Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   26 / 94

75K to 78K   out of 279.4K words

also take your blood sample for some test to see if everything is normal”

Shuru amra tayi ta fara nazari don ita bayaga amfanin wani blood test ba infact check up dinma bashi da wani amfani don ta warke sosai bata jin wani ciwo don haka ta dan tabe fuska tace “okay”

Doctor da kanshi ya deba jininta ya aje a cikin wani box ya sake diba wani Jinin, Har tazo tambaya sai kuma ta fasa harya gama ya duduba ta da Heart rate dinta kafin ya masu sallama ya fuce.

Shima m5 bin bayanshi yayi ya fuce.

Doctor na zuwa asibiti ya shiga lab da kanshi ya fara running test Har Sai biyu just to confirm, cikin minti talatin test din ya fito, baima kaiga dubawa ba ya saka a envelop ya wuce office dinshi don Kiran amar.

Karfe uku daidai haifa ta iso penthouse din general wanda ya girgizata sosai, Duk kudin da abuh dinta ke dashi bai mallaka penthouse ba Sai normal apartment, kuma tabbas tasan me iya mallakar wannan sai wandaya amsa sunansa mai kudi sosai.

M5 ne ya shigo da ita don Akwai tight security for visitors don haka tana shigowa parlor nanma ta baza idanunta tana yaba irin kyau da tsari da yayi, amra na ganinta ta taho da dan gudunta ta rungumeta tsam,ba karamin dadi yake ji ba ganin haifa, Nadine ma karasowa tayi suka gaisa kafin amra ta jata zuwa dakinta. Suna shiga suka baje akan gadon suka fara hirar yaushe gamo, Nadine ce ta shigo masu da abun sha da snack kafin ta aje masu ta juya? Kallonta amra

tayi tace “Nadine zo, inason kema ki judging abunda Zan fada ma haifa, inason ku fada kin Idan Har inada laifi a cikin wannan alamarin”

Dawowa Nadine tayi ta zauna gefen ottoman dake maqale da gadon.

Nan amra ta soma yima haifa bayanin komai tundaga kan lokacin da m5 ya kaita airport zuwa rayuwarta da sukayi a cikin gidan wanda Nadine ce sheda zuwa ga guduwa da tayi”

Shuru haifa tayi ta ta yayi mugun baci tace “kina nufi. Duk wannan abun ya faru?toh menene dalilinsa na jin rabuwa dake, ko ya manta yarjejeniya akayi kuma da shiada, it’s clearly jikinki dama chan yake so shiyasa yayi amfani dake” ba karamin haushi haifa taji ba da bayanin amra Nadine dai ta Kasa kunne tana sauraron su saida suka gama inda haifa ta bata shawarar taimakonta don filing for sharia divorce sannan zatayi ma abu magana don shine waliy dinta, Nadine dai na jinsu bata ce kala ba amra kuwa sai kuka take don takaicin komai ma

Saida Nadine ta bari suka gama Duk surutansu kafin ga soma magana “I’m sorry with the language that I will Be using, I don’t know if this might make you feel bad”

Haifa ce ta kalleta tace”it’s okay just speak your mind I’m sure it’s because she trusted you that’s why you’re here”

Dan jin Nadine tayi kafin tace “ I understand all

Your problems because I’ve been in a similar situation, saidai ni you choose to stand for my self,yanxu duk abunda yayi maki you’ll just let it go?

Shuru amra da haifa sukayi don su kadai suka san waye general don haka dai suka kasa kunne suna sauraron ta 

“You’re young and very very beautiful, your beauty is irresistible, and I think with your beauty you dont have to file any divorce, that beauty will give you power, and based on what you just said that beauty is the reason why he keeps holding right? Then use that beauty and make him running to you like crazy,make him understand that you’re the lady and you run the world,”

Take haifa ta sauke lafiyayyan murmushi ta kalli mata tace “she’s right, babe she’s right, make him fall for you, make him regret all He has been doing to you, no man will Ever turn a blind eye on your beauty then use it to make him understand your worth”

Tsuru amra tayi don sun fara sakata shiga tsoro, gashi bata gama gane me suke nufi ba, “how???”

