Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   31 / 94

90K to 93K   out of 279.4K words

ya sauke wani wawan nunfashi yace “ya Allah what’s wrong with me”

Har ta haura sama yana jin takunta da sound din Har cikin zuciyarshi, kwata kwata baya son feeling din da yake ji gane da ita don haka yayi saurin hade rai ya mike don kallon news dinma ya fita akanshi,sama ya wuce cikin kamewa  yanason shiga dakinta saidai yana tsoron abunda zai biyo baya don baya jin ayanda yake jin kanshi Yanxu zai iya controlling kanshi, bayan wannan Ma baya son raini ya shiga tsakani tunda ta fada mashi maganganu between yau da jiya musamman akan budurcinta yayi alqawarin bazai sake shiga sabgar ta ba, sannan zuwa gobe monday yayi alqawrin suna asibiti ya tabbatar da sakamakon zai yanke hukunci.

Tunawa da wannan ya sashi komawa dakin nata fuskanshi a hade kamar bai taba murmushi ba ya  bude kofar kamar yanda ya saba, yana shiga  yabi dakin da kallo ganin bata nan yasashi bin dakin da kallo, Duk ta barbaza abunda ta sayo akan gado, hardasu pants da bras masu kyau sai beads dinta da hotunan da suka dauka ita da haifa na skydriving da sukaje.

Takowa yayi har gaban gado ya zubama hotunan idanu, jin alamun sound din dazu ya sashi saurin runtse idanunshi ya tattaro da kuzarinshi ya Tamke fuska ya furta “why are you loosing focus mehn”

Ya fada yana hade rai, amra da taje wanke hannunta cikin toilet tana fitowa ta riskeshi, saurin kauda kanta tayi ta basar tare da karasowa gaban gadon daga chan nesa ta zauna tare da daura kafanta kan daya ta nannade gashinta, gaban rigarta data soma balle boturan abayar ta kalla tana shirin maida botir din don boobs dinta sundan fito 

“Daga Ina kike?”

Kamar dirar aradu taji tambayar Tashi, bata son wani stress don haka ta bishi ayanda yake so tace “Munje shopping nida haifa”

Banza ya yi da ita kafin ya hade rai ganin yanda take kakkare jikinta yace “get ready tomorrow by  10am zamuje asibiti”

Dan dagowa tayi Har zata tambayeshi maysa zasuje asibiti ta tuna da yanda yake yasa tayi saurin tsinke Bakinta tace “okay Allah ya kaimu”

Ba tare da gardama ba, haushin amsarta yaji don yayi expecting zatayi jayyayya sai ya samu akasin haka janyo cinnabon tayi ta soma ci tana lumshe idanu Duk akan idanunshi hade rai yayi don yana son ya mata fada saidai ya rasa dalili da zai dake dashi gashi ita kuma ta kama kanta taki cewa komi, dan dagowa ta tana girgiza kafarta alamun abun ya mata dadi tace “sorry yayana bismillah”

Saurin runtse idanunshi yayi don kamarma Idan tayi magana turning dinshi on take, idanu ya zuba mata yana kallon nose ring din naata da yaune ya fara gani a kan hancinta, ba karamin burgeshi abun yake ba sometimes Idan yaga indians dashi sai ya dunga shaawan kallon nose ring din, ganin yanda take lashe lashe lower lips dinta tana rufe ido tare da hannunta ya sashi juyawa ya fuce daga dakin, don he can’t take it don zai iya saba alqawarin daya dauka yana fita ta tabe baki tace “daman nima ba baka zanyi ba”

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 122

Update!!!!

