barcin baby ne ke sakaki daughter” ta karashe tana dariya,
da mamaki amra ke kallonta gaba daya kanta ya kulle Bakinta na karkarwa tace “ammah wani baby kuma? Ina baby yake?”
“Listen to me daughter, kin kusa zama uwa, Allah ya amsa addua ta, you’re pregnant” a furgice amra ta daga ta kalli ammah da mamaki, gaba daga kana ganinta kasan she’s shocked, “yes dear you’re pregnant, tun daga ranar da kika shigo gidanan naga hakan a tare dake saidai ban tabbatar ba na barma Allah komai,”
Kasa motsawa amra tayi sai binta take da idanu haka zalika ta kasa cewa komai, riko hannunta ammah ta sakeyi tace “listen to me dear, karkiji komai kinji ko, wannan kyauta ce daga Allah nasan zaki shiga rudu,Akwai wani abu daban fada maki ba acahn baya, tabbas Muhammad baya haihuwa kamar yanda na fada maki abaya don dalilin aurenki da yayi was his last chance of having his own blood line, nasan kunje asibiti ko? Kuma an gwadaki babu, wannan jarabawa ce daga Allah kuma hakan na Kara tabbatar mana da allah baya barci kuma mai yanda yaso ne kuma yana bayarwa a lokacin daya ga dama kuma ya hana a lokacin daya ga dama, zamuje asibiti gobe don muga how far you’ve gone don naga baby bump din namu mai boye wa ne,saidai bana son Muhammad yasan da wannan zancen kinji ko sai mun Kara tabbatarwa kema dole ne yasa na fada maki don ya kamata ki sani.”
Girgiza mata kai amra tayi kamar wata doluwa, ta kasa daina kallon bakin ammah dake furta mata tana da ciki cikinma na ya muhammad don sai yanxu kwakwalwarta ta fara processing.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 142
Update
Unedited
Mikewa ammah tayi fuskanta dauke da lausansan murmushi dake nuna tana cikin farin ciki sosai “Akwai abunda kikeson ci?”
Sauke kanta tayi qasa tana mai jin kunyar ammah ayanxu sosai, “ah ah”
“Daughter ki ajiye kunyan nan fah, yanxu ba lokacin kunya bane ba kinji ko, ba abun jin kunya bane abun farin ciki ne”
Da kyar ta iya bude Bakinta ta amsa ammah “tohm ammah”
“Bari na barki ki shirya saiki sauko qasan ko”
Ammah na kaiwa nan ta fuce daga cikin dakin fuskanta dauke da murmushi, tana gab sauka qasa saiga Amar ya fito daga part dinta Ganin bata ciki, kallonshi tayi fuskanta dauke da murmushi da fara’a, “son Har ka Tashi”
“Yes ammah na shiga naga bakya nan” ya amsata anatse yana me karasowa inda take “naje wajen daughter ne” ta amsashi kai tsaye tana murmushin jin dadi
“Good Morning, ya karfin jiki” ya fada fuskanshi asaka yana kokarin maida wayar hannunshi cikin aljihun gajeran wandon jikinshi don daga gym yake., “morning son, jiki kam Ay ya gama sauqi Alhamdulillah, muje ciki daman inason muyi wata magana”,
Cikin part dinta suka wuce Har zuwa sitting room dinta, zama tayi akan doguwar 3 seater kafin tayi mashi nuni da gefenta akan yazo ya zauna, takowa yayi ya zauna gefenta ya tattara duka natsuwarshi gareta, “yaushe zaka koma uae?”
Dan shuru yayi yana nazari kafin ya soma magana “Duk ayyukan da zanyi na gama yinsu, anytime from now za a iya nemana a office don na rigada na gama tura duka report din ayyukan danayi anan so anytime from now Zan koma”
Nunfasawa ammah tayi, jikinta yayi sanyi sosai, harga Allah tafison ya hakura da aykin na chan don ya samu ya kuka da dukiyarsa, saidai bazata taba hanashi yin abunda yafi so ba don wannan burin shi tun yana karami na zama babban soja, don haka ta dan nunfasa tace “matar Ka fah?”
