kari gashi babu.
Cikin minti biyu sai gashi ya shugo cikin sitting room security’s na biye dashi da da ledoji, anan parlor ya basu umarnin ajiyewa, nan suka jera komai anan parlor, ammah ne ta fara saukowa kasan bayan ta ajiye wayarshi don tabbatarda ko ya dawo, kallon ledojin da ake ta shugowa dasu tayi kafin ta maida kallonta kan Amar, karasa takowa tayi parlorn ta tsaya daga nesa ta kalleshi “Muhammad wannan fah?
Kanshi a kasa ya amsata “abubuwan ne”
Sakin baki ammah tayi tana kallonshi tana kallon ledojin, “yanxu son Ina zata shanye wannan abun duka?”
Sunkuyar da kanshi ya sake yi yama rasa mai zaice “daman na sayo da yawa ne saboda bansan ya ake amfani dasu ba, and I thought maybe zata buqata nan gaba”
“Fruits ne fah? Zasu iya lalacewa yanxu ina zamu kai wannan”
Yar tsuka kawai ammah tayi ta soma bude ledojin, saida ta bude duka tace “ya banga dataa ba?”
“Ammah Wallahi babu na duba ban samu ba”
Ya fada ranshi a hade kamar an sashi dole, dukda kanshi na kasa, “Ay kuwa saika nemo shi Wallahi, kaje wannan dinma yayi”
Tana kaiwa nan ta deba ko wanne guda biyar ta wuce dashi kitchen, nan ta zuba su cikin sink ta wanke mata su tass kafin ta yanka mata yanda zataji dadin sha, yana nan tsaye ammah ta fito hannunta rike da tray harta wuce sama batabi ta kanshi ba, shiko binta yayi da idanu yana mamakin abubuwan da suke wanzuwa.
Kasa daga kafafunshi yayi har saida ta bace mashi daga gani kafun ya dan cije lebe nshi ya wuce bedroom dinshi don watsa ruwa.
Ammah na hawa sama dakinta ta wuce direct inda ta tadda amra harta koma wani barcin wahalar, cikin tausayinta ammah ta kalleta, ciki, haihuwa,goyo , ba abu bane mai sauqi ko kadan shiyasa take tausayinta sosai, Nunfasawa tayi kafin ta karaso bakin gadon ta ajiye mata tray sun kan gado, anatse ta soma tashinta “daughter daughter”
Bude jajayen idanu ta tayi da suka koma ciki sosai, ramar datayi ta futo sosai a fuskanta, “sorry dear gashi an kawo maki” ammah ta fada cikin lallami
Ahankali ta soma gyara kwanciyar ta mike tana cije lebe, “sannu dear it’s not easy, allah ya raba lafiya” kasa dagowa amra tayi kanta a kasa, turo mata tray din ammah tayi gabanta “gashi nan an kawo daughter”
Cikin sauri ta dago idanunta ta sauke su akan tray din, da sauri takai hannu ta dauki agwaluma hannunta Har yana karkarwa takai Bakinta ta soma sha, har wani lumshe idanu take yi na samun abun da take so, she has been craving for it sosai, saida ta shanye kusna uku kafin ta ajiye ta dauka kwakwa, guda daya kawia taci ta ajiye ta janyo yalo, haka ta dunga ci hannu baka hannu kwarya, saida tasha da yawa ta ture, “ya isheki daughter?” Ammah ta tambayeta, “eh, Nagode ammah”
“Alhamdulillah bari na ajiye maki, Akwai wani abun da kikeso again?” Girgiza mata kai kawia amra tayi tana lumshe idanu saboda barcin da bai gama sakinta ba , ammah na Ganin haka tace “shikenan dear kwanta abinki”
Kwanciya amra tayi ammah ta janyo mata duvet kafin ta fuce da sauran zuwa kasa, tana sauka salima na dawowa daga school agajiye, tundaga bakin stair ammah tace “yarinyar kirki Har an dawo”
Hammar gajiya salima tayi ta kalleta tace “barka da rana ammah na, Wallahi yau nasha wahala,maths mukayi and it’s so hard but Alhamdulillah”
Karasowa inda take tsaye ammah tayi tace “sannu dear, Allah ya taimaka, kije kiyi wanka saiki sauko ki diba abunci”
“Tohm ammah na, yau adda ta barki da aiki ke kadai ko? Ni na kasa gane wani irin barci ne wannan takeyi kullum”
Murmushi kawai ammah tayi kafin ta juya zuwa kitchen da tray din hannunta “yarinyar kirki basai surutu ba, Ina ruwan Ki da barcin ta”
Tabe baki salima tayi cikin shagwaba tabi bayan ammah tace “Toh Ay ammah barcin ne ya wuce normal barci wannan, Allah ya kamata take asibiti a duba ta”
Ajiye tray din ammah tayi a gefen kitchen island kafin ta maida duba ta ga salima “Toh naji, kije ki wanka saiki sauko kici abunci”
“Tohm ammah,”
Juyawa salima tayi ta fuce daga kitchen din.