Nadine ce ta juyo ta kalleta tace “haba mana you’re not young basai nayi maki bayani ba ko?”

Girgiza kai amra tayi fuskanta ashagwabe tace “no nifa ban gane me kuke nufi ba”

Haifa ce ta kalli Nadine tace “can you please help us on that?”

Da sauri Nadine tace “yea I can give a helping her, but she also needs you also”

Dariya kawai haifa tayi tana jin dadin wannan conversation din Nadine kuwa murmushi kawai takeyi hoping komai zaizo da sauki kanta yanda tayi hangen haka, 

Haifa ce tayi saurin mikewa tace “now we need to spice you up baby girl,he will surely regret the way he treated special you like a trash I promise babe”

Amra dai su yanxu ta dago inda suka dosa,take komai nashi da halayyanshi suka fado mata tunda ita ke zaune dashi ita tasan shi, jikinta ne yayi sanyi sosai tace “ni inajin tsoro gaskia, bakisan koshi waye ba, I can do this”

Zama haifa tayi kusa da ita tace “hey look at me babe, you can do it, yes you can do it, say it to yourself, say it loudly”

Nadine ce ta tsomo baki tace “whenever you feel like you can’t do it just remember all he has done to you, all of the pain, the lies”

Take idanun amra suka dau jaaa, idanunta sunyi tauu fuskanta na bayyanar da bacin rai da takaici tace “I can do this, wallah I promise I will make you understand that no man in this world treat a lady like that, we’re all special”

Fuskanta dauke yake da fushi da takaici sai ya zaman kamar she’s ready for battle da enemy dinta.

The revengeee……

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 12

0

Update!!!

20/05/2023

Unedited

Ranar haka suka wuni suka tufka da warwara,inda sabo ya shiga tsakanin su sosai kamar kawaye, Nadine na mamakin yanda suka sake da ita dukda ita ba kowa bace face yar aiki,Sai wajen karfe takwas haifa tayi masu sallama ta shiga motan ta wuce gida.

Bangaren Amar kuwa tunda doctor ya kirashi ya shiga tashin hankali da abunda ya shaida mashi, don haka ya yanke shawarar zuwa dan dole yazo ya tabbatar da kanshi, ranar dai haka yayi ta babu walwala kwata kwata,koda ammah taga yanayinshi ta tambayeshi abunda ke damunshi nan take ya shaida mata baya jin dadi ne.

The next day…

Da wurwuri ta shirya cikin Kamala ta sauko kasa, Nadine na ganinta tayi saurin zuwa gabanta tace “good morning ma”

Murmushi kawai tayi ma Nadine kafin su wuce wajen dining,Nadine ce tayi serving dinta special English breakfast da pablo ya dafa, bata ci da wani yawa ba ta mike tayi Ma Nadine sallama ta fuce daga parlor zuwa inda m5 ke parking? Yau ya chanza mota zuwa wata Bakar benz,Tana karasowa yayi saurin fitowa ya bude mata bayan motar ta shiga kafin shima ya shiga ya jasu, “good morning ma’am”

Bata kalleshi ba tace “morning”

tafiyar minti ashirin suka iso headquarters, yana parking ta fito rike da wayar ta da laptop dinta ta shige ciki a tsanake.

