ba asi ba yace “yes sir”
Ko kallon inda suke Amar baiyi ba ya juya, nan take call suma ya shigo masu.
Harya shiga daki ya fito lokacin har sun fita suna shirin fucewa daga gidan, karasowa Har inda suke yayi ya kira ogan yace “check that part”
Ya fada yana nuna tsohon part din su aman, agurguje suka shiga part din, bin bayansu Amar yayi ya tsaya daga chan gefe, saida sukayi buncike dakunan kaf Har suka zo kan dakin sirri ajiyar, dakyar suka samu suka bude kofar dukda suna da wata na’ura ta scanner da ke detecting abubuwa da suke amfani wajen scanning da bude komai dayake digital, gaba daya suka shiga cikin dakin, masu daukan hotuna sunayin job dinsu masu scanning suma haka suka fara, daya bayan daya saida suka fito da komai saikace masu operation, Amar dai yana tsaye daga baya baice komai ba, ya kyalesu ne suyi nasu job din don yanason duniya ta shaida hakan kafin ya karbe case din, agabanshi suka bude safe dinnan basuyi yinqurin tabawa ba Har ya futa bayan yayi observing wajen shima, sake Kiran head chairman din efcc din yayi, saida suka danyi magana kafin ya kashe,bangaren ma’aikatan kuwa kowa mamakin waye wannan da yake hanasu yin aykinsu daya kamata sukeyi saidai tunda sukaji order ne daga chairman gaba daya yasa basuyi yunkurin taba komai ba saidai sun dauka hotuna da za aje a record, Amar dai abunda baya so saida ya fito fili wato identiti dinshi as the only son of taura kuma general uae armed force, da farko baiso hakan ta faru ba saidaga baya ya gane dole saiya fito ya wanke company mahaifinshi daya gina da guminshi don duniya ta shiada cewa babu hannun company a cikin mugayen ayyukan daddy saima amfani da companying da yake yi don kariyar kansa wanda yaci galaba akan hakan don yanzu duniya kowa ya dauka kan cewa da company Alhaji kabiru yake amfani wajen boye Duk wasu miyagun ayyukan shi, lokaci guda sales din kamfanin yayi kasa, shareholders kowa na neman janye hannu, abubuwa da yawa sun ma Amar yawa, dole haka ya jajirce ya tsaida natsuwarshi waje daya wajen gyara alamuran daya shafi family name dinshi, dukda dole yayi alkawari sai ya gurfanar da daddy no matter what, he
will make sure justice has been served, a ranar m5 da soldiers dake karkashin amar suka hau private jet suka taho kasar suma.
Ammah…
Tana shiga toilet ta dafe kirjinta dake mata zafi da nauyi at the same time, wasu irin hawaye tausayin danta ke silalo wa afiskanta,she can’t believe cewa Amar yayi inheriting oligospermia from mahaifinshi, dan she can clearly recall lokacin da suka dauka shekaru basu samu haihuwa ba Har saida suka asibiti a Germany nan aka gano mahaifinshi nada oligospermia, tun samartakar shi,a lokacin har sun cire hope don babu abunda yayi masu saura, sai cikin ikon Allah, Allah ya azurtasu da Muhammad wanda yawanci dada ke kiranshi da kyautar Allah don lokacin da sukaji asibitin an shiada masu bazai taba haihuwa ba don stage din chance din samu ya wuce sai gashi allah ya basu, saurin goge hawayen da takeyi tayi ta dauro alwala ta fito,sallaya ta shimfida ta fara jero salloli tana kai kukanta wajen Allah, harta idar tana kuka tana rokon Allah ya kawo masu sauqi, wani irin tausayi da qaunar dan nata na ninkuwa a zuciyarta, kwata kwata gama manta da alamarin wani daddy gaba daya, tana nan zaune salima ta shigo dakin sanye da hijab, karasowa Har inda ammah yake tayi ta zauna gefenta kamar zatayi kuka tace “ammah jikin ne? Are you feeling sick”
Saurin share hawaye dake kan fiskanta tayi tace “no dear, kunci abunci?”
