dago ya miqe tsaye don wani irin kuzari ne yazo mashi lokaci guda ya bude baki ya kasa cewa komai, babu abunda yake fada a zuciyarshi sai hamdala, baima tsaya ya saurari bayanin da suke shirin yi mashi ba ya juya ya fuce zuwa dakin da aka kwantar da ammah, suma bin bayanshi sukayi harda amra gaba daya zuwa inda aka kwantar da ammah, har lokacin ba a ganinta don tana kwance an kafa mata na’urar dake supporting heart dinta don ya dunga beating on a normal rate, tunda ya kaarso wajen bakin kofar ya kafa mata idanu, he cant believe idanunshi, ammah is alive bata mutu ba, doctors na karasow da amra ya juyo ya kallesu, ran shi adan bace yace ‘’wani irin useless facilities kuke dashi ko ince wani irin aiki kukeyi da bakwa tantance idan mutun yam utu ko be mutu ba, im going to sue duka ma’aikatan asibitin nan’’ ya karashe a fadace
Kallonshi wani magidancin doctor yayi kafin ya soma Magana cikin kamewa ‘’we’re very sorry sir, mutuwa bata zuwa sai lokacin mutun yayi, sai dai wannan zamuce it’s a miracle,ko zamuje office sai muyi maka bayanin komai’’
Tamke fuska yayi sosai, ganin girman mutumin yasa yace ‘’no need for that, I just need explanation’’
Gyara tsayuwa doctor yayi don daman shine yake Magana don dayan ya kasa cewa komai don shine ya fada masu ay ta rasu lokacin da zuciyarta da nunfashin ta ya tsaya
‘’theres a condition whereby someones heart stops and then it starts again which is called heart palpitation, idan har mutun ya wuce 10mins babu heart response after cpr anan ne muke declaring time of death, abunda ya faru da hajiya Kenan muna kiranshi da lazarus syndrome wanda hakan yasa mukayi declaring time of death don nunfashinta ya tsaya tare da zuciyarta lokaci guda’’
Ba tare da ya kallesu ba idanunshi nakan ammah yace ‘’whats her condition now? Is she stable’’
Doctor ne ya gyara tsayuwanshi ya kalli amar yace ‘’yes shes stable hajiya is very brave, she’s a fighter, alhamdullahi, shes out of coma, zata iya tashi anytime, muna rokon allah ya bata lafiya ‘’
Amra ce kawai ta amsa da ameen kafin suyi masu sallama su
Takowa amra tayi har gabanshi, farin ciki y agama lulubeta bata ma san lokacin data rungumoshi ta bay aba tana hawayen farin ciki, tunda ta frungumeshi yayi shuru ya kasa motsawa, don he needed it sosai, ta zaman mashi kamar wani source of confort, sun dade sosai a tsaye suna kallon ammah babu wanda yace qala tsakaninsu, kiran sallar asuba ne ya fargar dasu su duka, kallonta amar yayi yace ‘’kije kiyi sallah, zanje masallaci aynxu’’
Kallonshi tayi itama kafin ta sauke kanta kasa tace ‘’ah ah yaya, kaje ka fara yi, zan tsaya anan idan ka idar sainaje nayi nima’’
Saurin runtse idanunshi yayi muryanshi baya futa sosai don harta dishe yace ‘’okay, wait for me here karkije ko’ina’’
Bata kalleshi ba kanta akasa tana gyara mayafinta dake neman sulalowa kasa ‘’tohm yaya saika dawo’’
Wuceta yayi ya fita daga emergrncy ward, yana fucewa ta samu waje anan ta zauna emergency ward din wajen waiting, minti kadan zata miqe ta leka wajen ammah kafin ta koma ta zauna, idanunta har wani rurufewa suke yi tsabar kasalar data dabaibayeta,
Mikewa ta sakeyi ta leka dakin, ta dan dade a tsaye jiri na neman dibanta, ahankali ta sake takowa ta koma ta zauna tana sauke nauyayyan ijiyar zuciya, tundaga nesa amar ya hangota da yanda take tafiya, ba karamin tausayi ta bashi ba, he never thought haka take, bait aba tsammanin haka take da jajircewa da dauriya ba, kana ganinta kasan shes not okay, but she’s acting as if she is, dan tsayawa yayi yana kallonta yana nazarin abunda ya faru daga cikin daren.
