiri Wallahi dani suka dogara ni kadaice gatansu saboda su bakiga yanda na koma ba”

Kallon yanda take abun tausayi salima tayi harta asma ma saida tayi mamakin furucin nata, aranta tace “munafuka annamimiya Wallahi Saina tona ki”

Kareema ma mamakin khady take da yanda take wani kwallar makirci, 

   “karya take Wallahi, muguwa azzaluma, babu abunda takeyi mana a gidannnan saidai taje ta sayar da gwanjonta ta dawo da ledar tsire ta cinye abunta ita kadai, munfi shekara bamu ci nama ba” asma ta fada tana kallon khady tana hararta, dizguwa dai khady ta dizgu don dama lankwasar da kai datayi tayishi ne don ta samu ta gudu tabar wannan jarababbiyar rayuwar ko zata samu wannan kyakyawan yace yana sonta.

Wani irin ashariya khady ta kwararo mata wanda yasa salima doka auziya tace “chapp Allah mai iko, haka kuka koma? lallai Allah baya barci,”

Kallonta kareema tayi har lokacin tana kan gwiwarta “don Allah ku yafe mana aisha, don Allah ku tausaya mana”

“Dame zamu taimaka mukun? Ay Wallahi bazan taba yafe maku abunda kukayi mana ba,” salima ta karashe rai abace 

Kallonta amra tayi tace “mey haka salima? Ina kika bar hankalinki?”

Kuka ne ya kubce mata tace “Wallahi bazan taba yafe wa adda, bakisan irin wahalar da suka bamu ba, ko ahaka aka barki Wallahi tallahi alhakinmu ke binko” tana kaiwa nan ta fuce tabi bayan babanta ya rage daga ammah sai Amar da amra.

“Hajiya don Allah ki taimaka ki taya mu basu hkuri su yafe mana,” wani irin tausayinshi ne ya durar mata, gaba dayansu kamar wasu mahaukata, amra ma dai jikinta ya gama yin sanyi sosai, tana shirin takawa inda suke Amar ya matso ammah tace “Aisha bashi yaran ya su jira mu a waje”

Karban su Hamid Amar yayi ya fuce daga gidan ya rage daga ammah sai amra, daddy dai gaba daya ya zauce don surutai kawai yakeyi kamar tababbe.

Amra ce ta karaso inda Haj kareema take ta dagota da hannunta ba tare da ta kyamaceta ba, Haj kareema na Ganin haka ta fara hawaye nadama, takaici, da dana sani, “dan Allah ku yafe mana aisha, Wallahi Wallahi alhakinku ke  binmu, kinga gaba daya yarnnan su tagaiyyara, bakuda cin yau balle na gobe,ga babansu nan kullum a kwance baya….”

Saurin katseta khady tayi tace “Kun manta baki fada mata cikin shegen jikinki ba”

Saurin runtse ido amra tayi ammah dai girgiza kai kawai tayi, wannan wace irin masifa ce ta aika masu haka,

“Kema Ay iskancin kikayi Har kika samu aids,” asma ta fada tana kallonta, 

Khady dai ji tayi kamar ta makure asma don takaici, babu kunya ta cigaba da taunar cingum dinta ta dauki gwanjonta ta kalli inda asma take tace “ke ay ba

iskancin kukaje yi club ba Har kika shawu keda dan iskan saurayinki kukayi accident Har kika rasa kafa daya, futsararriya”

Tana kaiwa nan ta fuce daga gidan, amra dai kasa cewa tayi komai haka zalika ammah ma don bankadar da sukeyi ma junansu Har taso tayi yawa.

 Khady na fucewa asma ta karaso inda amra ke tsaye tare da Haj kareema Duk gaba Dayan su babu abunda suke sai kuka,

Kallon asma amra tayi tana hawaye tace “haba asma meysa kika lalata rayuwarki?”

Sauke kanta kasa tayi ta kasa cewa komai, ammah ce Tayi breaking silence din nasu tace , “baku da yayyu ne?”

“Muna dasu, ya Wahab yana prison, shi kuka ya Ibrahim Har yanxu ba a san inda yake ba, ya muhammd kuma yau shekara daya kenan namiji daga gareshi ba, daman shike tura mana kudin da zamu saya abunci dana makarantar su jalal”

Shuru ammah tayi tana dan nazari kafin tace “toh Allah ya rufa asiri, shi maisa baku kaishi asibiti ba?”

Ta karashe tana nuni da daddy daya kafe amra da idanu yana sambatu, 

Hajiya kareema ce ta iya cewa “hajiya babu kudin zuwa asibitin ne,”

Juyowa amra tayi ta kalli ammah ta dan girgiza mata kai, Nunfasawa ammah tayi tace “Allah ya rufa asiri” 

Bude handbag ammah tayi ta zaro bundle din dubu gida biyu ta miqa ma amra tana miqa mata tayi mata murmushi ta kalli kareema tace “Toh sai anjima ku”

Tana kaiwa nan ta juya ta fuce daga gidan, daddy daya kyallarawa kudin nan idanu ya kasa rufe bakinshi.

