abu baki bani amsa ba,inason ki cire kunya ki fada min komai kinji’’
Sunkuyar dakai amra tayi don ta tuno da tambayar da ammahn tayi matan akan wani irin zama sukayi ita dashi, bat agama tunanin ba ammah ta kasa ta ta hanyar cewa ‘’daga jiya zuwa yau na fuskanshi yanda kuke treating juna, karki boye min komai ki fada min kinji?’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’tohm’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’kina tsoronshi ne?’’
Kanta a kasa ta dan dago ta kalli amah kafin ta girgiza kai, sake tambayarta ammah tayi tace ‘’kinyi mashi laifi ne achan dubai?’’
Samun kanta tayi da cewa ‘’banyi mashi komai ba, bansan meysa yake jin haushi na koda yaushe’’
Dan murmusawa ammah tayi ganin yarinta baro baro a tattare da amra. Shuru amra tayi tana nazarin sus u duka, na farko abunda ta lura dashi shine amar bai karbi auren ba, don kwata kwata babu alamun ya damu da auren ba, lallai akwai gyara sosai ammah ta fada aranta, don babu wani alamun closeness a tsakanin su, don bazaka ce mata da muji bane kwata kwata.
Kallonta ammah tayi tace ‘’daughter kince min kin karbi aurenku hannu bibiyu ko?’’
Ammah ta tambaya tana kallonta, dan dagowa amra tayi ta girgiza mata kai, ‘’kinsan aure a addini basai na maki bayani ba right?’’
Ammah ta tambaya tana kallonta duk don taji daga bakinta ‘’eh amra ta fada kanta a kasa
‘’now you have to do your duty as a wife kinji,kinga muhammd mutunne mai wuyar fassara, ba kowa zai iya karantar shi ba, karkiga kina da kananun shekaru, you have right on him, karkiji tsoron komai, ki cire tsoronshi aranshi’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’insha allah…’’
Kiran lantana ammah tayi tana zuwa tace ‘’ki nuna ma daughter part din muhammd, daga yau zata dunga kula da chan’’
‘’tohm hajiya’’ lantana ta fada tana kara tabbatar da maganar auren amar da bakuwar don ranar da aka kama daddy har yace amar yayi aure ba tare da sanin kowa ba tana wajen saidai sanin cewa ba huruminta bane yasa bata cusa kai ba, kallon amra ammah tayi kafin ta miqe tace ‘’daughter bari na wuce sama, lantana zata nuna maki part dinshi’’
Murmushi amra tayi mata tace ‘’tohm ahuta lafiya’’
Sama ammah ta wuce kafin lantana ta mata jagoraan part din amar,suna zuwa bakin kofa salima tace ‘’nan ne part dinshi, akwai duk wani abun buqata wajen gyara dakin a ciki’’
Girgiza mata kai amra tayi tace ‘’okay’’
Bude kofar part din amra tayi, kafin ta shige ciki, bin parlor nashi tayi da kallo, parlor ne maid an girma babu abunda babu a ciki, set of kujeru farare da suka sha pillows sai center table a tsakiyan parlor da furr carpet shima fari tarr sosai, koina fessfess babu datti ko kadan, idanunta ne ya sauka akan katon frames da aka jea a bango guda uku, wanda duk hotunanshi ne da kayan sojoji sai kuma daya daya dauka da ammah da dada sun sakashi a tsayi suna murmushi, kallon hoton amra tayi tana mamakin fuskanshi a hoton, yayi wani masifar kyau sosai, gashi yayi dariya wanda zatace wannan ne first time data ganshi yayi dariya guineuly, ba karamin tafiya da ita yayi ba don wani irin kyau yayi mata a hoton, ta dauka kusan awa kusan minti biyar tana kallon frames din kafin ta wuce cikin bedroom din, tana shiga sanyi ac ya daketa hade da kamshin turaren shi dake tafiya da ita, lumshe idanunta tayi sosai ta karema dakin kallo, ko’’ina neat babu kazanta ko kadan, kallon bed dinshi tayi da white beddings dinshi