Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   22 / 94

63K to 66K   out of 279.4K words

din health team, saida akazo tafiya da amra yace su dakata, nuni ya masu da su sakata a helicopter sun da yake, haka suka gurgura emergency bed din zuwa cikin helicopter din suka saka ta tare da likitoci biyu daga cikin health team, shi dai asad bai bisu ba ya tsaya tukunna saboda motocin da zasu zo su dauki mutanen wajen.

Tunda ya suka Tashi sama bai sake kallon ko inda take ba, saboda yanda yake jin wani zafi ganin yanayin da take ciki,tunanin yanda zaiyi dealing da ita yake yanda bazata sake tunanin taka umarnin daya bata ba, kamar wanda aka tsungula ya zaro wayanshi ya soma kira, yana gamawa ya kashe ya kira landline din gidan shi na larrics, Nadine dake zaune hankali tashe tayi picking call din kafin ta saka a kunnenta, “go and bring her few clothes and pack your belongings,” damm gabanta ya fadi da jin abunda yace bata gama tunani ba ya cigaba, “driver will be waiting for you outside, come along with your passport”

Yana kaiwa nan ya kashe wayar, da sauri ta miqe ta tattara kayanta Harda kukanta don tunaninta korar ta yayi saidai tayi mamakin jin yace driver na jiranta a waje, agurguje ta fito da yar jakar kayanta ta shige motar driver ya jasu,

Agaban  headquarters driver ya dire ta, cikin Yan mintuna qalilan helicopter su ya dira a field din headquarters, ahankali ya soma saukowa kafin a sauko da amra wadda Har lokacin bata dawo hayyacinta ba, dan asibitin dake cikin headquarters aka wuce da ita aka cire mata kayan zuwa wasu wanda Nadine ta taho dashi kafin a mata allura don zuciyarta ta samu relive din shock din data shiga.

Takowa Nadine tayi Har gaban gadon da aka kwantar da ita ta kare mata kallo, fuskarta tayi fayau Har wani yar rama tayi, dukda bata san wani hali take ciki ba tausayinta ya gama dabaibaiye zuciyarta take tayi alqawarin koma menene damuwarta zata taimaka mata.

Manyan ambulance ne suka shigo cikin headquarter aciki aka saka ta tare da Nadine, kowa dake cikin headquarters saida ya shaida qila yar governor ce aka ceto ko kuma yar wani minister din, baibi motar ambulance ba ya shige cikin Tashi ya figi motar, wayarshi dake Kara yayi saurin picking yana dauka ya saka a hands free, daga chan baba garen aka soma magana “sir the visa is ready, and the private jet also”

“Okay” kawai yace ya kashe wayan kafin ya Kara ma motarshi speed sosai.

Agurguje dai saiga amra a airport ita da Nadine, dayake ya rigada yayi proceeding komai in less than an hour suna zuwa airports aka wuce dasu wajen private jet Har aka shige da amra wanda ke kwance kamar gawa, kallon Nadine yayi don shi bazai bisu ba tukunna saiya gama abunda ya kawo shi

“When you arrive my personal guard will be there to pick you up,”

Kallon agogon shi yayi ya juya harzai tafi ya dawo yace “take care of her”

Yana kaiwa nan ya fuce suna suka hau jirgin, abun mamaki Nadine na ganin jirgin tana an rubuta Taura baro baro, tasan sir yana bearing sunan saidai bata kawo ko nashi bane ko ba nashi bane saidai taga abunda ake kira da luxury lokacin da ta shiga cikin jet din gashi sak nan nan ake da su.

Bangaren Amar kuwa wata zuciyar nashi na mashi fadan yin hakan don yasan zai sha wahala idan bata kusa don ya fara sabama kanshi da abubuwan da Allah ya albarkaceta dashi, saidai kuma yana ganin wannan opportunity ne da zai tabbatar idan Har cikinshi ya shiga jikinta ko bai shiga ba bayan wannan plans dinshi da yake akanta na nan yanda ya tsara tun farko kafin ta dawo Nigeria.