Hawaye ne ya soma gangarowa a fuskan salima Ganin yanda ammah ta sauya lokaci guda gashi tana Ganin hawaye kwance a fuskanta “ammah dan Allah ki daina kuka, mu roki Allah ya kawo mana sauqi, bana son wani abu ya sameki dan Allah ki bar zubarda hawayenki”
Kauda kai amma tayi gefe tace “dear kije ku daura abuncin dare, nasan bakuci komai ba ko”
Shuru salima tayi don ta gane space take nema don haka ta mike ta nufi kofar,
Amar dake shirin shugowa dakin ya jiyo su suna magana, daman yazo ne don ya duba ko ammah is okay, don ya damu da lafiyarta sosai samun kanshi yayi da kasa bude kofar yana sauraron maganganunsu, ragewa ta gefenshi salima tayi tace “Ina wuni yaya”
“Lafiya” ya amsa ataqaice shima Har wata yar Rama yayi,
Dakyar ya samu ya tattara natsuwarshi cikin kamewa ya shiga dakin, juyowa ammah tayi Ganin shi a tsaye yasa ta kauda idanunta gefe, takowa yayi har Inda take idanunshi sunyi jaa ya karaso Har inda take ya zauna agefen ta kanshi a kasa ya kamo hannunta cikin nashi muryarshi a sanyaye yace “ammah!!!”
Banza tayi dashi ta kauda kanta gefe don ba karamin bata mata rai yayi ba na boye mata da yayi,
“Ammah na please ki diana fushi dani,“ banza ta sake mashi, haka ya dunga rokon ta bata ce qala ba karshe ma miqewa tayi ta koma bakin gado ta zauna, ba tare da ta kalleshi ba tace “ina ce na fada maka karka sake yunqurin explaining
komai saika kawo yarinyar da kaje Ka aura ba tare da sani ba? Now get out my room”
Dago da jajayen idanunshi yayi sai a lokacin ya tabbatar ranta ya baci sosai, don bata taba bashi silent treatment ba sai yanxu, dole ya bata space, don haka ya juya ya fuce daga dakin jiki a mace kamar maraya, bin bayanshi tayi da kallo tana tausaya mashi sosai saidai dole ta nuna mashi fushinta akan abunda yayi.
Fucewa yayi gaba daya ma daga gidan don ji yayi gidan yayi mashi fadi sosai, ga kanshi dake blowing saboda abubuwa da sukayi mashi chaaa akai.
Saukowa salima tayi sanye da hijab ta wuce kitchen suka daura abuncin dare ita da lantana, koda suka gama Har wajen karfe takwas babu wanda ya sauko, sanin yanayin da ammah ke ciki yasa ta deba mata a cikin flask ta wuce mata dashi sama, tana zuwa ta taddata akwance tana haki, cikin sauri salima ta aje abuncin a gefe ta karasa inda take, magani ta ta dauko mata ta bata kafin hakin ya lafa, gefen gadon salima ta zauna tace “ammah na please ki kwantar da hankalinki dan Allah”
Murmushi kawai ammah tayi mata tana yaba kyawun haki irin na salima, kallon abunci data aje mata tayi tace “yarinyar kirki yau me aka dafa”
Murmushi salima tayi mata tace “tuwo da miyan ganye da kika fi so Harda fish”
Ahankali ammah tace “thank you dear”
Miqewa salima tayi tace “Bari na barki ki huta ammah na”
Futa tayi ta sauko kasa tana nazari, dakin Amar ta wuce Ganin ko Ina akashe alamun baya nan yasa ta fito, tunanin shiga dakin Aman ta soma yi,ahankali ta Taka Har zuwa dakin ya bude,babu kowa a sitting room din sai tv dake aiki don haka ta wuce hanyar bedroom din tayi knocking, ta dauka kusan minti biyar a tsaye shuru, ganin haka yasa ta dan bude kofar kadan, dakin is dim babu haske sosai sai na inner lights, ganin haka yasa tayi tunanin baya nan don haka ta soma kokarin janyo kofar, karaf kunnenta ya jiyo mata sheshekar kukan shi, hankali a tashe ta shiga dakin a daddare ta kunna light din daki, a zaune ta ganshi ya hada kai da gwiwa yana kuka, gefen shi kwalbar giya ne Ganin bai bude giyar ba yasa tayi hamdala ta karaso inda yake ta tsugunna a gabanshi tace “ya aman!!!”
