Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   14 / 94

39K to 42K   out of 279.4K words

baiyiba. 

Yana nan kwance yayi godiya Ma Allah, kafin ya mike baima tsaya kallon gefenta ba ya wuce toilet, yana tsayawa kan shower ya sauke idanunshi kan manhood dinshi dake tsaye kamar bashi ya gama aiki ba, ganin yanda jini ya bata shi gaba daya kamar wanda yayi yanka yasa gabanshi faduwa, “shin daman haka ake zubda jini da farko ne ya tambayi kanshi don gaba daya ya mata a wani situation ya barta”wanke jinin ya soma yi Ganin Jinin ba daga jikinshi bane ya sashi saurin watsa ruwa ya nado towel ya futo, yanda ya barta haka ya taddata kamar matacciya Har fuskanta yayi sandare,hankali a tashe ya karasa gabanta, kamar ance ya kalli cinyoyinta nan take yaga aika aikar da yayi, gaba daya daga kan blanket din zuwa duvet din Duk ya gama baci da jini,ga wani Jinin Ma na fita daga kasanta, da sauri ya runtse idanunshi “dude what have you done”

Ya fada a cikin zuciyarshi, da sauri yakai kunnenshi daidai zuciyarta jin tana dan bugawa ya sashi sauri mikewa don gaba daya ya gama burkicewa ya rasa mema zaiyi mata don Duk mai tausayi Inya kalleta yasan ta shiga hannun manya, kamar wanda aka tsikara ya nufi inda ya aje wayanshi ya jawo tare da budewa ya shiga goggle yanda zai Taimaka mata, nan base on reserch din da yayi ya gano yayi mata da karfi ne sbd ita virgin ce,wanda yawanci wasu virgins na experiencing irin haka Idan aka yi masu da karfi, saurin aje wayan yayi ya wuce bathroom ya kunna hot water cikin katon bath din toilet din saida ya kusa cikawa kafin ya kashe ya fito ya cicibeta gaba daya kamar gawa ya wuce da ita toilet, da kanshi ya soma shiga ciki bath din tana rike a hannunshi ya zauna tare da ita a jikinshi ya kwantar, ta dauka kusan minti goma kafin

ruwan ya fara ratsa ta, ta bude idanunta da suka kumbura sosai ta sauke akanshi, nan take ta runtse idanunta jin azaba gadan gadan gadan, gata ruwa gata mugun aiki da yayi mata,gaba daya she’s helpless, kukan Ma baya futa kwata kwata ganin haka ya sashi jin wani irin ya runtse idanunshi gam ya rasa mai ze ce mata, sun dauka kusan awa a cikin bath tub kafin ya fiddosu,still tana hannunshi ya riketa kamar yar baby, wucewa da ita gaban shower yayi ya sakar masu ruwan zafin a kansu, gaba daya tunda ta rufe idanunta taqi budesu shiko idanunshi na kanta kyam, tausayi ta na ninkuwa a zuciyarshi, tausayawan da bai taba yima wata ya mace ba a duniya face ammah shi.

Ganin jikinta na bari, bakinta ta na karkarwa idanunta ma da suke a rufe ta soma bude su tana kakkafe su, yasa hankalinshi Tashi sosai ya kashe shower din, ya fiddo su daga shower, harya bude kofar toilet din ya tsaya ya zare towel dinshi da ya jike ya barshi anan ya wuce da ita cikin dakin, tana jikinshi ya karasa gefen gado da basu bata ba ya kwantar da ita ya kafeta da idanu ya rasa abunyi, ganin kamar tana abu kamar wadda take da seizure ya sashi saurin janyo shorts dinshi dake yashe a Kasa ya saka ya matso gabanta ya soma dabbing fuskanta “Aisha!! Aisha keee open your eyes”