Gida ya tafi direct don wani irin ciwon kai ne ya addabeshi sosai, yana zuwa ya wuce dakinshi ya watsa ruwa ya kwanta don ya samu ya danyi barci kozai ji saukin abunda yake ji, saidai kuma barcin gaba daya ya kaurace masa, tunanin da baya son yin ya tsaya mashi arai, zuciyar shi nayi mashi wani irin nauyi ganinta da yayi a wannan yanayi, runtse idanunshi yayi sosai aranshi yace “why won’t you get out my mind”

Tsaki ya danyi ya sake juyawa tare da kure ac din dakin ya janyo duvet Har ya samu barci ya nasarar daukanshi.

Dubai United Arab Emirates Uae …..

Jet dinsu na sauka a uae international airport akayi masu Duk wani arrangement na shiga kasar ba tare da sun motsa ba, Nadine dai tana ganin rayuwar manya, don gaba daya ta gama tsurewa, Duk rayuwar a Cameroon bata taba shiga jet ba, amra dai tana daga chan wani bangare na cikin jet din da masu bata kulawa don Har lokacin bata farfado ba, minti bayar da landing din wata ambulance din ta karaso, m5 ne ya shigo Har cikin jet din ya jagoranci Nadine din suka sauka

kasa zuwa motar dake harabar filin jirgin, iska ce mai dadi ke kadawa sosai. Ahankali aka saka amra cikin ambulance din itakuma Nadine ta shiga wata haddaiyar motar daban wanda m5 yazo da ita suka wuce gida tare da special doctor din Amar don shi zai kula da lafiyar amra.

Tafiyar minti talatin suka iso tafkeken penthouse din general Amar,inda tundaga shigarsu Nadine ta soma bama idanunta hakkinsa, tunda take harkar aiki wayo house keeping bata taba ganin gida makamancin wannan ba, Har m5 yayi parking bataji ba don ta Lula tunani, saida ya bude mata kofa kafin ta dawo hayyacinta ta fito daga cikin motar, already motar data shugo da amra tayi parking itama Har an sauko da ita daga cikin motar, m5 ne yayi gaba suka bishi abaya dukkansu, doorbell ya dannan pablo dake expecting dinsu yayi saurin budewa kafin su saka kai cikin main parlor din, Nadine dai ta zama kamar jaka don da kyar ta shiga cikin gidan, direct wurin suka wuce kafin m5 ya Danna floor 2 don nan ne masaukin su, fadar haduwa floor dinnan Ma bata lokaci ne don dakuna ne ajere Sai babban cozy sitting room tamkeke da yasha kayan duniya na gani na fada, babban dakin aka wuce da amra nan Ma ba a cewa komai Sai Masha Allah don an zuba duniya ba kadan ba,  akan wani hadadden English bed aka kwantar da ita da taimakon nurse din dake tare da doctor din kafin su fara dubata don Har lokacin barci take sakamakon allurar da akayi mata.

A Last floor m5 ya nunama Nadine dakinta wanda yaci uwar na wanda aka bata a larrics don itama harda dan coffee table and chairs aka aje mata da tv Sai tamkeken bed dinta..

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 118

Update!!!

18/05/2023

Unedited

Aranar dai Nadine taga abunda ake kira da duniya, don tana daga kwance aka kawo mata abunci Har bedroom dinta kamar basarakiya, daman tafiyar yamma sukayi so sun iso wajen karfe sha daya na dare don haka tana cin abunci tayi kwanciyarta don m5 ya shaida babu wanda zaije wajen madam for now sai likitan ta da nurse saboda tana buqatar hutu saboda zuciyarta ta takusa bugawa.