Unedited

Zama tayi ta cinye cinnamon rolls din duka ta hada da ice cream ta shanye tass, boba tea ne kawai ta aje shi ta shiga duben duben abubuwan da suka sayo, saida ta tattara komai ta aje inda ya dace kafin ta wuce toilet, wanka tayi da bath soap dinta mai kamshin strawberry kafin ta fito daure da towel dinta a kugu, Yan shafe shafe tayi kafun ta janyo waist beads din da matar nan ta bata, tsaye tayi tana kallon yanda beads din ke shining, saita tsinci kanta da smiling don tana bala’in son jigida sosai, saurin sauke towel dinta tayi kasa ta nada jigidar around her waist a kugunta, yanda ya zauna akan ass dinta ita kanta saida ya burgeta saboda yanda waistline dinta ya rike shi sosai, tsayawa tayi kallon kanta ta cikin mirror, ahankali maganganunshi suka fara mata yawo a kanta, the word common da yayi using ya hadata da kowa abun ya tsaya mata arai, ita kanta tasan she’s a spec, tana da kyau sosai ga uwa uba diriqda kyawun sura, she keeps wondering menene aibu a jikinta da Har zaiyi mata irin kallon nan ya fada mata maganganu Mara sa dadi, jiki a mace ta maida towel dinta ta saka pjs dinta ta daura hijab akai kafin ta tada sallah don ko sallan magrib bata samu tayi ba.

Tana idarwa yabi lafiyar gado hankali kwance tana tunanin rayuwarta tundaga ranara da ta fara haduwa dashi da events din da ya dunga hardasu unintentional Har izuwa yanxu, harga Allah tana jin zafi da haushinsa sosai saidai wani

bangare na zuciyarta is soft, don koba komai tana tuna wasu abubuwan Alkairi da yayi mata musamman lokacin da akayi mata operation lokacin data kamu da appendix,shuru ta danyi tana tunani kafin ta janyo duvet ta lullube jikinta gaba daya.

Bangaren Amar dai barci gagarar sa yayi, tunda ya dawo daga dakinta ya soma zarya? Yana mamakin kanshi da Sabon alamarin dake Bukit’s mashi, ya kasa gane why jikinshi ke neman rinjayarshi, he’s physically attracted to her, yana son all the feelings around her, zama yayi bakin gado ya runtse idanunshi yana tuna yanda yake lashe lips dinta, saurin kame kanshi yayi tare da reminding kanshi cewa he’s above that, ya wuce wannan yafi karfin wannan, menene take dashi da Har zai tada mashi da hankali, kiri kiri yana son yayi denying kanshi abunda yake ji, mikewa yayi ya wuce bathroom ya wanke bakinshi kafin ya futo ya sauya zuwa pajamas dinshi, yana gamawa ya kwanta, babu yanda baiyi ba barci ya kaurace mashi, tsintar kanshi yayi da tunani daban daban aranshi.

The next morning…

As usual kamar kullum yanda ta saba Tashi haka ta Tashi da asuba ta wuce toilet ta dauro alwala tana fitowa ta shimfida Sallaya ta gabatar da sallah, tana idarwa ta danyi azkar, karar notification yasa ta maida idanunta kan wayarta dake gefen bedside tana blinking light, mikewa tayi ta zare hijab din nata ta aje shi gefe kafin ta zauna bakin gadon ta janyo wayar,message ne ya shigo, saurin budewa tayi don ganin koma waye, mamaki ta soma yi ganin message daga same exact number daya mata message jiya, “sabah alkhayr ayataha aljamilah”

Ahankali ta furta kalmar ta karshe, zaman da tayi a dubai ta koyi larabci saidai bai zauna sosai a Bakinta ba, dukda haka bai hana ta gane abunda message din ke nufi ba “good morning beautiful”

Tabe baki tayi ta aje wayan gefe don bata gane koma waye ba.

Ganin karfe shida da kwata yasa ta koma ta kwanta don gari bai gama wayewa ba.

