Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   15 / 94

42K to 45K   out of 279.4K words

saidai Allah Allah take ya fuce daga dakin don gaba daya ji tayi nunfashinta baya fita a daidai dalilin zamanshi a dakin, don a yanxu ko Inuwa daya bataso suna yin sharing.

Haka ya karaci zamanshi bai sake ce mata komi ba itama bata ce mashi qala don karshe Ma kwanciyarta tayi ta juya mashi ba.

Kallon agogon hannunshi yayi ganin kusan karfe daya da rabi ya sa ya miqe tako gaban godon wanda yasa zuciya ta bugawa don turarenshi ne ya fara kai mata iso Sai takunshi zuwa gadon, hannunshi na zube cikin aljihu ya zuba Ma bayanta ido yasan ba barci take ba pretending kawai take yi don haka ya juya kawai ya fuce daga dakin yana futa kuwa ta juyo ta karema kofar kallo ta tabe bakinta ta mike zaune tare da  fashewa da wani matsanancin kuka sosai.

Ganin lokacin sallar yasata mikewa ta shige toilet ta wanke fuskanta ta dauro alwala ta fito tana dingisawa, rigar asibitin ta sake maidawa kafin ta zura hijab dinta ta zauna kan sallaya ta tada sallah don yanxu tsayuwa ma gagarar ta take yi Idan ta dade a tsaye.

Shima yana futowa ya wuce masallacin dake cikin asibitin yana idarwa ya futo ya shige motarshi  yabar wajen.

Karfe goma na dare Sai gashi ya sake dawowa, hannunshi dauke da ledoji na mishal medi mart, dakinta ya sake wucewa direct, this time around saida yayi knocking kafin ya bude bakinshi dauke da sallama, chan kasan maqoshi ta amsa dukda bata kalli gefenshi bama, takowa yayi har gabanta don tana zaune kan sallayan,

Tun kafin ma ya mata magana tace “ina wuni”

Bai amsata ba itama bata damuba don haka ta kauda kanta gefe,miqa mata wayanta da Nadine ta bashi daketa ringing wunin ranar yayi tare da ledojin daya shigo dasu yace “if you need anything, just call me”

Wayar da yake miqa mata kawai ta daga kanta ta amsa ba tare da ta karbi ledan Dayan hannunshi nashi ba ganin haka ya sashi ajewa gefenta ya fuce daga dakin, bin bayanshi tayi da harara da leader daya aje ta miqe tsaye ta dingisa zuwa gadon ta ba tare da ta kalli abunda ya aje matan ba don bata buqata koma menene indai daga gareshi ne.

Yana komawa gida ya wuce dakinsa direct ya watsa ruwa yabi lafiyar gado, gaba daya yana cikin wani yanayin mata misaltuwa, tun yana kokarin forcing kanshi yayi barci harya hakura, tunani ne ya mashi yawa sosai a ranshi ciki kuwa harda amra, yana jin kamar bai mata adalci ba, yana jin kamar yaso kanshi, da kyar wata zuciyar ta lallabashi ta nuna mashi cewa Ay yarjejeniya sukayi shida ita,kuka kina komai dai she’s his legal wife, “legal wife” yadan fada da karfi kafin yayi tsaki yace “why did you have to stoop so low akan yarinyar nan, what’s so special about her? Karka yaudari kanka”

Buga gadon yayi yana mai takaicin kanshi wata zuciyar na kara tunzura shi “that was the best feeling ever,warm and….”

