hamad da Hamid, gefen ta salim ne shima rike da princess, zama sukayi gaba dayansu nan Abban su ya fara nuna masu girman halacci, waazi yayi masu sosai mai shiga jiki sosai dazai amfani rayuwarsu, amra dai na daga gefe tana hawaye Har lokacin,…..
Bayan ammah ta futo daga bedroom din amra dakinta ta wuce direct ta soma dialing contact din Amar, yana daukan wayar tace “idan Ka gama Ka same ni a bedroom dina,”
Daga chan ya amsa da tohm kafin ya kashe wayar,
Yana kashe wayar ammah ya gaggauta goge jikinshi da towel dinshi, yana gamawa ya tsaya gaban dresser yayi yan shafe shafenshi, yana gamawa ya tsaya baki gado yana kallon kayan dake gabanshi, wata bugaggiyar gezner ce fara tass sai kyalli takeyi, Daukan inners dinshi yayi ya zurasu
Cikin Yan mintuna qalilan ya gama shirinsa, Kyan da yayi na daban ne ma yau dinnan kamar wani Sabon ango, fuskanshi fayau, babu abundake kunshe a zuciyarshi sai fargaba Mara dalili,
Saida ya gama feshe jikinshi tass da turarukanshi kafin ya zari wayarshi da laptop dinshi ya wuce dakin ammah, lokacin daya futo babansu amra na zaune baima Lura da fitowan shi ba don haka ya wuce sama, alokacin da ya shige dakin ammah a lokacin amra ta sauko kasa wajen babansu.
Da sallama ya shige dakin ammah, tana zaune bakin gado har a lokacin sanye take da hijabi, saida ya gaisheta kafin ya zauna,
Fada sosai ammah tayi mashi inda ta nuna mashi mahimmacin amra a rayuwarshi da yayanshi, sun dade sosai tana mashi fada mai shiga jiki kafin su fito a tare,
Hannunta a cikin nashi suka sauko kasa, zuwa sitting room Har lokacin amra kanta a kasa yake tana hawaye, suna zama ammah ta Dora daga inda Abban amra ya tsaya, fada sosai sukayi masu a tare mai shiga zuciya kafin baban amra yayi masu sallama don kusan karfe Tara na dare.
Yana tafiya ammah tace “ya kamar ku wuce kuma don dare nayi sosai”
Mikewa sukayi gaba dayansu inda ammah tayi masu sallama daga nan sitting room, saurin rungumeta amra tayi tana hawaye, dabbing bayanta ammah tayi tace “daughter kukan ya isa haka, zai dunga kawo ki ay, gasu salima nan zasu dunga zuwa Ay suma”
Ta dade sosai a jikin ammah tana hawaye, Amar dai fucewa yayi ya barsu anan sitting room din,
Sallama ammah tayi mata ta wuce sama don itama jikinta yayi sanyi.
Ammah na wuce sama suka fito a tare dasu salima da triplets, gaban Ind akayi parking suka tsaya, daya bayan daya amra ta karbi yayanta tana kissing dinsu taba hugging dinsu, tana jin kamar karta tafi saidai bazata iya yi hakan ba, amar dai na daga zaune a cikin motar yana jiranta, ganin lokaci na tafiya ya futo daga motar shima ya karbi yayansa yayi kissing dinsu kafin ya bama su salima suka wuce dasu cikin gida don baya son Ana futa dasu da daddare.
Suna wucewa amra Har alokacin kuka takeyi shabe shabe , bai kualata ba ya shige cikin motar tana Ganin haka ta bude gaban motar itama ta shige kafin ya jaa motar suka bar compound din.
Tunda suka futa daga estate din babu abunda takeyi sai kuka ahankali, yana jinta Har lokacin baiyi kokarin lallashinba kwata kwata, Har suka karaso gidan shi larrics, yana parking ta bude motar bata ma taaya kiranshi ba ta wuce wajen entrance ta tsaya, saida ya rufe motarshi ya bi bayanta yana kallon yanda take qunquni,
Gefe ta matsa mashi ya bude kofar yana budewa ta shige ciki ta tsaya kikam a sitting room kamar wata soja, don haushinsa take ji sosai, ahanakli ya karaso inda take calmly ya soma mata magana “Aisha!!”
