Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   17 / 94

48K to 51K   out of 279.4K words

ko”Ina a kashe yasa ammah cewa mu koma da alamu bai Tashi ba, haka suka koma yuuuu zuwa parlor, breakfast suka fara yi kafin ammah tasa a dafa mashi favourite dinshi, anan parlor suka ya da zangon zaman jiran, salima na gefenta tana mata tausa,

Karfe goma daidai ya fito cikin shirinsa, cikin kamewa ya tsaya daga gefe don basu Lura dashi ba ganin su a zazzaune ya sashi kallonsu daya bayan daya, idanunshi ne suka sauka kan salima, take gabanshi ya fadi ganin kamannnin ta da amra wadda ya kwana da ita a ranshi, saidai ita batakai amra kyau ba sannan ita siririya ce, salima dake gefen ammah ya kalla, kanshi akan cinyarta salima kuwa tana Kasa tana matsa mata kafa sai suka burgeshi sosai, Gyaran murya yayi gaba daya suka maido da hankalisu kanshi, fuskanshi Adan sake ya karaso parlorn da sauri salima ta miqe, fuskanta dauke da murmushi don tana ganinshi ta tabbatar da ya Muhammad dinsu ne, salim ma da sauri ya Tashi ya tsaya gefen salima, ammah kuwa wadda tun fitowarshi ta karfe shi da idanu, murna da farinciki tare da kewar danta yasa ta miqe itama tare da bude mashi hannunta kamar baby, da sauri ya tako ya karaso yayi hugging dinta, “welcome son, Alhamdulillah nayi kewar ka sosai, ka iso lapiya ya hanya”

Yana cikin jikinta yana jin kaunar mahaifiyarshi na ninkuwa sosai a ranshi ya dago yace “nayi kewarku sosai nima, na sameku lafiya,“

Janshi tayi Har kujeran da take zaune suka zauna, da sauri su salima Ma suka karaso suka tsugunna Har kasa “barka da dawowa ya Muhammad, ya hanya an iso lafiya”

Kallo su yayi fuskanshi dauke da murmushi yace “Alhamdulillah how are you? Ya school Ana kokari dai ko?”

Bakinta a washe tace “Alhamdulillah Muna yi”

Hannu ya miqa Ma Salim ya tako Har gabanshi ya zaunar dashi gefen shi sanin baya magana, shafa kanshi yayi yace “how are you dude”

Girgiza mashi kai Salim yayi bakinsa a washe, ba qaramin dadi amra taji ba ganin su a zaune, nunfasa tayi tace “son breakfast is ready”

Dining suka wuce shida ammah ta zuba mashi abunci da kanta kafin ta zauna gefenshi tana kallonshi, suna yar firar yaushe rabo.

Suna nan zaune Aman ya shigo cikin parlor, da masoyiyar shi ya fara cin karo wadda ta zabga mashi harara kamar idanunta zai fado kasa, dariya kawai yayi kafin ya maida idanunshi kan dining, mamakin ganin Amar yayi sosai, kafin yayi dariya ta gefen baki ya wuce wajen dining din, kallo daya amar ya mashi ya kauda kai shima baice mashi Kala ba saika kallon ammah yayi yace “ashe manyan baqi mukayi, barka da dawowa”

Amar bai kalleta ba yace “thanks”

Akufule yabar dining din don baya qaunar attitude irin na amar.

Yana gama breakfast ya koma daki ya shirya cikin kananun kaya ya fito cikin kamewa ya hau sama zuwa dakin ammah, yana shiga ya taddata zaune kan gado, karasowa yayi ya zauna gefenta “babana zaka fita ne ko hutawa baka gama yi ba kayi doguwan tafiya”

Kallonta ya danyi kafin yace “I have to go ammah, harda fitan da zanyi a cikin dalilin zuwa na Niger, ina buqatar addua ki”

Hannunshi ta kama ta rike tace “Allah yayi maka albarka, ya baka zuri’a mai albarka ya tsareka kuma ya baka sa’a”

Da sauri ya amsa da Amin fuskanshi a sake don  yana jin dadi adduoin ta agareshi.

