wani progress shiyasa yake Ganin komai na Nigeria yana baya, babu cigaba kwata kwata, yanxu inda achan dubai ne da tuni an rufe shafin sa kamar yanda aka rufe na alif dukda cikin sirri ne saidai hakan bazai yuwu ba don ba a kasar bane dole saida sojojin nigeria da maaikanta dake karkashin ta.
Bai dade a office din asad ba ya wuce forensic lab don ko asad bai fada ma komai akan plans dinshi ba, akwanakin baya da aka kama saurayin daya so smuggling drug din, an kamashi da kwayar wadda dakyar amar ya samu ya dauka sample dinta daga chan headquarters don Har an kai maajiya mai karfi,haka ya taho da ita Nigeria,da farko baiyi tunanin bincike akan kwayar ba anan Nigeria sai daga baya private investigator dinshi ya buqaci any little hint akan bunciken da sukeyi nan amar ya tuna da kwayar, take suka kai forensic lab don su duba abubuwan dake cikin kwayar don suyi tracking drugs manufactories na nan Nigeria, buncike ne mai karfi don kamar yanda private investigator dinshi ya shaida mashi dole sai sunyi abubuwan da are illegal don su samu amsan da suke buqata.
Lokacin daya karasa lab din yaga result hankalinshi yayi mugun Tashi, don sinadarin abubuwan da akayi amfani dashi wajen production din kwayar masu illa ne sosai,don masu karfi ne sosai da suke illah, musamman idan akayi over dosing, result din kawai ya karba yayi saurin tura ma investigator dinshi kafin ya koma gida.
Tun akan hanya ya lura da Ana binshi abaya, bai wani damu ba ya cigaba da tafiya harya karasa gida hankali kwance.
Alhaji kabiru…..
Zaune yake wayar da yake expecting ya shigo, hankali kwance yayi sipping drink din dake cikin cup dinshi kafin ya daga wayar, magana akayi chan kafin
ya sauke wayar ya na murmushi, aranshi yace “alif you’re useless to me now, bana buqatar ka,”
Dariya kawai ya kece dashi kamar wani zautacce, kallonshi Aman dake gefenta anan guest house dinshi yayi yace “dad what’s your plan now? Ka rigada ka gano yaron nan na buncike akanka, ya zakayi dashi kenan?”
Kallon dan nashi Alhaji kabiru yayi yace “kasan ance idan kana son kama karamin kwaro saikayi amfani da abunda zai kasheshi directly”
Wata irin dariya yayi ya sake kallon Aman yace “weakness!!!!!, I’m going to use him, atafin hannuna yake,idan kaga an kama hero toh an tabo weakness dinshi”
Kallonshi kawai Aman yayi yana dan murmushi yaqe shi yasan abunda hakan ke nufi. Tunani ya soma yi yanda zai yi stopping din baban nashi don kiri kiri yanason ya salwantar da rayukan da basu jina basu gani ba.
Ganin ya fada tunani yasa kabiru cewa “kai dan ubanka fatan Ka rarraba wa mutanenka wanda na baka kwanaki?”
Firgigi Aman ya dawo daidai yace “eh, Ina buqatan more badge, kudin suna nan cikin gida yanda kace a ajiye su”
Juice Alhaji kabiru ya sake kurba ya kalleshi da kyau yace “why do I feel like you’re changing? Yau kai da kanka Ka aje min kudi na? Ka daina kashewa kenan?”
“No dad, kawai I’m being serious ne,when it comes to business it’s strictly business”
“Now that’s what I’m talking about, I’m proud of you,go and spend it, kudinka ne tunda na ubanka ne babu wanda zai hanaka” Alhaji kabiru ya fada yana wani shu’umin murmushi
Wani tunani aman yayi take yaji wani irin dadi aranshi yace “Zan iya diba yanda nake so?”
“Yes son,” Alhaji kabiru ya fada don yaji dadin yanda Aman yake nuna interest dinshi akan business din, daman burinshi kenan,yanxu yana jin zai iya yarda da danshi sosai.