Bata motsa ba kwata kwata daga inda take harya karaso inda take tana Ganin haka Tayi saurin jaa baya,
Murmushi kawai yayi don yasan halin nata zatayi shi kuma baya jin yana da lokacin wannan don haka baiyi wata wata ba ya sungumeta, babu zato ba tsammani ta jita a sama, wutsilniya ta fara yi tana san ya sauketa yaki, karshe ma dai fashe mashi tayi da kukan shagwaba, yana jinta babu abunda yakeyi sai murmushi, bai tsaya ko Ina ba kuwa sai bedroom dinshi tana nade a hannunshi, harya karaso bakin gadonshi ya ajiyeta akai,yana ajiyeta ya danyi baya yace “wait for me here karkiji ko’ina”
Wata yar harara ta Galla mashi kuka ya gani saidai kawai yayi dariya aranshi yace “Zaki I kaniyanki ne yau dinnan” yana kaiwa nan ya fuce daga bedroom sun ya sauko kasa, kowani ango yana shugowa dakin Amarya ma da kaza shi kuwa general sai ganinshi nayi da flower, wata katuwar rose mai shegen kyau da tsada ya zaro daga bayan booth dinshi, yana daukowa ya rufe motarshi ya koma cikin gidan, yana shugowa ya rufe kofar mai entrance din ya wuce sama cikin izza da kamewa,
Bedroom dinshi ya wuce direct har alokacin fuskanshi dauke da murmushi yana bude kofar yaga wayam,….
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 153
Last Update part 2
Shuru ya danyi son yasan zata iya guduwa don haka ya fuce daga bedroom din ya nufi nata dake next floor yana zuwa ya nufi hanyar bedroom din nata,
Hannunshi ya fara sanya akan handle din kofar, yana danna handle din kofar yaji a rufe, shuru ya danyi yasa kunnenshi jikin kofar nan ya soma jin kukanta na Tashi a hankali,
Gyara tsayuwar shi yayi kafin ya soma magana “Aisha open up let’s talk”
Banza tayi dashi kamar batasan yana yi ba saida ya sake maimaitawa,
A taqaice sai ya dauka kusan 30mins yana karanta taki bude kofar saima Kara saurin kukanta da tayi, ranshi ya sosu sosai saidai yana kokarin dannewa saboda ayanxu dole ya lallabata, “okay shikenan ki kwanta ku huta pls ki dina kukan nan”
Yana kaiwa nan ya ajiye mata yar bunch of roses din a gaban dakin ya wuce sama zuwa bedroom dinshi, yana shiga bedroom dinshi ya soma rage kayan jikinshi zuwa pjs, kafin ya kwanta ranshi Duk a dagule, dukda yaji zafin abunda tayi mashi hakan baisa yayi gushi da ita ba don yanzu ya koyi yanda zai dunga controlling anger dinshi.
Washe gari da safe amma ta aiko driver da breakfast,
Haka ya sauko kasan da kanshi ya karba hasket din kafin ya wuce dining dashi, da kanshi ya koma sama zuwa bedroom dinta yayi mata knocking shuru bata bude ba, ya dauka kusan minti goma yana knocking Ganin bata da niyar budea Yasa ya kyale ta ya wuce bedroom dinshi, wanka yayi ya sauya kaya zuwa kamani kafin ya sauko kasan for the second time ya sake yi mata knocking, “Aisha!!!” Shuru babu response at that Point hankalinshi ya gama Tashi don haka yace “dan Allah say something mana? Are you okay”
Daga ciki ta amsa shi da “yes I’m okay”
Wata nauyyyay ijiyar zuciya ya sauke kafin ya sauka kasa yayi breakfast dinshi yana gamawa ya fuce daga gidan gaba daya don he’s preparing for something.