Sallama yayi mata ya fuce daga gidan, direct gidanshi ya wuce, koda ya shigo a parlor y yasa zango, ya dauka kusan minti talatin a zaune yana kallon stairs kafin ya miqe ya wuce sama, dakinta ya wuce direct, bai tsaya knocking ba ya bude kofar ganin babu haske a dakin Sai duhu duhu ya sashi shigewa ciki ya rufe kofar ya kunna switch din dakin, nan take dakin ya dai haske bauuuu, idanunshi ya sauke kan gadon da take kwance ta qudundune bargo a jikinta ,fuskanta a waje, karasowa yayi gefen daidai gadon ya nannade hannayenshi a kirjinshi ya kura mata idanunshi, waigowa yayi ganin akwatinta agefe ya sashi maido da idanunshi kanta ahankali ya furta “stubborn girl”

Kamar tajishi kuwa ta fara bude idanunta ahankali jin turarenshi na shiga cikin hancinta yana kaiwa ziyara kwakwalwarta, arazane ta mike zaune tama manta da yanayin kayan jikinta, saurin kauda kanta tayi shiko ganinta da yayi ahakan yasa ya baka idanunshi abuncin da suke marari, farar singlets silky night gown

ce a jikinta, tayi laping a jikinta tayi Ma fatarta kyau sosai, maido da idanunta data kauda gefe tayi ta kalleshi ganin ya kura mata idanu yasa ta duban jikinta da sauri ta janyo bargon ta lullube jikinta da kyau ta bata rai tammm.

Gungunita soma yi “mutun Sai kallon tsiya “

“What did you just say?”

Bata daga ba haka zalika bata ce mashi Kala ba saima Kara hade rai datayi 

Ganin haka ya sashi hasala yace “karki sake ina maki magana kina kauda min kai”

Kamar bata jishi ba haka tayi banza dashi saima wani abu daya shiga a zuciyarta, kokarin cire tsoronshi tayi kamar bata san yana existing a wajen ba ta janye bargon kyawawan cinyoyinta suka bayyana, wata irin miqa tayi cikin yauki daya sashi danyi tagal tagal kamar zai fadi idanun nan Har wani ruwa ruwa suke fiddawa, sauke kafafunta tayi ta miqe tsaye, yar rigar ya karema kallo don ko gwiwarta kadan ta karasa, ta gefen shi ta rabe kamar batasan yana wajen ba cikin tafiyarta ta natsuwa ta wuce toilet ba tare da ta kalleshi ba, haka ya raka ta da idanu harya shige cikin bathroom din don ko kallon yanayin daya shiga batayi ba, wato tun bayan tsyauwarta ya kame kamar soja anyways daman chan sojan ne, gaba daya tsikar jikinshi ta tashi m, saida ya dan dawo daidai ne ya soma jin kunyar kanshi baiyi wata wata ba ya fice daga dakin.

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 115

Update!!!

14/05/2023

Unedited

Tun bayan fitarshi daga cikin dakinta motar ya shige ya fice daga gidan rai abace.

Bayason komawa gida don haka yayi saurin Kiran asad a waya, “kana Ina ne?”

“Morning oga, Ina gida asad yayi saurin amsa shi, 

Azafafe yace “meet me at the resort,inaga hanyar daka kawo shawara ita zamubi,”

Sauke nunfashi asad yayi yace “okay ba damu zanzo yanxu.

Juya akalar motar shi yayi da mugun speed, yana isa resort saida ya jira isowar asad kafin su shige tare.

Babban wurine babu hayani kwata kwata, mutane qalillan ke yawo, bangaren zama suka samu suka zauna kafin asad ya soma magana “ka koma gida ne?” Cije baki yayi ya kalli asad yace 

“Yea na koma jiya”

Kallonshi asad ya sake tare da tattara nutsuwarshi

“Oga are you sure akan batun nan kuwa,”

Tabe baki ya fuskanceshi da kyau yace

“Dude in banyi da kaina ba wazai yi, I’m the only closer person to them, ta haka Zan tattara Duk wani evidence akansu”

Girgiza kai asad yayi alamun gamsuwa zancen sa kafin yace “okay then, amma you have to be careful, this man is dangerous,musamman yanda familyn ka ke tare dashi, idan bamu zama very careful ba zai iya yin abunda bamuyi tsammani ba”

Runtse idanu Amar yayi don maganar kadai ma zafi yake mashi a zuciyarshi “Akwai abunda ke daure min kai, I don’t even want to think about it,”,

Kallonshi asad yayi yana son Karin bayani

“It’s about dada,I’m beginning to suspect kasheshi akayi”

Saurin runtse idanunshi da sukayi jaa yayi 

Ganin haka yasa asad dan dafashi yace “meysa kake zargin kashesa akayi?”

