kuke tantama akan shine ko bashi bane? ‘’ amar ya sake tambayar su
‘’saboda da daddy yace sun mutu gaba dayansu kuma salim yace yaga sun mutu’’
‘’kunga gawarsu ne?’’ ya sake tambayarsu
‘’ah ah bamu gani ba’’ suka bashi amsa a tare
Nunfasawa yayi yana kallon inda amra ke zaune yace
‘’okay akwai wani abu ko tabo da kukasan abban ku yana dashi?’’
Shuru duk sukayi gaba dayansu kafin salima tace ‘’ah ah’’
Amra ne ta katse su bata dago ba kanta a kasa tace ‘’eh, abban mu yana da yanka a keyarshi bazan manta ba duk sanda naga yankan saina taba wajen’’
Girgiza masu kai kawai yayi ya fuce daga dakin, yana futa amra ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi sosai.
After 1 month….
Karfe biyar na yamma, Amra ne zaune a sitting room din kasa gefenta yan triplets dinta ne kowannen su yana cikin baby swing,hannunta rike da waya tana latsawa, sallamar amar ne ta sata dagowa, sunayin ido hudu ta kauda nata gefe, yau kusan wata guda kenan baya shiga harkanta itama bata shiga nashi, saidai yazo ya kula yayanshi yayi pecking dinsu sannan ya futa, ita kuwa ko a jikinta don daman hakan takeso, ko yanxu ma daya shugo gaban yayanshi ya tsaya yayi pecking dinsu, ammah ne ta fito daga kitchen gefenta maid ce hannunta rike da warmers suna jerawa akan dining, kamshin amar ne ya shaida mata ya dawo, don haka ta soma takowa zuwa sitting room, yana hangota kuwa ya mike tsaye yace ‘’barka da yamma ammah’’
‘’barka son harka dawo’’ ammah ta amsa shi
‘’eh yanxu na shigo,’’
‘’yauwa daman inata jiran dawowarka, yarannan kuwa bazaku koma asibiti ba?,sunqi karban mama kwata kwata sai madara, kodan sun saba da madarar ne na kasa ganewa, yau saura kwana biyu suyi arba’in fah’’
Shuru amar yayi yana dan nazari kafin yace ‘’okay gobe saimuje’’
Tunda suka fara Magana amra batace komai ba, wannan sabon shuru shurun nata yana damun ammah sosai, don tun bayan ranar da suka hadu da mahaifnsu ta sauya gaba daya, bata Magana, bata walwala ko kadan dukda farin ciki ya kamata tayi.
‘’daughter, daughter tunanin me kikeyi ne haka?’’ ammah ta tambayeta, dan dagowa tayi tana dan sauke murmushin karfin hali tace ‘ba komai ammah, kaina ke danyin ciwo’’
‘’allah ya sawaqe gobe inkunje saikiyi ma doctor complain ko?’’ ammah ta fada tana kallonta
‘’tohm ammah’’
Daukar little princess amar yayi ya wuce dakinshi da it aba tare da ya kalli inda amra ke zaune ba.
Washe gari da safe suka wuce asibiti, salima ce yar rakiya don tana rike da rike da princess kullum bata rabo da ita sai lokacin barci don yawanci hidiman ta ita keyi daga kan abunci zuwa changing diapers, Hamid ne ma da Hamad amra ne dawainiya dasu dukda yawanci ma suna wajen ammah, yara dai sai wayo sukeyi da girma sukeyi bulbul gwanin burgewa, babansu kuwa Har lokacin jin su yakeyi aranshi sosai, harda maman nasu, saidai irin halayen data tsiro ne yasa ya danyi baya baya da ita don yana kallonta ne kawai ya bata space din data buqata, bayan wannan ma ya lura tun bayan lokacin da Allah ya hadasu da mahaifinsu ta zama wani iri, bata walwala kwata kwata wanda yasan dalilin hakan.
Suna isawa asibiti suka fito daga motarshi, zagayowa yayi ya amshi Hamad daga hannunta kafin su wuce cikin asibitin.