Takaicin kanshi yake n tunanin da yakeyi, kokari sosai yake yi wajen hana zuciyarshi yin sake saken da takeyi

Washe gari Wednesday tun da sassafe ya fuce daga gidan don Kiran gaggawa da asad ya mashi, koda ya isa headquarters din  direct office din asad ya wuce kafin su gaisa ya fara mashi bayani “oga a binciken danayi, Akwai manyan maqudan kudade a cikin bankin alhaji Mustapha, sannan Duk wasu mugayen ayyuka da danshi ke yi da drug dealing din da yake yi da sanayyar sa, saboda lokacin da aka yi scandal dinshi shi ya da kansa yayi amfanida power dinshi ya toshe Duk wata kafa da zata saka a kama yaron, Mun samu wannan bayanan ne daga wata ma’ajiya mai karfi da wani tsohon gidan rahota da sukayi confirming, a yanda muka samu wasu bayanai sun nuna kashi tamanin 80% na kudinshi ba nashi bane na marayun da yake rikon su ne, saidai Har yanxu a binciken da mukayi bamu samu inda ake shige da fuce da kudin account din din nashi ba.

“Keep an eye on him, yanxu dai na samu wasu bayanai daga wajen hammam wanda yake tabbatar min da Akwai wata a kasa, Zan koma gidan jibi, Duk wani sauran bayanai zaka ji daga wajena”

“Oga Sai fa hakuri,Duk abunda ya faru mukaddarine daga Allah”

“Asad bazaka gane yanda nake ji bane, I just wish ba abunda nake zargi bane, it’s just a mistake”

Amraa…

Tun bayan fitarshi tayi kwanciyar ta, washe garin ranar ma da kanta ta gasa kanta sosai don ta samu kuzari sosai don koda doctor yazo da safe ya dubata ya shiada mata zasuyi discharging dinta.

Tana zaune tana cin breakfast da nurse ta kawo mata akayi knocking kofar, ba tare da tunanin komi ba tace come in, Nadine ce ta bude fuskanta dauke da murmushi ta karoso cikin dakin hannunta dauke da basket tace “good morning ma, ya jikin ki”

Fuskanta dauke da murmushi ta kalli Nadine tace “Nadine ashe kin warke yaushe kika dawo”

“2days ago ma’am,”

Cikin jin dadin ganin ta amra tace “me kika kawo min”

“Breakfast ne ma”

“Thank you nadine Ay anjima kadan zasu sallameni ma”

“Shiyasa nazo Ma, ga kayanki Ma nazo dasu”

“Yauwa daman inata tunanin wanda zansa,thank you nadine “

Shuru duka sukayi kafin nurse ta shigo “amarya mai kuka” ta fada tana dariya don itake kula da ita wajen yin gashi Har sun saba 

“Nurse beauty kin dawo”

“Na dawo amarya ya kikeji yanxu?”

Dan kauda kanta gefe tayi tace “I’m feeling much better all thanks to you”

“Ah haba, that’s my profession, doctor ya rubuta maki sallama, an gama all necessary arrangements, ga billing papers, jiya da oga yayi signing na manta ban bashi ba,Allah ya Kara sauqi sai kinzo scanning”

Gabanta ne ya bada daram kafin ta dago ta karba paper din ta dan tabe baki a ranta tace “allah ya tsare ni, ni aisha”

Sallama nurse din tayi mata kafin ta fuce da gefen idanu ta kalli Nadine wadda tayi gum kamar bata san suna yi ba saidai kunnenta tass ya nadi komai, mamaki ne karara a fuskanta saidai sanin babu huruminta yasa ta yin gum.

Saurin maida idanunta tayi kan papers din kafin ta soma karantawa, paper bill ne wanda aka shigar cikin file dinshi na nan asibiti akayi registering sunanta under nashi as her guardian, kurama bill din kasan idanu tayi dan kwanakin da tayi Har taci Rabin miliyan, runtse idanunta tayi tana mai jin wani irin sauyin

yanayi haushinsa na raguwa cikin ransa, dama chan bata kullace shi ba saidai tayi alkawarin barin rayuwarshi gaba daya.

Karfe goma suka ta gama kimtsawa cikin abayar da nadine ta kawo mata, bata saka hijab din nata ba ta saka mayafin abayar suka fito Nadine na biye da ita da basket din data taho

Dashi, daidai wajen motar da driver ya kawo Nadine suka tsaya ya bude masu suka shiga yaja motar sukabar asibitin.