Tun daga bakin reception haifa ta hangota, da sauri ta karaso gabanta tace “kinyi latti fah”

Dariya amra tayi tace “lattin 10mins ko”

Dariya sukayi gaba daya kafin haifa tace “let’s go in, yau Akwai aiki da yawa inaso muyi mu gama da wuri Akwai inda zamuje”

Kallonta amra tayi feeling so excited tace “daman na gaji da zaman gidan nan, Ina zamuje”

“It’s a secret” haifa ta bata amsa 

Ciki suka wuce ta aje laptop ta saka lab coat  dinta kafin su fito tare gwanin ban sha’wa, saida saida suka fara first round medical check wanda ya dauke su kusan awa guda son Akwai patients da yawa don Akwai manyan officers da sukaje operations, wasu sun raunata wasu cikinsu kuma sun samu minor injury, da yake aikin nada yawa yasa suka raba, don yawanci daman chanza dressing ne Sai nada magunguna da duba pulse din patients, abunda yake burge amra shine Duk wannan aiki da sukeyi wanda yawanci duba maza ne basa samun matsala dazu, don wasu saikaga har flirting mutane suke yi saidai banda larabawa, kwata kwata basa flirting da mata musamman waenda ba al’adar su daya ba ko Yan wata kasar,dama dama haifa, ita yar kasar ce saidai hakan baisa suna shiga sabgar su ba.

Ahankali ta janye labulen dake rufe da gadon patients don yawanci Ana janyo shi ne Idan za ayi Ma mutun allura, ko idan patients zai kwanta, wani saurayi ne Akwance ya juya ma labulen baya, kafanshi na daure da igiya dake rike da gadon da alamu ya samu karaya ne ko ya buge akafan, dogo ne sosai bashi da qiba dan daidai jikinshi, kanshi kwance da gashi irin na larabawa, saurin kauda kanta tayi tace “salam” duban file din hannunta tayi tana karanta maganin da ya kamata yasha da safiyan, bai waigoba sarai kuma yajita idanunshi a lumshe saidai muryarta yasa ya bude idanunshi tare da dan waigowa dan ganin me zaqin murya irin wannan, kyakyawan saurayi ne balarabe sak, yana da kyau daidai musali don fuskanshi yar siririya ce, wannan yana da gashi daya rufe kusan duka goshin sa, tunda ya kafa mata idanu yaqi saukewa don bai taba ganinta anan dukda shi bangaren department din da yake basa zama a headquarters, yawanci operation suke, batasan kallonta yake ba don idanunta

nakan file din saida ta gama ta dago, murmushi ne dauke a fuskanshi kafin yayi saurin dauke idanunshi don lowering gaze, murmushi kawai tayi tace “good morning sir”

Dan dagowa yayi yace “morning”

Matsowa tayi da hannunta sanye da glove ta fara kokarin duba kafan nashi, tana tabawa ya danyi Kara “ouch”

Da sauri ta dago tace “so sorry, futa tayi kafin ta dawo da tray a hannunta dake dauke maganin sai wani disposable cup, Miqa mashi maganin tayi da ruwan, karba yayi ya sha kafin yace “thank you”

Tana shirin juyawa yace “you’re beautiful!”

Chak ta tsaya kafin ta juyo,ba kallonta yake ba fuskanshi a kasa yayi maganar, wani kayataccen murmushi ne ya Kubce mata tace “thank you!” Kafin ta fuce.

Tana futowa ta hango haifa dake shirin wucewa office, cikin yar sassarfa ta karaso kusa da ita tace “you!!” Da dan karfi da yasa haifa razana tace “ya Allah! Babe qin bani tsoro”

Dariya amra tayi Har set of hakoranta na futowa sosai, kallonta haifa ta tsaya yi tace “you look so happy today, is there anything that I need to know?”

Jan hannunta amra tayi tace “nothing let’s go”

Office suka wuce kafin lokacin sallah,

Karfe daya da rabi suka fito daga masjid suka wuce cafe, ice tea suka karba da snacks kafin su koma office.

Karfe hudu daidai suka fito,cikin shiri, haifa ce ta kalli amra tace “ga wanchan bodyguard din naku yana jiranki, ya zamuyi da fitan namu”

Kallon inda haifa ke nuna mata tayi kafin tace “muje”

Suna zuwa daidai inda m5 yake Har yana shirin bude kofa ta tsaya tace “hey!