Karfe takwas daidai ta Tashi ta wuce toilet agurguje tayi wanka ta fito ta shirya cikin abaya milk color, bata tsaya wani shafe shafe ba ta goga kohl sai dan lip gloss kafin ta janyo Jakarta  da suka sayo jiya ita da haifa ta zura wayarta ta fito a anatse,tun da ta sauko Nadine ke kallonta tana murmushi tace “good morning ma’am”

Itama murmushin tayi mata tace “morning dine, yau tea kawai zansha don I’m running late”

Zama tayi akan dining ta zuba tea ta hada kafin ta fara sha cikin sauri, bata ida shanyewa bama ta aje cup din tayima Nadine sallama ta nufi hanyar futa, tana futowa taga inda m5 ke parking wayam babu motar babu shi nan gaban gidan don Duk Safiya nan yake aje motar ya zauna harta sauko, tayi mamakin ganin baya wajen don haka bata tsaya tunanin komai ba ta karasa tsakiyan compound

din ta fara leke leke, rasa abunyi tayi, gashi she’s running late, haushi ne ya turniketa, gashi tasan yanxu idan tayi requesting ride ba zuwa zasuyi ba don ta tuna last time data so fita hakan bai yuwu ba, juyawa tayi don komawa ciki don bata san me zatayi ba kuma, gashi bata da number shi, mamakin rashin ganinshi ta soma yi harta shige cikin gidan kamar zatayi kuka, don kullum inta tashi fatanta ta fuce daga gidan, don ko weekends da tayi a cikin gidan ba karamin rashin sukunki tsinci kanta aciki ba.

Nadine na ganinta dake kokarin gyaran floor hannunta rike da mop tace “ma’am baki tafi ba?

Kallon Nadine tayi kamar zatayi kuka tace “na fita banga wannan sojan ba, inaga kamar bai zoba ni kuka bansan ya zanyi ba Wallahi I’m running late, yanxu ko nayi requesting ride basa zuwa nan palm jumierah”

Kallonta Nadine tayi fusknata dauke da damuwa itama tace “Toh ko zaki je ki tambayi sir kiji meysa baizoba?”

Saurin kallonta amra tayi tace “gaskia bazan je ba Har gwara na fasa fitar kawai Idan na koma gobe Nace masu banida lafiya shiyasa ban zoba dukda nasan zaiyi affecting report dina”

“Ma’am indai zaiyi affecting din aikin ki gwara kije Ki sameshi kiji”

Kasa motsawa amra tayi tana tunanin Anya zata iya zuwa kuwa, tunawa da itace a damuwa Idan bataje bama yasa tayi saurin kallon Nadine tace “Nadine Kinsan bana son abunda zai hadani dashi, is it not better kawai na hakura”

“Not ma’am kije kawai tunda tambayanshi abu kawai zakiyi” Nadine ta fada tana kallonta

Haka nan badan taso ba ta aje handbag dinta da wayanta a gefen console dake dauke da kayan ado ta wuce sama zuwa dakin nasa, ahankali take tafiya kamar wadda kwai ya fashe Ma ajiki, leg chains dinta na fidda sound, samun part dinshi nada nisa yasa ta shiga lift ta taaya tare da Danna last floor. Cikin Yan seconds lift ya bude ta fita ta nufi kofar daze sadaka da sitting room dinshi na sama, daidai ta natsuwar ta ta fara yi kafin tayi knocking, jin shuru yasa ta bude kofar ta shiga cikin sitting room din, saurin kame jikinta tayi jin wani irin sanyi dake ratsata don ya kure sanyin ac dake parlor din, tunda ta tsaya tsakiyan parlorn ta Kasa motsawa, tunawa da wani abu yasa kawai ta juya zata fuce, bude kofan shugowa akayi, tundaga kafanshi dake sanye da nike metcon training shoes ta fara kallo zuwa ga shorts din dake jikinshi da  armless rigar kayan na under armor black, kayan sun kamashi sosai, six packs dinshi ya fito a jikin rigar alamun daga training yake, saurin kauda idanunta tayi daga kanshi, shiko tundaga sama yake kallonta Har kasa, hannunshi rike da hydrated bottle water sai wayanshi dake maqale a kunnenshi, mamakin ganinta ya tsaya yi a wajen, kauda idanunshi yayi daga kanta ya cigaba da wayanshi tare da wucewa zuwa ga dakinshi ba tare da yace mata ci kanki ba, tunda ya shige bata dago kanta ba, saidataji karat rufe kofa ta juyo ta kalli hanyar dayabi tare da tabe baki, rasa abunyi tayi don haka ta bi bayanshi, lokacin data bude yana shirin

sauke wayan daga kunnenshi, juyowa yayi ya zuba mata idanunshi, kallo daya ta mashi ta kauda kanta, ta Kasa cewa komi, shiko mamakin yanda ta chanza yake sosai, kamar daga sama

Taji muryarshi asanyaye “kina buqatar wani abu ne?”