Dan dago da jajayen idanunshi yayi don Har cikin kwanyar kanshi yajiyo sunan shi data kira for the first time kafin ya sauke kanshi
Ba karamin tausayi ya bata ba don dole yayi kuka, agaban idanunshi akayi arresting mahaifinshi, shuru ne ya ratsa tsakaninsu don batasan wani word zatayi using ba wajen comforting dinshi,
Cikin natsuwa ta Dora hannunta kan kafafunshi tace “ya Aman dan Allah kadaina kuka,Duk abunda kaga ya faru da bawa Toh daga Allah ne”
Dagowa yayi ya kalli kyakyawar fuskarta kafin ya kauda kanshi gefe yace “I hate my life, I hate my miserable life…look”
Taba zuciyar shi yayi still idanunshi nakan nata yace “the pain in here is unbearable, I have no one, no one can understand what I’m going through ina maraicin mahaifiyata”
Fashe wa da kuka itama salima tayi Ganin yanda hawaye ke zarya a fuskanshi Tayi saurin toshe bakinsa tace “haba ya Aman, ya zakace you have no one? You have ammah, ammah loves you so much”
Girgiza kai yayi yana hawaye “not as much as she loves Amar, I’m always a sucker, who disobey her, I’m very disrespectful towards her”
Kallonshi salima tayi idanunta cikin nashi cikin natsuwa ta soma magana “ya Aman you have us, ammah loves you so much Duk da abubuwan da kake yi she still care about you so please Ka daina cewa you’re alone”
Yatsunta biyu ta saka ta soma goge hawayen dake zarya a fuskanshi Adan shagwabe ta kalleshi tace “kuka baya maka kyau wallahi”
Dariya ya danyi ya rike hannunta cikin nashi muryarshi chan kasa yace “sal, I’m willing to change for better, I want to be a good god fearing man, saidai inajin kamar Allah bazai yafe min ba”
Dan dago da fuskanshi tayi da hannunta daya tace “ya Aman, you can change for better, Allah mai jiqan bayin shi ne kuma mai yafiya ne, idan har kayi alkawarin bazaka sake saba mashi ba, I will be by your side during this journey in sha Allah”
Wani irin dadi yaji da maganganun nata,take yaji kamar gaba daya damuwarshi ta wanke tass, miqewa tsaye tayi ta mika mashi hannunta daya alamun ya miqe, yana Ganin haka ya rike hannun nata ya miqe tsaye baiyi wata wata ba ya rungumeta tsaf a jikinshi, salima daga jishi a jikinta babu zato babu tsammani Tayi saurin yin baya, hannunshi daya yasa ya saqalo kwakwasonta, sun dauka kusan minti biyu ta kasa motsawa ko kadan don kamar wata yar tsana haka ta jiya a jikinshi,ganin kamar yama manta da yanayin da suke ciki yasa ta dan tureshi baya tace “ya aman Ka sakeni”
Ahankali ya soma tsame jikinshi daga nata kafin ya dan juya mata baya yace “sorry sal”
Bata ce komi ba ta fuce tana dan smiling, after like 5 mins ta dawo hannunta dauke da plate na abuncin ta aje mashi kan side stool Ganin baya dakin kafin ta fuce daga dakin.
The next day….
Gidan is just like yesterday, kowa yana jimami, ammah dai damuwar Amar ta kwana don saida doctor yazo ya dubata ba tare da sanin kowa ba a gidan Har yazo yayi mata prescribing magunguna ya tafi.