Sunkuyar da kanshi yayi yama rasa abunda zai ce, “ya zakayi da ita? Zaka tafi da ita ne?”
Ammah ta sake tambayarshi
“Zan barta anan, Zan dunga zuwa every month”
Shuru ammah tayi kafin tace “okay!”
Da mamaki ya dago din baiyi tsammanin zata amince ba cikin sauqi don yanda yaga gana ji da ita cikin kwanakin nan ko shi bata bashi attention kamar haka,
“Inason Ka gyara gidan Ka na larrics, a refurnishing din gidan”
Ba tare da ya tambayi dalili ba yace “Insha Allah!!” Dukda yasan dalilin hakan.
“Allah yayi albarka ya Kara arziki da lafiya,” ammah ta sake fada tana murmushi
“Ameen” ya amsa ta anatse cikin kamewa, mikewa yayi tsaye ya nufi hanyar futa “Zan dan futa Zan kai dare”
“Allah ya kiyaye, yauwa kaje Ka duba daughter bata jin dadi”
Anatse ya amsa ta “Okay”
Yana futa ammah ta mike tana hamdala ta wuce bathroom.
Tun bayan fitan ammah amra ta kasa mikewa tana nan zaune, lost in her thoughts completely, tunanin abun takeyi kamar a mafarki, maganganun ammah sun tsaya mata sosai, “I’m pregnant???” Ta tambayi kanta in a confusing way, samun kanta tayi da taba tummy dinta dake a shafe kamar babu komi, dan matsawa tayi kadan taji tauri, sai alokacin ta tabbatar da wannan ma yana cikin changes din datake gani a tattare da ita cikin kwanaki,dan matsawan nan da tayi taji abu nayin zillo a cikinta, a rude ta miqe tsaye cikin firgici, is not like bata san komai
Game da ciki ba saidai Har Yanxu ta kasa yarda da abunda ammah ta fada mata, tabbas sunje asibiti kuma doctor ya tabbatar bata da ciki, Toh ya haka kenan? Boye wa cikin yayi komenene? Gaba daya ta gama daburcewa she’s so confused, tana nan tsaye tana kallon cikinta Amar yayi knocking harya shugo dakin kai tsaye bata sani ba, tundaga bakin kofa ya tsaya ya kura mata idanu, towel ne kawai a jikinta sai gashi ta data baza a kafadarta, kallonta yayi daga sama zuwa kasa, ta dan rame kadan a fuskanta zuwa wuyanta, saidai kwata kwata ranar batayi affecting structure dinta ba da dirinta, idanunshi ne ya sauka akan inda yake kallo, bai gane dalilinta na kallon cikin nata ba don haka ya soma takowa Har inda take, ahankali ta soma jin daddadan turarenshi na shiga hancinta, da sauri ta dago idanunta ta sauke a cikin nashi dake yi kyalli, zuba mashi idanu tayi ta kasa daukewa don yau kusan sati guda kenan rabonta dashi, ya dan chanza ba kamar lokacin da suke jigilar zuwa asibiti ba, ya Kara kyau da kwarjini, bata ankare ba ganshi a gabanta ya zuba hannayenshi cikin aljihun wandonshi, Gyaran murya yayi ya dan kauda kanshi gefe “meke damunki?”
Ba zato ba tsammani taji tambayar nashi, gabanta ne yadan fadi Tayi saurin kauda zancen ta hanyar cewa “Ina kwana”
“Morning how are you feeling?” Ya tambayeta daga nan tsaye ya kame
“Alhamdulillah da sauqi” ta bashi amsa
Sake tambayarta yayi fuskanshi na nan yanda take a kame “meke damunki?”