Nan take hakoranta suka fara kaf kaf, ganin haka ya sashi janyo wayarshi yayi reserching, da sauri yayi wurgi da wayar ya maida idanunshi kanta, tabbas Idan ya barta a haka zata gatsa harshenta da hakorinta, duban dakin ya soma yi, ganin babu komi a kusa dashi dazai iya saka mata a bakinta ya sashi saurin bude bakinta ya daga hakoran ya saka tafin hannunshi, nan take kuwa ta hade hakoranta kan tafinshi ta kankameshi Har jini na dan fita, dake shi mai karfi ne babu alamun jin zafi kwata kwata a fuskanshi Har kusan minti goma kafin ta sassauta ta dawo daidai, lokacin har an fara kiraye kirayen sallan farko, mikewa yayi da sauri ya bude closet ya fiddo da jallabiyanshi ya zura tare da saurin bin dakin da kallo harya hango rigarta daya yasar a Kasa ya dauko tare da hijab dinta ya wuce gabanta ya tallabo ta ya saka mata rigar a jikinta, gaba a baya Ma ya saka rigar kafin ya zura mata hijab din ya dauki keys dinshi ya cicibeta ya fuce da ita daga dakin.

Yana saukowa kasa ya danna key din motarshi ya bude baya ya kwantar da ita, ya gyra mata mata kwanciyan ya rufe kofar, gaban motar ya wuce cikin sassarfa ya bude ya shige cike tare da kunna motar ya fuce daga gidan.

Tunda ya fuce da mugun speed bai tsaya ba don gari bai gama washe wa ba babu motoci sosai akan titin hakan ya bashi damar tafiya da mugun speed, tunanin asibitin da zai kaita ya soma, bayason ya kaita family hospital da suke zuwa don Duk wani treatment na ammah da sauran Yan gidan su anan akeyi, gashi ba sanin wani asibitin yayi ba, don nan yakai nadine, ganin bashida wani options ya sashi gangarawa gefen titi yayi parking tare da bugun steering yace “ya Allah!!!!”

runtse idanunshi yayi yana mai takaicin abubuwa da yawa ya dauka kusan minti biyar a haka kafin yadan juya ya kalleta, yanda ya ajeta babu abunda ya sauya, wayanshi ya jawo yama rasa wa zai kira, ganin bashida wani option ya sashi juya akalar motar ya nufi hanyar asibitin, cikin Yan mintuna qalilan ya iso yayi parking, agurguje ya fito ya zagaya ya fiddota tare da yimata kyakyawan riko ya wuce da ita asibitin, yana shiga aka karbeta cikin gaggawa sanin waye shi, emergency aka wuce dashi, kafin wani doctor da nurse da suke duty suka soma dubata, tunda suka shige emergency da ita ya samu wajen private reception ya zauna, ya dauka kusan awa guda yana nan zaune ya daura kafanshi daya akan daya yayi relaxing kanshi, yanda yake girgiza kafanshi zaka gane he’s eager to know her well-being,babu kowa a reception din don haka yana jin takun tafiya yasashi bude idanunshi ganin nurse tsaye agabanshi “good morning sir, the doctor wants to see you in his office”

Harta qare maganar ta bai bude idanunshi ba haka zalika baice mata ci kanki ba harta sake maimaita abunda tace, mikewa kawai yayi yace “lead the way” jin haka yasata juyawa tayi gaba yabita abaya Har office din doctor din, yana shiga doctor ya miqa mashi hannu suka gaisa kafin ya mashi nuni da ya zauna, 

“Is she married sir?”

Wani irin kallo yayi ma doctor din still idanunshi na Kansa baice mashi qala ba saima Tamke fuska da yayi kamar an bashi sakon mutuwa

“I asked to confirm because it looks like a rap….”

“She’s…my…wife..!!!!!”

Yayi saurin tarar nunfashin doctor tare da kauda kanshi gefe 

“Alhamdulillah she’s stable now, but we have to admit her, yanxu dai ta samu barci sakamakon dinkin da akayi mata,”

Maida idanunshi yayi kan doctor yayi yana sauraronshi kafin ya sauke boyayyiyar ijiyar zuciya

“But sir, gaskia you need to be careful next time, healing process din baya dadewa but give her atleast a month”

Shuru ya danyi kamar bazai ce komi ba, kamar Ana ingiza shi yace

“Why did she loose so much blood”

Yar dariya doctor yayi don yaga alamun virgin da virgin ne suka hadu

“It’s because she’s a virgin,and you force your self”

Mikewa kawai yayi ya kalli doc din “I want her to be moved to the vvip, and be sure she’s taken care of properly”

Yana kaiwa nan ya miqa Ma doctor hannu sukayi sallama ya fuce, jinjina kai doctor yayi yana jinjina nuna isa irin na wannan bawan Allah.