Mamaki ne karara afuskanshi kafin yayi saurin kauda kai yace”good evening ma’am “

Banza tayi dashi tace “kaje Zan taho daga baya”

Bai kalleta ba yace “I have to inform s..” saurin katseshi tayi ta hanyar cewa “I messaged it him”

Tana kaiwa nan ta wuce motar haifa da ke jiranta, bude gaban motar tayi ta zauna haifa taja motar suka tafi, ganin haka yasa m5 shiga motar shima yabi bayansu.

 Gaban wani pink spa and haifa tayi parking, kafin su fito atare gwanin nan sha’awa, suna shiga ciki haifa tayi clearing bookings dinsu kafin attendee dinsu ta masu jagora, saida suka sauya kaya zuwa bathtub kafin a fara masu spa da massage, same room aka basu kowa da massage bed dinshi, hira suka sha Ana masu spa, nan haifa tasa akayi Ma amra waxing dukda fatarta babu wani gashi sosai, girly gyra akayi masu sosai inda suka sha hira sosai tsakaninsu, amra Ma ta sake sosai don Sai taji rabin damuwarta ya ragu saboda peaceful conversation da suka yi ita da haifa, shuru ta danyi aranta tana godema Allah daya bata aminiya kamar haifa.

Karfe shida daidai suka fito daga spa din, kafin su fito, saida haifa ta Kara masu booking wani session din don tana son su amra ta gyaru sosai, 

Gaban wani pink lush restaurant suka taaya haifa ta karbo masu take away na Italian food da grilled kafin su wuce, suna isa gida haifa tayi parking Har cikin penthouse din, sallama sukayi da amra kafin ta juya abunta, m5 dake biye dasu shima don tunda suka wuce spa yake binsu a baya ganin sun wuce hanyar gida yasa ya wuce inda zaije shima.

Baiyi gangancin kiran Amar ba don haka yabar alamarin tunda yasan wacece haifa a wajenta bayan wannan kuma yanda general ya bashi order akan safety dinta dole ya bi Duk wani sahu nata.

Washe gari haka m5 ya kaita asibiti lokacin Tashi nayi tace mashi ya tafi zata biyo bayanshi, this time around bai mata maganar tambayar oga ba ya taaya saida suka fita kafin ya hi bayansu,wannan Karan ba spa din da sukaje suka koma ba wani peacefully vally suka je mai hade da park, ciye ciye babu wanda basu yi ba, they had so much fun sosai kafin su koma gida.

Cikin kwana biyun nan amra ta nemi damuwarta ta rasa, don wannan treat din da haifa ke bata ba karamin kwantar mata da hankali yayi ba, gashi ta dafe da bata shawarwari akan ta kwantar da hankalinta tayi kokari ta karasa housemanship Dinta ta karbi certificate dinta, don yanxu anzo yabar da ta yanke shawarar gwara ta koma kawai Duk abunda ta tarar achan zata rungume shi ita da kannenta ba kamar lokacin da taci burin kawosu ba don zaman nan yafi na chan din, kuma anan zata dogara da aiki mai kyau don suna gama housemanship yawanci asibitocin nan uae Idan ka samu certificate mai kyau Har competition akeyi wajen daukan sabbin upcoming doctors ko nurses because they belief the younger ones are better.

Kano state Nigeria….