Basu wani jima ba suka fito, fuskan Amar wasai shi kadai yasan abunda ke cikin zuciyarshi, game da bayanin da doctor yayi masu akan rashin Shan mama da yaran keyi, wanda ya shaida masu normal ne hakan ba wani matsala bane don wasu matan ma dakansu suke hana yayan nasu mama saboda wasu dalilai.
Karfe biyar daidai suka iso taura estate, direct apartment dinsu Amar ya wuce yayi horning bayan an bude gate ya cuna hancin motar wajen parking space, yana parking suka fito gaba dayansu, amra ce agaba sai salima a biye da ita har suka iso main entrance,
Da sallama suka shiga cikin gidan, waigowa ammah da malam labaran sukayi fuskansu dauke da murmushi suka kalli inda suke tahowa, karasowa amra tayi salima na biye da ita kanta a kasa
“Har Kun dawo sannun ku daughter”
“Thank you ammah, amra ta amsa tana sauke kanta kasa ta kalli inda labaran ke zaune cikin shiga ta alfarma kamar bashi ba, “Ina wuni”
“Lafiya Lau anini baba” ya amsa ta yana murmushi
Cikin sauri amra ta dago ta kalleshi, har lokacin murmushi yake mata yana kallonta,mikewa ammah tayi ta karbi Hamid da hamad da suke hannunta don gaba daya yanayinta ya sauya, “Abba?? Yanxu da gaske kai abba ne? Ka tuna mu?”
Amra ta fada tana kallonshi, “kwarai kuwa shatun baba, mai gashin Yan india mai komai dozin “
Wannan kirarin da yake mata bazata taba mancewa dashi ba har abada, sai ayanxu zuciyarta ta samu sallama tabbas wannnan mahaifinta ne, ko ada chan kwanaki da Allah ya Hadasu bawai bata yarda da shi din mahaifunsu bane saidai wasi wasin da zuciyarta keyi mata ne yasa ta shiga rudu, cikin sauri amra ta mike ta karasa inda yake ta rungumeshi tsam tana hawaye, “Allahu akbar abba na, baban anini dakai zamuje makka”
Tana kaiwa nan ta kyalkyale da dariya, murmushi gaba dayansu sukayi don idan yayi mata kirari abunda take fada mashi kenan itama “abba yaushe memory dinka ya dawo? Ya akayi ka tuna mu?” Salima ta tambaya, kallon inda take yayi yace “ mai irin talent din babanta, hope dai Har yanxu kina zanen? Don na tuna lokacin da kike cewa ummanku zaki gado abba, kema zaki dinga yin Zane kuka zaki zama mata gida babba”
Hawaye ne ya sauka akan idanun salima ta karaso inda suke hannunta rike da princess tace “abbah!!!!”
Rungumesu yayi gaba dayansu yana godiya ga Allah kafin su zauna, Amar da tun shigowansu ya kafe su da idanu yana jin dadi aranshi saidai bazaka gane hakan ba harya karaso parlor din Duk suka zaun gaba dayansu bayan an gaggaisa.
“Alhamdulillah, babu abunda zance saidai nayi godiya ga Muhammadu, shine yayi sanadiyar dawowar memories dina don shine ya dinga kaini repressed
memory therapy har Allah yasa komai ya dawo min alhamdullah, ada banso na yarda ba saboda bana son tuna komai don babu abunda Zan tsinta aciki sai abubuwan da zasu sanya min bakin ciki da irin cutar da akayi min saidai mijinki aisha daya kawo min shawarar neman past life dina saboda mu samu sauqin Amincewa da juna, don nasan hankalinku bazai taba kwanciya dani ba har sai Kun tabbatar ni mahaifinku ne, haka zalika nima hankalina bazai kwanta ba dukda inajinku a jinina, cikin ikon Allah sai gashi allah ya dawo min da komai, Allah ya jiqan mahaifiyarku” gaba daya suka amsa da Ameen Harda amra dake cikin wani irin jin dadi sosai.
Hira suka dan taba inda ammah ke tambaya “baban aisha..”