Saurin sauke kanta kasa tayi tana jin yanda kirjinta ke yin lugude, pat pat, Bakinta na karkarwa ta soma magana “ciwon kai da zazzabi”
Juyawa yayi ya nufi hanyar fuce “get ready muje asibiti”
Cikin sauri ta katse shi tunawa da maganar ammah “noo basai naje asibiti ba, ammah ta bani magani I’m okay now”
Ba tare da ya damu ba yace “okay”
Yana kaiwa nan ya fuce daga dakin, saurin dafe kirjinta tayi ta zauna saboda wani jiri jiri daya soma dibanta, saida ta dauka kusan minti ashirin a zaune saiga salima ta shugo da tray a hannu da ammah ta aikota dashi don tasan amra ba lallai ta sauko ba saboda yanayin jikinta, plates da bowl biyu ne akan tray din daya pepper soup din gizzard da liver ne a ciki sai kuma fruits da ammah tasa salima ta yanka mata,
Da sallama salima ta shigo “oh yau ashe za ayi ruwan sama da kankara kin Tashi da wuri adda Wai, nikam adda Anya wannna barcin naki na lafiya ne kuwa? Kodai zamuje asibiti”
Banza amra tayi mata don ba surutun ta ne agabanta ba yanxu, confusion din dake kanta ma ya isheta don gaba daya ta kasa gane yanda akayi ciki ya zauna a jikinta bayan doctor yace babu shi.
Ajiye tray din salima tayi a gefenta tace “gashi ammah tace na kawo maki, wannan special treatment dun da ammah ke baki yana bani mamaki” ta karashe tana kama habar Bakinta, dafe kai amra tayi ba tare da ta kalleta ba tace “dan Allah salima kije kawai, ni ciwon kai surutunki ke sani Wallahi, Ki tafi da wannan abun ma banason cin fruit kawai zaki barmin” ta karashe tana nuna mata plate din gizzard. Da mamaki salima ke kallonta, kafin ta tabe baki “uhm Toh shikenan,“
Daukan plate din salima tayi ta bar mata bowl din fruit ta fuce daga dakin tana mamakin yanda gaba daya amra ta sauya kamar ba ita ba.
Salima na futa ta janyo plate din fruit ta fara ci tana tunani harta cinye tass ba tare da saninta ba, gaba daya jin tayi tana son karasa don haka ta zari hijab dinta ta sauko kasan, yau kusan sati kenan rabonta da saukowa kasan kullum tana kunshe a daki, anatse take tafiya harta shugo kitchen din, ammah ce sai salima a tsaye suna Dora lunch, da mamaki duka suka juyo suka kalleta, ammah ce Tayi saurin cewa “shugo daughter ya kika tsaya”
Karasowa amra tayi kanta a kasa “ammah ke da kan a kitchen?”
“Ay naji sauqi sosai daughter, dole na sauko Kar ayki yayi ma anty salima yawa” dariya ammah tayi tana kallon salima, amra ma dan murmusawa tayi don ta gane dalilin kiranta da anty da tayi, kallon bowl din hannunta ammah tayi Ganin ta shanye tace “ Masha Allah, kina buqatan wani abun? Ko a sake yanka maki wani fruit din”
Girgiza mata kai amra tayi tace “Zan yanka”
“Ah ah bazaki yanka ba, kije ki kwanta ki huta, salima zata kawo maki yanxu”
Kallonsu kawai salima keyi tana kallon ikon Allah, tabe baki tayi ashagwabe tace “ni gaskia ammah wannan nuna kulawa da kikeyi ma adda yayi yawa Wallahi ni kwata kwata ba a yimin haka”
Dariya ammah tayi ta wuce gaban fridge ta zaro bunch of different fruits ta ajiye akan island “haba mutuniyar, bakiga addan taki bata jin dadi bane?”
Karban wukan da ammah ta dauko salima tayi tace “Bari na yanka bana son kina son wahala, Amma dai gaskia ammah nima adunga kula dani haka I’m jealous”
Rankwashi amra takai mata tare da hararta, da sauri ta kauce tana mata gwalo, dariya ammah ta dunga yi masu kafin ta tsagaita “oh Allah kuma kuna yin yar saqo da saquwa kenan, yanxu dai daughter ki wuce sama karki biye mata ta wahalar dake”
Sunkuyar dakai amra tayi cikin jin kunya tace “Toh ammah” kafin ta juya ta nufi hanyar futa daga kitchen din, kallonta ammah tayi harta fuce daga kitchen din kafin wani tunani yazo mata, “daughter!! Daughter!!! Zo”
Salima ce ta ajiye wuqar ta nufi hanyar futa kitchen ta tsaya daga bakin kofar tace “addaaa kizo ammah na kira” tana kaiwa nan ta juya cikin kitchen din ta cigaba da yankan fruits.
