Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   10 / 94

27K to 30K   out of 279.4K words

wa tayi Har kasa tace “barka da fitowa hajiya, ya ciwon kafar”

“Alhamdulillah lantana na barki da aiki ko”

Ta amsa mata fuskarta asake

“Ah ah ba komai hajiya Ay na gama, miyar Ma na sauke, Kajin ne nan gama soyawa ba,”

“Yauwa daman inata tunanin yarannan karsu dawo da yunwa ba a gama ba”

“Ay an gama yanxu zan karasa, Har kunun Salim  ma an gama”

Madallah sannu lanatana Allah ya biya ki”

Sunkuyar da kanta tayi alamun kunya tace Ameen hajiya.

Juyawa ammah tayi tare da dan dingisa kafafunta Har takai bakin kofa lantana tace

“Yauwa hajiya malam labaran yazo bai dade da tafiya bama, lokacin kina hutawa, na shaida mashi baki Tashi ba tukunna, yace zai dawo anjima”

“Allah sarki Ay da kin kirani na sauko Mun gaisa, mlm labaran dai Akwai kokarin zumunci”

Ganin yanda lantana ke murmushi yasa ammah murmusawa ta fuce daga kitchen din, parlor ta samu waje ta zauna ganin Ana program din wa’azin da bata bari yana wuceta a sunnah tv, mintuna kadan karar horn ya karade gidan alamun Yan makaranta sun dawo.

Ana bude gate driver ya samu wajen parking ya parker motar, salima ce ta fara fitowa sanye cikin uniform da ya mashi jikinta sosai daman bata yar kiff kiff batada wani qiba saidai itama Allah ya bata sura mai kyau don tana da shafe dinta daidai jikinta,ganin Ana zabga rana tace “Wai Malan Mamman yau Ana rana sosai gaskia”

Dariya wanda ta kira da mammman yayi bayan ya gama parking yana shirin kashe motar yace “yar gidan hajiya Ay kwana biyu nan Ana rana sosai”

Janyo kamar school dinta tayi kafin ta bude kofar baya ta futo tare da janyo Jakarta tace “mlm mamman wallahi bazan iya dauko wannan katon yaron ba, ka tasoshi ya tako da kafarshi”

Tana kaiwa nan ta wuce hanyar dazai sadaka da entrance, motar Aman ce ta kutso kai, tunda ya hangota daga nesa yaji wani sanyi aranshi, yanda ya karade gidan da horn da yanda ya karaso compound din yasata tsayawa daga nesa don Akwai rana sosai bata ganin gabanta sosai, lumshe idanu tayi tare da sanya hannunta kan fuskanta don kare rana, ganin motar shi da yanda yayi parking ya tabbatar mata dashi ne, kusan wata guda kenan rabonda ta ganshi a gidan, dan tabe baki tayi Har zata juya ta tsaya ganin ikon Allah, mlm labaran dake shirin futa daga gidan ganin motar aman ya sashi tsayawa don baimaga motar su salima ba data shigo don ya dade wajen mai gadi kafin ya zaga bayan gida, yana karasowa ya soma bude mashi kofar motar, yana futowa kuwa ko amsa gaisuwar da yake mashi baiyi ba yace “ka wanke min motar nan Zan fita anjima kadan”

Cike da biyayya yace “Toh yallabai “

 

Salima wanda ta tsaya ganin iko da isa da kuma wulaqanci irin na aman, tabe baki tayi don tsaf taji abunda suke cewa saidai bata hangosu sosai sbd rana da ake kwallawa sosai,

“Mutun kwata kwata baisan darajar mutane ba,”

Tsaki ta buga wanda tsaf ya hangota kafin ya shige cikin parlor, bin bayanta yayi da kallo yana ayyana abubuwa da dama aranshi, gaba daya ta tafi dashi yarinyar dukda taki sakawa dashi.

Parlor ya wuce shima? Yana shiga ya ganta gefen ammah Sai zabga shagwaba take

“Wallahi amma na gaji yau dinnan, mid term test mukeyi”

Shafa fuskanta ammah tayi tace “sannu yarinyar kirki Ay an kusa gamawa Insha Allah, Allah ya taimaka”

“Ameen ammah na” ta karashe tana zabga ma aman dake shugowa ya kafeta da idanunshi, 

“Ammah bari naje na cire kaya nan Sai nazo na maki tausa”

“Toh yarinyar kirki”

Murmushi tayi Ma ammah tare da wucewa sama  bayan ta gama zabga mashi harara a karo na biyu.