“Baban salima dai ammah” salima tayi saurin katse ammah,
Dariya sukayi gaba dayansu Harda malam labaran kafin ya maida kallonshi ga ammah “hajiya bazan gaji da gode maku ba, Allah ya saka da Alkairi Nagode Nagode sosai allah ya Kara arziki da Rufun asiri”
Gaba daya amsawa sukayi da Ameen, kallon inda amra labaran yayi yace “Aisha yanxu ke
Uwace kuma kin mallaKi hankalinki, Ina rokon bazaki bani kunya ba zaki kunya ba, Ina rokonki da kiyi ma mijinki biyayya, bakuda wasu fatan daya wuce su hajiya, koni da nake matsayin uban daya haifeku inada iko daku sosai saidai ayanxu bakuda kamar hajiya da Muhammad, ni Zan koma katsina wajen inna”
Dagowa amra tayi kamar zatayi hawaye tace “abba tafiya zaka yi?”
“Eh anini dole na tafi wajen inna don dole duniya ta shaida da raina ban mutu ba,”
“Toh amma abba Kar daddy…”
Saurin katseta yayi ta hanyar cewa, “Bana son ki saka kanku cikin alamarin nan, nasan tsoro ku ko zai sakeyi jin wani abun ko? Babu abunda zai iyayi min da yardar allah”
Gyaran murya ammah tayi tace “baban aisha ni Ina Ganin why not muje gaba daya katsinan, saboda hankalinsu ya fi kwanciya gaba daya”
“Ah ah hajiya bana son na jawo ku cikin matsalalolin…”
“Haba baban aisha yanxu mun rigada mun zama daya, mun hada zuria daya don haka Duk mun zama daya, zamuje tare dakai katsinan Insha allah gaba Dayan mu Harda yaran”
Sunkuyar da kanshi yayi kasa “allah ya saka da Alkhairi hajiya saidai…”
“Baba ayi hakuri abari muje gaba Dayan kawai” Amar ne yayi saurin katse shi with his calming voice,
Dan jinkirta yayi kafin yace “Toh shikenan babu damuwa muhammadu allah yasa hakan shi yafi alkhairi”
Gaba daya kowa ya amsa da Ameen.
Waazi sosai malam labaran yayi ma amra bayan sun rakoshi ita da salima lokacin da zai wuce gida, kafin suyi mashi sallama su koma gida.
Weekend na zagayowa suka dunguma zuwa katsina, kowannen su cikin shiga ta alfarma, kowa yasha manyan kaya masu shegen tsada, Harda malam labaran, amar ne yayi masu booking flight abuja to katsina inda yayi preparation din komai don bazasu kwana ba zasu dawo aranar, a motar amar duka suka dunguma suka wuce airport, suna zuwa Amar yayi parking motar wajen airport parking service.
Karfe goma dadai flight dinsu ya daga zuwa katsina cikin business class,wanda Amar yayi masu booking gaba daya business class din gaba daya,
Amar ne da malam labaran da Salim a gaba gaba while su amra da salima da ammah a baya baya don suna rike da su baby Hamad a hannu, amra dai tunda ta lumshe idanunta bata budesu ba har suka daga, Hamad na hannun ammah while princess na wajen babanta sai Hamid da salima ta rike shi yanata faman tsala kukan sa,“adda Wallahi yaqi karban milk din ni bansan ya zanyi mashi ba, yaro sai ci tubarkallah shiyasa yake zama chubby kullum har yafi yan uwansa qiba”
Kallonta ammah tayi tace “haba mama salima, yau da kanki kike complain keda kullum kike jin dadi idan ya fara neman abunci?”
“Ay ammah babyn Nawa ne Akwai rigima, ba kamar princess ba babu ruwanta kinga yanda tayi shuru abunta wajen dadyn ta”
Dariya amra tayi batace komai ba don tana jin kunyan ammah sosai indai tana waje to fah bata wani shiga alamarin yaran, karshe dai dataga kukan nashi yaki karewa tace “kawoshi,kece kike yawan jagwalgwalamin yaro”
Saurin toshe baki tayi tunawa da ammah na wajen don tana jin kunyarta sosai”
Dariya ammah tayi aranta tace “yarinya mai kunya kenan ba kamar ubasu ba? “
Ay bata gama rufe baki ba sai gashi ya taho hannunshi rike da princess fuskanshi tam “ammah why’s he crying ne?”
