Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   60 / 94

177K to 180K   out of 279.4K words

just ripping her yanda yake so, wani irin dadi na ziyartashi that is out of the world, ahankali ya soma jin ya fara dawowa daidai, ko kadan baiyi gangancin kusantarta ba, saidai babu irin jagwagwalon da baiyi mata ba, ita kuwa gaba daya ya karar mata da ruwan jiki don har lokacin jikinta karkarwar sanyi yake yi ga azabar muguwar shaawar da takeji, sun dauka kusan awa guda a yashe a kasan, harya rage wahala, itama dai fita tayi a hayyacinta dukda zazzabin dake ciyota saida sakon da yake aika mata ya isa gareta dukda a wahale komai ya wakana.

Saida komai ya lafa mashi ya miqe tsaye yayi satisfaction stretching, amra da idanunta ked an kafeta tana jin ya miqe ta fashe da matsanancin kuka, shuru ya danyi yana mamakinta, don yasan baiyi mata komai ba tunda bai shigeta ba balle ace ko ta samu tear kamar last, then whys she crying ya tambayi kanshi yana karemata kallo daga sama har kasa yana mamakin yanda ta kara komai ba kamar yanda ya sameta a lokacin daya kusanceta ba, tabe bakinshi yayi ya fuce daga closet, tana jin alamun rufe kofar da yayi ta miqe adaddafe ta janyo hijab dinta don batabi takan kayanda ya faffarka bag aba daya, tana zura hijab din ta allabo ta fito ta fuce daga dakin.

Tana hawa sama kamar ana ingizata dakinta ta wuce direct ta kwanta kan gado tana kuka mai cin rai, tabbas tayi alkawarin komai zai mata zata zauna dashi saidai batasan hes this heartless ba, babu abunda ya sani sai kanshi, lallai tana da aiki agaban, tambayar kanta ta soma yi anya ya Muhammad zai taba sonta kuwa?

Ta dauka kusan awa guda akwance tana hawaye, gab daya jikinta y agama tsami ga zazzabin da takeji, da kyar ta samu ta mike ta wuce bathroom ta watsa ma kanta hot bath kafin ta fito, ko kaya bata tsaya ta saka ba ta balli Panadol biyu tasha ta kwanta, nan take barcin wahala ya dibeta.

 

Shiko goga koda ya fito daga bathroom closet room ya koma kugunshi daure da towel, bin closet room din ya farayi da idanu, ganin batanan, yar tsuka yayi ya

wuce gaban closet ya bude ya dauka kayansa ya shirya, gaba daya jinshi yayi kamar an zare mashi duk damuwarsa, abunda yaji adazun is unexplainable.

Agurguje y agama shirinsa ya fuce daga gidan gaba daya yanajinshi relaxed and stree free.

 

Amra dai wunin ranar a kwance tayishi, koda salima tajita shuru ta leko dakin tana ganinta kwance ta fito ta barta don yanxu ta daina mamakin yawan barcin da takeyi, direct dakin ammah ta wuce ta sameta zaune, nan ta zauna suka sha hirarsu har tana yi mata tausa.

 

Ta daddare ma salima ce kawai ta sauko don bata tsaya duban amran ba, daga ita sai lantana sukayi preparing dinner atare.

Suna gamawa ta fara jerawa akan dining, saida ta tabbatar ta kammala komai ta nufi hanyar stairs, tana shirin hawa saiga aman ya fito daga dakinshi, kasa motsawa tayi daga tsayuwan datayi ta zuba mashi idanu yanda shima ya zuba mata, tun bayan zuwanta dakinshi da tayi last har sukayi musayar yawu yake ignoring dinta, bata taba sanin tana mashi so, mahaukacin so ba sai yanxu, gaba daya bata iya barcin saida tunaninshi, sonshi ya rigada ya mamaye zuciyarta, shiko a yanxu yayi moving on don ta nuna mashi bata sonshi, dukda deep down baya jin zai iya rabuwa da ita saidai ya bama kanshi hakuri akan ta, tare da barma allah komai, don yayi Imani idan har akwai rabo tsakaninsu zasu dawo don babu macen daya taba so duk duniya kamar baby sal dinshi.