da suka dan yamutse saboda kwanciya, babu komai a dakin daya yi datti sai gadon kawai dake buqatan gyara don ko beddings dinma babu datti ko kadan, karasowa tayi gaban gadon kafin ta waiga ganin wani sako daga gefe wanda a alamu nan ne hanyar toilet, takawa tayi har wajen sakon, walk in closet ne babba a ajen sai kofa daga gefe wanda da alamu kofar toilet ne, bin kayan cikin glass clost din tayi, don akwai lightings sosai, komai tsaf neat and clean an jerasu, fadar yawan kayan wajen ma bata lokaci ne harda section din takalma da agogon sa da neck ties harda manyan kaya, murmushi kawai tayi chan kasan maqoshi tace ‘’mr perfect guy’’
Dube kofar toilet tayi shima babban toilet ne sosai kamar daki, very clean an neat, futowa tayi daga toilet din ta wuce bedroom ta fara gyara mashi, tana gamawa ta wuce toilet din ta wanke mashi fess fess kafin ta futo, tana fitowa taci aro da lantana da burner, mika mata lanatana tayi ‘’sorry na manta ban baki burner ba, na saka turaren already a ciki’
Karba amra tayi tace ‘’thank you’’
Komawa tayi ta jona burner din kafin ta fito daga dakin, sama ta wuce, tana shiga ta karasa gefen bedside sai a lokacin ta tuna da wayarta dake a kashe tun bayan data shiga flight ta kashe, nan take tunanin haifa yazo mata, ita da Nadine, yanxu haka suna chan hankalinsu atashe suna tunanin ta, saurin zuge handbag din tayi ta zaro wayar kafin ta zauna gefen gado, kunna wayar ta fara yi kafin ta danyi jimm, tunawa da bata da sim card din Nigeria,jikinta ne yadanyi sanyi, ganin bata da wani option yasa ta jawo charger wayar ta jonata a jikin bedside socket da wayar.
Karfe uku su salima suka dawo daga school, lokacin da suka shugo babu kowa a sitting room don haka suka wuce sama, part din ammah suka fara shiga suka
gaisheta kafin su wuce na amra cikin zumudi, a kwance suka taddata, da sauri salima ta karasa bakin gadon tace ‘’adda, kina zaune ke kadai’’’, miqewa amra tayi zaune da sauri salim ya karaso kusa da ita ya zauna fukanshi dauke da murmushi, tana ganin haka tace ‘’duk dadin hutun da aka baku ne ya saka murna haka’’ ta fada tana kallon salim, bude handabag dinshi yayi ya zaro mata result report dinshi na mid term, tana gani ta karba tace ‘’ wow, kayi kokari’’
Dariya yayi kafin ya miqe yayi ma salima gwalo ya fuce, hararashi tayi tace ‘’mara kunya’’
Yana fucewa salima ta kalleta tace ‘’adda, nayi missing dinki’’ ta fada tana rungume amra, dariya amra tayi itama ta rungumeta tace ‘’ay gani nan saikin gaji da gani na ma’’
Mikewa salima tayi tace ‘’bari nayi wanka na chanza kaya saimu sauka kasa tare’’
‘’okay’amra ta amsa ta harta fuce daga cikin bedroom din.
Kasa suka sauka zuwa parlor, salima ta kunna masu tv, salim dake gefensu yana cin abunci amra ta kalleshi tace ‘’acici ashe har yanxu kana nan da halin naka’’ amra ta fada tana mashi dariya, murmushi kawai yayi mata ganin salima ta dawo itama hannunta dauke da plate na abunci, zama sukayi anan sitting room suna hira suna kallon tv, amra nayima salima tsifar gashi, suna nan zaune ammah ta sauko tana binsu da idanu tana murmushi ganin irin bond din dake tsakanin su, wani irin dadi taji ganin su ahaka, suna hangota kuwa salima tace ‘’barka da hutawa ammah’’
Amra ma kallonta tayi tace ‘’ina wuni ammah’’
Salim dai miqewa yayi ya rungume ammah kafin taja hannunshi suka karaso gaban sitting room din, kallonsu tayi tace ‘’daughter sun cikaki da surutu ko?’’