Daga kafarshi yayi ya tako har inda take ya tsaya ya kalleta ganin yanda ta lafe jikin kujerar fuskanta tayi paling, bakinta duk ya bushe idanunta a lumshe.
‘’aishaaa!!’’
Bude idanunta tayi ahankali ta sauke akanshi, bakinta na karkarwa tace ‘’ya..yaa.. har ka dawo’’
‘’jekiyi sallah’’ ya fada ahankali yana zama gefen kujerar fuskanshi na nan yanda yake babu yabo ba fallasa
Mikewa ta soma yi kafarta ta rike kafin ta sulale ta zauna, kallonta yayi cikin tausayin yanayinta adan kausashe yace ‘’whats wrong?’’ ya fada yana lumshe idanu, hawaye ne ya soma zuba a fuskanta ‘’yaya im weak’’
Ta fada ahankali kamar bakinta bazai furta ba, ganin haka yasa shi mikewa ya sungumeta gaba dayanta ya daga ya wuce dakin da aka kwantar dashi, da hannu daya ya bude kofar ya shige dakin da ita, bai tsaya ko’ina ba sai bathroom ya sauketa ba tareda ya kalleta ba yace ‘’kiyi alwala, zan tsaya idan kin gama just call me’’
‘’no yaya ka koma wajen ammah, zan iya’’ amra ta fada tana wasa da yastunta
‘’bana son gardama, just do as I say’’ ya fada akausashe kamar bashi ke Magana calmly ba daxun.
Yana kaiwa nan ya futa ya rufe mata bathroom din, bin bayanshi tayi da idanu har ya rufo kofar, ta dade a zaune abubuwa da dama suna yawo a qwaqwalwarta kafin ta fara gyara jikinta jiki a mace.
Shima yana futa ya dan tsaya nesa da bathroom din, yana son futa yaje ya duba ammah saidai yana tunanin maybe idan ya futa kafin ya dawo zata buqace shi, juyawa kawai yayi ya fuce daga dakin zuwa emergency ward, yana zuwa yadan tsaya wajen ammah ganin da nurse a gefenta yasa ya juya zuwa dakin da yabar amra, yana shiga tana kokarin fitowa tana tangadi ruwa na diga daga fuskanta, tana hangoshi tadan daidata natsuwarta.
Takowa ya soma yi cikin kamewa ya karaso inda take fuskanshi adan murtuke yace ‘’youre so stubborn’’ yana kaiwa nan ya sungumeta gaba daya ya dorata kan gadon marasa lafiya yace ‘’zansa a aiko da abunci yanxu, idan kin idar kici abunci ki kwanta bana son gardama’’
Yana kaiwa nan ya juya yana shirin futa tayi saurin tsaidashi tace
‘’yaya kaifa? Bakaci komai ba fa’’
Dan tsayawa yayi bai juyo bay ace ‘’I’m okay’’
‘’toh yaya ka huta ni zan tsaya wajen ammah’’ amra ta fada in a concerning way
Sai alokacin ya juyo ya kalleta adan harzuke yace ‘’bana son gardama, nace maki ki kwanta ki huta kici abunci why are you being stubborn, do you want to fall sick ne? just do as I say’’
‘’tohm yaya’’ ta fada ashagwabe tana sunkuyar da kanta kasa harya fuce daga dakin.
Yana fucewa ta gyara mayafin abayrta ta fuskanshi qibla ta tada sallah anan zaune saboda jirin datake ji, tana idarwa ta fara azkar tana yima ammah addua sosai har chef ya shigo da tray a hannu na abunci daga kitchen, gaisheta ya fara
yi kafin ya janyo mata table din da ake ajema marasa lafiya abunci, yana aje wa ya juya ya fuce daga dakin, yana futa ta daidata zamanta ta janyo table din inda take zaune ta soma bude food cover din, chips ne da egg sauce sai custard a gefe cikin wani bowl an zuba madara sosai a ciki, kallon abuncin tayi tana tunanin shi, shi baici komai ba tun bayan breakfast din safe wanda lantana ta katse masu, batajin zata iya cin abuncinnan tunda shi ma baici ba, saidai tunawa da maganrshi yasa hakanan ta soma cin abunci ba don tana soba, baifi spoon biyar tayi ba ta ture gefe ta koma bakin gado ta lafe, har barci ya soma fusgarta dukda tana kokarin hana kanta yin baccin,
Tun bayan futarshi daga dakin amra ya koma wajen ammah, nan ya tadda nurses na kokarin futowa da ita daga ward din zuwa dakin marasa lafiya, cikin sauri ya kaarso inda suke, likita ne daya biyo bayansu yana ganinshi yace ‘’good morning sir’’
‘’morning’’ ya amsa mashi ataqaice
‘’sir zamuyi shifting dinta zuwa ga recovery room, alhamdullah jikinta yana recovering sosai’. Doctor ya fada yana mika mashi mashi hannu
‘’thank you so much’’ amar ya fada fuskanshi na nan yanda take saidai kana ganinshi kasan yana cikin farin cikin wannan news din.