Da saurin cikin bacin rai yace “Saboda alamu sun nuna, Akwai wani secret information daya turamin a day before rasuwanshi, and Duk abunda yake buncike akai yayi ya danganci wannan empire din, da wannan nake ji ajikina there are a lot behind the doors”

Shuru asad yayi yana sauraronshi kafin yace “kabi komai a hankali, yanxu mu jira muji daga wajen hammam Idan Har Mun samu wani abu daya danganceshi to tabbas yana cikin kungiyar”

Dafe kanshi yayi dake mashi ciwo sosai, baya son tuna komai ayanxu, basu wani dade ba sukayi sallama kowa ya hau motarshi.

Taura estate…

Yana parking ya fito ya wuce cikin gidan, ganin babu kowa a sitting room yasa ya wuce dakinshi, wanka kawai yayi ya kwanta kafin lokacin sallar asr yayi.

Karfe 3 daidai karar wayarshi tashesa, rai Adan bace ya bude idanunshi ya dubai wayar, ganin I know called yasa ya danyi tsaki ya aje wayan,ringing din na katseta wani call din ya shigo, ranshi Adan bace ya dauka wayan ya saka a kunnenshi, shuru ya danyi na Yan mintuna jin ba ayi magana ba sauke huci yayi mai zafi ya doka tsaki zai zare wayan kenan muryar mace ta katse mashi tunani “pleas don’t hang up,”

Bai bude idanunshi ba saidai yayi mamakin mai Kiran don bai dago muryar koma waye ba, cikin yauqi meeda tace 

“Dan Allah spare me just 5mins”

Baice mata qala ba haka zalika bai cire wayan ba idanunshi still a lumshe

“ uhm nasan bazaka ganeni ba,sunana hamieda, Mun taba haduwa a airport, Ina magana ne da Muhammad Amar?”

Mamakin tsagerancin ta yayi, baya kaunar mata marasa aji kwata kwata

Jin yayi shuru yasa ta cire wayan kafin ta maida kunnenta ganin bai kashe wayan ba ta cigaba 

“Sorry ko na kira lokacin da bai daceba?”

Tsaki ya buga yace “whoever you are, karki sake kirana, rubbish”

Yana kaiwa nan ya kashe wayan yayi wurgi da ita gefen gadon ya miqe ganin lokacin sallah har yana neman giftawa.

Yana dawowa daga masallaci ya wuce sama wajen ammah, a zaune ya taddata, cikin kamewa ya tako Har gabanta yadan duka kasa “son harka dawo”

Murmushi ya mata yace “na dawo tun dazu nadan kwanta ne,”

Shafa kanshi tayi tace “abinci fah? Kayi lunch?”

Kallonta yayi cikin kyaunar ta da kulawarta a gareshi “Alhamdulillah Sai zuwa anjima,ya kafar kinashan magani kuwa?”

Fuskarta dauke da murmushi tace “ay naji sauqi alhamdlh, girma ne yazo mana”

Yana jin haka ya dago inda zancen ta zai nufa saurin kauda zancen yayi ta hanyar cewa “yarannan fah?ban gansu ba”

“Sun tafi islamiyya Ay, yauwa son inata so muyi maganar yarannan, baka taba hadani da mahaifinsu ba, haka zalika nan taba jin sunyi magana akan iyayen su ba,nima ban tambaye su ba”

 Hannayenta ya rike ya sumbace su ya kalli cikin idanunta yace “ammah, lokaci zaizo very soon Zan maki bayani daga baya in sha Allah”

Sanin halayyanshi yasa ta daga kai alamun gamsuwa tace “Allah ya nuna mana”

Chan kasan makoshi Ya amsa da “Ameen”

Shuru ya danyi yana san tambayarta abu saidai yana tsoron tambayoyin da zatayi shi kuma baya son ta shiga rudu da tunani, cikin da bata ya soma tambayarta“ daddy fa? Yayi tafiya ne”

Mamakin tambaya akan dady tayi sosai don Idan yazo ko shekara zaiyi Idan basu hadu da dady ba baya damuwa kuma baya tambayar da, dalilin ne Ma take yawan yi mashi fada tare da nuna mashi mahimmacin dadyn a matsayin shi da wa in mahaifinshi kuma uba a wajen shi saboda aurenshi da take.