Dariya duk sukayi salima tace ‘’chapp ammah kodai ta cikamu da surutu ba’’
Dungure mata kai amra tayi tace ‘’kundai sani surutu, nida bana surutu’’
Dariya duk sukayi ammah ta kallesu tace ‘’ay gwara ayi tsifa,daman inata tunanin wannan weekend mu fita saloon’’
Da sauri salima ta dago tace ‘’ammah wannan weakend din banda kitso wallahi zafi kaina kemin idan akayi’’
Kallonta amma tayi tace ‘’haba dear wannan gashi naki saida kitso ay, ga cika ga yawa’’
Tabe baki salima tayi ashagwabe tace ‘’dama irin gashin adda nake dashi wallahi,’’
Dungure mata kai amra tayi tac eke har kina fatan irin gashi na idan ya nannade dinnan wahala yake baki’’
Turo baki salima tayi tace ‘’allah ki godema allah kina a coily gashi, ba kamar nawa ba’’
Dariya ammah tayi ganin conversation din nasu gwanin burgiwa da yanda suke,
Suna nan zaune aman ya shugo lokacin an gama tsifar, salim na kwance gefen amma yana barcin shi daya saba, salima kuwa na zaune a kasa, amraa na gefen single seater sun kafama tv idanu,suna kallon wani series da salima ta dunga zuzutawa akan yana da dadi, sallamar da akayi ne ya dawo dasu daga kallon da sukeyi, anatse aman ya shigo sitting room din idanunshi akan salima, wadda itama ta dauke idanunta kan tv ta maida kanshi, ammah ce ta ankare dasu tace ‘’ehmmm’’ da sauri suka ankare amra kam bata ma lura da kallon da suke ma juna ba sai gyran murya da ammah tayi, wani irin kunya ne ya lullube salima tayi saurin kauda kanta, ‘son har an dawo, sannu da dawowa ya aiki’’
‘’alahamdullahi ‘’ya fada yaana murmushi, kallonshi amr tayi tace ‘’ina wuni’’
Lafiya lau sister inlaw’’ ya fada yana kannema salima idanu wanda akan idanun amra, kallon inda yake ma winking tayi ganin salima na murmushi, mamaki ne karara a fuskanta ganin yanda salima ke blushing, maida idanunta tayi kanshi tana mamakin yanda shi baya kama da ammah da ya amar don kammanin shi daban ne, duk a tunaninta qanin amar ne, sauke kanta tayi tana mamakin irin kallon da yake ma salima wanda tana gani tasan kallon so ne, jin ana kiran sallah yasa ammah cewa ‘’ oh har lokacin sallah yayi allah kasa muyi karshe mai kyau ’’
Da ameen duk suka amsa kafin ammah ta tashi salim ta wuce sama, amra ma mikewa tayi tana kallon salima dake blushing idanunta kan tv tace ‘’small madam ay saiki hakura da kallon haka ko’’, tana kaiwa nan ta wuce sama ta barta zaune aman na zaune shima ya kafeta da idanu, yana ganin duk sun wuce sama ya matso kusa da salima yace ‘’baby sal babu welcome’’
Dan waigowa tayi ta mashi wani fari tace ‘’sorry my yaya, ina jin kunyar ammah ne’’
Dariya yayi yace ‘’ay taga yanda kike blushing’’
Zaro idanu salima tayi tace ‘’toh ay kaine, dana ganka sai naji sanyi araina bana sanin lokacin da nake smiling din ma’’
Dariya yayi sosai harda kyakyatawa yace ‘’sister inlaw ma ta ganki’’
Zaro idanu salima tayi tace ‘’da gaske adda ta ganni’’ jin tace adda yace ‘’yes ta ganki, taga yanda kike kallona cikin so’’
Tabe baki salima tayi ta miqe tace ‘’ni ba sonka nake ba’’ wata yar bazawarar dariya yayi yace ‘’don’t deceive your self baby na’’ yana kaiwa nan ya miqe shima yayi pecking kumatunta ya wucewarshi ya barta tsaye kamar sanda,da sauri ta wuce sama tana blushing, tana karsawa cikin bedroom dinsu ta tadda amra zaune kan sallaya, wucewa cikin bathroom tayi ta dauro alwala kafin ta shimfida sallya kusa da amra, tana idarwa amra ta kalleta, kamar bazata ce komai bat ace ‘’meysa kike blushing dazu’’