Yana futowa bai tsaya komai ba ya wuce motarshi don saida ya tabbatar tana lafiya yana tuna da baiyi sallah ba gashi har kusan karfe 8, yana kunna motar shi ya fuce daga compound din.

Bayan futarshi saida doctor ya tabbatar an kaita vvip, daki ne babba sosai wanda yake dauke da gadon mara lafiya Harda na mai kula da mai jinya, nurses biyu yasa su kula da ita waenda suke duty na ranar.

Yana isa gida ya wuce dakinshi, saida ya shige ciki yaga yanda dakin ya sauya gaba daya ya burkice, idanunshi ya sauke kan dresser,nan take komai ya fara dawo mashi saurin kauda idanunshi yayi ya tako zuwa gaban gadon, ya baci sosai don Har jinin ya bushe, nannade zanin gadon yayi da bargon ya hade su waje daya ya wuce cikin toilet ya jefa cikin washing machine,wankan sunnah ya farayi kafin ya gaggauta ya fito ya shirya ya fara sallah, yana idarwa ringing din wayanshi da kira keta shugowa ya sashi saurinya mike ya dauko ya fara duban mai kira don call din harya tsinke, ganin asad ya mashi wajen 5 missed calls yasashi saurin dialing number shi ya Kara kunnenshi yana dauka suka gaisa kafin yadan jinkirta domin sauraron abunda yake fada “okay gani nan”

Ya fada tare da aje wayan ya wuce closet ya dauko Riga da wandon shi kamar koda yaushe, a gaggauce ya gama shirin ya fito daga dakin zuwa qasa,ya fuce daga gidan gaba daya.

Bata samu farkawaba Sai wajen karfe goma, lokacin daya daga cikin nurses din dake kula da ita na cire mata drip da aka sakamata, saida tabi dakin da kallo kafin ta maida idanunta kan nurse din, nan take ta Kara tabbatar Ma da kanta ba mafarki take ba gaskia ne, nurse sun na ganin ta farka tayi saurin cewa “sannu ya kike jin jikinki yanxu? Kina buqatar wani abun?”

Hawaye ne suka soma yi mata zarya saboda zafin dataji lokaci guda daga kasanta “zafi nake ji a kasa na” ta fada fuskanta gwanin nan tausayi

“Sannu zai daina saboda aikin da akayi maki ne”

Da sauri ta furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun a cikin ranta, ta rasa wani tunani ma zatayi, zuciyarta tayi mata nauyi, 

“Sannu ko, bari muje toilet na gasa ki zakiji dadin jikinki sosai”

Nurse din ta fada tana me kallonta cikin tausayi halin data shiga.

Da taimakon nurse din ta miqe da kyar tana jin zafin da tunda aka haifo ta duniya bata taba experiencing ba, cije Bakinta tayi hawaye na zarya akan kuncinta Har suka shiga cikin toilet din, nurse dinta ta gasa ta sosai da ruwan dumi kafin ta bata waje tayi wankan tsarki ta dauro, daman nurse din na baki kofa, tana ganin ta kammala ta shigo ta taimaka mata suka dawo dakin, kayan asibitin nurse din ta sauya mata kafin ta kawo mata abunci datayi order daga kitchen din asibitin.

A zaune ta samu tayi sallah, koda ta idar tama rasa adduar da zatayi saidai ta nemi Allah ya sassuta mata radadin da yake ji na jiki harda na zuci ma don yanxu gaba daya bata son abunda zai tuna mata da makamacin Daren jiya wanda bazata taba mantawa da wahalar daga sha ba da sanadin hakan.