Waje gari haka Nadine ta Tashi da sassafe kamar yanda ta saba achan, ta fito damin tambayar ayyukanta nan m5 ya shaida mata ba aikin datazo yi kenan ba, aikin ta shine kula da madam kawai wanda hakan yayi mata dadi sosai don haka ta koma daki aka kawo mata lafiyayyan breakfast taci tayi nak ta koma barcinta.

Bangaren Amar Duk wani update saida m5 ya kirashi ya fada mashi daga kan progress din lafiyar amra zuwa isowar su babu abunda bai fada mashi ba don daman hakan ya buqata, don yasashi ya dunga updating nashi Duk wani movement dinta sannan ya bada kwakwaran rules akan kula da sa ido akanta.

Kullum doctor ke zuwa duba lafiyar ta while nurse ke zama da ita kullum tana monitoring Duk wani health care dinta da medication dukda bata farka ba dalilin maganin da aka sanya mata cikin drip saboda zuciyar ta ta samu hutu.

After 2days…

Kwana biyu kenan da isowarsu Nadine uae, tun bayan ranar da suka iso babu wanda ke shiga wajen amra don har lokaci bata farka ba, doctor na kula da ita sosai da nurse din dake kwana da ita.

Ahankali ta soma bude idanunta da suka dan qanqance sukayi jaa, maida idanun nata tayi ta rufe don sunyi mata nauyi sosai kamar an daura mata dutse, budesu ta sakeyi for the second time don Har wani dishi dishi take gani, nurse dake tsaye a gefenta tana gyara mata cannula dake dauke da drip din da aka cire mata tun Daren jiya ta waigo ganin hannunta na motsawa, da sauri ta matso da stethoscope dinta ta fara dubata don daman suna expecting tashinta saboda allurar ya sake ta, murmushi matar tayi mata ganin yanda yake kallonta kamar yau ne ta fara bude idanunta a duniya, Bakinta yayi mata nauyi sosai haka zalika jikinta saidai fuskanta na nuni da mamaki take, ko she’s confuse, shafa goshin ta nurse din tayi kafin ta soma magana ahankali kamar mai rada “hello good morning how are you feeling today?”

Shuru amra tayi ta Kasa cewa komai don Bakinta yayi mata nauyi sosai, ganin hakan yasa nurse din ta tabbatar da she’s weak sosai don haka ta Kara tambayarta to be sure she’s in her senses 

“Can you blink your eyes?”

Ahankali tayi blinking idanunta, 

Smiling nurse din tayi tace “very good, let me help you freshen up okay?”

Dago bed din tayi yanda zata danji dadin saukowa don dole jikinta ya sage sosai, da taimakon matar ta mike zaune hawaye na zubowa daga kunchinta kallonta nurse din tayi tace “sorry ma’am, it’s just for the mean time okay?”

Yanda take mata magana ya nuna she’s so nice and calm, har toilet matar ta taimaka Ma amra wadda gaba daya kanta ya gama kulle wa don bata gane Ina ne ba, sannan nurse din ma kamar balarabiya don fara ce tass, tana son tambayarta Ina take saidai ta Kasa saboda yanda bakinta ya mata nauyi sosai Har throat dinta Ma, da taimakon matar ta samu tayi wanka wanda ya taimaka sosai taji dan kuzari sosai a jikinta saidai Har lokacin idanunta fal yake da

hawaye suna fitowa matar ta taimaka mata ta zauna akan gado dukda zaman Ma ya gaagara saboda kwanciyar da tayi na kusan kwana uku ba tare da juyawa ko motsawa ba don jikin yayi tsami sosai, ganin yanda take yatsine fuska yasa matar cewa “sorry okay,!!!!it’s going to be fine” ahankli ta bude Bakinta tace “tha…nk…yo..u”

Yanda take maganr Ma kamar yar koyo don haka matar ta gane cewa Duk effect din allurar ne, agurguje ta bude wajen closet ta dauko mata doguwar Riga cikin kayan da m5 ya sayo don buqatun su, don aranar da zasu taho general ya kirashi akan ya shirya Duk wani abubuwan da yasan zata buqata ya sayo daga kan kaya takalma jaka, skincare, perfumes, jewelries kayan barci babu abunda bai sayo ba.