Dariya kawai yayi tare da zama gefe yace “barka da hutawa “

“Thank you son,Ina ka shiga kwana biyu koma kiraka bana samunka “

“Mikewa yayi ya nufi hanyar part dinshi yace “nayi tafiya ne”

Yana kaiwa nan ya shige dakinshi

Murmushi kawai ammah tayi tana mamakin hali irin na aman babu ladabi kwata kwata bai damu da girman kowa ba ahankali ta furta “Allah ya shirya mana”

Salim dake barcinsa hankali kwance  cikin mota baima san sun iso ba saida malam mamman ya tasheshi kafin ya mike, jakarshi shima ya janyo kafin ya wuce hanyar dazai sadaka da cikin gida, bai kaiga karasawa ba ya tsaya tare da juyowa jin maganar da mai gadi yake yima labaran “malam labaran Sai hkuri fah, yaran zamani daman Sai hakuri Allah ya shirya mana “

Dariya labaran yayi kafin  ya janyo tiyo da suke Jan ruwa ya soma wanke mashi motar yace “ba komai ay malam dauda,Allah ya shirya mana kawai”

Kurama labaran idanu Salim yayi dukda hasken rana ya hanashi ganinsa da kyau yana son tuna abu saidai ya Kasa tunawa, 

Ammah data hango shi tsaye don abude aman yabar kofar daya shigo bayan salima tace

“Babana shugo mana ya ka tsaya bakin kofa”

Waigowa yayi ya shige cikin parlorn tare da karasawa jikin ammah ya zauna gefenta yana mata murmushi, shafa kanshi tayi tace “sannu babana ya gajiyan makaranta, nasan ka gaji sosai ko”

Girgiza mata kai yayi don baya magana Har lokaci ko a makaranta saidai ya rubuta baya iya karantanwa.

“Maza aje ayi wanka Sai’a sauko aci abunci ko, anty lantana tayi maka kunun madara da kake so sosai”

Murmushi yayi harda tsallen murna ya mike ya wuce sama zuwa dakinsu.

Bangaren amra…

Tun bayan abunda ya faru tsakaninta da general ta fara wasan yar buya dashi,kwata kwata ta daina zaman parlor data saba dalili kuwa shine kunyar shi takeji sosai hade da tsoronshi daya ninku a zuciyarta Har yafi na da,cin abunci ke sauko da ita Kasa tana gamawa kuwa zata koma daki abunta, abubuwa da yawa sun dameta, na farko tanason tunkarar shi da maganar yarjejeniyar don harya Allah yanxu hankalinta ya soma tashi, abubuwa suna neman zautar da ita, na farko tunanin qannenta daya dawo mata sabo ace ta dawo nigeria amma bata tafi wajensu ba abunda ya kamata tayi tun farko, na biyu zamanta anan gida

bashida wani amfani, gashi ta kasa tunkarar shi da yarjejeni don taji abunda zatayi mashi don ta samu ko zataji saukin blaming kanta da take akanshi,bayan wannan Ma don ta samu ta kawo karshen zaman nasu don ita dai ta bangarenta babu riba saidai kuma tana tsoron shi don batason ta yanda zata tunkareshi ba.

Ta bangarenshi shima tun bayan haduwarsu ta karshe bai sake bi takanta ba don daga baya Ma haushin Kansa ya soma ji, don rashin ganinta dinma ya sashi jin kamar ta soma raina shi, in badan haka ba kullum idan ya dawo komi dare zai taddata a parlor, ganin kamar raini ya neman shiga yasashi cigaba da harkokinshi shima, don yanxu yana jin komai yana gab da zuwa karshe.

Karfe biyar na yamma ta sauko qasa domin duba Nadine dake zazzabi, doguwar rigace a jikinta kamar koda yaushe abaya, Sai kamshin turaren ta take yi mai dadi wanda ya fara zama jikinta, futowa tayi daga dakinta cikin natsuwa ta sauko kasa, direct dakin Nadine ta wuce, tana knocking ta shiga ciki, a duqunqune ta ganta cikin bargo, da sauri ta karasa gabanta tare da mata sannu, Nadine na ganinta tayi kokarin zama dukda tana jin jiki tace “sannu Ma,”

“Ayya sannu Nadine, ya jikin kinsha Magani ko za a kaiki asibiti ne?”