Wani card ya aje agefen Aman yace “spend as much as you want, bazan sake hanaka ba”
Kallon card din Aman yayi cike da tambaya don card din baiyi kama da card din zarar kudi ba,kamar Alhaji yasan abunda ke cikin ranshi don haka yace “entrance key”
Godiya sosai Aman yayi mashi kafin ya fuce daga gidan jikinshi na rawa, daddy dai dadi yake ji sosai Ganin Aman na bashi hadin kai ayanxu.
Wani call dinne ya sake shugowa wayar alhaji kabiru bayan fitar Aman, yana dagawa yace “kuma bibiyarshi?”
Jan ido ne yayi saurin cewa “yea oga, da alamu bai karaya ba, don kamarma cikin sirri yake wasu abubuwan,“
“Ina da Ina yaje yau” Alhaji kabiru ya tambaya
“Forensic lab,munyi kokarin sanin abunda yaje yi achan bamu samu ba, saboda wajen Akwai security sosai”
Dariya Alhaji kabiru yayi yace “ay daka fada min da baku wahalar da kanku ba, ni nasan me yaje yi chan”
Yana kaiwa nan ya kashe wayar, ahanakli ya soma cewa “you’re not ready to give up, Saina koya maka karamin hankali”
Ya karashe yana jefar da glass cup din hannunshi, gaba daya ya fashe anan kasan.
Aman na karasawa gida kamar zautacce ya wuce cikin tsohon part dinsu inda nan ne secret ma’ajiyar alhaji kabiru da yake aje Duk kudadenshi harda stock drugs din, ahankali ya bude kofar yabi gidan da kallo, komai taaftsaf babu datti Yan nan yanda yake, wani irin hawaye ne ya soma zubo mashi lokaci guda tunawa da rayuwar da sukayi a cikin gidan tare da mahaifiyarshi kallon kujerar data zauna lokacin daya kawo mata juice din da ya daddy ya saka mata drug aciki yayi, I can clearly recall ranar,ya dade sosai a tsaye kafin ya daga kafanshi ya fuskanshi dakunan, normally idan zai aje ma dadi kudin a cikin daya daga cikin dakunan yake aje mashi, dukda yasan ba anan daddy ke ajewa ba bai taba tunanin son shiga inda yake aje kudin ba, wato dakin daya banbanta da sauran dakunan, gaban dakin ya tako ya tsaya, kofar is smart don idan akayi attempting shiga tana warning din Alhaji kabiru,
Card din daya bashi ya dauka ya saka a kofar, ahankali kofar tayi verifying ya bude,ahankali yasa kai ya shige, da farko babu komai a cikin dakin don empty room ne sai shelves dake tsagaye da dakin saida ya saka kafanshi yayi taku daya nan take shelves din suka fara budewa, ba karamin furgici ya shiga a wannan lokaci ba, duban dakin yayi da kyau Ganin ko’ina is surrounded with cameras, maido da idanunshi yayi kan shelves din dake shaqe da different currency na kudi, daga kan dollars, euros, naira, dirhams babu wanda babu a ciki,Dayan gefen shelves din kuwa different types of drugs ne ashake,ahankali ya dunga zagaye dakin, daidai wajen wani safe ya tsaya aranshi yace “I’m sure anan yake ajiya molly”
Dan taba wajen yayi safe din na sensing finger prints dinshi ta fara Kara, mai gama tunani ba daddy ya kirashi yace “kaida Nace Ka dauka kudi Ka tsaya kana shirme daban”
Gaban Aman ne ya fadi damm, wato daddy na kallonshi kenan, saurin tsaida nutsiwarshi yayi yace “sorry dad, dan Allah daddy Ka nuna min wannan molly dinne”
“Why kake so Ka gani?” Daddy ya tambayeshi
“Kawai inason naga yanda take”