Karfe takwas da rabi salima ta sauko sanye cikin atamfa wadda akayi mata dinkin doguwar Riga, rigar tayi mata kyau sosai, bata daura dankwalin atamfar fa sai hula data saka same color da atamfar,gaba daya jikinta ya gama sanyi da alamarin gidan, musamman ammah, don ta shiga dakinta donmin ta gaisheta, a yanayin data tarar da ita hankalinta ya Tashi sosai, Duk a tunanin ta saboda
arresting daddy da akayi ne yasa ta tada hankalinta sosai, da wannan tunanin ta sauko kasan jiki amace, da sallama ya shiga cikin kitchen din Ganin lanata tana moping, jiki a mace ta kalli lantana tace “sannu da aiki ina kwanta anty lantana”
Juyowa lantana tayi ta kalleta tace “lpy Lau alhmdlh kin Tashi ashe?”
Anatse salima ta kalleta tace “eh, yau me zamu dafa?”
Ba tare da ta kalleta ba lantana tace
“Ki tambayo hajiya”
Kauda kai gefe salima tayi tana kokari daukan wuka tace “bata tashiba tukunna”
Irish salima ta kwaso ta fara ferewa while lantana ta soma yankan veggies,cikin mintuna qalilan suka gama, acikin warmers salima ta zuba soyayyan Irish din da egg sauce da plantains kafin ta fara fita dashi zuwa dining, saida ta kai duka warmers din ta jera kan dining kafin ta wuce sama, dakin ammah ta shiga cikin sallama,babu kowa cikin dakin don haka ta dan jinkirta jin alamun saukan ruwa, Gyaran dakin ammah ta soma yi saida ta gyara mata dakin fess ta saka bakoor mai kamshi a burner kafin ta wuce dakinsu dake nan gefe chan don tashin Salim,tana shiga dakin ta wuce kan gadon Ganin yanda yayi dare dare,zama tayi gefenshi ta dan bubbuga kafadunshi tace “Salim kai wake up, wannan barci naka kamar gawa”
Mutsika idanu Salim ya fara kafin ya miqe zaune ya rungumeta, tana Ganin haka itama ta rungumeshi tsam dan normally idan yayi mata hakan to maybe yayi mafarki ne ko ya tuna da adda, tunawa da adda yasa taji wani irin, bata don ta tuna da ita kwata kwata don haka ta dago kanshi tace “go and shower, you’re stinking hmmm” ta fada tana dariyar mugunta, ashagwabe ya miqe ya wuce toilet domin yin wanka, yana shigowa ta miqe ta fuce daga dakin,dakin ammah ta shige anatse tace “assalam alaikum”
Juyowa ammah tayi sanye cikin hijab, fuskanta tayi fayau Har yar Rama tayi murmushi dauke a fuskanta tace “wa alaikum salam my dear Har an Tashi”
Wani irin dadi Salima taji Ganin yanayin ammah, karasowa tayi da dan gudu ta rungume ta tace “ammah….”
Shafa kanta amma tayi tace “yea daughter”
Dan dagowa salima tayi ta kalleta cikin kulawa tashe “are you okay now ammah? Hope babu abunda ke damunki? Ko muje asibiti”
Hannunta ammah taja Har bakin kofa tace “sorry for worrying you dear, yau ke kikayi girki?”
Kallonta salima tayi cikin so da kaunarta har suka sauko kasan tace “yes ammah, kuma nasan yayi dadi”
“Uhmm sai munyi tasting zamusan idan yayi dadi” ammah ta fada tana kallon ta, kujera salima ta jawo mata fuskanta dauke da murmushi tace “ammah sit, bari nayi serving dinki”
Murmushi ammah tayi ta rike hannunta tace “no dear jeki kira yayyunku sai muyi breakfast gaba daya”
Cikin nishadi salima ta juya zuwa dakin aman, da sallama ta shiga cikin daki kai tsaye ba tare da tunanin komai ba, juyowa Aman yayi jin sallamarta, da sauri ta
juya baya ganinshi tsaye da towel a kugunshi, agigice tace “ya aman ammah tace….breakfast”
Tana kaiwa nan ta fuce ba tare da Tashi amsan shi ba, murmushi kawai tayi ya cigaba da shiri aranshi yace “silly girl”
Cikin nishadi ya shirya cikin Riga da gajeran wando saida ya feshe jikinshi da turare kafin ya fito, fuskanshi Har wani annuri take saboda gaba daya daga Daren jiya zuwa yau yaji komai ya ragi a zuciyarshi saboda sallan dare daya kwana yana yi.