Tunda ta kura mashi idanu ta kasa saukewa, ya mata ram a idanu, tausayin na ninkuwa aranta, harga allah she wants to open up, she wants to tell him how much she love him saidai ganin yanda ya watsar da ita yasa ta watsar dashi itama ta fara nuna kamar bata damu ba.

Kauda kanshi yayi daga kanta ya wucewarshi kamar bai ganta ba, haka ta dunga binshi da idanu harya fuce daga gidan, ahankali siraran hawaye ya soma sauka akan fuskanta, ‘’yaya dan allah ka daina wahalar da zuciya ta’’ ta fada acikin zuciyarta tana share hawayen daya zubo mata.

 

Karfe tara daidai amar ya shugo gidan, jikinshi a mace, gaba daya haka ya wuni yau sukuku da tunaninta don saida ya fita ya tuna yanayin daya barta, haka kawai yaji zuciyarshi na iching musamman idan ya tunata.

Yana shugowa direct sama ya wuce zuwa dakin ammah, da sallama ya shiga dakin, ganin babu kowa a dakin yasa ya zauna gefen gadonta don yaji alamun mutun abandaki.

After like 10mins saiga ammah ta fito, hannunta dafe a kirjinta dake mata zafi, bata lura dashi ba saida ta karaso cikin dakin ta ganshi, yana ganin futowarta yace ‘’barka da dare ammah na’’

Fuskanta dauke da fara’a , tana kokarin karasowa tace ‘’barka dai son, ya aiki harka dawo’’

‘’ya amsa yanxu na shigo gidan,’’ ya amsata

Zama tayi gefenshi ta kalleshi fuskanta dauke da murmushi, kallonta shima yayi sai alokacin ya lura da yanda ta dafe girjinta, ganin haka ya sashi saurin cewa ‘’are you okay ammah?ko baki jin dadi ne’’

‘’im okay son lafiyata kalua’’ ta bashi amsa tana kauda kanta gefe, batajin zata iya fada mashi abunda ke damunta don tasan tabbas zai tada hanaklinshi, shiko kallonta yake yana karantarta, sai alokacin ya lura da yar ramar datayi, ga idanunta ya fada sosai.

Mikewa yayi tsaye yace  ‘’gobe zamuje asibiti,I want to be sure youre fine ammah na, goodnight’’

Dan murmusawa tayi don daman tasan halinshi idan ya fara sensing abu don haka bata musa bat ace ‘’allah ya kaimu son, saida safe’’

Yana fucewa daga dakin ammah yabi dakinta da kallo yana nazari, yanason ya shiga dakin nata saidai ego dinshi bazai barshi ba.

 

 

The next day….

Saturday morning 8am

Da sallama salima ta shigo dakin amra, sanye take da hijab har kasa, amra dake zaune baking ado ta rafka uban tagumi, sanye take da doguwar riga abaya baqa, fuskanta tayi fayau alamun damuwa kwance akan fuskan nata.

Anatse salima ta kaarso har inda take ta zauna gefen gadon ta dafa kafadarta ‘’adda lafiya dai? Are you okay ko akwai abunda ke damunki,’’

Firgigi amra ta farga da ita, jiki amace ta kalleta tace ‘’yashe kika shugo’’

Da mamaki salima ke kallonta, ‘’adda something is wrong with you ko? Ki fada min dan allah, akwai abunda ke damunki da kike boyemin’’

Murmushin yaqe amra tayi ta miqe tsaye tayi rolling mayafin abayarta akanta tace ‘’babu abunda ke damuna, kece dai kike boye min abu, na lura kwana biyu bakya cikin wlwala’’

Shuru salima tayi son tasan waske zancen take son yi don haka itama tace ‘’ni babu abunda yake damuna, abu daya ne ke damuna’’

Da idanu amra ta kalleta ‘’meke damunki fda min my baby sis’’

‘’kece adda na, wallahi damuwata damuwarki ce,ki daina boyemin komai don allah, we only have each others back’’

Nunfasawa amra tayi ta dan kakalo murmushin d bai kai xuci bat ace ‘’nidai babu abunda ke damuna, kinga taso muje mu daura breakfast yanxu naga karfe tara ta kusa’’

 