Dan dagowa tayi kanta a gefe tace “Ina kwana”

Bai amsa mata ba ya soma cire rigar jikinshi, ganin haka yasa ta saurin cewa “daman Zan tabayeka wannan sojan ne naga baizoba kuma inason Zan tafi”

Aje rigarshi yayi ya shige bathroom ba tare da ya kalli inda take ba, tunda ya shige toilet ta hade girar sama da Kasa, tana nan tsaye kusan minti goma sai gashi ya fito daure da towel a jikinshi, hannunshi riqe da hand towel yana kokarin goge gashin dake kwance akan sajen fuskanshi da karamin towel dake hannunshi, ganinta a tsaye ya kauda kanshi gefe yace “what are you still waiting for? Tsayuwan me kikeyi anan?”

This time around in a harsh tone yayi mata magana don haka ta sake hade rai tace “ni ba wani abun na tsaya yiba, na tambayeka wann….”

Kasa karasawa tayi ganin yana shirin sauke towel din dake kugunshi kasa, da sauri ta juya tana kokarin bude kofar tace “na shiga uku”

Aguje ta fuce daga dakin kamar taga dodo, dan waigawa yayi, ganin yanda ta fita yasa ya danyi tsaki yace “I tot bakida kunya ai rubbish”

Karasa sauke towel din yayi gaba daya ya janyo shorts dinshi ya saka.

Karfe goma  da rabi daidai ya sauko kasan cikin uniform dinshi, saidai bai saka rigar kaki ba Sai fadar white shirt, anatse yake takowa Har ya sauko kasa, dining ya wuce Nadine dake tsaye kusa da ita a sitting room tayi saurin karasawa wajenshi tare da gaishesa, serving dinshi ta fara yi kafin ta koma kitchen,anatse ya fara cin kalaci harya gama ya miqe, ganinta zaune a sitting room hankalinta nakan waya yasa yayi hanyar futa yace “don’t waste my time na baki minti daya ki fito”

Yana kaiwa nan ya fuce, da idanu ta bishi tare da tabe Bakinta, miqewa tayi ta wuce kitchen ta dauko bottle water kafin ta dawo ta dauki jakanta ta fuce.

Abun mamaki tana fitowa taga m5 a tsaye jikin mota, yana ganin futowarta ya bude mata kofar baya, saida yazo dab da inda yake yace “good morning ma’am”

Kamar bazata amsa shi ba tace “good morning”

Kafin ta shige bayan motar, saida ta zaune ta Lura dashi dake gefe, idanunshi akan waya, dan waigawa yayi gabin m5 na zagayowa yace “behave your self, ki aje wannan rawar kan naki”

Bata ce mashi komi ba ta maida kanta ga window Har suka fuce daga cikin compound din.

Tafiyar minti ashirin ta kawosu uae specialist hospital dake deira, m5 nayi parking ya fito ya bude mashi kofa, kafin ya zagaya ya bude mata, kallon

asibitin ta fara don Sai a lokacin ta tuna da yace mata zasu zo asibiti, shuru ta danyi tana nazarin dalilinshi na kawo ta asibiti, bata kawo komai a ranta ba don haka ta bi bayanshi ganin yayi gaba, suna shiga cikin asibitin yayi clearing Duk wani booking da zaiyi kafin wata nurse tayi directing dinsu ta private reception don doctor da zai gani yana emergency room, amra de na biye dashi Har suka karasa reception din,  dan nesa dashi ta zauna tana rarraba idanuwa, sun zauna kusan minti goma kafin nurse din ta dawo, ta jagorancesu zuwa office din doctor, miqewa yayi tana ganin haka itama ta bi bayanshi Har suka karaso office din doctor.