Karasowa yayi kanshi a kasa Har gaban ammah kafin yadan duqa yace “good morning ammah”
Da mamaki ammah ta dago ta kalleshi cikin fara a da jin dadin sauyawarshi tace “morning son how was your night?”
“Alhamdlh” ya fada ataqaice kafin ya wuce gefe ya zauna,
Daga Dakin Amar salima ta fito, jiki a mace ta karaso dining din kallonta duka sukayi
“Ammah ya Muhammad baya nan”
Kauda kai ammah tayi tace “Zaki zauna kici mu karya”
Karasowa tayi ta soma serving din kowa saida ta zo kan aman nan ta jawo plate dinshi ta zuba mashi dayawa, kallonta yayi ta gefen idanu ahankali murya chan kasa kasa yace “tare zamuci ne?” Da sauri ta waigo ta kalleshi kafin ta kauda kanta gefe tana murmushi tayi banza dashi,tare da tura mashi gabanshi, wani plate din ta jawo don zubama kanta, bata zubama kanta da yawa ba ta dauka plate din don seat din zaman ta na daga gefen ammah, bata kaiga karasawa ba ta saki plate din a kasa tare da dafe kirjinta, kallonta duka sukayi atare, da sauri aman ya miqe yaa kawota gefe don karta Taka ceramic plate din daya fashe din, hankali atashe ammah tace “dear are you okay?”
Dan dago da kanta tayi tace “yea ammah, gabana ne yadan fadi bansan plate dinma ya subce ba”
“Ayya ki kula next time” ammah ta fada tana kallon Salim dake shirin saukowa fuskanshi babu walwala, karasowa yayi ya zauna gefen ammah yana mata murmushi.
Jan hannun salima Aman yayi ya zauna da ita don kamar ta furgice lokaci guda, playe dinshi ya jawo ya aje mata yace “eat” dan dagowa tayi gabanta na faduwa tace “thank you ya aman”
Wani plate din ya jawo ya diba shima yaci.
Nnamdi ezikewa International airport….
Karfe sha biyu daidai flight dinsu amra ya sauka a babban airport din nnmadi azikiwe dake cikin garin abuja, tunda suka shiga cikin jirgi take barci har suka iso, about 7houra flight, ahanakli ta janyo handbag dinta da passport dinta ta fito daga cikin jirgin, tunda ta fito daga jirgin gabanta ke faduwa wanda kwata kwata last time data dawo Nigeria bata ji wannan fargabar ba sai yanxu, runtse idanunta tayi ta sauko daga stairs din jirgin tabi hanyar arrivals, bata tsaya bin
wani layi ba don a first class ta zo, don haka tana shigowa airport din tayi clearing komai ta fito harabar airport din ba tare da bata lokaci ba don batada wani baggage’s da zatayi clearing, hankalinta ne ya soma Tashi don bata san Ina zata bi, kallon gefenta tayi Ganin wani security yasa ta tambayeshi wajen chanza cash nan ya Kun mata wani waje cikin airport din inda ake chanza kudi, gaba daya babu wani kudin arziki a jikinta sai 100 dirhams don haka ta wuce wajen don chanza kudin, tana zuwa ta chanza su zuwa naira, gaba daya subu sha biyar ne, jikin Jakarta ta tura kudin kafin ta sake fucewa daga cikin airport din, dube dube ta soma yi don neman taxi, ta dauka kusan minti biyar a tsaye ta rasa taxi din da zata shiga don masu taxi dinma suna ganinta babu wanda yayi mata tayin shiga motar don kana ganinta batayi kamar wadda zata shiga taxi ba, Fendi bag dinta ta janyo ta lalubo wayarta, gaba daya tama manta bata da sim din nigeria don haka ta aje wayar kawai kamar zatayi kuka ga rana