Bai dawo gidan ba sai wajen karfe uku na rana, Yan shugowa part dinta ya wuce yana zuwa yayi knocking Har lokacin bata bude ba saima kukanta daya jiyo, at that point yakai maqura don haka yace “what’s the meaning of this aisha? What is wrong with you? Nace Zan mai wani abu ne ko nayi maki wani abun ne? At least ki fito kici abunci karkiyi ma kanki illa”
Shuru tayi banza dashi saima daga karshe yaji tace “ni bana jin yunwa”
Shuru kawai yayi ranshi ya sosu sosai don haka ya kyaleta kawai tayi abunda yake so.
Bangaren amra kuwa ta zabi zaman dakin ne saboda bata son anything dazaiyi encountering dinta dashi, ga ciwon mara daya dan riketa ya hanata sukuni,
Duk wannan magiyar daya dunga yi mata bai sata ta bude kofar bedroom dinba tana zaune a bakin gado wani irin haushinsa takeji Har barci ya kwashe ta, washe gari haka ta lallaba tayi wanka ta sauya kaya zuwa wasu marasa nauyi dake Jere a cikin wardrobe dinta wanda tun last zuwanta suke cikin wardrobe din, tana gamawa tabi lafiyar gado abunta.
Tana daga kwance ya sake yi mata knocking lokacin da aka kawo breakfast, harga Allah yunwa take ji sosai saidai taurin kanta yasa taqi futo wan balle taci abuncin.
Sai wajen yamma bayan data gama galabaita ta bude kofar ta sauko ta diba abuncin ta koma daki ta sake kullle kofar.
After 2days…
Haka suka dunga wasan buya ita dashi inda ya kyaleta kawai don baya son takurata saidai Duk Safiya saiya leko bakin kofar dakin nata yayi knocking ya duba lafiyarta, wani sa’in tana amsa shi wani sa’in kuwa bata kulashi haka zai tsaya inya gaji yayi tafiyarshi.
A cikin kwanakin kullum amma ke aiko masu da abunci Duk Safiya da yamma.
Bayan sati guda zaman dakin ma ya gudureta da kanta ta soma futowa tana saukowa kasan tana shiga kitchen ta dafa ma kanta abunci, don yanxu saidai ya fita ya sayo takeaway ya aje mata nata don baya son ya dunga zuwa gida saboda Kar ammah tayi sensing wani abu dukda ya sayo komai na provisions da za a iya dafawa..
Bangaren su ammah, gidan is so lively, daman gida indai da yara bazai taba zama shuru ba, Salim ya koma school, salima kuwa yanxu itace kamar second mum din triplet, itace cin abuncinsu itace wankan su Dukda sometimes tare da ammah suke yi, don yawanci ma a dakin ammah suke wuni gaba daya, yara dai sai girma suke sai san barka kwata kwata basa koke koken neman uwarsu, daman inkaji yaro na kukan neman uwarshi to fah yunwa ce, su kuwa basa Shan komai sai madara da puddings.
Aranar labaran yazo gidan don amsa Kiran da ammah tayi mashi, bayan ammah ta sauko suka gaisa gaisuwar mutunci kafin ta soma magana “daman na buqaci gani Ka ne saboda inason muyi wata magana,”
“Toh hajiya Ina sauraronki” ya bata amsa kai tsaye
“Dama maganar Salima ne da Aman,”
Dan Gyaran murya tayi kafin ta cigaba “Aman maraya ne , nasan kasan tarihin gidan nan basai na dago zancen ba,….Baban aisha Ina neman ma dana Aman auren yarka salima, Ina fatan zaka amince da hakan”
Murmusawa labaran yayi kafin ya kalleta yace “hajiya ai kece uwarta kume kece ubanta, komai yana hannunki, Duk zabin da kikayi mata nayi naam da shi, fatan mu Allah ya sanya albarka a cikin wannan”
Murmushin jin dadi ammah tayi sosai tace “Nagode Nagode da wannan karamci baban aisha, Allah ya saka da Alkhairi”
“Hajiya babu godiya Ay tsakaninmu Wallahi duk abunda kikace hakan za ayi Insha Allah”
…….
Saturday morning….