Murmushi ne shimfide a fuskarta don taji dadin tambayar da yayi, tace “baya nan yayi tafiya zuwa china, Yau wata guda kenan”

Da sauri ya kalleta yace “yaushe zai dawo”

Ba tare da tunanin komai ba tace “yace min business trip ne, Sai Mun ganshi kawai”

Nazari ya soma yi kafin ya kauda zancen ganin yanda yake mashi kallon tuhuma, “uhm ya company kuwa?hope komai is under control”

Take fara’a r fuskarta ta dauke, yana  ganin haka ya fuskanci Akwai problem, saurin kauda tunanin daya zo kanta tayi ta saki fuskarta tace “kwanaki an dan samu problem but everything Is under controlled,”

Miqewa yayi ya mata sallama ya fuce, yana fucewa wasu hawaye suka sauko kan idanununta, tunanin dada ne ya fado mata Idan Har ya kalli Muhammad komai nashi irin na babanshi, tsayuwanshi da yanda yake miskilancin sa magana Ma wuya yake mashi, idan zaka zauna dashi a wuni daya bazaice Tak ba, ahanklai ta furta “Allah ya jiqanka dada”

Yana futowa daga wajen amma ya sauko kasa, anan kasan ya riski aman zaune kan kujera yana waya, kallo daya ya mashi ya kauda kai ya wuce dakinshi, da harara Aman ya bishi. Kafin ya cigaba da wayanshi. 

Karfe shida da rabi daidai su salima suka dawo daga islamiyya,ammah ce kawai a zaune a parlor tana kallon tashar sunnah tv hannunta rike da charbi, da gudu Salim ya zo jikinta ya zauna gefe, salima na biye dashi tace “kai karka balla mana ammah”

Dariya ammah tayi ta kallesu su duka tace “Yan islamiyya, Yau Ansha hadda”

Dariya salima tayi tace “Wallahi ammah dakyar Allah ya taimake ni na biya”

“Kinyi kokari Ma my dear, kuje sama ku chanza kaya lokacin sallah ya kusa”

Suna cikin magana kamshin turaren shi ya sanar da isowanshi wajen, ya fito daga bedroom dinshi sanye cikin jallabiya, takowa yayi har inda suke zaune, da sauri salima ta tsugunna Har kasa tace “barka da fitowa ya Muhammad ina wuni”

Hannu ya miqa Ma salim alamun ya taho kusa dashi, kallon saliman yayi aranshi yana yaba halayyanta yace “ya karatu?, ana dagewa dai ko”

Da saurin ta cikin zumudi tace “Alhamdulillah munayi sosai”

 Murmushi ya danyi ta gefen baki ya shafa kan salim yace “jeka chanza kaya mu tafi masjid lokacin sallah yayi”

Da sauri Salim ya hau sama salima Ma ta bishi, maida idanunshi yayi kan ammah itama shi take kallo fuskarta dauke da murmushi tace “za aje masjid ne son”

“Uhm kawai yace mata ya zauna gefenta Har salim ya futo suka wuce masallaci,itama saman ta wuce.

Zama sukayi a masallaci Har akayi sallan isha’I dasu, suna idarwa hannunshi rike dana salim suka wuce cikin motarshi, wani katin mall suka tsaya yayi parking suka wuce tare, hannunshi hade dana salim suka shiga ciki, kallon yanda Salim yake murna yayi yace “dauka abuna kake so and don’t forget your sister okay”

Salim najin haka yayi tsalle,janyo trolly yayi suka shiga zagayen wajen, yana kallon yanda Salim ke tsalle tsallen shi, saida suka gaji kafin su fito da ledoji

niki niki, yana son zuwa gidanshi dake larric, tuna wani abun ya sashi wucewa gida kawai.