Dan fusgewa salima tayi kamar bata gane inda ta dosa ba tace ‘’blushing kuma? Mey zai sani blushing’’ dan bugu amra takai mata tace ‘’soyayya kike ko’’
Dariya salima tayi tace ‘’kai adda ni babu wani soyayya’’
‘’soyayya kuke mana, naga yanda kike kallonshi shima yana kallonki, wai shi waye ne?kanin ya muhammd ne?’’ amra ta tambayeta tana kallonta, dariya
salima tayi,don shes enjoying the conversation tace ‘’chapp yayan ya muhammd ne saidai shi bad an ammah bane, babanshi shine qanin baban ya amar and shi ne mijin ammah ayanxu kafin a….’’ nan take salima ta bata labarin gidan da yanda suka zo suka samesu, ba karamin tausayin aman amra taji ba jin yanda mahaifinshi ya kasance dukda ita kanta salima bata san dalilin kamashi da akayi ba, ‘’back to our discussion, fada min gaskia soyayya kukeyi’’
Dan dukar dakai salima tayi daga zaune ta dan tabe baki tace ‘’yace dai yana sona, ni kuma ban amince ba’’
Idanu amra ta kura mata kafin tace ‘’ke kina sonshi ne’’ shuru salima tayi ta kasa cewa komais aida amra tadan yi dariya tace ‘’ na wa wo, my sister is in love, oh salima har kin girma’’ mikewa salima tayi tana turo baki ta koma baking ado ta jawo book din zanen ta tace ‘’ni adda bance maki ina sonshi ba fa’’
Wani irin dadi amra taji ya ziyarce ta,ba tareda tace mata komai ba ta dawo inda take zaune tace ‘’small madam, bazan hanaki abunda zuciyarki ke so ba, I will always support you, idan har kina sonshi’’
Shuru salima tayi kafin ta dan dago tace ‘’bazaki min fad aba?’’ grigiza mata kai amra tayi ‘’meysa zanyi fada, youre an adult now, kuma kin kusa gama school, duk abunda kike raayi shi nake raayi’’
Rungumeta salima tayi gam hawaye nabin kuncinta tanajin kamar mam ice agabnta, itama amra rungumeta tayi gam a jikinta.
Kasa suka sauko atare zuwa kitchen, nan suka tadda lanatana tana tuka tuwo,da murmushi amra ta karba mata tace ‘’kawo na taya ki’’ mika mata lantana tayi haka suka karasa girkin atare suna hira gwanin burgewa, salima harda cocnut drink tayi, karshe dai lantana barinsu tayi suka karasa miyar ogu daya sha nama da ganda da kifi, sun agamawa salima ta fidda warmers kamar yanda suka saba ita da ammah, anatse suka fara fidda komai zuwa dining, ammah dake saukowa t hangosu suna shirin komawa kitchen, kallonsu tayi yanda suke dariya suna hira, anatse ta karasa cikin kitchen din tace ‘’my daughter wannan kamshi haka ay saiku sakamu jin yunwar dole’’ dariya salima tayi ta karaso kusa da ita tace ‘’wallahi ammah nay au idan kikayi tasting miyar adda sai kunnenki ya kusa cirewa, shes a best cook’’
Kallon inda amra ke tsaye amma tayi tana murmushi hannnunta dauke da warmer da suka zuba miya,
‘’ashe daughter ce tayi mana wannan delica din, shiyasa naji kamshin gidan ya chanza gaba day aba kamar ba da ba’’
Dan tabe baki salima tayi cikin shagwaban tace ‘’ámmah ni nawa girkin bashi da dadi ne?’’
‘haba dear kema naki yana da dadi sosai’’
Dariya duk sukayi gaba daya kafin su fito atare, zama amma tayi a sitting room don sai kowa ya hadu ake cin abunci, su salima kuwa sama suka koma, amra ma dakinta ta wuce tayi wanka ta dauro alwala, sallah ta fara yi tana idarwa ta
sauya kaya zuwa marasa nauyi cikin wanda ammah ta kawo mata, doguwar rigace saidai ba bubu bace ba, rigar tabi jikinta ta zauna mata dam, gaban dresser ta karasa ta fesa turare kafin ta futo zuwa dakinsu salima.