Wani irin kallo ammah tayi mashi irin na Ka bar sirikinka saboda baka da kunya Ka taho duban danKa, “ga mamanshi nan Ay Ka tambayeta”
Ammah ta bashi amsa a kule, ya lura da hakan don haka ya kalli amra yace “meysa yake kuka?” Da mamaki ammah ta juyo ta kalleshi wato bai san gatse ba kenan?, chap wannan abun kunya da nuna so karara ga yayanshi ya wuce tunaninta.
Karfe sha daya daidai suka sauka a Umaru Musa Yar'adua airport dake garin katsina, wata zabgegegiyar suv mota ce mai nunfashi ke parke tana jiran isowarsu a arrival parking lots, Amar ne ya jagorancesu Har inda motar take kafin ya karba key din daga hannun yaron daya kawo motar, cikin motar kowa ya shige kafin yaja motar. Malam labaran na gefenshi cikin shigar alfarma while su amra na bayan motar suna kula dasu triplet,.
Malam labaran ne ke jagorantarsu acikin motar Har suka iso anguwar, cikin natsuwa Amar ke driving yana kallon anguwanin Har suka shigo wani layi,
“nan ne” labaran ya fada yana mashi nuni da gidan, parking Amar yayi daga gefe Ganin wasu yara suna wasa a kofar gidan kamar almajirai.
Amar na parking ya bude motar kowa ya fara saukowa, suna fitowa ya rufe motar kafin labaran yayi amau jagora su amra dai na daga gefe suna biye dasu don suna rike dasu triplets, kowannensu yayi kyau sosai, daga chan nesa salima ke hango yaran dake wasa tana nazari,Har suka karaso inda yaran suke wasan su, kama haba salima tayi don Duk a tunaninta ko tayi gamo ne,ko ta fara gane gane, kallonta amra tayi Ganin ta tsaya tana kallon yaran suna suna kallonta,
“Kai jalal kaga wata mota mai kyau irin taohuwar motar daddy”
Dan jaa da baya salima tayi don sun zo dan da yaran, Salim ma kuri yayi masu da idanu yana tunanin waennan fah, wanda aka kira da jalal ne yaja hannun dan uwan nasa suka shige cikin gida a guje suna ihu, “mummy anyi baqi,wata katuwar mota ce Tayi parking”
Hajiya kareema dake zaune tayi nashe Nashe da katon cikinta akan tabarma tana cin masara tana kallon hanyar shugo wa cikin gidan, gaba daya gidan yayi wani uban datti ga qudaje ko’ina don tsakar gidan ma wari yakeyi sosai saboda hannun daddy daya soma rubewa,gefenta daddyn ne da yau kusan watanshi biyu baya iya daga hannunshi da kafarshi daya, kullum yana kwance jinyar yau daban ta gobe daban,
Kallon yaran tayi Ganin sun shugo a guje tace “ku kuma daga Ganin mota tazo anguwa saiku dauka nan zasu shigo”
“Wallahi da gaske muke” jalila ya bata amsa
Shuru ta danyi tana nazari, “to kodai Muhammad ne ya zo?” Ta tambayi kanta, daidai nan khady ta futo da tulin kayanta na gwanjo ta kullesu Harda yar kwalliyarta tasha bulin hanci, tana taunar cingum, yanda yake tauna kamar wata tsohuwar kilaki, “dan Allah Zan fita kuma zanyi dare, karma ku jira dawowata,” ta fada tana kallon Inda karema ke zaune washa rere
“Toh yar albarka bazasu jiraki ba, ammah dan Allah ki ajiye mana dubu mana yau don mu samu ko dan balangu ne mu saya muci”
“Kutuma, lallai ma, don rashin godiyar Allah irin taku shine kike tunanin Zan ajiye dubu? Wanda nake bayarwa ma Kun raina kenan”
Sallama akayi Inda labaran ya shigo Amar na biye dashi tare dasu ammah da amra Duk lokaci guda suka shugo inda khady batama Lura dasu ba ta cigaba da zazzaga mata rashin kunya “ki Tashi wannan mai zaman banzan mana, Ay shine ya kamata ya nemo bani ba, kinga nifa na gaji da wannan masifar taku, Wallahi in ban shiga duniya ba ba sunana khadija ba, na gaji, ace iyayenka Duk sun zama asarraru, wannan wace irin masifa ce, fita ma yanxu wahala take min saboda wannan shegen cikin da kikayo, shi kuma wannan gumama bansan amfanin shi ba, sunan uba kawai yake takama dashi babu amfanin da yake mana aikin banza mteww”