Atare suka sauko kasan zuwa kitchen, anan suka tadda lantana tana ayyukanta, saida suka gaisa kafin su fara preparing breakfast, suna gab da gamawa amra tace ‘’baby sis, kije ki fada ma ammah an gama breakfast, sannan ki taso salim’’

‘’okay adda’’ salima ta fada tana kokarin fucewa, amra ce da kanta ta jera komai saboda salima ta wce sama, saida ta gama tsaf ta dawo kitchen ta kalli

lanatan dake yankan avocado tace ‘’oh anty lantana bakya gajiya da aiki, ayda kin ajiye idan kin gama cin abunci saiki hada juice din’’

Da murmushi lantana ta kalleta tace ‘’ah ah gwara n agama duka na huta’’

Shuru amra tayi tace ‘’toh shiknan bari na wuce sama’’

Amra nakaiwa nan ta juya zuwa sama, bata kaiga karasawa ba ta tuna da wayanta data bari a kitchen don haka ta juya zuwa kitchen din, koda ta karaso kicin din batayi sallama ba ta kutsa kai, ‘’kingaa na man…’’ kasa karaswa tayi ganin yanda lantana ta daburce kamar wata barauniyar da aka kama, da mamaki amra ke kallonta da yanda take kokarin kare abunda ke hannunta da zaninta, staff amra ta ngo qamshin rashin gaskia a tattare da ita, ance kayi ma mutun kyakyawan zato koda yaushe don haka ta basar kamar bata ga komai bat ace ‘’ashe anan nabar wayar’’

Cikin yaqe lanatana ta juya gefe tace ‘’au laa ashe mantawa kikayi, kinga nida nayi zaman akuye daurin zani na neman gagarata’’ ta fada tana gyaran zani, murmushi kawai amra tayi ta fuce daga kitchen din tana mamakin abunda ta gani.

 

Karfe goma daidai kowa ya hallara banda amra, ammah na zaune salima tayi serving dinta, kafin tayi serving salim, tana shirin zubama aman yayi saurin janye plate dinshi ba tare da ya kalleta bay ace ‘’no thanks’’

Jiki a mace ta zubama kanta ta zauna chan gefe ta fara cin abunci, da sallama amar ya shugo shima ya zauna, saida ya fara gaisheda ammah kafin suma su gaishesa, duban dining din yayi zuwa kofa hoping ko zai ganta, ganin babu ita yasa ya fusge, salima ce tayi serving dinshi tana gamawa shima yayi bismillah ya fara ci.

Suna nan zaune saiga amra kamar wadda aka wullo, ta sauyo kaya zuwa wata abayar mai kyau lemon green color, tayi mata kyau sosai kmar ba ita, anaste cikin takunta mai daukar hankali ta karaso dining din fsukanta fayau, kusa da ammah ta fara zuwa ta gaisheta kafin ta ja kujera kusa da ita ta zauna, daya bayan daya ta bisu ta gaishesu, amar dai tunda ta fito ya kasa dauke idanunshi akanta, har saida ya kusa kwarewa kafin ya sauke idanun nashi, itako bata wani bi takanshi ba ta soma serving kanta.

 

Shuru kake ji a dining,babu wanda yace kala sai karar spoon dake tashi.

Da sallama lantana ta shugo dining din hannunta dauke da dogon cup data hadama ammah green juice aciki, saida ta gaishe da kowa kafin ta matso kusa da ammah ta aje mata kan table tace ‘’hajiya ga girin juice din’’

Dariya salima ta danyi data kubce mata tace ‘’kai anty lantana, keda wannan girin din’’

Murmusa duk sukayi ammah tace ‘’nagode lantana sarki aiki, bakya mantuwa,ni wallahi mantawa ma nakeyi da green juice din’’

Murmushi kawai lantana tayi ta juya da nufin shiga kitchen, amra data kafeta da idanu tana ganin juyawarta tace ‘’ji mana’’

Juyowa lanatana tayi ta tsaya tace ‘’naam anty’’

Miqewa amra tayi ta tako inda ammah take zaune tana kokarin kai juice din bakinta tace ‘’ammah zansha’’

Da mamaki ammah ta kallota, kafin ta dan murmusa tace’’ gashi doctor ay bana hanaki ba,’’