A cikin dakin kuwa bayan fitarsu amra mai shara da goge goge na zuwa Gyaran dakin taga ledaji a kasa, da farko tama dauka trash ne saida ta bude taga kayan zaqi Kala Kala Harda wanda bata taba gani ba a rayuwarta dasu cakes kusan Kala biyar different flavour, chocolate masu tsada da sauransu ledoji biyu ne tam a cike da su a ciki, tana ganin haka kuwa ta qulle abunta ta karasa gyara ta fuce daga dakin.

Tafiyar minti Talatin suka karaso gida saboda traffic daya dan tsaida su don Safiya ce kuma Akwai masu zuwa office da wuri, driver na parking ya bude mata baya ta fito tadan tsaya tana karema gidan kallo kamar mai nazari kafin ta karasa ciki nadine na biye da ita a baya.

Tana shiga cikin parlor ta wuce sama zuwa dakinta ta zare mayafin abayar ta zauna gefen gado ta doka uban tagumi, ta dauka kusan minti goma a zaune kafin ta miqe ta wuce toilet jin futsari ya matsota, da kyar ta samu tayi futsarin tana cije lebe don Har yanxu tana jin zugi a wajen, tana gamawa tayi tsarki da warm water don yanxu likita yace mata komai da warm water zata yi har bayan ta warke ma.

Tana fitowa daga bathroom din nadine na shugowa dauke da ledan magungunanta tace “ma gashi jin manta a mota”

Ta aje mata tare da juyawa ta nufi kofa 

“Oh thanks nadine” ta fada tare da wucewa kan gado ta janyo duvet ta lullubama kanta, barci take son yi saidai tunani ya hanata ayanxu ta yanke shawarar yana zuwa zata shaida mashi zata bar gidan ta koma kano wajen Yan uwanta don zaman ta anan batada guaranteed din abunda zaije ya biyo baya, bayaga wannan Ma babu amfani sannan zata nemi ya saketa ta kama gabanta.

Lokacin daya shigo gidan wajen karfe sha daya kamar kullum, tsayawa yayi a sitting room ya qare Ma ko’ina kallo babu kowa a parlor,kallon inda take yawan zama ta jirashi yayi kamar mai tunani wani abu kafin ya kauda kanshi gefe ya wuce sama, koda ya hau second floor tsintar kanshi yayi da tsayawa gaban dakinta, cikin natsuwa ya bude kofar, ganin duhu babu haske Sai dan hasken bedside lamb ya tabbatar mashi tayi barci don haka ya karo mata kofar ya haura sama zuwa dakinsa.

Kwanan ta biyu da dawowa daga asibiti, cikin kwanakin nan koda wasa bata yarda ta hada hanya dashi ba, Duk wani abu da tasan zai hada ta dashi kauce Kasa take yi, cikin Yan kwanakin nan ta warware sosai don gaba daya ta daina jin zafin da yake ji, kullum Nadine ke kawo mata abinci daga na safe zuwa na dare, daga daki Sai bandaki babu inda take zuwa Har zaman ya fara gundurar ta, gashi wayanta bashida wani amfani don bata da masu kiranta ko ta kira, daman haifa ce, itama yanxu kusan wata guda kenan rabon data sameta a waya.

Thursday morning…

Tun bayan data Tashi sallar asuba bata koma ba, wanka kawai tayi ta shirya cikin English gown mai dan tsayi don ta wuce gwiwarta sosai ta shan iska ta feshe jikinta da turarenta masu sanyin kamshi kafin ta zauna kan gadon ta soma latsa wayan ta don kwana biyu Instagram na debe mata kewa sosai, 

Tana nan zaune Nadine ta kawo mata breakfast, fada da murmushinta tayi don daman harda yar yunwarta ta Tashi, Har gabanta nadine ta karaso ta aje mata a gefen gado tace “Ma ga breakfast”

karban abincin tayi tace “, thank you so much nadine daman yunwa nakeji sosai”

Murmushi kawai tayi mata ta fuce

Janyo tray din tayi ta bude plates din abunci ta fara ci hankali kwance.