Ranar an kwana da bala’i a cikin gidan alhaji mustapha,rasuwar hilma ba karamin tayar da hankali hajiya labiba tayi ba don mutuwa ce tayi sanadiyar cikin da aka sameshi ta haramtacciyar hanya, abun kunyar da suke rufewa sai gashi duniya ta shida hakan, gashi yanxu komai ya tsaya ma alhaji Mustapha daman Duk kudaden da yake samu haramtattu ne kuma akan yayanshi suke salwanta kamar gadon su amra wanda ya kwace shi kirikir, karshe dai bayan ya sanya HAYA gidan yazo ya sayar dashi inda ko rabin kudin filin gidan kafin a gine shi bai samu ba, karshe kudin Ma ya tafi a banza, kasuwan ci sun tsaya mashi chak,babu gaba babu baya, yaya Duk sun tagayyara, ahankali ahankali asirin kowa yake futowa, da farko babu irin cin mugunci da Haj labiba bata sha ba wajen shi alhajin da Haj kareema harma da duniya don ko futa ta gagaresu ita da diyarta lokacin da ciki ya bullo wanda dukda yarinya tace ga wanda ya mata babu wanda ya yarda harma da daddy din wato mahaifinta,Haj kareema dai cewa tayi za ayi Ma danta Sharri, kowa dai da kashinsa a mazaunanta sa inji labiba don har lokacin babu labarin Ibrahim din, dukda suna boyewa sai daga baya haj labiba ta dau alkwarin daukan fansa, mutuwar hilma kuwa ta Kara

hargitsa labiba wanda yasa ta daura damarar yanda zatayi ta rama,da taimakon Rita ta gano khady bugaggiyar yar kwaya ce, don harya soma taba kanta sannan zubda ciki babu wanda batayi ba, Haj kareema kuwa tasan halin da harta ke cikin na shaye shayen da take yi saidai boyewa takeyi da cewa shedanu ne suka shigeta, alokacin ne cikin hilma ya ya futo kafin ta rasu, babu irin cin mutunci da kareema batayi Ma labiba ba akan wannan dukda tasan itama yarta hamshakiyar kanta ce, sannu a hankali ta tsaya akan  khady harta samu natsuwa ta daina shaye shaye, cikin shekarar wani hamshakin mai kudi da suna ya futo neman aurenta wannan abun yayi ma kareema dadi ganin inda yarta zata tafi, Duk wannan abubuwan akan idanun labiba da tayi sanyi agaban su saidai basu san tarko take nada masu ba, ana sauran sati biki labiba ta tarwatsa auren ta hanyar fidda hotunan khady da tsiraicinta tana maye, wanda ta samu hakan ne ta hannun Rita, take wanda zai aure ta yace ya fasa, don bazai auro wadda ta gama lalace wa ba, ya barsu da Allah da sukayi mashi karyar cewa kamilalliya ce Har yayi niyar aurenta,sanadiyar wannan yasa aka koma gidan jiya, khady ta dawo da shaye shaye ta har yakaiga an kaita dawanau don ya taba kanta, Haj kareema tayi kuka kamar ranta saidai bata kawo cewa Duk wannan sharrin labiba ne ba, akwana a Tashi case din asma shima ya futo wanda ita kuma taje club da take satar hanya tana zuwa da saurayinta, aranar Ma haka ta fito wajen karfe goma ta saci hanya ta futa tare da saurayinta saida sukaje club suka shawu kafin su fito a make wajen karfe biyar na Safiya don su koma gida,haka suka hau hanya ita abuge shima saurayin abuge, suna hawa banban titi saurayin ya dauke wuta,don steering kubce mashi yayi nan take motar ta fara juyawa har ta gangara ta buge wata katuwar bushiya, Allah ya taimaka Akwai tsirarrun mutane da suka fito daga masallaci, nan take mutane suka fara ta ruwa don Har motar ta fara hayaki, dakyar aka futo dasu don saurayi Ma ya rigada ya mutu cikin maye wa’iyazubillah, itama Har an fidda rai aka hango yatsunta na motsi kafin aka ita asibiti, Ana kaita asibiti aka kai cigiya gidan radio, Harda police station don asibitin Ma anki attending dinta Sai taimakon gaggawa da aka bata, koda ta farka azaba ta sata kwala ihu agigice don ta samu karaya a duka kafafunta biyu,

26 / 94