Karba amra tayi ta juyo gaban lantana ta kalleta tace ‘’anty lantana ko zaki fara sha kiji min idan da daci’’ adaburce lantana ta kalleta tana yaqe tace ‘’ay na taba sha, akwai daci kam wallahi, anya zaki iya sha kuwa keda kike son zaqi’’

Shuru amra tayi ta sake kallonta fuskanta babu wasa, tace ‘’yaushe nace maki inason zaqi?, kedai ki dandana min kawai’’

Atsorace lantana ta sake kallonta tace ‘’kaii ni zawayi yake sani saidai ki bama ammah ta dandana maki’’

Amar da kanshi ke kasa yana jiyo su sama sama ya dago ya kallesu, nan kowa ma ya maida kallonsu kansu, amra dai ta dage akan lantana saita dandana, ita kuwa lanata data gama tsurewa sai dojewa take karshe ma cewa tayi, ‘’na doraruwan zafi akan gas bari na kshe’’

Kamar daga sama taji muryar amar ‘’stoppp there’’

Ya fada a kausashe kafin ya tako har inda suke, hannu ya sanya ya janye amra gefe anatse kafin ya karbi juice din daga hannunta ya kalli lantana yace ‘’shaaa’’

Haba waa nan take lantana ta saki futsari, gaba daya alamunta sun nuna bata da gaskia kiri kiri,

Akaro na biyu ya daka mata tsawa yace ‘’takeeee it and drink it up’’

Jiki na bari ta karba ta fara kokarin kaiwa bakinta, bata kaiga sha ba ta saki cup din a kasa wanwas ya fashe juice din ya malale, saurin miqewa duk sukayi daga kan ammah zuwa ga aman da abun shima ya daure mashi kai,

Kallon cup din amar yayi zuwaga juice din dake Malala, ahankali idanunshi suka sauka kan wani yellow drug da bai gama melting ba a cikin juice din, tsugunnawa yayi ya dauka kwayar yak are mata kallo sosai, if hes not mistaken wannan molly ce wanda daddy yake safarar su ga manyan kasashe, wanda a shekara sau daya yake hadata kuma baifi mutun biyar yake sayarma ba duk duniya, kuma da ita yake amfani yake kashe mutanen da suka nemi susha gabanshi, hankali atashe amar ya dago idanunshi sun kada sunyi jaaaa, jikinshi harya soma bari barr barr, ya kalli lanta adata saki futsri, yau karyarta ta kare asirinta ya tonu, yanxu ko tace zata falfala ta gudu bazata tsira ba, ammah ce ta kaste silence din ganin amar ya furgice lokaci guda, anatse ta tako inda suke tsaye don nesa kadan suke da dining tace ‘’muhammad whats wrong? In tace bata son sha ku kyaleta mana’’

Hanakali aatshe ammah tayi baya ganin yanda amar ya karade ya sauya, idanunshi sunyi jaaa fuskanshi ma tayi jajawur, lantana na ganin haka tayi saurin zubewa a gwiwarta ta dora hannu aka ‘’na shiga uku ni abida wayyo allah na, yau karshena yazo, don darajar allah ku yafe min wallahi wallahi bayin kaina bane, sharrin shaidan ne na rantse da allah’’

Kallonta amma tayi don bata gane kan zancen ba ‘’ke lantana meke faruwa anan? Me kikayi da kike neman gafara’’

‘’wallahi hajiya ba laifin…’’ tassss taji saukan marinda saida ya toshe mata kunnenta nan take taji wani dummmm saida ta yi baya, bata gama jin zafin marin bay a sake kwasheta da wani marin, fuskanshi yayi jaa sosai jikinshi har rawa yake,wanda yasa ammah da amra yi baya son sun tsorata da yanda suka ganshi, lantana dai ta tafi hutun wucin gadi kafin ta dawo ya sake ball da ita, aman ne yayi saurin taro shi yana kokarin kamashi ya hambare hannunshi gefe ya sake bata wani blow daya sata gangarawa har wajen parlor, dukda haka bai barta ba saida ya bita ya dunga kwallo da ita gaba daya ya fuce daga hayyacinshi, ammah na ganin zai kashe yar mutane tayi saurin bin bayanshi tana ‘’muhammd kaii muhammd menene haka, dukan mace kakeyi? Kome tayi maka bai chanchanci kayi mata haka ba’’