Atare suka wuce dakin da aka kwantar da ammah tare da doctor din, sai alokacin ya samu damar zuwa har gaban ammah ya rike hannunta yana jin kaunarta da tausayinta na yawo a jinin shi, sallama doctor yayi mashi ya fuce daga dakin while nurse ta tsaya tana gyara mata drip din jinin da ake kara mata.
Nurse na futa ya zauna gefen ammah ya soma ya zuba mata idanu,addu’a ya soma yi mata akanta na neman lafiya da kariya daga duk wani sharri, ya dade sosai yana mata addua kafin ya ruko hannunta ya soma Magana kamar tana jinshi ‘’ammah na, allah ya baki lafiya ya tashi kafadunki, im so sorry for not protecting you,’’
Hannunta ya dago yayi kissing tana mai jin tausayinta da kaunarta da tausayinta, tunanin halin daya shiga daxu yayi lokacin da doctor yace mashi zuciyanta ya tsaya ta daina nunfashi, ya shiga mummunan tashin hankali sosai, tashin hankalin da bai taba tunanin zai shiga ba. Shuru ya danyi yana nazari gaba daya rayuwarshi baitaba tsintar kanshi a wannan yanayin ba sai yanxu, tsoro da fargaba da baitaba jiba arana irin ta yau yaji, ada chan baya yana ganin babu abunda zai furgitashi koya bashi tsoro anan duniya ko yayi breaking heart dinshi, saidai yau halin da ammah ta shiga yasa ya gane cewa itace weak point dinshi wanda bai sani ba, fadin irin tsoron dayaji daga wunin jiya zuwa safiyar yau ma bata lokaci ne,donma shi jarumine kuma yana da jarumta sosai.
Ya dauka kusan awa guda yana zaune wajen ammah kafin ya mike ya wuce wajen amra, ahankali yake tafiya harya shiga dakin nata, yana shiga dakin tun bai gama rufe kofar ba idanunshi ya sauka akanta, tana rakkube bakin gado tana barcin wahala, rufe kofar yayi ahankali ya karso bakin gadon ya zuba mata idanu, knocking kofar dakin akayi kafin a shugo, su salima ne da aman sai
salim, gaba dayansu sunyi zuru zuru don daga wajen emergrncy ward suke inda aka kwantar da ammah, ganin bata wajen yasa hankalin su ya tashi sosai suka taho dakin, da sallama suka shugo suka zuba mashi idanu, takowa aman yayi su salima suna biye dashi, ‘’ina kwana yaya’’
Juyowa yayi ya kalli salima dake gaishesa ita da salim yace ‘’lafiya’’ ataqaice, aman ne yayi jarumtar tambayarshi jikin ammah, nan amar ya shaida masu an fiddata daga emergrncy ward an maidata recovery room, hamdala sukayi gaba dayansu, nan amra ta bude idanunta ganin su a tsaye, don barcin mai nisa ne ya dauketa bata maji shugowansu bag aba daya, ganin su chirko chirko tayi saurin mikewa tsaye ta kalli amar tace ‘’yaya jikin nata ne?’’