Amra bata Tashi ba sai wajen karfe biyar na yamma, tana mikewa zaune ammah ta shugo dakin, gefen inda yake zaune ta zauna tana kallon ta fuskanta dauke fa murmushi “daughter kin Tashi? Ya jikin? Daman yanxu nake shirin zuwa na tasheki kiyi sallah”
Muryanta a kasa tace “Alhamdulillah da sauqi ammah, bari naje daki”
Miqew amra tayi ta fuce daga dakin, tana fitowa taci karo da amar, bata ma dago ta kalleshi ba kanta a kasa ta wuce daki don wani jiri jiri take ji, shiko saida ya tsaya ya kare mata kallo, fuskanshi tam babu fara’ a,harta shige daki bai daina kallonta ba yana waya tunani.
Yar tsuka yayi kafin ya wuce dakin ammah.
Yana shiga ya same ta a zaune, hira suka danyi inda ta tambayeshi maganar Gyaran gidan nan ya nuna mata abubuwan daya sauya na gidan, ba karamin dadi ya gani a tattare da ita ba lokacin da yake nuna mata abubuwan, “Allah yayi albarka son, gida yayi kyau sosai, Allah ya saka da alkairi”
Da mamaki ya dago yana kallonta jin yanda take zabga mashi godiya sosai,baice komai ba sai sauke kanshi da yayi kasa.
“Asad zaizo anjima, bai samu zuwa dubiya ba kwanaki saboda ayyukan da mukeyi tare”
Kallonshi ammah tayi fuskanta dauke da murmushi don batayi tunanin suna zumunci sosai ba kamar yanda iyayensu sukayi, “Masha Allah asad dan gidan Alhaji abdallah abokin marigayi?”
Girgiza mata kai amar yayi yace “uhm shi”
“Ahh to Masha Allah, Allah ya kaimu”
“Ameen” ya amsa kai tsaye
Kallon agogon dake maqale a bango ammah tayi kafin ta miqe “Bari na dubo daughter ko zata buqaci wani abun”
Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin ta barci a zaune sakeke.
Ammah na futa daga bedroom dinta dakin amra ta wuce, a zaune ta taddata ta hada kai da gwiwa, saurin karasowa inda take zaune kan sallayan ammah tayi kafin Tayi saurin miqa da ita “daughter Yadai? Ko zamuje asibiti? Akwai abund ake damunki?”
Ammah ta jero mata tambayoyin, fuskanta dauke da damuwa don saida ta dagata taga yanda idanun ta yayi jaa sosai alamun kukan da tayi, hankali atashe
ammah ta riko hannunta ta zaunar da ita bakin gadon tace “muje asibiti ne dear?”
Kanta a kasa ta kasa dagowa ta kalli ammah,”ah ah basai munje ba kaina ne ke dan ciwo”
“Subhanallah Allah ya sawaqe, now tell me me kikeso kici ko akawo su agwaluman ne?”
“Wainar fulawa” amra ta fada anatse jiki a mace, kanta a kasa
“Tohm Bari ayi maki,Kinsha magani kuwa?”
“Ah ah ban sha ba ammah, amai yake saka ni” amra ta amsata
“Daughter haka zakiyi hakuri kina sha saboda ki samu kuzari keda babyn okay?”
“Tohm” amra ta amsata kanta a kasa.
Mikewa ammah tayi ta fuce daga dakin ta sauka kasa, nan ta tarar da salima tana diban abunci a kitchen, kallonta ammah tayi tace “Har an sauko ni kam Ina Salim ne?”