Ay muhammd fa ba sauraron ta yake ba, haka su amra sukabi bayan su suma aman ma da y agama gano komai yayi saurin bin bayansu don tabbas amar zai iya kasheta anan take, don haka yayi gaggawar janyo wayarshi ya soma kiran hukuma,

Ammah dake bin amar har suka fito tsakar gida yana ball da lantana tayi saurin kallon amra tace ‘’aisha meke faruwa ne?,’’

Kasa cewa komai amra tai don itama Karin bayani take nema, saida amar yayi mata lugu lugu idanunshi sunyi jaa sosai ya janyo wayarshi daga aljihunsa baya gani ma sosai yayi dialing number asad,yana picking azafafe yace “idan ka wuce 5 minutes baka zo nan gida b azan kashe wannan wicked soul din’’ yana kaiwa nan ya kashe wayar ya fara neman abunda zai dauka ya karasata, ganin wani karfe daga chan gefe yayi saurin juyawa ya dauko yayo kanta dashi, ammah na ganin haka ta dafe kirjinta tana innalillahi, Muhammad zaiyi kisa akan idanunta, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, bat agama tunani ba taji kwal ya bugama lantana a kafa daya saida kafar ta balle, daga hannu yayi zai sake buga mata amra tayi saurin tahowa inda yake ta rungumeshi ta baya ‘’yayaa don allah calm down, karkayi abunda zakazo kayi dana sani’’

Baya ji baya gani yace ‘’sakeni,’’

‘’wallahi bazan sakeka ba yaya, bazan taba bari kayi abunda zai jefa rayuwar ka a halaka ba,’’

‘’aishaaaaaaaaa’’ ya daka mataa tsawa, dukda ta tsorata hakan baisa ta sakeshi ba, wani irin juyi yayi ya zubar da ita a kasa, nan take ta kwala uwar kara dayasa ammah ta kalleta, kankace me cikin kankanin lokacin ammah ta zube a kasa wanwas, jini na fita daga bakinta da hancinta hankali atashe salima ta kwala kara ‘’ammahhhhhhhh!!!!! Wayyo allah na shiga uku’’

Amra da bat agama dawowa daidai tana ganin ammah a yashe a kasa tayi saurin rarrafowa ta karaso wajen, ganin ammah a kwance hankali aatshe ta taba ammah tace ‘’ammah ammah’’ jin shuru ya sata taba wajen zuciyar ammah, dipp komai ya tsaya chak, hankali atashe amra ta dago agigice ta kalli salima da aman da suka zagaye ammah tace ‘’am….mahhh..ta mutu.uu..’’hannunta da

bakinta duk karkarwa suke, da sauri ta miqe tsaye kamar mahaukaciya har veil dinta na faduwa ta kaarso inda amar ke bugun lantana da duk jini ya gaba malalewa a jikinta ga uban raunuka daya ji mata, amra na karasowa ta daka mashi tsawa daya sashi tsayawa babu shiri ‘’amarrrrrrrrrr!!!!!’ idanunta sunyi jaa sosai sai sauke nunfashi takeyi

Da sauri ya waigo ya kalleta ya zuba mata idanunshi, tana ganin haka ta juya ta nuna mashi ammah ‘’ammahhhh’… ammahhh’’’

Ay baisan lokacin daya saki rodin ba taku biyu uku ya iso inda ammah ke kwance kamar gawa, salima a furgece ta dago tana kuka ‘’ya aman wai ta mutu, ammah ta mutu, na shiga uku na wayyo allah na’’

Amar daya tsaya kikam ya kasa yin komi, jikinshi na bari ya durkuso ina ammah ke kwance rai a hannun allah………

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 137

Update

Unedited page

Wani irin jiri ne ya soma dibanshi ganin yanda jini kebin fuskan ammah ta baki ta hanci, idanunshi sunyi jaa suna neman kawo ruwa, thie is the most painful day of his life, ammah is his life entirely, he cant take it idan abu ya

60 / 94