Tana gamawa nadine na shigowa dakin,  hannunta dauke da bottle water tace “sorry ma, na manta zaki buqaci ruwa zai yanxu na tuna”

“ thank you daman yanxu nake tunanin saukowa da plates din”

“No ma’am Zan sauka dasu kasan”

Murmushi kawai tayi bayan fitar Nadine tana yaba irin mutuntuwa da take dashi, batada damuwa kwata kwata, aikin ta ne kawai a gabanta.

Uae Haifa’s res….

Kusan wata guda kenan tana neman line din amra bata samu, ta shiga damuwa sosai na rashin jinta cikin kwanakin.

Bude kofar toilet dinta tayi ta fito da sauri jin karar wayanta alamun kira na shigowa,da sauri ta daukan wayar ganin tana neman yankewa, ganin sunan Hammam kan screen ya sata yin yar tsuka ta aje wayan tare da komawa toilet ta cigaba da abunda yake,daman wanka ta gama tana cikin yin skincare dinta karar wayar ya cika mata kunne. Saida ta fito ta shirya fess kafin ta janyo wayan nata ta soma kiranshi, ringing daya ya daga Wayar tare da yi mata sallama, saida suka gaisa kafin ya tambayeta ummi da abuh, mamakin shi take sosai, abubuwan da baya yi mata achan baya wanda a lokacin take son haka yake mata ayanxu, sama sama ta dunga amsa shi don garashi take yi sosai shi kuma yana lallabata.

“Uhm how’s your friend?”

“You mean amra?” Tayi saurin bashi amsa 

“Yes”

“Tana nan lpy, but I’m not sure don tun bayan 

 banning dinta a akayi daga uae akan auren katin kasa ta koma nigeria ban sake samunta ba, I’m sure ka san zancen tunda Harda abokinka akayi suspending”

Dariya ya danyi Har tana jin sautin dariyar tashi

Shuru ta danyi tana sauraron sa don ya dan daure mata kai, don maganar da yake mashi ba abun dariya bace

Da sauri adan qule tace “I’m I making a joke here?

Da sauri yace “sorry dear”

“Then why are you laughing”

“It’s just that…..”

A harzuke tace “let me just end the call”

Da sauri ya ce” it’s just a fake scandal,”

 “I don’t understand, what do you mean by it’s a fake scandal”

“I can’t tell you everything, but it’s a fake scandal, no one Is banned,not even the general, it’s just a plan”

Shuru tayi tama rasa me zatayi murnar abunda ya fada mata ko haushinsa,”you mean it’s all a plan?, and you didn’t even bother to…” da sauri taja Bakinta tayi shuru Tunawa da lokaci da abun ya faru basa tare, “hold on a sec” 

Tana fadin haka ta kashe wayanshi ta shiga Kiran amra ba qaqautawa stil baya shiga, burinta yanxu kawai ta samu amra ta daga wayanta ta bata wannan kyakyawanan albishir,saurin sake kiranshi tayi tace “do you know a way that I can reach some one that is in nigeria?”

“I’ve been trying to reach her out”

Da sauri yace “kina da contact dinta na chan ne?”

“ eh ina dashi but it’s useless , don ina kira baya shiga” ta bashi ansa

Gyara zaman wayan yayi a kunnenshi don yana office nema 

“What does the number start with”

“It’s start with zero” 

Da sauri yace “hold on a sec”

Sauke wayanshi yayi ya shiga contact din Amar na nigeria.

Sake kiranta yayi yace “I don’t know if this will work but you have to add 3 more digit before the first digit, let me send you an example through sms”

Da sauri ta sauke ijiyar zuciya tace “thank you so much” ta kashe wayan

Yana tura mata ta saka tare da saurin dialing, nan take wayar ya shiga Har ya fara ringing, da sauri ta miqe fuskanta dauke da murmushi farin ciki.