 

Watery soup nurse din tasa a kawo mata daga kitchen in less than 20 mins pablo da new help din da aka kawo ta taimaka mashi suka kammala aka kawo mata, har lokacin babu wanda ke zuwa dakin da take, nurse since ta taimaka ta bata white soup din, kadan ta sha kafin ta kauda kanta, babu yanda nurse din batayi akan ta Kara ko kadan ne ta nuna bata so don haka ta kyaleta kawai ta ballo medication ta bata, dan resting bayanta, “Ina ne nan? Waya kawo ni nan?”

Tambayar da take ma kanta kenan, take abubuwan da suka faru suka dawo mata, saurin runtse idanunta tayi nunfashinta nayi sama sama, nurse din na ganin haka tayi saurin riko hannunta tace “hey look at me, calm down don’t think about it okay”

Da sauri ta bude idanunta tana sauke nauyayyan nunfashi don gaba daya ji tayi zuciyarta na Harbawa sosai, runtse idanunta tayi ta bude Bakinta tace “why…I’m ..I..here?”

“Where is this place? “

Cikin tsoron take tambayar don haka nurse din tayi saurin bata amsa don dole sai Ana bata amsa saboda confusion din datake neman shiga Ma zai iya haifar mata da problem.

“Ma’am you’re home, and safe, I’m nurse jalila from uae specialist hospital”

Da sauri ta bude idanunta har tana dagowa  zaune da kyau, “can…you rep..eat”

Maimaitawa nurse din tayi take hankalin amra ya sake Tashi badai uae taji a kunenta ba?

Bata gama tunanin ba saiga m5 ya shigo bayan yayi knocking, saurin dago kanta tayi ta kalleshi tare da kura mashi idanu sosai alamun mamaki sosai da tayi na ganinshi “you!!!!!!”

Ta fada da dan karfi, sunkuyar da kanshi yayi yace “good morning ma’am”

Bata tsaya amsa gaisuwar sa ba tace “what is this place? Where I’m I?”

Kallon ta yadanyi kafin ya kauda kanshi gefe yace “you have to calm down ma’am,”

Da dan karfi ta daga muryarta tace “calm down?, you’re asking me to calm down?”

Nan take idanunta sukayi jaa sosai Har jijiyoyin kanta na firfitowa sosai, da sauri ya fuce daga dakin ya kira doctor, Nadine dake zaune a Kasa ta hango saukowanshi daga stairs tayi saurin zuwa wajen shi don tana son taji yanayin jikin amra, tana zuwa gabanshi tace “good morning sir”

“Morning” yayi saurin amsa ta tare da cewa “she’s awake you can go in”

Da sauri ta fara hawa stairs don, tana nishi da baki haka ta hau floor din da amra ke ciki, saida tayi knocking kafin tasa kai zuwa ciki, amra dake neman burkicewa tana ganin Nadine tayi shuru tare da cewa “Nadine kece?”

Da sauri Nadine ta karaso ganin yanayin data shiga ta karasa kusa da ita , tana ganinta kuwa ta rungumeta tsam tana hawaye, “Nadine waya kawo ni nan? Meysa basu barni na mutu ba, I prefer to just die than to stay like this”

Dagota Nadine tayi ta share mata hawayen dake ga gari wa daga fuskanta tace “ma’am you have to calm down, everything will be okay,you’re safe now, kamata yayi ki godema Allah da ya baki second chance bawai kiyi fatan mutuwa ba”

Shuru ta danyi ta fara sauke ajiyar zuciya, doctor ne ya shigo cikin dakin kafin ya soma dubata, wasu alluran ya sake bata wanda zai sata barci, nan take barci ya dauketa, ganin hakan yasa doctor ya kalli m5 yace “she’s still in shock, but she’s stable now, there will be no need for the nurse assistance anymore”

Futa doctor yayi m5 yabi bayanshi, saida nurse jalila tayi ma Nadine bayanin medication dinta kafin ta masu sallama.