Da kyar ta bude baki tace “no ma, basai an kaini asibiti ba, inajin sauki”

“No Nadine kalli fa da kyar kike zama, Bari na nemi driver a kaiki asibiti”

Shuru Nadine tayi don gaskia idan tayi kawaici zata cutu sosai.

Fitowa Amar tayi hankali a tashe don ta rasa abunda zatayi, ba tare da tunanin kayan jikinta ba don abaya ne kuma yadan kamata sanin cikin gida ne yasata bataji komai ba ta gyara hulan kanta ta gyara ta fito daidai baki kofa, ganin garin ya dan soma duhu, daga chan nesa ta hango gateman, kiranshi tayi da sauri ya karaso gabanta yace “good evening ma”

“Evening please where’s the driver?”

“Driver is not around ma,ya fita da oga”

“Okay” ta juya cikin gidan

Binta da kallo gate man yayi kafin ya koma kan aikin shi

Shuru tayi tana rasa abunda zatayi gashi bata da number shi balle ta kirashi, shima oga kwata kwata dinma bata da line dinshi, Kasa zama tayi ta koma dakin Nadine, ganinta soma barcin wahala yasata dawowa parlor don zaman jiran tsammani, gani kusan karfe 6:50pm lokacin har an kira sallah yasa ta miqewa ta wuce sama da dauro alwawala tana idarwa ta sake saukowa kasa don duba lafiyar Nadine, barci takeyi saidai. Ranar sanyi da jikinta ya dauka ya sata shiga fargaba sosai sanin baya dawowa da wuri ya sata futa neman number general ko zata samu wajen gate man, tana futa kuwa ana bude gate, mamakin dawowa shi a lokacin ta soma yi saidai kuma ta dan fuzge don taji dadin dawowa nashi adaidai lokacin, tunda suka kutso kai ya zuba mata idanunshi, kusan kwana uku kenan rabon shi daya ganta, mamakin ganin ta tsaye a wajen yayi, ganin ta koma ciki ya sashi futowa bayan driver yayi parking, cikin parlor ya shige cikin

takushi mai daukan hankali da natsuwa fuskan nan tamm, yana shugowa ta miqe tsaye, kallo daya tayi mashi suka hada idanu kafin ta sauke nashi tace “barka da dawowa”

Ya dauka sakanni kafin ya kauda kanshi ya soma bin hanyar wucewa sama

Daman batayi expecting amsawanshi ba don haka tayi saurin cewa “uhm daman Nadine ce bata jin dadi,”

Tsayawa yayi kafin ya juyo ya kalleta kamar bazai ce komi ba yace “meke damunta”

“Zazzabi ne ya sata zama so weak”

Sama ya wuce ba tare da yace mata komi ba ganin haka ya sata zama dabas  Har aka kira sallar isha I tana nan zaune akan kujera don batasan me zaiyi ba, gashi baice mata komi ba, bayan mintina Sai gashi ya sauko, ya sauya kaya zuwa wasu daban na Shan iska alamun ya sake wanka, key ne a hannunshi Dayan hannun kuma wayanshi ce dake ta ringing babu qaqautawa.

Kallonta yayi ta gefen ido yace “kije ki fito da ita”

Da sauri ta wuce dakin Nadine tana shiga kuwa ta taddata tana amai, saida ta taimaka mata kafin suka fito tare don ko tsayuwa bata iyayi, harya kai wajen parking ya fidda wata zabgegeiyar motarshi, suna fitowa ya hango su, saida ya masu horn kafin su ta taimaka wa Nadine suka karasa wajen motar, bayan motar ta bude ta taimaka wa Nadine ta shiga ciki kafin itama ta shiga bayan ta zauna.