Ammah na zaune amar ya shigo gidan da sallama, kallonshi tayi fuskanta dauke da murmushi tace ‘’welcom son’’
Wani irin dadi yaji ganin mood dinta, anatse ya tako har inda take yace ‘’thanks ammah na barka da dare, seems like youre in a good mood’’ dariya ta danyi tace ‘’ba dole ba son, yau zanci girkin matar ka, oh ashe inada rabon ganin wannan rana’’
Take yadan hade rai ya tsuke fuska, ammah na ganin haka tace ‘’go and freshen up’’
Mikewa yayi ya wuce bedroom dinshi,yana shiga ya aje wayanshi ya rage kayan jikinshi ya wuce bathroom, wanka yayi atsanake don already yayi sallah kafin ya shugo, agurguje y agama shirinsa cikin gajeran wando da riga na under armor, rigar ta kamashi sosai ta fidda asalin kyawun surarshi, anyways shi komai ma kyau yake mashi lols..yana gama saka kaya ya feshe jikinshi da turaren shi kafin ya fito, ganin ammah a zaune ya karasa inda take ya zauna, hira suka farayi, nan aman ya fito, kallonshi amar yayi yace ‘’ka dawo ashe ya office din?hope komai na tafiya daidai,’’ aman yayi mamakin Magana da yayi mashi haka me tsayi don haka yace ‘’alhamdulillah, komai yana tafiya daidai,’’ murmushi amar yayi mashi nan suka cigaba da hira harda aman din, sun saka ammah a tsakiya.
Anatse su salima suka fara saukowa, salima nag aba amra na bayanta tana zolayarta, ‘’mara kunya, kema wai kin girma ko, ko kin manta lokacin danake tare maki fada a islamiyya’’ amra ta fada tana dariya, dan juyowa salima tayi ta kalleta tace ‘’kai adda, ammah dai kinsan na fiki baki nima ranar nan ay na tare maki fada’’
Tana kaiwa nan ta ruga a guje, amra ma binta tayi da dan gudu ta kamo hannunta tace ‘’ni kika tare ma fada yaushe, ay wallahi saikin fada min’’ ta fada tana kai mata dundu, ‘’wayyooo bayana allah zan fada ma ammah kin bugeni’’ wani dundun takai mata har suka sauko kasan,
Tunda suka sauko ammah da aman suka bisu da idanu suna dariya,amar dai kallo daya ya masu ya kauda kanshi gefe saidai yana jin duk conversation din nasu, kallonsu ammah tayi tace ‘’yau fada sako da sakuwa akeyi kenan’’ sai alokacin suka lura da mutanen dake parlor, da sauri amra ta kame kanta salima ma haka kafin su wuce sitting room, amra dai ji tayi kamar karta karasa parlor, salima na karasowa ta zaune akan carpet kusa da kafan ammah inda aman ke zaune tace ‘’barka da dare ammah, ina wuni ya muhammd, ina wuni ya…yaa’’
Ta fada tana kallon aman da shima kallonta yake, ammah ce kawai ta amsata kafin ta waiga wajen amra data kasa daga kafafunta, saida ammah tace ‘’karaso mana daughter zo ki zauna’’ ta fada tana mata da nuni da gefen amar,tunawa da zancen ammah yasa ta karaso anatse ta zauna gefen da yake zaune a kasa, sai ya
zamana kowacce tana gefen nata zabin, ammah dai dadin da takeji baya musaltuwa, amar dai tunda yaga haka ya hakimce a bayan kujera ya janyo wayarshi,
Sauke kanta kasa tayi tace ‘’’barka da dare ammah, ina wuni ya aman’’
‘’barka daughter ya gajiyan girki’’
‘’babu gajiya’’ amra ta amsa mata kanta a kasa
Aman ma kallonta yayi y ace ‘’sister inlaw kin cika mana gida da kamshi’’
Dan murmusawa amra tayi batace komai ba idanunta akan yatsun kafar amar dake gabanta da huge tigh dinshi, ahankali ta dan dago tace ‘’ina wuni ya