jiki a mace amra ta juyo don Har takai stairs, dan saukowan nan datayi da tsayuwar datayi gaba daya taji ta fara galabaicewa jikinta ya fara mutuwa, daman tana jin haka sai barci gaba daya tama manta da maganar ciki da ammah tayi mata akan shike sata barcin don yabi jikinta,
Da sallama ta sake shugowa kitchen din, ammah na ganinta ta soma magana anatse “sorry dear Har kin gaji ko? Ungo wannnan ki kaima Muhammad, na manta tun dazu ya buqaci akai mashi”
“Ah ah ban gajiba bari nakai mashi” amra ta amsata tana Karban mug din da ammah ke miqa mata tayi da yake turiri sosai kafin ta juya ta fuce daga Kitchen din, harta fuce ammah na kallonta tana karantar yanayin ta sosai saboda bayanin da zatayi ma doctor insunje asibiti akan yanayi ta, kana ganinta kasan she’s so excited, fara’ar fuskarta taqi yankewa kwata kwata, babu abunda take sai godiya ga Allah da kuma fatan abunda take tunani ya tabbata insunje asibiti dukda ta tabbatar da hakan a nata hasashen.
Anatse take tafiya harta shugo part dinshi, kamshin parlor ne ya bugeta don parlor ya dau sanyi sasai wanda taji lokaci guda cikinta ya hautsina, saurin toshe hancinta tayi ta wuce bedroom dinshi cikin sassarfa, tana bude kofar ta shige ta sauke wata nauyayyan ajiyar zuciya saboda kamshinsa daya bugeta wanda ya sata jin cikinta ya lafa, Har wani dadi taji ya ziyarceta aranta, tana bala’I son kamshin musamman a yanxu.
Bin dakin nashi tayi da kallo, it’s been long ta inda ta tako da kafarta ta shugo tun bayan last day din da suka dawo tare daga asibiti bayan yayi mata korar kare Inda tayi alqawarin bazata sake takowa ba tazo Inda yake harya daukota ya kawo ta, babu abunda ya sauya adakin, it’s still so clean kamar yanda yake, ko’ina fess fess gwanin ban shaawa, baya cikin dakin ta tako gefen bedside ta ajiye mashi mug din, saukan ruwa ta ji a kunnenta nan ta gane yana cikin toilet
kenan m, har zata fuce daga dakin ta dawo bakin gado ta zauna tana jiran fitowa shi dinta bashi sakon ammah, tana nan zaune Har kusan minti goma bai fito ba, ga wani irin barci dake fusgarta sosai, zungudawa tayi kadan tayi kwanciyarta nan take barci ya kwasheta anan kan gadonshi,ba tare da sanin ta ba.
After like 10mins da kwanciyarta ya bude kofar bathroom, ya futo anatse kamar basarake, wani irin kamshi ne ke fita daga jikinshi mai kamshi dadi sosai at the same time ga tururin ruwan zafin da yayi wanka dashi, towel ne kawai a kugunshi, sai dan hand towel daya rike a hannunshi yana goge qirjinshi daya mummurde sosai, kwata kwata bai Lura da ita ba ya wuce gaban dresser ya fara Yan shafe shafen shi cikin class kamar wani mace, shafa chan goga chan, saidaya gama kafin ya nufi gadonshi don yana son yadan kwanta kona 2 hours ne don baiyi barcin safe ba tun bayan sallar asuba daya dawo daga masjid ya wuce gym.
Gaban switch na dakin ya wuce ya kashe ya rage bedside lamb kawai, dakin yayi duhu sosai don da hadari aka Tashi a garin daman abuja badai ruwan sama ba kullum cikin hadari ake ko ruwa haka garin zai hade sosai.
Juyowa yayi ya tako bakin gadon idanunshi a lumshe yana hamma.