Tana kaiwa nan ta dago ta kalli inda jalal yake tace “kai Tashi Ka fitar min da gwanjon…”
Kalamanta ne suka maqale don kwata kwata bata ma san mutane san sun shigo ba. Su amra dai kasa motsawa sukayi gaba dayansu suka binsu da idanu kowannen su ya toshe hancinsa saboda wari, Amar dai shi ta yayansa ma yake don wannan wasun zai iya illatar mashi da babies dinshi, labaran dai mutuwar tsaye yayi ganin dan uwansa a kwance hannu a shanye, ko ba a fada mashi ba ya gane matar kusa dashi kareema ce wato matar yayan nashi ta farko kenan,
Kamshin daya bade gidan ne yasa dady ya bude idanunshi da sukayi jaa tsabar azaba ga cin mutuncin da khady take yi mashi, rai abace yace “tsinanniyar yarinya Allah yasa idan jin fita karki dawo, wannan sabon kamshin daga Ina haka” yana kaiwa nan ya sauke idanunshi akan fuskokin da bai tantancesu ba, kareema dai tun bayan khady ta gama zazzaga mata nata tijarar idanunta ya sauka akan mutanen da suka shugo gidan, wani hazo hazo ta fara gani don bata yarda da abunda idanunta ke gane mata ba…
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 151
Update
Unedited page
Daga nesa daddy ya hango baban su amra dake tsaye yana kallon daddy, kallonshi daddy yayi da kyau kafin ya zabura ya mike zaune, shida baya Tashi da kanshi saidai a daga shi saiga shi ya zauna jiki na bari ya fara furta “wa inaahu suleimanu wa innahu….ku kuke Ganin mu bamu muke Ganin ku ba, na shiga uku kareema na fara gane gane, innalillahi wa inna ilaihi rajiuna kumin agaji, kodai na mutu ne nima”
Kareema dai dake zaune a gefenshi itama wata irin naquda ce ta kusan zuwan mata daga nan zaune don Harda futsarin zaune tayi bata ma tasan yi ba, daman zanin dake daure a jikinta ba wani zanin arziki bane, hankali atashe take kallonsu daya bayan daya, tabbas idanunta sun hango mata badaru, badaru dai, gefenshi kuwa wasu mutane ne da bata gane su bama kwata kwata don itama badaru ta hango, khady ce Tayi wulli da kullin nata tace “amra?????? Salima kune??”
Yanda take kallonsu ta zaro idanu cike da mamaki haka suma suke kallonsu kamar sunga tv dukda hancinsu a toshe yake, asma ce ta fito daga cikin uwar dakan su da ledar arziki ma babu da yar sandarta tana dogarawa,
Kiff kiff da idanu kareema tayi tana kallon inda khady ke nuni da ikirarin sunan su amra, gabanta ne ya bada dam tana kokarin mikewa zaune tana kakkbe zanin nata jiki na bari don tabbatar da abunda idanunta ke gane mata, amra dai hannun salima ta kankanme itama hannun nata ta rike tana kallonsu su duka,
Lokaci guda kareema ta burkice ta Dora hannu aka “na shiga uku ni kareema, Wallahi su ne, kadai wata masifar kuka kwaso yayannan kuka dawo nan don wallahil azeem babu abunda zaku tsinta anan, wannan kuma daga Ina kuka kwaso shi kamar ubanku?”
“Kinga sunyi maki kama da matsiyata ne?” Ammah ta fada tana murmushi ta karaso inda suke, “babu abunda suke tafe dashi sai alkhairi,wannan kuma mahaifinsu ne dai da kuke tantanma akanshi bai mutu ba yana nan da ranshi”
“Karya ne Wallahi karya ne, akan idanuna motar ta kone karya ne Wallahi,“ daddy ya fada yana rawar jiki kamar mahaukaci
“Ka daina rantse wa Mustapha, ban mutu