“ yana chan yana game,Ay Wallahi Saina fada ma ya Muhammad ya kwace game din ammah,” dariya ammah tayi tana kokarin diban flour tace “ki kyaleshi ya huta, anyi hutu ay”
Kallonta salima tayi Ganin tana kwaba kulli “Ammah ne zakiyi? Kawo nayi maki”
“No dear kici abunci, kafun ki gama ma na soya mata daughter ke son cin wainan flour” ammah ta fada
Ajiye abuncin salima tayi tace “Toh fa yanxu kuma har wahalar dake takeyi ammah, hmm nidai Wallahi ammah Kin fison adda Wallahi,”
Dariya ammah tayi ta kalleta “inason ku duka kowa da irin son da nake mashi, kinga bata jin dadi shiyasa dole na tausaya mata”
Turo baki salima tayi ta karbi kulli tace “ shikenan Ay, kawo nayi Wallahi bazan iya tsayawa ina Ganin kina aiki ba, daman bana jin wani yunwa sosai, kawo nayi”
Karba salima tayi ta karasa hada komai kafin ta fara so yawa ammah na tsaye harta gama soyawa tass daman bashi da wani yawa don baifi guda uku ba, tana gamawa ta zuba akan plate tace “bari na kai mata”
Tana kaiwa nan ta fuce ta wuce sama zuwa dakin amra.
Da sallama salima ta shiga dakin, ahanakli amra dake jingine bakin gado, har lokacin towle ne a jikinta ta amsa mata sallaman da tayi.
Karasowa cikin dakin salima tayi hannunta duake da plate din wainar, zama tayi gefen amra kafin ta ajiye plate din a gefenta “barka da yamma addah ya jiki? Ammah tace bakya jin dadi”
Dan dagowa mara tayi kafun ta kauda kanta gefe jin turaren dake Tashi daga jikinta na danunta tace “Alhamdulillah!!, kije bana son wannan scent din”
Da mamaki salima ta mike tsaye tana kallonta tana wani nazari, dukda tana da kananun shekaru hakan baisa ta Lura da changes a tattare da yar uwar Tata ba “kije banson scent dinki pleas”
Da sauri salima ta mike ta fuce daga dakin, tana futa ta mike ta wuce bathroom a guje tana kelayar da amai m, saida ta fidda komai kafin ta dawo agalabaice, kallon wainar tayi, ranta naso saidai tana tsoron amai, haka nan ta janyo plate din ta tsakuri kadan ta kai bakinta, haka ta dunga tsakura tana ci tana tsoron amai harta ci guda daya kafin ta ture plate din ta kwanta kafin a kira Sallar magrib.
Tunda ta kwanta take juye juye don ta hana kanta yin barcin.
Salima na fitowa ta sauko kasa zuwa kitchen lokcakin ammah ta wuce bedroom dinta, abuncin data ajiye ta dauka kafin ta koma sitting room ta kunna tv ta fara kallo.
Tana nan zaune Har aka kira sallan magrib tana kallo saboda she’s off bata sallah.
Kitchen ta mike ta wuce ta Dora simple dinner, stir fry noodles, saida ta gama ta jera akan dining kafin ta dawo parlor ta cigaba da kallonta
Ahankali yake takowa bayan ya hangota daga nesa don daga masjid yake, a bayanta ya ya tsaya ya sauke kanshi saurin kunnenta daga bayan kujeran murya shi chan kasa ya soma magana “my beautiful wifey to be”
Da mamaki salima ta juyo don ta tsorata kafun ta dan turo baki “haba yaya Ka bani tsoro”
Zagayowa yayi ya zauna gefenta “ sorry baby kinyi sallah?”
Sunkuyar da kanta kasa tayi ta kasa cewa komai “uhm I guess mun tafi off kenan,”
Saurin rufe fuskanta tayi tana jin kunya, hira suka shiga yi ta masoya anan zaune.
Ammah ne ta sauko fuskanta dauke da murmushi ta kallesu “son abarmin yarinya haka Kar a cikata da surutun karya na sama din zamani”
Dariya ya danyi yace “barka da dare ammah”
“Barka my dear,” karasowa parlor tayi ta zauna, nan suka shiga hira gaba dayansu anan zaune.