Amra dake zaune tun bayan sallar la’asar bata motsa daga inda take ba tana tunani duniya da makomar rayuwar ta sanin cewa yanxu ita baza a saka kanta cikin jerin budurwa ba hawaye na saukowa daga fuskanta tayi saurin goge wa, tunani ta shiga yi da zuciyarta inda ta yanke samunshi don suyi magana akan

rabuwar su don bazata tafi da auren wani ba gida koda wasa, bala’in da zata tarar a gidan uncle na banning dinta da akayi babu karatun ma ya isheta.

Tana cikin wannan tunanin wayanta yayi ringing…….

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 114

Update!!!!

13/05/2023

Da sauri ta dauka wayan ganin contact din haifa akan screen din, Har jikinta na bari

“Hello….haifa, is that you”

Cikin murna da farin cikin samun kawar Tata tayi saurin cewa “habibty Ina kika shiga,I’m so sorry, bansan yanda Zan sameki ba saida hammam yam min bayanin yanda Zan kira ki” cikin mamakin abunda haifa ta fada tayi saurin cewa “hammam? Are you guys back together?

Sauke nauyayyan numfashi haifa tayi tace “it’s a long story,and what I will tell you now will shock you even more”

Shuru amra tayi cikin damuwa da daurewar kai tace “haif, so much has been going on in my life recently, na shiga damuwa sosai na rashin samunki”

 cikin farin ciki da zumudin abunda zata fada mata tace “babe abunda Zan fada maki yanxu zai kawo karshen damuwarki I promise”

“Haif na…” saurin katseta haifa tayi tace “babe you’ve not been banned from uae  all that scandal is fake infact your marriage has been  proved legal by the marriage consent group and I’m sure zasu baki katin kasar”

Da sauri amra ta miqe tsaye idanunta tap da qwalla  kanta ya gama qullewa da abunda haifa take fada mata “babe what, what are you talking about, ban gane ba kimin bayani yanda Zan gane”

“Yea babe, abunda na fada maki gaskia ne, Duk abunda ya faru a lokacin it’s just a plan made by general for some certain reasons,dazu hammam ya fada min,“

“Then that means he used me?,haifa you mean all That has happened kwanakin Duk karya ne?innalillahi wa inna ilaihi rajiun, haif Im so stupid”

Tana karashewa ta fashe da kuka, tsagaitawa haifa tayi hankali tashe jin kukan da amra keyi tace “babe what wrong, na dauka you’ll Be happy with the good news”

Cikin dacin rai da baqin ciki tace “no…noo haifa,”

Ta sake fashewa da kukan, abunda take son fada mata ma ya maqale, sanin halin amra yasa haifa yin shuru, saida ta dauka kusan minti ashirin tanayi kafin ta tsagaita don kanta, hankalin haifa ya gama Tashi gaba daya saidai ta Kasa gane dalili kukan kawar tata

“Babe” ta kira amra ahankali cikin natsuwa

“What’s wrong? Why are you crying?”

“Haifa he lied to me, he used me” dan kukan data tsagaita ta cigaba 

“Amra pleas explain to me yanda Zan fahimta, who used u?”

“He played with my innocence, shine ya kawoni gidansa don ya samu cikar burinsa, yanxu ne Ma komai ya gama dawowa kaina”

Da sauri haifa wadda ta gama kufuluwa da zancen tayi saurin cewa “kin saka ni a duhu, kimin bayani”

Nan take amra ta fara zayyano mata bayanin tundaga lokacin da m5 ya dauko ta ya kaita airport zuwa lokacin da aka kawo ta gidan, shuru haifa tayi don itama kanta ya gama daurewa “you mean, kina zaune a gidanshi? And bai fada maki gaskia ba? What’s his motive kenan, to protect you?”

Cikin bacin rai amra tace “to protect me? He lied to me because all this while ya nuna min saboda ni da taimakon da yayi min akayi banning dinshi shima Har yayi affecting all his achievements,I was so

15 / 94