Yanxu zuciyarta ta gama dushashewa ko tunaninshi bata son yi, ta fawwala Ma Allah komi fatanta kawai ta samu ta warke tabar rayuwarshi gaba daya don ko second daya bata son ta sake a cikin rayuwarshi, don yanxu kam kallon dodo take mashi, bata da abun tsoro sama dashi, saidai bata ji haushinsa ko kadan ba saima haushin kanta dataji,don komai ya faru Duk ita ta saya da kudinta saidai bata chanchanci abunda ya mata ba kuma hakan ya faru ne dalilin nuna mashi raunin ta a fili Har yaci galaba akanta.

Bai samu dawowa daga wajen asad ba Sai wajen karfe goma sha daya, gaba daya ranar irin ta yau ta zama mashi baqar rana, don abunda yayi finding out wajen asad ya sashi bazai iya hakura ba saiya tabbatar, gaba daya ya chanza lokaci guda, zafi da baqin ciki babu wanda baya ji a ciki ranshi, harya kusa isa gida ya tuna da wani abu ya juya akalar motarshi zuwa asibiti, koda ya isa lokacin har tayi barci, ya Dan dade a dakin zaune kan kujeran baqi dake zuwa ziyara wajen patient ya kafa ma bayanta idanu don tana kallon chan gefe yana jin kamar ya tashe, saida ya dauko kusan awa guda ya jingina da kujeran ranshi na mashi susa sosai, da baqin ciki abubuwa da dama kafin ya miqe ya fuce daga dakin, tana jin karar rufewar kofa ta juyo ta kalli kofar ta bishi da harara hawaye na ambaliya a fuskanta.

A mahaukacin gudu ya karasa gida ya fito daga motar shi ya wuce ciki, yana shiga cikin seating room yaga nadine a zaune tana gyangyadi, Gyaran murya yayi kafin tayi firgigi ta Tashi “welcome back sir”

Baice mata komi ba Sai kallonta dayi da gefen ido 

“Daman dazu na dawo don an bani sallama”

“Okay” kawai ya iya cewa kafin ya nufi hanyar stair ganin haka ya sata saurin cewa “do you need anything sir nayi dinner?”

“Bring me just coffee” ya fada yana wucewa cikin parlor shi dake sama, yana bude kofar

Dakin ya tsaya chak ganin ko’ina ah gyare Har duvet dinma Duk an sauya zuwa wasu sabbi Sai kamshi dakin keyi,Kara sa shigewa yayi ya saka wurga keys dinshi da wayan shi kan gadon ya wuce bathroom, nanma ta gyra tsaf tsaf, rage kayan jikinshi yayi ya watsa ruwa ya fito hannunshi rike da towel yana goge sajen fuskanshi,gaban dresser ya tsaya ganin few turarukan shi da basu fashe ba Nadine ta jera su tass, nan take moments don jiya ya fadi mashi,saurin kauda zancen yayi ya dauka body mist kawai ya fesa kafin ya zura kayan barcinsa, nan Nadine tayi mashi knocking, gaba daya baya jin bakinshi zai iya daukan komai don haka yace “just take it back” yabi lafiyar gado.

Ya dauka kusan awa biyu a kwance Har kusan karfe uku ganin barci kiri kiri ya kaurace Ma idanunshi ya sashi mikewa ya dauro alwala ya shimfida sallaya ya gabatar da sallolin dare, ya dade sosai a tsugunne yana neman taimkon Allah

dan ya bashi sa’ar abunda yake shirin yi. Har aka kira sallan asuba ya mike ya wuce masallaci.

Ana idarwa ya dawo gida ya kwanta ya cigaba da azkar Har barci ya kwashesa don jikinshi na buqata.