Tunda suka shiga office din amra ta kafa mashi idanu ganin yanda yake magana da doctor din fuskanshi dauke da dan murmushi kamar bashi ba, gaisawa tayi da doctor din kafin ya masu nuni da wajen zama dake fuskantar shi,shuru ne ya biyo baya lokacin da doctor ya fara bayani, kallon Amar doctor yayi yace “uhm I wanted to send the results to you saidai dole saikazo don Akwai tests da dole we have to run”

Gaban Amar ne ya dan fadi dukda bai tabbatar da hasashen shi ba, saidai he’s sensing something, dukda he’s prepared with Duk wani outcome na result din don ya bar komai wajen Allah don shike badawa kuma shike hanawa.

 

Mika Ma Amar file din doctor yayi kafin ya danyi shuru don ya bashi damar dubawa da kanshi, tunda ya rike file din gabanshi yake faduwa ya kasa budewa, amra dai ta shiga rudani da tunani, don sun barta a duhu.

Saida ya dan runtse idanunshi kafin ya bude file din ya fara karantawa, baima kaiga karasa karantawa ba ya kai idanunshi ga result inda “negetive” ya fito baro baro a jikin, wani irin sanyi jikinshi yayi don yasan me hakan ke nufi, na farko batada ciki na biyu kuma bazai sake haihuwa ba, aje paper din yayi ya dan runtse idanunshi, doctor ma ganin haka ya soma mashi bayani yace “I’m very sorry,…there’s nothing we can do about it but we have to run some tests on you, and we can also re-do the pregnancy test again to confirm if you’re not convinced with the…”

“No need for that”

Ya fada yana dagowa ya sauke idanunshi da yayi jaa sosai Har jijiyoyin Kanshi na tashi, akan doctor, “no need for the test also, mikewa yayi ya kalli doctor tare da mika mashi hannu yace “thank you”

Kafin ya fuce, amra da sai a lokacin ta fara dago

Zancen nasu ta miqe ganin ya fuce itama tabi bayanshi, abunda ke yawo a kind dinta shine “test?” “Pregnancy”

Kanta itama ya gama daurewa sosai don bayani take nema,

M5 na ganin fitowarsu yayi saurin bude mashi kofa, itama bata tsaya m5 ya bude mata ba ta shige cikin motar ta kalleshi tace “can you please explains what’s going on”

Yanda ta fada ma ita kanta bata san ta fada ba,bai dago ba haka zalika bai ce mata qala ba Har saida m5 yaja motar suka bar wajen.

Magana ta sake mashi daka mata tsawa dayasa Ranta yayi mugun baci tana son taji dalilinshi na taho wa da ita asibiti don Idan Har tayi la’akari da komai ya tafi da ita asibiti ne don tabbatar da Idan tana da ciki, so me hakan ke nufi kenan? Daman tun farko ya ajeta ne to confirm Idan ta samu ciki? Ko kuma yanada wani hidden agenda ne akanta da bata sani ba, Har suka karasa gida bata cikin sukuni kwata kwata, tunda ya dafe kanshi bai sake dagowa ba Har suka karasa gida yayi saurin ficewa daga motar ya wuce sama, bin bayanshi tayi itama Har zuwa dakin nashi, anatse ta bude kofar dakin ganinshi zaune bakin gado tayi saurin karasowa kusa dan nesa dashi tace “please I will like to know why you take me to the hospital?“

Dan dago da idanunshi yayi da sukayi jaa ya kalleta yace “get….out ….of my room before you regret coming in here”

Dakewa tayi ta cire Duk wani tsoron shi don abun nashi ya fara yawa, it’s just a question she ask kuma tana buqatar sani, tace “noo I’m sorry I’m going no

31 / 94