Tafiyan minti ashirin ta kawo wani hadadden private hospital, kamar Ana jiran su kuwa wasu nurses biyu suka karaso da gado aka fito da Nadine, amra wadda ke shirin fitowa don tabi bayansu ta tsaya kyam jin abunda yace “karki sake ki fito”

Komawa tayi ta zauna ganin yayi kicin kicin, wucewa yayi cikin asibitin ya barta a cikin motar, saida ya tabbatar an aje Nadine a daki mai kyau an bata taimakon gaggawa don Har drip aka kara mata kafin ya bada umarnin a kula da ita Har a sallameta kafin ya fito.

Tun bayan fitarshi kuwa hankalin amra ya Tashi sosai ganin a gaban idanunta bayan ya shige aka shugo da wani yaro ranga ranga yayi accident nan take ya tuna mata da salim, cikin tashin hankali ta soma tunanin qannenta hawaye nabin fuskanta kamar ruwa.

Yana shiga cikin motar baima tsaya kallon inda take ba ya fuzge motar ya futa daga compound din, ahankali ahankali ya soma jin sheshekar kukanta yana shiga kunnenshi don goshi Bakinta tayi sanin cewa baya son kuka, dagowa yayi ta glass ya kura mata idanu dukda idanunta na kasa hakan bai hanashi fuskantar kuka take ba saida ya hau babban titi kafin ya gangara gefen titin inda babu mutane Sai hasken street light ya Parker motar, jin alamu tsayawar motar yasata tunanin ko sun iso ne, dagowa tayi ta kalli glass din gefenta, ganin su gefen titi yasata dagowa ta kalleshi ta cikin glass din gaban motar, ganin idanunshi a Kasa

ya sata sauke kanta kasa ta cigaba da kukan zuci dana fili gabanta na faduwa kadan kadan, bataji alamun futarshi daga motar ba Sai gefenta daya bude ya shigo kai tsaye ya rufe bam, ganin haka ya sata dan kara karfin kukanta wanda ya sashi runtse idanunshi ya kwantar da kanshi bayan kujerar tare da lumshe idanunshi.

Shuru kusan minti biyar baice mata komi ba itama tunda ta rakube gefe bata dake motsawa ba saima dan kara volume din kukanta da tayi tare da shesheka, ganin kukan nata yaqi karewa ya sashi bude lumshenshun idanun shi ya kalleta tsaf, fuskanta ya kurama idanu don dan hasken street light din ya bashi damar ganinta da kyau, lashes dinta sun kwanta lub lub don ta rufe idanun gam taqi budesu

“Stop that”

Ta gama karantarshi tsaf, don tana jin haka tayi tsit saidai kukan na nan a maqale.

“Open your eyes and loook over here”

Ya sake fada cikin natsuwa

Juyowa tayi kamar yar koyo tana tsoron laifi ta kalleshi, ganin yanda idanunta sukayi jaa saida ya sashi lumshe idanu

“Why are you crying? Saboda na hankali fita haka?”

Da sauri ta girgiza mashi kanta tace “ah ah”

“Why are you crying then,I hate those tears”

Shuru ta danyi don bata fahimce shi ba 

“Uhm why?”

Ya sake tambayanta 

“Na tuna da kannena ne”

“Okay so?” Ya sake tambayanta 

Hawayen da take hiding ne suka sake sauko wa, take ta fashe da wani matsanancun kukan da baima san lokacin da ya janyota ba jikinshi, Sai jinta tayi a jikinshi tsamm, abunka da mai neman sassauci, tana jin haka tadan kama rigarshi ta fashe baiyi yinkurin yin komi ba haka zalika baice mata qala ba, harta gaji ta fara sauke ijjiyar zuciya, ahankali ta soma dawowa natsuwarta harta fuskanci tana cikin jikinshi, kamshinsa dake fuzganta Har wani barci barci ke neman kwasarta a wajen, yana jin alamu ta daina kukan bai sauketa ba still tana jikinshi itama batayi yinkurin Tashi ba don tana tsoron yin laifi, sun dauka kusan an hour a haka kafin ya fiddota daga jikinshi, “ke mage ne?”

Tambayar Tashi ne ya bata dariya har dan dimple dinta ya fito, ya fahimce tana da son jiki, rashin iya hausanshi sosai ya sashi fadin hakan.

Gyara zamanshi yayi kafin yace “kinason ganin qannenki ne?”