Kashe wayar Alhaji kabiru yayi ba tare da ya bashi amsa ba, juyawa Aman yayi jiki a mace, dan tsayawa yayi jin safe din ya bude da kanshi, juyowa yayi don he was amazed, dady nada control akan komai kenan, lallai yau ya sake tabbatar da how dangerous he is, karasa bude safe din yayi nan take yaga molly din a cikin safe din, hayaki na fita daga safe din, hannunshi ya saka a ciki nan take yaji wani irin sanyi kamar cikin safe din freezer ne,wayarshi ne yayi kara Ganin number daddy yasa ya dauka “don’t touch, inba so kake a yanke hannun naka ba, kasan how strong and effective wannan drug din yake? Ba a tabawa da bare skin”
Saurin cire hannu Aman yayi dukda yana cikin furgice yace “wow daddy you’re genius”
Dariya kawai dady yayi ya kashe wayar, sai Aman ya kalli wajen da kyau kafin ya rufe safe din ya koma wajen kudi ya deba bundle biyu na dollars kafin ya fuce daga dakin, koda ya fito da Amar yaci karo yana shirin parking, da sauri ya shige cikin gida, ammah na Ganin shugowa shi tayi welcoming dinshi baima taaya ya amsa ta ba ya wuce dakinshi yana sauke wani wahalallen nunfashi,he can’t believe what he just did, gaba daya ataorace yace ahanakli ya furta “ya Allah ka bani karfin gwiwar abunda nake shirin yi” rigar jikinshi ya soma un buttoning saida ya zo na tsakiya ya finciko camera daya maqala a wajen, da sauri ya samu gefen gado ya zauna ya jawo wayarshi ya shiga app din mini unnoticeable camera din yayi connecting nan take Duk inda yaje d conversation dinshi da dady ya bayyana akan screen dinshi, Har cikin safe din saida camera ya dauko, wani irin sanyi da daci yaji a zuciyarshi, “I have to do this,I’m doing what I’m supposed to do years back, ya Allah ka karfafa min” ya fada ahankali.
Yana nan zaune ya kasa motsawa Har aka kira sallar magrib, mikewa yayi ya dauro alwala kafin ya sauya kaya zuwa jallabiya ya fito zuwa masallaci, yana futa Amar shima ya fito, ammah dake zaune babu abunda yake sai murmushi Ganin aman ya fara natsuwa, Aman ne ya karaso inda take yace “ammah na seems like you’re in a good mood today”
Murmushi tayi ta kalleshi tace “yea son I am, by d way kaje masallaci Ka dawo inason magana dakai”
Sunkuyar da kanshi yayi don yasa me hakan ke nufi don haka yace “okay, nima inason zamuyi wata muhimmiyar magana”
Mikewa yayi tace “adawo lpy”
“Ameen” ya amsa mata
Amar bai fito daga masallaci ba saida akayi sallar isha’I, yana idarwa yadanyi adduoi kafin ya futo, dake masallacin cikin estate ne few steps zai kaika cikin apartment dinsu, tundaga nesa ya hango aman a bankin gate, kauda kai aman yayi har ya karaso inda yake, kamar bazai ce komai ba ya kalleshi yace “excuse”
Dan dagowa aman yayi yana wani nazari kafin yace “inason zanyi maka wata magana”
Tsayawa aman yayi ya hade hannunshi a kirjinshi alamun yana sauraron sa
“I don’t have to say much, Ka aje Duk wani buncike da kake yi,”
“Why?” Amar ya tambayeshi ba tare da yaji tsoron abunda yake fada ba
“Because you’re going to hurt people around, I’m just advising you” Amar ya fada kafin ya wuce ciki ya bar aman tsaye da mamakin shi, bai gama tunanin ba ya jiyo muryar aman yace “be careful”
Murmushin gefen baki amar yayi kafin ya shige cikin gidan, dakin ammah ya wuce direct, yana zuwa ya taddata kan sallaya, zama yayi kan couch din dakin saida ta idan ta shafa kafin ta karaso can couch din, kallonshi tayi da kyau kafin tace “baka fada min zaka kai yarannan ayi masu passport ba, is there something that I need to know?”