Wunin ranar Nadine na tare da ita don ko motsawa batayi ba, Sai wajen karfe takwas ta farka, ganin Nadine a kusa ya sa ta danji sanyi da fargaba da take son gaba daya gani take kamar mafarki take yi Harda abunda ya faru.

Da taimakon Nadine ta sake yin wani wanka ta sauya kaya don yanxu taji dadin jikinta sosai, abunci Ma ta danyi babu laifi,tana maqale da nadine taqi barinta ta futa kwata kwata, ganin haka yasa nadine ta zauna da ita, tunda ta zauna ta doka uban tagumi take hawaye, kallonta nadine tayi tace “ma ya kamar ki daina kukan nan”

Kallon nadine tayi jin abunda ta fada tayi saurin cewa “waya kawo mu nan?”

Shuru Nadine tayi tana nazari kafin tace

“Sir ne”

Saurin runtse idanunta tayi jin yanda taji kamar an tsira mata kibiya a zuciyarta, ita kadai yasan abunda yake ji a ranta, bata nayi tunanin koma waye yayi saving dinta ba kawai dai ranta yana mata quna sosai jin cewa shine ya maidota, Toh ma waye zai maidotan in bashi ba, ta Kasa gane dalilinshi na qin freeing dinta, wani irin tsanarshi yake ji na yawo a ranta, ne yake so ne a wajenta tabbas tasan ba haka kawai yaqi rabuwa da ita ba dan jin tayi da tunanin da take kafin tayi saurin bude Bakinta tace “my body” da sauri Nadine ta kalleta don gani take kamar ta fara zaucewa 

Tunani ta farayi, Duk wani abu da tasan zai sashi qin rabuwa da ita ta duba taga babu sai jikinta, so that means jikinta yake so kuma yake sha’awa kenan, take shaidan ya dinga ingiza abun a cikin ranta.

Washe gari taji sauqi sosai saidai babu inda ta fito, Nadine ma na tare da ita tana tausasa ta don ta maida kuka kamar waqa,misalin karfe biyu suna zaune aka kawo masu lunch ita da Nadine, yanda aka fara jerawa a sitting room dinta zaka dauka yar wani hamshakin ce zata ci abunci, different varieties of food aka jera a dining din, m5 ne da kanshi yayi masu knocking kafin nadine ta fito, ledoji biyu ya miqa mata yace “ga wannan ki bama madam, wannan kuma naki ne”

Ko ba a fada ba tasan daga inda sakon yake don haka tayi mashi godiya ta koma dakin wajen amra.

“Ma gashi”

Mika mata ledan tayi ta dago kanta kafin tace “daga Ina kenan?”

“Sir ne yace a baki”

“Ki maida baran karba ba”

Kallonta Nadine tayi da kyau, babu komi a fuskanta sai kuruciya, murmushi kawai Nadine tayi ta aje mata ledan a gefen gado kafin tace “lunch is ready ma”

Adan fusace ta kalli Nadine tace “I’m full”

Sarai Nadine tasan cewa bataci wani abun kirkiba lokacin da aka kawo breakfast, futa tayi daga dakin ta Debo mata abunci daga dining din nan parlor nata na saman kafin dawo ta aje mata kan luxuriou stools don da akayi decorating dakin dashi, kallonta tayi da kyau tace “ma’am I will like to advice you, Duk abunda ke damunki nasan zakiso ki samu solution to the problem”

Dagowa amra tayi ta kalleta fuskanta harta fara kawo ruwa,

“Karki bari abunda ke damunki ya bata maki rayuwanki, be strong and brave that’s how you’ll overcome every problem”

Hawayen daya zubo mata ta goge ta kalli Nadine tace “thank you Nadine”

Bata ma tsaya ta kalli abuncin

22 / 94