Karfe Tara daidai wayanshi ya shiga ringing, kamar bazai dauka ba sanin yanayin aikinshi da binciken da yakeyi yasa Duk Kiran da zai shigo mashi yana da mahimmaci, cikin muryarshi dake a shake ya dauka wayan ba tare da ya duba mai Kiran ba

“Assalamu alaikum son”

Da sauri ya bude idanunshi da sukayi jaa alamun barci bai ishesa ba yayi saurin gyara muryarshi yace “wa’alaikum salam ammah good morning”

“Morning son yanxu ku dare ne achan dubai ko” 

Da sauri ya zauna yace “uhm ammah ya kuke ya yara”

“Muna nan lpy babana, na tasheka a bacci ko?”

“No it’s okay ammah”

Shuru ta danyi kafin ta Nunfasawa tace “dazu doc bilal ya kira ni,yace yaganka a asibiti, Nace mashi Ay baka dawo ba maybe yayi mistaken wani dakai, yaushe zaka dawo ne son”

Shuru ya danyi, yana jin zafin rashin fada mata yana Nigeria saidai yanxu is high time ya fada mata zuwan shi nigeria don yanxu kam dole ya koma gida saboda Sabon al’amarin daya bullo mashi wanda ya sashi shiga rudani da mamaki saidai yayi alqawarin yin kwakwaran buncike don Sai yanxu ya fara zargin su.

“A tayani da addua Zan dawo jibi friday Insha”

cikin murna tace ”Alhamdulillah gaskia naji dadi sosai allah ya kawoka lpy son”

Sun dan taba hira kadan kafin suyi sallama ya kashe wayar. Sosai yake jin qaunar mahaifiyarshi sosai aranshi wannan yayi alqawarin protecting dinta da duk wanda ke karkashin sa.

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 113

Cikin shirin sa casually kamar koda yaushe ya sako kasan, dining ya wuce direct kafin nadine tayi serving dinshi abunci, baici da yawa ba ya fuce daga gidan.

Karfe sha biyu daidai tayi mashi a cikin asibitin, yana fitowa daga cikin motarshi ya dan tabe baki ya zaro sunglasses dinshi ya saka don wani irin zafi akeyi sosai a garin sosai, yana rufe motar shi ya shige cikin asibitin, bai tsaya ko ina ba sai dakinta dake chan sama na vvip, ba tare da tunanin komi ba ya bude kofar dakin ya sako kanshi tare da rufewa, dagowa yayi ya kafeta da idanunshi itama idanun ta zuba mashi tare don tayi mamakin ganinshi, daman futowarta kenan daga bandaki nurse ta taimaka mata ta gasa ta kafin ta bata waje don ta samu tayi wanka, futowa tayi dana dan dingisawa don ba laifi tana dan jin sauqi sosai don yanxu takan kai kanta toilet din tayo futsari da alwala ta dingiso ta dawo saidatazo daidai tsakiyar dakin ya shugo, arazane ta dawo ta kalleshi suna hada idanu tayi saurin kauda nata gefe, kokarin saurin karasa gaban gadon ta soma yi don hijab dinta nakan gadon gashi babu komi a jikinta Sai towel din data nade jikinta dashi, cikin sassarfa ta fara  takowa tana jin yanda wajen ke mata radadi,cije bakinta tayi ta karasa bakin gadon tare da saurin janyo hijab din nata ta zura ta zauna gefen gadon kanta a kasa.

Yana ganin haka ya kauda nashi kan gefe ya samu waje kan kujeran baqi ya zauna ya daura kafa daya kan daya.

Dan waigowa yayi ya sashi kallonta ta gefen ido,ganin Duk tayi fayau fuskanta babu walwala akai, 

“Baki iya gaisuwa bane?ko Har da bakin naki aka dinke “

Ya fada yana kare mata kallo, ko kallon inda yake batayi ba saima kauda kanta gefe datayi ta hade rai murya chan kasa tace “ina yini”

Shuru ne yadan ratsa wajen don bai amsa gaisuwan nata ba saidai yana kan tunanin abunda zai ce mata, muryanshi chan kasa yace “how are you feeling now”

Kamar wanda ta kosa ya fita ta hade rai sosai tayi saurin cewa “Alhamdulillah!”

Yana ganin haka ya danyi relaxing kanshi bai sake cewa komai ba itama bata yi gigin kallonshi ba bare ta ce mashi wani abu

14 / 94