futa yayi kwanciyar sa hankali kwance.
Update!!!!!!
Yau kusan kwana biyu kenan rabonta da dashi,haka zata wuni a parlor bata saka shi a idanunta ba haka zalika idan dare yayi haka nadine zata tasheta dan barci ya kwasheta anan zauna a parlor, idan ta tambayi Nadine ko ya dawo cikin rashin sa a zata shaida mata ya wuce daki.
Tun bayan kai masa coffee datayi tya korota bata kara yunqurin shiga dakinsa ba don tsoron ma ya ninku akan wanda yake mashi a baya, goga kuwa yana sane da ita bayaga wannan Ma ayyuka sun mashi yawa don abubuwan dayazo yi sunma nunku akan wanda ya tarar.
Yau weekend bai samu fita ko ina ba saidai yana kunshe daki kamar koda yaushe yana aiki, baici wani breakfast ba Sai coffee daya buqata nadine ta kawo mashi wanda yasha kusan sau uku, dayake shiba ma’abocin cin abunci bane sosai, farar jallabiya ne a jikinshi sai zabga kamshi yake yi, zura bedroom slippers dinshi yayi wanda suka fidda da asalinsa kyawun yatsunshi kamar na mace wanda suna nan kamar na jariri babu tabo ko daya, kallon agogon hannunshi yayi ganin karfe 3 na yamma ya sashi tunkarar kofar dakin nasa ya bude ya fito saida ya tsaya a sitting room din daman kafin cikin kamewa ya nufi hanyar stairs, yana sauka stairs din farko ya dan tsaya tare da kallon dakin nata, wani tunani ne yazo mashi harya tunkari kofar dakin nata sai kuma ya juya ya nufi stair din kasa, amra wadda ta kurama tv idanu hankalinta sam baya jikinta, idanunta sundan fada, doguwan rigar shan iska ne ajikinta as’ual kanta yar hula ce data danyi baya kadan don kusan Rabin sumar kanta a bayyane yake, bataji motsin saukowan shiba don hankalinta yayi nisa sosai saidai kamshin turarensq dake shiga hancinta kadan wanda take alakanta shi da kama gidan da yayi gaba daya, zura hannayenshi yayi cikin aljihun jallabiyan nashi, saida ya mata kallo daya tsaf kafun ya kauda kanshi gefe ya fara takowa zuwa sitting room din, saida yazo daf da ita don tana zaune a kan 3 seater dake facing tv station, nan take taji turarenshi ya shiga cikin hancinta sosai, runtse idanunta tayi kafin cikin hanzari ta soma bin parlorn da kallo, karaf idanunta suka sauka cikin nashi, mikewa tayi zumbur da sauri tare da sauke kanta kasa, tunkarar inda yake yayi cikin sauri tayi baya, zama yayi inda ta tashi tare da daura kafanshi daya kan daya, maida idanunshi yayi zuwa ga tv , bai cemata kala ba haka zalika itama batace komi ba Sai wasa da yatsunta datake, kamar wadda aka tsungula tayi saurin dago idanunta ta mashi kallo daya ganin fuskan nan babu yabi ba fallasa tayi sauri kauda nata gefe tace “barka da fitowa”
Shuru babu amsa daman batayi tsammanin amsawan nashi ba, bata ida tunanin ba yace “call that lady”
Cikin sauri Harda dan gudunta ta nufi hanyar kitchen, bayanta yabi da kallo yanda mazaunanta suke muskutawa dalilin gudu da take, saida ta daukema ganinshi kafin ya maida idanunshi kan tv, fitowa tayi Nadine biye da ita a baya, chan gefe ta samu ta tsaya kafin nadine ta soma magana “gani sir”
Bai kallesu ba su duka idanunshi kan tv yace “what do you cook for lunch”
“Sir mac and cheese ne sai pepper soup”
Shuru ya danyi kafin yace “prepare tuwo against dinner”
Shiru Nadine tayi hankali tashe tace “I’m sorry sir but ban iya tuwo ba,”
Mugun kallo ya watsa mata kafin yace “daga wani company aka kawoki”
“Cameroon sir”
Shuru ya danyi na Yan mintuna bai sake cewa komi ba, amra dake tsaye kamar munafuka ta dan dago ta kalleshi da gefen ido kafin ya sauke wata dog uwar ijiyar zuciya tace “in ba damuwa na iya Zan dafa”
Karo na biyu daya dago kenan ya kare mata kallo harna da bakin nata daya karshe zancen, jin yanda yayi shuru yasata dagowa idanunta suka shige cikin nashi, da sauri ta sauke nata kasa, tabe bakinsa yayi ya fuzge ganin Nadine na wajen ya sashi hana kanshi abunda yake shirin fada yace “okay”
Da sauri ta dago fuskanta dauke da dan murmushi tayi saurin cewa “miyan me kake so”
Bai kalleta ba yace “anything”
Cikin jin dadi ta kalli Nadine tace “muje”
Wucewa kitchen sukayi kitchen yana jin yanda she’s so excited, maida kanshi yayi baya yayi relaxing tare da shafa suman kanshi data taru kafin ya dan runtse idanunshi shi kadai yasan me yake ji.