Anatse take saukowa daga stairs, sanye take da Riga da skirt daya kamata sosai chip chip fuskanta fayau sai dan kohl data saka a a idanu ta, anatse take saukowa zuwa kitchen,
Kofar kitchen din ta bude, tana bude wa tayi turus ta tsaya Ganin tsaye yana kokarin hada tea a mug,yanda take kallonshi bai shima yake kallonta kafin ta kauda kanta gefe, ganinshi a kitchen din baisa taki karasowa ba don haka ta wuce hanyar pantry ta dauko noodles guda biyu da kwai biyu kafin ta fito, lokacin data fito yana tsaye Har lokacin ya zuba mata idanunshi yana sipping tea din hannunshi, fuskanshi tarr alamun bai dade da Tashi, kallonta ya dunga yi daga sama Har kasa Yan ajin kaunarta da shaawar ta yana double a kanshi, tayi mashi kyau sosai fatarta sai sheki takeyi don sai yanxu ya samu damar yi mata kallo kurulla sosai tundaga sama Har kasa, her body da yanda take komai a natse babu hayaniya is driving him crazy….
Gyaran murya ya danyi Har lokacin yana kallonta bayan ya sauke mug din daga bakinshi yace “good morning beautiful, Har kin gama gudun Nawa?”
Dan tsayuwa tayi chak daga dauraye tukunya dake hannunta tayi bata juyo ba haka zalika bata ce mashi Tak ba,
“Me zaki dafa mana” ya tambayeta yana ajiye mug din hannunshi kan granite din dake kan table din kitchen,
Nan ma bata ce mashi ci kanka ba saima cigaba da abunda takeyi tayi, ganin haka ya sashi cewa
“Wifey bazaki kulani ba?, Wai har yanxu hukuntanin akeyi haka? Ya kamata a yafemin haka nan mana, Wallahi nayi regretting Duk abubuwan da nayi abaya”
Yana kaiwa nan ya soma takowa inda take, Lola in tana tsaye a bakin plate cooked gas tana kokarin daura pot din akan plate din,
Murmushi kawai tayi don tasan daman abunda yake so kenan, yayi mata dadin baki saboda ya samu kanta cikin sauqi toh kuwa hakan bazai taba faruwa ba, Duk a tunanin ta taba ta zaiyi, abun mamaki kuwa sai taga akasin haka don yana zuwa dan da ita bai taba ta ba ya dan tsaya daga bayan nata yace “I know what you’re thinking right now, inason ki san cewa bazan Kara takura ba sannan bazan fasa baki hakuri ba because I mean it, I want us to work this out, please..”
Yana kaiwa nan ya wuce ya ajiye mug din kan sink kafun ya fuce daga kitchen din
Yana futa amra ta tabe baki tabi bayanshi da kallo Har fuce babu abunda yake Raya wa a zuciyar ta sai “hmm tanan Ka bullo kuma, Wai ni zaiyi ma dadin baki, idan har kaga na sauko da wuri ba sunana aisha ba”
Tana gama tunanin nata ta juya ta kunna gas din.
Koda ta gama dafa lafiyayyiyar indomie din parlor ta dawo ta zauna ta kunna tv, sai a lokacin ta lura da nan ma an sauya komai ba dakinta kadai ba don komai dake dakinta saida aka sauya zuwa sabbi daga kan gadon zuwa carpet da sauran abubuwan dakin, nan ma parlor an sauya komai zuwa sabbin kuka wanda suka fi wanchan kyau sosai,
Gyara zama tayi ta fara cin indomien saida ta cinye tass ta rage kwai daya don ta cika cikinta sosai kafin ta mike ta wuce kitchen ta wanke plate din da mug din daya sha tea kafin ta dawo kitchen din ta zauna….
Karfe sha biyu daidai ya fito daga part dinshi, ahankli yake saukowa babu abunda yake sai kamshi, hannunshi rike da wayanshi sanye yake da kananun kaya as usual kamar koda yaushe, fuskanshi na nan yanda take,
Tundaga bakin stairs ya hangota a kwance akan doguwar kujera tana latsa waya hankali kwance,
Karasowa yayi har inda yake bata ba lura dashi ba don waya take daga kwance “salima meysa yake kuka? Kin bata abunci kuwa”
Amra ta fada Har lokacin wayan na hannunta don ta saka wayan a speaker
Daga chan bangaren salima ta amsa ta “Adda Wallahi rigima ne, yanxun nan ammah ta gama bata abunci”
“Kinbar ammah da hidimansu ko?”