Maido da idanunshi yayi kanta yace ‘’no shes fine’’
Sauke nauyayyaiyar ajiyar zuciya tayi don sai alokacin ta lura dasu salima atsaye, gyara mayafinta tayi tace ‘’ina kwana yaya’’
‘’lafiya alhamdulillah ya jikin ki’’ aman ya tambayeta yana kallon gefe
‘’alhamdullah naji sauqi’’
Salim ne ya matso kusa da ita tare da salima duk idanunsu yayi jaa sosai alamun basuyi barci ba kwata kwata, salima ce ta dan rungumet tace ‘’adda ya jikin ki’’
‘’da sauqi’’
Juyawa amar yayi yace ‘’muje’’
Bin bayanshi duk sukayi zuwa dakin da aka kwantar da ammah, suna zuwa dakin amar ya bude duk suka shiga gaba daya, karasawa sukayi gaba dayan su suka tsagaye ta, kwance take kamar yanda suka barta saidai ta rame sosai jikin wuni guda, ta sauya kamar ba ammah ba saboda yanda taji jiki sosai, salima ne ta riko hannun ammah ta soma yi mata addua, tana gamawa aman ya kalli amar yace ‘’yu should go and freshen, mu zamu zauna’’
Amra ce ta dago tace ‘’no zan zauna yaya yaje ya huta bai samu yaci komai ba kuma bai samu runtsawa ba’’
Kallonta salima tayi tace ‘’adda kema kije ki dan huta saiku dawo tare mu zamu zauna da ammah’’
‘’please call me if idan wani abun ya taso’’ amar ya fada yana fuskantar aman, girgiza mashi kai aman yayi alamun gamsuwa.
Kallon amar amra tayi shima ita yake kallo kafin ya kauda kanshi gefe, miqa mashi keys din mota aman yayi, karba yayi ya fuce amra tabi bayanshi, ahankali take tafiya har suka zo wajen motar, budewa yayi ya shige itama ta bude ta shiga gaba yaja motar suka bar harabar asibitin.
Tunda suka shiga cikin motar babu wanda yace da wani kala, hannunshi nakan steery, gaba daya hankalinshi yayi nisa dukda tuki yake yi hakan baisa tunaninshi ya rabu gida biyu ba, dan waigowa yayi ya kalleta ganin yanda ta kafa ma window idanu jikin ta duk yayi la’asar babu kuzari, ‘’how are you feeling now?’’
Juyowa tayi ta kalleshi tace ‘’naji sauqi’’
Maida hankalinshi yayi kan titi ya cigaba da cewa ‘’baki iya karya ba,’’
Dan waigawa ta sakeyi ta kalleshi alamun bata gane abunda yake nufi ba, bai kalleta ba but yayi sensing kallonshi take, hankalinshi nakan tukin da yakeyi yace ‘’you don’t look okay’’
Sauke kanta tayi kasa, muryanta a kasa tace ‘’yaya kaima you’re not okay, bakaci komai ba, kuma..’’
‘’I’m okay’’ ya katse ta yana kokarin juya akalar motar ya shiga cikin estate.
Securites na bude mashi gate din apartment dinsu ya shige yayi parking motar, yana kashe motar ta bude kofar, shima bude bangareshi yayi ya futo ya rufe motar tabi bayanshi.
Tunda ta shiga gidan gabanta ya fadi dam, gidan ya zama very empty kamar anyi masu mutuwa, part dinshi ya wuce direct ya barta tsaye tana nazari, kamar zata wuce sama ta juya zuwa part dinshi, da sallama ta bude bedroom din nashi, a zaune ta taddashi ya dafe kanshi da hannu biyu don bata hango fuskanshi, takowa tayi dan nesa dashi ta tsaya tace ‘’yaya me zakaci na dafa maka’’
Dan dagowa yayi ya zuba mata rinannun idanunshi da sukayi jaa baice mata komai ba,tana ganin haka ta wuce cikin bathroom dinshi ta tara mashi hotbath kafin ta fito ta kalleshi tace ‘’yaya ka shiga na sa maka ruwa’’
Kanshi a kasa yace ‘’thanks’’