Amra ne ta kalli Haj kareema tace “mummy ga wannan ku saya kayan abuncin dashi”

Kallon kudin kareema tayi nan take ta duka kasa tana hawaye, babu yanda amra batayi ba akan karta duka mata amma taqi, asma ma ajiye sandar Tata tayi ta rungume amra tana hawaye, “dan Allah kuyi hkuri ki yafe mana, Wallahi alhakin ne yake binmu, mun wulaqantaku, mun zalinceku”

Zame wa amra tayi daga jikinta ta share mata hawaye “na yafe maku duniya da lahira, Allah ya bawa daddy lafiya,”

Tana kaiwa nan ta juya ta fuce, harta fuce hajiya kareema na hawaye haka zalika asma ma, daddy kuwa babu abunda yake cewa sai “kudi kudii miqo min nan kiga”

Wani irin banzan kallo kareema tayi mashi kafin ta miqe ta wuce daki tana zubar hawaye.

Amra na fitowa ta wuce wajen da sukayi parking lokacin kowa ya zauna Duk sunyi jugum jugum, tana shiga motar amar yaja sukabar wajen.

Tunda suka shiga mota babu wanda yace da wani uffan Har suka iso airport, nan cikin airport din Amar yayi masu wani booking sun don daman flight sun yamma yayi masu.

Tun a cikin motar malam labaran ya yanke shawarar zama anan katsina don tund ayaji ance inna ta rasu kuma ba a gidan ta rasu ba Toh tabbas tana wajen Yan uwanta da suke Yan uba don hakan ya yanke shawarar zama don ya samu yaje chan kauyen don daman chan kauyen katsina suke, don haka sukayi sallama su kuma suk wuce abuja….

Tun bayan zuwansu katsina komai ya sauya, labaran ya samu yaje kauyen dangin inna, sunyi mamakin ganinshi sosai don kowa yasan ya rasu shekaru da suka wuce sai gashi kwatsam, bai tsaya yin wani dogon baya ni ba ya shaida masu bata yayi daga baya kuma Allah ya dawo dashi.

Har labarin inna saida dan uwanta ya kaishi, ya dade sosai yana mata addua yana hawaye kafin yayi masu sallama bayan ya danyi masu sha Tara ta arziki.

Bangaren Yan abuja komai ya sauya, zaman lafiya sukeyi mai tattare da farin ciki da kwanciyar hankali, Har lokacin babu abunda ya sauya tsakanin amra da general wanda ammah ta zuba masu idanu kawai,

Kullum triplet kuwa na wajen ammah, don wataran ma a dakinta suke kwana tare da ita, basuda rigima kwata kwata, don idan kaji kukansu Toh suna son madara ne, yara dai girma sukeyi sosai suna kyau, kamannin su da iyayensu na fitowa sosai kamar Ka sace su Ka gudu.

Amar dai ya dauka son duniya ya daura masu, idan har yana gidan dashi ake rainon su  wani sa”in ma a dakinsa suke wuni saidai a buyosu da madara, gwanin ban sha awa, gidan kuwa daga shugo babu abunda zakaci karo dashi sai kayan wasan yara tun basu kai lokacin wasan bama, gata dai babu wanda basa sha wajen amar da ammah.

Har lokacin shima yana sane da amra yana timing dinta yana kokarin karantarta da abubuwan da take so daga nesa, kwata kwata ya daina shiga sabgarta, wani sa’in saisuyi kwana biyu ma bai ganta ba don koda yaushe tana zaman daki sai Yan kwanakin nan ne take yawan futowa ta shiga kitchen.

Bangaren Aman gaba daya ya maida kanshi busy man, gaba daya ya maida hankali wajen ci gaban company saboda yanda Amar ya bashi babban mukami wanda haka ke nuni da ya bashi yardarsa da amanarsa wanda hakan yasa yake son ya nuna mashi how hardworking he is,

Ta wani bangaren kuma ya danyi baya baya da salima wanda Intayi complain saidai yace aiki ne yayi mashi yawa  don yanda suke yin waya suna soyewa suna raba dare yanxu sun daina, wayar ma itama ce ke kokarin Kiran sa, daga kira kuwa saidai su dan gaisa yayi shuru idan ta fara janshi da hira sai yace mata

Ay he’s busy, abun na damunta sosai haka zalika shima, shi a bangarenshi dalilin da yasa yake mata haka ba komai bane sai guilt din abunda yayi ma mahaifunsu dake cinshi sosai, yana jin kunyar tasan abubuwan da yayi mashi, wanda hakan yasa yake danyi baya baya dukda abun na damunshi sosai.

After few months….

Yau wata biyu kenan da tafiyar Amar dubai don yanzu yana zuwa ne yayi wata daya ko biyu idan ya koma kafin ya dawo Nigeria saboda tarin responsibility daya hau kanshi, acikin watannin nan ya samu Karin girma, don yanxu yana matsayin overall major general.