Shuru ya danyi kanshi a kasa kafin ya kamo hannunta ya dago yace “ammah na, nasan you trust Duk wani decision dina, nasan u understand me better, gobe da karfe goma zaku wuce dubai,”
Bude baki tayi zatayi magana yace “no please ammah, dan Allah karki ce komai, you trust me right?”
Girgiza mashi kai tayi kanta Duk ya gama kullewa, maisa yake don su tafi dubai cikin gaggawa haka,
“Son, I trust you and your decision, shiyasa I never question you on that, but hakan bazai hana zuciyarta tunani da kokonto ba,”
“Ammah I promise I will explain everything daga baya, don Allah kiyi min alfarmar hana zuciyarki tunanin komai, kinga yanda health dinki yake yanxu,I don’t want to say anything for now”
Murmushi kawai tayi ta shafa kanshi tace “I owe you thousands of explanation son, Allah ya kaimu goben”
“Ameen” ya amsa mata shima fuskanshi dauke da murmushi
Bai wani dade ba a dakin ammah ya fuce zuwa dakin su salima, da sallama ya shiga dakin, a zaune yake daga ita sai yar shigo da dogon wando, karasowa yayi cikin dakin, da sauri ta janyo hijab dinta ta saka tace “Ina wuni ya Muhammad”
“Lafiya” ya amsa mata atakaice
“Get your ready you’ll be traveling with ammah tomorrow Insha Allah” ya fada yana juyawa
“Okay ya Muhammad Allah ya kaimu”
Chan kasan maqoshi ya amsa da Ameen, yana shirin fita lanatana na kokarin shugowa, hannunta rike da bowl din fruit, gaishesa tayi kafin ta shige ciki, kallon salima tayi daga sauke hijab din data saka tace “yarinya mai kyawu ga fruit din”
Da sauri ta tako Har inda lantana take ta karba bowl din tace “thank you anty lanatana”
Kallonta lantana tayi tace “naga ya Muhammad din naku yanxu daga nan ya futo?”
Ba tare da tunanin komai ma salima tace “eh”
Fita lanatana tayi tace “saida safe”
Daki Amar ya wuce kai tsaye, kayan jikinshi ya sauya zuwa pjs kafin ya zauna kan couch ya janyo laptop dinshi ya soma wasu ayyukan yana nan zaune ya kafa ma laptop dinshi idanu, file din da suka samu a cikin flash drive din nan ya tsaya mashi arai babu yanda baiyi ba ya kasa budewa,Har hiring manyan hackers saida yayi but yaqi budewa kwata kwata don wani irin encrypted password aka saka wanda file din da shi da babu Duk daya ne idan babu password din, kamar ma password din shine video din gaba daya, Har wajen karfe hudu da rabi yana nan zaune barcin ma ya kaurace ma idanunshi, gaba daya, haka ya miqe ya dauro alwala ya wuce masjid yana dawowa ya wuce bathroom
Ya watsa ruwa don yaji dadin jikinshi da yayi mashi tsami, yana fitowa baima tsaya ya saka kaya ba ya bi lafiyar gado nan take barci ya fuzgesa mai nauyi, bai wani jina da barcin ba karar wayarshi ya karade kunnenshi, bude jajayen idanunshi yayi da barci ke kwance akai ya jawo wayar ya ansa ba tare da sanin wanda ke kira ba, da sauri ya bude idanunshi tare da cewa “send it through my email”
Miqewa yayi daga kwance ya zauna, janyo laptop dinshi yayi ya kunna, direct ya shiga cikin email dinshi, nan take email din investigator din yayi popping, ahankali ya soma bin diddigin yanda Alhaji kabiru yake sayar da kwayoyin da yanda yake transferring komai zuwa wata kasar , runtse idanunshi yayi yace “this Isn’t enough,”…kamar zaiyi shutting system din chan kuma ya tsaya Ganin wani email da bai taba budew ba, gaba daya tubda yake bude email dinshi bai taba Lura dashi ba, duban sunan sender yayi nan take hankali shi ya Tashi Har hannunshi na Rawa wajen dannawa, sunan meeda ne baro Baro, bude email Din yayi babu wani bata lokaci, nan take yaci karo da wasu numbers, nazari ya fara gaba daya tunanin babu inda ya tsaya sai password din file din nan, da sauri yayi copying ya shiga cikin file din ya yayi pasting take file ya bude, wata irin Kara ya buga “yesssssss!!!!!”