Karfe takwas daidai saiga Amar ya shugo shida asad don, da sallama suka shugo atare, har zuwa parlor, su ammah dake zaune ne suka amsa sallamansu, kallonsu ammah tayi fuskanta dauke da murmushi tace “lale maraba yau PA alhaji ne a gidan namu”
Saurin sunkuyar da kai asad yayi don baiyi tunanin zata tuna da sunan ba saboda sunan ne dada ke kiranshi dashi Duk sanda suka zo gidan..
Karasowa sukayi, Har kasa asad ya tsugunna ya gaisheta, da fara’a ta amsashi tana tambayar mutanen gida da hajiyarsa.
Amar na daga zaune ya hakimce ya Dora kafa daya kan daya, salima ce Tayi saurin dukawa ta gaisheda da asad, kallonta tayi fuskanshi duake da murmushi ya amsa, maida kallonta tayi ga amar shima ta gaishesa, fuskannan Tashi a hade ya amsa ta.
“Kunzo a daidai, bari a kawo dinner”
Da sauri asad yace “Wallahi hajiya akan hanya nake, daman ayyuka ne sukayi min yawa shiyasa ban samu nazo ba”
“Ahh Toh ko dan lemo Ay Ka tsaya kasha” ammah ta fada tana murmushi kafin ta maida kallonta ga salima, “yarinyar kirki a kawo ma baqo juice ko”
Mikewa salima tayi ta fuce daga parlor asad ya bita da kallo wanda Aman ya ga hakan, take ranshi yadan sosu saidai bai nuna ba harta dawo da tray a hannunta, serving dinshi ta fara yi kafin ta miqa mashi.
Godiya ya mata in a calming tone kafin ya karba yana mata wani irin kallo mai wuyar fasaara da alamu dai asad ya kamu.
Saida ya gama sha yace “Alhamdulillah Zan wuce hajiya Allah ya Kara lafiya”
“Tun yanzu PA? Baka tsaya Kun gaisa da matan abokin naka bama bari a kirata”
Da mamaki asad ya kalli Amar daya hade rai yana latsa waya Har lokacin baice qala ba,
Kallon salima ammah tayi tace “Kira min daughter”
Mikewa tayi asad ya sake binta da kallo harta wuce sama, tana zuwa ga taddata zaune kan sallaya ta idar da sallar isha’I, daga nesa salima ta tsaya ta soma magana “adda kizo inji ammah”
“Okay” amra ta fada jiki a mace, saida ta dauka kusan minti biyu kafin ta mike tabi bayanta don harta fuce.
Anatse ta futo sanye take da dogon hijab har kasa don towel ne kawai a jikinta, gaba daya dagowa sukayi suna kallonta harta sauko Banda amar da asad, tana karasowa ta gamsu zazzaune, “ammah gani”
Ta fada muryanta a kasa don bata tsaya ta tantance su waye a parlorn ba,
Dagowa asad yayi ya kalleta, kasa dauke idanunshi yayi akanta, yana tunanin inda ya santa, aranshi babu abunda yake furtawa sai “waiii perfect match”
Ammah ce ta danyi Gyaran murya “daughter ga abokin mijinki,”
Dagowa ta danyi suka hada ido kafin ta sauke “Ina wuni”
“La..fi..ya..” ya amsa ararrbe
Saurin dagowa amar yayi don haka kawai yaji yana son ya dago, kallon Ind a take tsaye yayi kafin ya maida kallonshi ga asad, Ganin yanda ya kureta da idanu yasa yaji wani irin abu ya tsaya mashi a maqoshi sa
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 144
Update
Unedited
Ammah ne ta dago ta kalleta Ganin ta takure waje daya “daughter jeki huta”
“Tohm ammah” ta fada a tsanake, kallon inda asad yake tayi tace “saida safe mun gode da ziyara “
“Ba komai nike da godiya” ya amsa ta Har lokaci idanunshi na kanta, Amar dai kasa dauke idanunshi yayi akanta, haka kawai yaji bayason ganinta tsaye a wajen saboda yanda Asad ke kallonta,ya kasa dauke idanunshi har ta wuce sama.