Hanyoyin alkhairi ta bude masa sosai don indai yasa hannu a cikin abu to fa sai abun ya zama alkairi, ayanxu babu abunda suka wuce family dinshi, he is a complete man, abu daya ne yake lacking which is love and care from a partner wanda a yanxun yasan da hakan ba kamar ada chan baya ba.

Ayanxu ya tabbatar namiji baya taba zama complete idan babu mace a kusa dashi,a Lissafin da yake yi kusan shekara daya da watanni kenan rabon shi da mace, wata irin matsuwa ce ke  damunshi na buqatar mace dukda yana dannewa don yayi alkawarin bazai sake takura ma uwar yayan shi ba, his heart wato “Aisha!!!” He’s loving her from far, aisha ta gama da kwakwalwarshi da zuciyarshi gaba daya lokacin da baima ankare da hakan ba, Duk sanda ya koma dubai baya samun sukuni, yana son jin muryarta yana son Ganin ta yana son kasan cewa da ita saidai hakan bazai samu ba saboda Har lokacin yasan bata sauko ba, and baya Ganin laifin ta don ya zauna yayi reversing Duk abubuwa da yayi mata da irin pain din dayayi causing mata a zuciya, idan ya tuna da abubuwan nan yana jin haushin kansa sosai, tabbas maganar ammah ta tabbata don sai yanxu yake regretting komai, don aisha is one in a million, ada chan bai ga worth dinta ba sai yanxu datayi mashi nisa, babu abunda yake gani a idanunta sai kiyayyarsa da haushinsa, sometimes idan yana zaune a penthouse dinshi saidai ya bude laptop dinshi yana scrolling recorded videos dinta na cctv lokacin da suke a apartment dinshi, baya gajiya kwata kwata da Ganin videos din, sometimes haka zai zauna ya dauka hours yana kallon videos din yana murmushi kamar bashi ba, bayan wannan countless of times haka zai dauka wayanshi yana kallon contact dinta, yana son kiranta wata zuciyar Tashi tana hanashi yin hakan.

Haka zuciyarshi zata dunga mashi wasi wasi idan ya gaji saidai ya kira ammah kawai a video call don ta nuna mashi babies dinshi.

Bangaren amra, a cikin watannin nan ta Kara kyau sosai tayi murmur, shape dinta ya dawo kamar wadda bata taba haihuwa ba, ta Kara kyau da cika idanu Har wani sihirtaccen kyau ta kara saboda yanda ammah ta saka ta agaba take yi mata gyara sosai kamar wata Amarya, musamman ammah ta kira yar chad

wadda ta taba yi mata wankan Amarya tazo ta fara gyara ta sosai, don saida suka dauka wajen sati biyu tana gyara ta ciki da waje nonstop,

Karshe ma dai ammah ta dage akan Duk end of the month yar chad zata dunga zuwa tana gyara ta, kudi sosai ammah ke kashe wa akan amra wadda ita batama wani damu da Gyaran ba don wanda tasan danshi akeyi bata ra’ayin shi kwata kwata.

 

    kyauta ta musamman ammah ta bama yar chad saboda yanda ta gyara amra sai san barka, Duk inda ta gifta kamshi ke fita daga jikinta,

 Dukda haka bata barta ba haka Tayi mata ordern kayan mata daga Sudan masu kyau sosai ta bata, babu wani kunyar surkunta ammah ta zaunar da ita ta nuna mata mahummacin Gyaran jiki a wajen mace, yanda ammah keyi ma amra ko uwar data tsugunna ta haifeta sai haka, shakuwa sosai ta shiga tsakaninsu, inda kwata kwata ammah bata mata maganar Amar ko zancen rayuwar aurensu wanda hakan kesa amra jin dadi don ko babu komai tana Ganin ammah na supporting dinta,

Duk wata zata ga alert a cikin wayarta na kimanin dubu dari biyar daga wajen dadyn  princess, oga kwata kwata kenan, batama san ya bude mata account ba ta karkashinsa sai aranar ta gani, abunda ya fara bata mata rai was sunanta datagani da nashi daga bank din “Aisha Muhammad taura” dataga alert din tabe baki kawai tayi batace komai ba, the second time daya sake tura mata same amount still bata wani damu ba don ta gama fiddashi daga ranta don haka bata buqatan wani abu daga gareshi kuma babu abunda zaiyi mata da zai girgizata ko ya sauya yanda ya Gina tsanarshi a zuciyarta

Yanxu in kunga Amra ta kile sosai don yanzu she’s socialise ba kamar da ba ta kara zama yar gayu sosai irin manyan classy matan nan, idan kuka ganta kamar bata haifa triplets ba, Har lokacin bata da wata kawa a duniya data wuce haifa da anty Madina wadda ayanxu ta zama abokiyar shawarar ta kuma

86 / 94