Da sauri ta dago ta kalleshi Adan shagwabe ta girgiza mashi kai hawaye na shirin zubo mata “inason na Gansu, inason nasan a wani hali suke ciki, saidai Ina tsoron zuwa gidan, bansan mai Zan tadda ba, Ina tsoron haduwa da uncl….”

Kura mata idanu yayi don tunda ta soma magana ya zubama idanunta da Bakinta idanu 

“Waye shi?”

“Uncle dina ne,wan babana kuma mariki na,”

“Maysa kike tsoron haduwa dashi,”

“Uhm saboda…saboda”

Ganin yanda ya kura mata idanu yasata cewa “saboda shine yayi sponsoring upkeep dina, kuma yace Saina biyashi gashi ban samu abunda naje nema ba, na janyo maka ka rasa aikin ka kaima bansan ya zanyi ba I’m so sorry, Wallahi idanda Akwai abunda zanyi na maida hannun agogo baya danayi, I’m feeling guilty, nabar siblings dina and I’m d reason kaima aka koreka daga aikin ka, I’m so sorryyyy ka fadamin abunda zanyi maka ko Zan rage jin zafin abubuwan dake damuna,..” ta karashe da kukan da ke nuni da abun yana mata ciwo sosai.

Mamakin yanda kalamai irin wannan suke futowa daga Bakinta yake,kallon shekaru ta yake all this while ba girma ta ba ko tunaninta, saidai yana hango tsantsar kuruciya a tattare da ita, kukan nata ma yanxu burgeshi yakeyi da yanda yake komai a shagwabe, bazaka taba tantance halin da yake ciki ba fuskannan dai tana nan babu alamun fara a, Sai kyalli da takeyi alamun hutu ya zauna a jikinshi.

Baice mata komi ba ya fito daga gaban motar ya koma gaba ya zauna kafin shi dai kamar wahainiya, yanxu saiya chanza launi shiyasa baka taba gane mashi hade fuska yayi yace “I’m sure Kinsan cewa niba driver ki bane ba,”

Jikinta ne yayi sanyi don taga fuskanshi lokacin da ta karashe maganar, futowa tayi cikin natsuwa ta dawo gaba ta zauna yaja motar da mugun speed suka bar wajen.

Akan hanya babu wanda yace da waninsa tak, Sai karar ac dake busowa tare da kamshi da dake addabarta, jifa jifa take waigowa tadan kalleshi ta gefen ido kafin ta dauke,gaba daya zaman Ma Ya gundureta ganin yanda fuskanshi ta janza lokaci guda.

Shiko sarai ya gama gane weakness dinta don haka tunda ya dauke kanshi bai sake kallonta ba Har suka iso gida, yana parking motar ya juyo ya kalleta ganin harta fara barci, barci ne takeyi peacefully kamar baby, fuskanta so cute, Kasa tashinta yayi sai idanu daya zuba mata,ganin kusan karfe 10 yasa ya dan taba hannunta,laushin fatarta ya sashi yana Kasa tashin nata, ahankali ta soma motsa yana jin haka ya dauke hannunshi yayi Gyaran murya, tana jin haka kuwa ta farka ganin inda suke yasata bude kofar ta futa, shima fitowan yayi yabi bayanta lokacin daya karasa parlor harta haura sama, kofan ya rufe kafin ya wuce sama.

Koda ya karasa sama kaya shi ya soma ragewa, wayanshi dake ringing ba qaqqutawa ya dauka ganin ba number da aka dunga kiranshi da shi bane daxu yasashi saurin dagawa 

“Oga barka da dare harka kwanta ne inason maka wani albishir ne”

“No ban kwanta ba, na fita ne, any update”

“Na samu binciken daka bada umarni ayi akan wannan Alhaji mustapha, sannan yarannan da akayi trafficking iyayen shi sunzo Yanxu haka Mun basu masauki don Yan kano ne,gobe saika zo muji ta bakinsu don alamu sun nuna kamar yaronnan wayo aka mashi shida iyayen nasa,Sai gayen daka buqaci ganinshi, zai shigo nigeria on Friday”

Murmushin gefen baku yayi wanda kana gani kasan shi kadai yasan abunda yake qissawa a cikin ranshi yace 

“Weldone lieutenant asad,”

Maganganu sukayi mai tsayi wanda ya danganci aiki kafin

10 / 94