Tana hawa sama ya sauke wata ijiyar zuciya dayasa Ammah dake gefen shi ta kalleshi, murmushi kawai tayi ta kauda kanta gefe.
Mikewa asad yayi ya ajiye bundle din naira note guda biyu a kan kujeran daya tashi kafin ya kalli inda salima ke zaune yace “kanwata thanks for the drink,ga wannan ba yawa a saya eyeshadow”
Ya karashe yana mata murmushi, kallonshi tayi itama fuskanta dauke da murmushi tace “thank you uncle”
Sallama yayi ma ammah, kafin ya kalli inda Aman yake ya miqa mashi hannu, Amar na Ganin haka ya miqe tsaye suka fuce atare, Har gaban motarshi ya rakoshi, suna karasowa asad ya miqa mashi hannu yana murmushi “congratulations oga, ashe itace madam”
Dan murmushin da bai kai zuci ba yayi tare da saurin basarwa cewa “thanks for the visit, Allah ya bar zumunci”
“Ameen oga” yana kaiwa nan ya mashi sallama ya shige motarshi.
Bayan fitarsu salima ta miqe ta kwashe juice da cups din da baqon yasha ta wuce kitchen dashi, tana wucewa Aman ya miqe ya bi bayanta.
A tsaye ya taddata tana kokarin wanke cup din, tana gama wa ta juyo “wayyo Allah na” ya fada da dan karfi saboda bataji shugowanshi ba kwata kwata, “ka bani tsoro yaya”
Hannunshi ya nade a kirjinshi ya matso kusa da ita “meysa kike ma wanchan gardin murmushi?, bakisan murmushinki nawa ne ba ni kadai?”
Da mamaki take kallonshi kafin ta kufce da dariya Ganin yanda yayi kicin kicin da fuska “yaya are you jealous?”
“Yea I am” ya bata amsa kai tsaye, tuntsirewa tayi da dariya kafin ta dan matso daf dashi fuskanta dauke da murmushi Har wani blushing takeyi, “ka kwnatar
da hankalinka my yaya, babu wanda zai chanza gurbin da kake dashi a zuciyata”
Hade rai ya danyi kafun ya kauda kanshi irin bai yarda dinnan ba tana Ganin haka ta dan shgwabe “yaya Wallahi da gaske nake , bakisan yanda nake jinka araina ba”
Dan murmusawa yayi kafin ya kalli cikin idanunta in a naughty way yace “zaki aure ni?”
Sunkuyar da kanta kasa tana mai rufe fuskanta cikin sassarfa ta gifta ta gefenshi Har takai bakin kofa tadan juyo “ yes honey”
Da sauri ya juyo ya kalleta harta fuce daga kitchen din aguje tana dariya.
Wani irin dadi ne ya ziyarceshi, soyayyar da yake mata ta dabance a cikin zuciyarsa.
Amar na shugowa gidan ya wuce bedroom dinshi, har lokacin yana jin wani irin zafin yanda asad yake kallonta, haka kawai yaji bayason ana kallonta kwata kwata, haka ya dunga zarya a cikin dakinshi ya rasa abunda ke damunshi, zuciyarci cushe take da bacin rai mara dalili, babu abunda yake sai tsuka, he can’t believe yanda yake behaving when it comes to her wanda ada kwata kwata baitaba tunanin zaiyi hakan ba akan wata mace ba.
Haka ya kwana cikin bacin rai, hade da tunaninta aranshi wanda ya kasa hana kanshi yin hakan.
Ita kuwa bayan ta hau sama hijab din jikinta kawai ta cire ta wuce bathroom jiki a mace tayi wanka ta sauyo wani towel din ta futo ta kwanta abunta.
After one week….
Yau sati guda kenan rabon shi da ganinta, tun bayan zuwan da asad yayi ta sauko kasan bai sake ganinta ba dukda baya wuni a gidan, yana tashi yake fucewa sai kuma yamma zai dawo.
Bangaren amra, itama dai rabonta dashi tun lokacin, bayan wannan ma yanxu bata wani damu da al’amarin shi ba, kamar yanda ammah ta fada mata akan tayi focusing akan lafiyarta da babyn dake cikinta kawai, har lokacin kuwa batayi gigin fada mashi komai
ba kwata kwata.