Sai wajen karfe Tara suka iso gida, babu kowa a sitting room sai tv dake aiki, kallon Salim yayi yace “kake sama ku taba kaifa sister ka”

Girgiza mashi kai Salim yayi kafin ya wuce sama da gudu don murna. Dakin ammah ya wuce shima ganin tana shirin kwanciya yasa ya mata sallama ya sauko kasa.

Koda ya sauko babu kowa a kasan, dining ya wuce ya tsaya ganin flask da ammah ke dafa mashi coffee, Harda mug din flask din, murmushin ya yi yana yaba kulawa da ammah kw nunawa a gareshi wanda Duk duniya bayan dada babu wanda ya taba mashi, coffee din ya deba ya wuce dakinshi,kayan jikinsa ya rage daga shi Sai inner shorts dinshi, janyo laptop dinshi yayi ya hau kan gado ya fara aiki, yana Shan coffee din, ya dauka kusan awa kafin ya gama, janyo remote din tv dake aiki yayi ya kashe ya kwanta, tunanin da yake son hana kanshi ya kasa, lumshe idanunshi yayi tare da forcing kanshi ko zai samu yayi barci har kusan karfe daya, ganin haka yasa ya zauna rai Adan bace yace “maysa kake yawan saka ta aranka Well its because she’s so important now,” runtse idanunshi yayi bayan ya gama bama kanshi amsa, ahankali ya furta “dude focus”

Komawa yayi ya kwanta da kyar mararshi na dan murda mashi yana jin haushin abun sosai, da zarar ya rufe idanu moments dinsu na dawo mashi, kokari yake yi sosai don ganin bai saka kanshi zancen da tunanin ba saidai ya kasa hakan, baya son yanda zuciyarshi ke ingiza shi don yayi alqawari bazai dake neman ta ba, ko last da ya nemeta yayi regretting hakan sbd ganin wahalar datasha da dinki da yaji anyi mata sai yayi tunanin saboda kananun shekarun ta ne, kwata kwata bai kawo daga shi bane, don shi cikakken namiji ne mai ji da lafiyar buqata.

Bangaren amra tayi mamakin kanta sosai da yanda ta fuskanceshi, daman zata iya, koda ta shiga toilet din gabanta bai daina bugu ba sosai, don ta dauka hakan da tayi zata jama kanta, Sai jin fucewar shi datayi don haka ta dauko damarar yin abunda yafi haka Ma tunda kiri kiri ya hanata tafiya saboda wani. Dalili nashi chan daban wanda bata gane ba.

Tun ranar da yazo bata sake sakashi idanunta ba, yanxu ta fara sakewa sosai tana saukowa kasa kullum, Har compound din gidan haka zata fito ta dan zagaye, kafin ta koma ciki, cikin kwanakin ta gano ba a gidan yake kwana ba hakan ya bata damar dagewa akan plans dinta, futowar da take yi ma tana monitoring securities din ne.

Saida ya shafe sati guda bai zo gidan ba, Duk kwanakin da suka wuce a lissafe suke akanshi, ranar saturday da daddare ya shigo anguwan, Yana parking ya wuce ciki ba tare da tunanin komai, lokacin daya shigo suna zaune ita da

Nadine a parlor suna kallon wani series dake, idanunshi ne suka sauka akanta ta maqure gefe, fuskanta yayi fayau harta dan rame, basu Lura dashi ba don haka ya danyi Gyaran murya tare da tura hannunshi cikin aljihun wandonshi ya kalli inda suke zaune, juyowa sukayi suka kalleshi da sauri ta dauke idanunta gefe, sarai ya ga abunda tayi da sauri Nadine ta mike tsaye chan gefe tace “welcome sir, good evening”

Bai kalleta ba idanunshi kan amra yana karantarta yace “evening”

Sun sum Nadine ta wuce daki domin basu space.

Tana ganin nadine ta fuce ta danyi shuru still bata kalleshi ba idanunta a gefe tace “Ina wuni”

“Kinga dama kenan?,”

Ya karashe yana zama kan 3seater ya daura kafa daya kan daya.

Haushi ne ya turniketa, zaman Ma Duk ya gudureta, kallon tv takeyi saidai bata gane abunda ake cewa kwata kwata, sun dauki

17 / 94