Kamar zautacce haka ya dunga bin file
Din da kallo Har ya rasa wanne daga cikin video zaiyi playing don kusan guda uku ne ajere, video farko ya soma playing, fadin irin tashin hankalinshi daya shiga a wannan lokaci bata lokaci ne, lokaci guda Allah ya bayyana mashi abunda yake nema shekara da shekaru cikin kankanin lokaci with just a clip, ga Alhaji kabiru nan Baro baro shida mutanen shi su alif suna meeting, da yanda introduction din ya fara Alhaji kabiru’ na zaune don shine head of the empire bayan su wani katon board ne an rubuta empire suna magana akan production din product din da suke developing wato molly, second kuwa gaba daya wurin production dinsu ne wanda bama a cikin nigeria bane achan waje wajen kasar ne inda babu wanda ya taba tsammani, na uku kuwa list of production da sukayi
da amount of product da suka sayar da Duk wani illegal transaction da komai ma a rubuce yace, mikewa Amar yayi ya gyara towel dinshi dake neman faduwa kasa yayi sujudul shukr, finally at long last ya gano komai, aggauce ya tura komai zuwa encrypted portal dinshi, barcin ma ya nemeshi ya rasa gaba daya, idanunshi dai na nan sunyi jaa sosai, yanxu ya gano komai yanada strong evidence akan daddy, ayanxu abunda ya rage mashi shine ya dauke ammah daga gidan daga baya sai yaji da komai, don bazai so taji komai ko tasan komai ba don zaiyi shocking dinta ga yanayin zuciyarta.
da sassafe ammah ta Tashi cikin shiri, black abaya ce a jikinta wanda ta amshi jikinta sosai tayi mata masifar kyau, dakin dady ta wuce, tana shiga wayam, daman tasan ba kalli ta sameshi ba son yanxu yawanci baya kwana acikin gidan, already bashi da matsala da Duk inda zataje da wani tafiya da zatayi don haka bata damu ba kawai ta sauko kasa, kitchen ta wuce direct nan ta tadda lantana tana ayyukanta na shirin breakfast tana Ganin ammah ta tsugunna ta gaisheta,
“Lantana zamuyi tafiya yau, jiya nan samu na fada maki da wuri ba, zaki koma gida idan muka dawo saiki dawo ko,”
Kudi amma ta mika mata dubu hamsin tace “ga wannan ki aje zai maki amfani kafin mu dawo”
Murmushin yaqe lantana fuskanta gwanin nan tausayi tace “hajiya yaushe zaki dawo”
“Bazamu wuce sati biyu ba Insha Allah, Muna dawowa Zan kiraki”
“Hajiya gaba daya gidan zaku tafi” lantana ta tambaya
Dariya amma tayi tace “wannan tambaya haka lantana Ay bazamu dade ba Insha Allah zamu dawo”
“Toh hajiya allah ya kiyaye”
Karfe takwas da rabi daidai suka fito gaba daya breakfast suka farayi suna gamawa ammah ta shiga dakin Aman don bai fito break fast ba, a kwance ta taddashi yana barci, karasawa bakin gadonahi tayi ta shafa kanshi, ahanakli ya soma bude idanunshi harya sauke akanta “good morning son”
Murmushi yayi mata yace “good morning ammah na”
Mikewa yayi zaune ya kalleta Ganin ta cikin shiri yace “zakije asibiti ne?”
“No son zanyi tafiya ne,”
Shuru ya danyi yana Nazari kafin yace “okay”
Tayi mamakin yanda ya amsa don haka tace “duka gidan zamu tafi Harda yaran, ko saka biyomi daga baya?”
Dan dagowa yayi ya kalleta yace “no ammah Akwai work anan, I have a lot to do sai