Fucewa tayi ta wuce kitchen ta hada mashi white soup sai coffee, ta dauka kusan thirty minutes kafin ta gama ta shirya komai ta wuce dashi bedroom dinshi, tana shiga ta aje mashi a kan side stool ganin kamar bai fito daga wanka ba kafin ta wuce zuwa nata bathroom din, tana shiga daki ta soma tube kayan jikinta ta wuce bathroom. Wanka tayi ta wanke bakinta kafin ta fito, agurguje ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ko dan kwalin atamfar bata daura ba ta sauko kasa zuwa bedroom dinshi, da sallama ta shige cikin bedroom din, akwace ta taddashi daga shi sai towel yayi rub da ciki, ko abuncin ma bai taba ba da alamu daga wanka ya fito ya kwanta don ko bathroom sleepers bai cire ba, tausayin taji sosai don kana ganinshi kasan barcin wahala yayi, karasowa tayi harinda yake kwance ta tsugunna bakin gadon ta zare mashi bathroom sleapers din, ganin kamar kafarshi zata sage don ba a kan gadon kafafun suke ba, don haka ta soma kokarin gyara mashi ta hanyar daga kafar tashi, yana jin motsinta yayi saurin bude idanunshi ya sauke akanta don barcin bai gama fuzgarshi ba, saurin sakin kafar tashi tayi ‘’daman zan gyara maka ne saboda kar afanka ya sage’’
Lumshe idanunshi yayi ya maidasu ya rufe kafin ya sake bude idanun nashi ya kalleta, miqa mata hannunshi yayi, bin hannun nashi ya soma yi da idanu tana son ta gane abunda yake nufi, ‘’come’’ ya katse mata tunani
Takowa tayi ta rike hannun nashi, baiyi wata wata ba ya fuzgota gaba dayanta zuwa jikinshi ya rungumeta, tunda ta fado jikinshi gabanta na faduwa tayi shuru tana sauraron yanda zuciyarshi ke bugawa ga wani irin zafi da jikinshi ke fiddawa na zazzabi, kankameta yayi gaba daya akan kirjinshi yana sauke nunfashin azaba, sun dauka kusan awa guda ahakan har nunfashinsa ya soma
daidaituwa, dan dago da idanunta tayi ta kalleshi, barcin ne ya sake fuzganshi ganin haka yasa ta soma lallabawa donta zare jikinta daga nashi, motsawan datayi yasa ya bude idanunshi kadan ya murginar da ida kan gado ya zamana yana fuskantar bayanta, gyara kwanciyanshi yayi ya rungumota ta baya ya janyo duvet ya lulluba masu, kasa sakewa amra tayi dukda bata hanashi ba saima lumshe idanu datayi har barci ya fusgeta tana jin saukan nunfashinsa a bayanta, wani irin peaceful barci sukayi na kusan awa uku, shine ya fara farkawa ya bude idanunshi, da mamaki yake kallonta saidaga baya kuma ya tuna, ahankali ya soma zare jikinshi daga nata ya gyara mata duvet din ya wuce bathroom, wanka ya sakeyi kafin ya shige cikin closet ya dauko jallabiyanshi ya zura ya wuce masallaci, harya dawo daga masallaci tana kwance tana barcin ta hankali kwance, kallonta yayi kafin ya kauda kanshi gefe ya maida idanunshi kan abuncin data aje mashi dazu dabai samu yaci ba, yana kokarin zama ta bude idanunta bakinta dauke da adduar tashi daga barci tayi miqa, kallo daya ya mata kafin ya dauke kanshi ‘’lokacin sallah ya wuce,go and pray’’
Saukowa tayi daga kan gadon tana dan jin kunya tace ‘’tohm’’, kokarin fucewa takeyi daga dakin nashi yace ‘’you can use that ‘’ yayi mata nuni da bathroom dinshi, juyawa tayi ta wuce bathroom din nashi tana mamakin yanda ya sauya sosai, shigewa tayi ta dauro alwala, tana fitowa ta taddashi zaune yana latsa wayarshi, abuncin data ajiye mashi a gefe, fucewa tayi daga dakin gaba daya ta wuce sama zuwa nata dakin ta zura hijab tayi sallah, tana idarwa ta mike ta sauko ta wuce dakinshi, a zaune data barshi haka ta taddashi don haka ta karaso gabanshi ‘’yaya do you need anything ko nayi maka warming abuncin?’’
Ba tareda ya dago ya kalleta ba hankalinshi nakan wayarshi ‘’yes’’
Ya amsata kai tsaye, daukan tray din tayi ta fuce tayi mashi warming abuncin kafin ta dawo ta aje mashi a gabanshi.
‘’bismillah’’ ta fada tana kallonshi, dan