Chak ya tsaya don saura kiris ya afka kan gadon saboda baiyi expecting dinta ba, don Yama manta when last ta shugo dakinshi da kafafunta, da fuskanta ya fara cin karo, da mamaki yake kallon yanda take barci hankali kwance, samun kanshi yayi da kallon fuskanta, Har lokacin he’s surprised, ta kwanta ta tattare hijab dinta sama don harya harde mata wuyanta, kana Ganin ta kasan kwanciyar baiyi mata dadi ba but she’s sleeping peacefully kamar wadda tasha wani abu, shuru ya danyi yana mamakin wannan wani irin barci ne haka? Bai kawo komai aranshi ba don haka ya dan harde hannayenshi a kirjinshi ya soma magana “Aisha!!! Aisha!!””
Tsit kake ji kamar da kanshi yake magana, sai fidda nunfashi takeyi akai akai kamar wadda aka shake, ganin nunfashinta na sama sama still tana barci yasa ya matso inda take kwance, Bakinta ta soma bude tana blabbering, Har lokacin barci na idanunta don ta rufe idanun gam, wajen wuyanta ta kama jiki a mace ta fara Jan hijab din “wayyo mamii.. wu..ya..na”
Ahankali take furtawa don kwata kwata bai ji abunda take cewa ba saidai bin Bakinta yayi da kallo harya gane abunda yake cewa, cikin hanzari ya karaso bakin gadon ya sake kiranta “Aisha aisha!!” Inaaa, bata jin shi, barcin ta kawai take tana surutai, Ganin tana kokari janye hijab din daga wuyanta ya gane damunta yake don haka ya zura hannunshi cikin hijab din da hannu daya Dayan kuma ya tallabo kanta gaba daya ya janye hijab din daga jikinta, yana cire wa ya sauke mata kanta ahanakli kan gado ya zame hijab din kasa, wani irin nunfashi ta sauke alamun samun relieve kafin ta gyara kwanciyarta tayi rub da ciki, dan yatsine baki tayi ta juya gefe saboda ta takura cikinta, Duk wannan juye juyen
da takeyi akan idanunshi, gaba daya mamakin yanayin ta ya gama dabaibayeshi, wannan barcin baba lafiya bane ya fada aranshi, karshe dai tabe baki yayi ya maida idanunshi kan fuskanta, wani siririn hawaye ne ke sauko a fuskanta kamar tana mafarki, lokaci guda kuma yaji yana tausayin ta babu dalili, tana kashe mashi zuciya sosai ba tare da saninshi ba, yanxu ya gama yarda ya bata special gurbi a zuciyarshi, tayi mashi abunda bazai manta da ita ba, yanda ta nuna jajirce wajen ceto mahaifiyarshi bazai taba mantawa da wannan ba, saidai Har yanxu he’s struggling akan karbanta a matsayin matar shi,he just feel like idan ya amince kamar ya cuceta ne, ko kuma he’s being selfish saboda baya haihuwa,cause she’s so young, tana da rayuwa anan gaba, idan ta zauna dashi a haka she will miserable ba kowa ne zai iya zaman auren da babu haihuwa ba,dalilin da yasa yaqi amincewa kenan da auren shiyasa tun farko da ya tabbatar babu cikinshi a jikinsa yaso ya saketa taje tayi aurenta tunda ita bata da matsalar komai.
Saurin dafe kanshi yayi yana tausaya mata haka kawai, yayi kokarin ya nunama ammmah manufarshi na qin karban auren ta amma ta kasa gane wa, saurin dafe kanshi yayi yana jin wani irin, dago da kanshi yayi da jajayen idanunshi ya kalleta kamar wani mai jin tsoro haka ya miqa hannayenshi ya fara gyara mata kwanciyanta zuwa jikinshi, ahankali yake matso da ita kamar kwai don baya son ta Tashi kafin ya janyo masu duvet ya rufa masu, tana jin kamshinsa na shiga hancinta cikin barci kuwa ta damkoshi sosai “uhm ina….shon..wannan..” ta furta tana turo dan bakinta ahankali kamar mai rada cikin barcinta.
Akan idanunshi tayi haka wanda yasashi Saurin runtse idanunshi yanajin yanayin shi na sauyawa, gaba daya komai ya tsaya mashi chak, baiyi wata wata ba yakai bakinshi kan