“Ah ah Wallahi, na dan shiga bathroom ne, kinsan yanxu mun koma part din ammah”
“Ina hero’s dina? Kai Wallahi I missed them so much, inason ganinsu Wallahi”
Amar ne yayi gyaran murya wanda yasa ta waigo ta ganshi tsaye, “kinason akawo su ne?”
Ya tambayeta, banza tayi dashi kafin tayi sallama da salima ta kashe wayar.
Bata kalleshi ba ta cigaba da kallon tv, Yan a Ganin haka ya dan hade rai don baya son yanda take banza dashi, idan zaiyi magana goma bazata ce mashi qala ba,
“Zan futa yanxu, zaki buqaci wani abun ne? Do you need anything?” Ya tambayeta sounding very serious,
Tana jin haka ta dan dago ta kalleshi , “bana buqatar komai”
Tana karashe wa ta kauda kanta gefe
Yana ganin haka ya girgiza kanshi kafin ya dan tako inda fuskanta yake, abunda bata taba expecting ba a wannan lokaci, sai jin lips dinshi tayi a kumatunta both sides, saurin runtse idanunta tayi sosai don kamshinsa daya bugu hancinta hade da kamshin breath dinshi da suka bugeta, “take care of your self bazan dade ba Zan dawo” yana kaiwa nan baima tsaya jin abunda zata ce ba ya fuce daga sitting room din, gaba daga amra sandarewa tayi, she can’t lie wannan peck din ya shige ta sosai,
Harya fuce tana jin presence dinshi da tausasan lips dinshi akan kumatunta…..
Tana nan zaune tana latsa waya tana duban hotunan da sukayi da triplets dinta lokacin birthday dinsu, babu abunda take sai murmushi musamman idan tayi playing videos dinsu, tana nan zaune saida lokacin sallah yayi ta mike ta wuce sama…
Bayan futar Amar daga larrics bai tsaya ko Ina ba sai taura estate don kusan kullum sai yazo gidan ya duba yayanshi, ya dade sosai a wajen su don sai wajen yamma likis ya futo daga gidan, yana futowa daga taura estate ya wuce shopping mall, don wunin ranar da amra yayi shi, sayyayyan kayan girke girke yayi mata ya karo wasu provisions din da yawa Duk wani abunda zata bukata Harda frozen namomi babu abunda bai sayo mata ba,
Saida ya shake motar da kayyayki kafin ya wuce gida, a hanyanshi ta zuwa gidan ma saida ya tsaya ya saya masu grilled chicken kafin ya wuce gidan, lokacin daya karaso gida Har anyi Kiran sallar isha’I don haka ya bude bayan yasa securities suka shiga da kayayyakin saida suka ajiye komai kafin ya wuce masallaci.
Saida aka idar ya fito ya shige cikin gidan, lokacin daya shiga sitting room babu kowa a kasan don haka ya wuce sama ya watsa ruwa ya sauya kaya kafin ya sauko zuwa part dinta,
Knocking ya danyi fir a seconds, baiyi gangancin bude kofar ba saida ta tako da kafarta ta bude kofar, kallonta ya tsaya yi kafin ya kauda kanshi, sanye take da hijab Har kasa da alamu bata dade da idar da sallah ba.
“Muje kasa na kawo provisions inason muyi sorting dinsu”
Kallonshi ta danyi for a seconds fuskanta babu wani fara’a ta dan tabe baki kafin tace “Ina zuwa” Tana kaiwa nan ta rufe kofar ta shige ciki,
Shima kasa ya sauko ya zauna akan kujera yana jiran saukowa ta.
Yan anan zaune saida ta duaka kusan minti ashirin kafin ta sauko, sanye take da Riga da wando na barci