A kitchen kuwa da idanu Nadine ta dunga bin madam dinta don wannan ne first time dataganta tana fara’a,nan take Nadine ta shiga taya ta fito da abubuwan da zata buqata don saida yasa aka zuba duk wani kayan abunci da za a buqata a gidan, cikin kwarewa amra ta dora ruwan tuwon shinkafa yanda zai ishesu duka, kadan kadan ta soma hira da nadine wanda tayi mamakin cewa ita ba yar Nigeria bace, aiki ne ke kawo su nigeria, cikin nishadi suka sauke tuwon inda amra ke nuna mata yanda ake mulmula tuwon a cikin leda, abun saiya kayatar da nadine don batasan tuwo ba, suna gamawa nadine ta dauko hadden warmer masu shegen kyau ta aje, nan ma amra ce ta jera tuwon a cikin warmer din, suna gamawa Nadine tace “ma, me zakiyi da wannan duka” ta fada tana nuna alayyahun da amra ta zaro daga cikin fridge da nama da bushahhen kifi Harda ganda.
Yanda tayi maganar yabama amra dariya tace “zanyi amfani dasu ne duka, abunda zanyi we call it miya, dashi ake cin tuwo”
Jinjina kai nadine tayi kafin tace “I want to learn from you ma”
Dariya kawai amra tayi ta bata jajjage tayi mata a cikin chopper, tana gamawa ta wanke mata su naman da Sauran, cikin qanqanin lokaci qanshin abuncin ya bade gidan, tun daga kitchen Har wajen gate, general dake zaune tunda ya jiyo kamshin ya soma hadiye miyau, sun dauka kusan awa biyu kafin su Kamala komai,su amra da kaudi harda su coconut drink ganin Akwai abubuwan hadawa available a cikin fridge, fita Nadine tayi don sanar dashi an kammala komai lokacin an soma kiraye Kirayen sallar magrib,bata sameshi a sitting room dinba don haka ta koma kitchen.
Futowa amra tayi daga kitchen din ganin baya sitting room din yasa ta wuce sama bata kaiga shiga daki ba ya sauko kasan kallo daya ya mata ya dauke kanshi tare da wucewa, tura kofar dakin ta tayi ta shige tare da jinjina kallon da ya mata kai Wayar fassara, dauro alwala tayi kafin ta tada kabbarar sallah, tana idarwa tayi soma addua, tana nan zaune aka kira sallan isha’I,mikewa tayi ta gabatar da sallah isha’I tana idarwa ta ninke sallayan ta soma tube kayan jikinta,
ta wuce bathroom wanka tayi da shower baths dinta masu kamshi lavender kafin ta Nado jikin ta da towel ta fito, zama tayi gaban dresser ta shafo kanta daya nannade sosai alamun yana buqatar gyara, karema kanta kallo tayi tsaf daga fuskanta zuwa kirjinta, fuskanta yayi fayau saidai ya soma dawowa daidai dalilin kukan nata data rage saidai damuwa da baza a rasa ba don tana son ta samu suyi magana dashi don ta nemi gafarar shi akan abubuwan da suke faruwa wanda a ganinta Duk ta dalilinta ne hakan ta faru,bayan wannan Ma tana son ta komawa Yan uwan ta don yanxu auren kuma babu amfani,zamanta dashi Ma babu amfani, saidai tana jin kunya da tsoron tunkararshi don tana ganin hakan kamar tayi mashi butulci ne saidai dubaga ga auren yarjejeniya ne tsakaninsu abu daya ne zai faru wanda saiza ta daina jin zafin kasancewa wanda ta lalata mashi aikinshi shine jin nashi dalilin aure ta da kuma buqatarshi ta auren da ya zama yarjejeniya tsakaninsu bayan wannan Ma tayi Ma kanta alqawari kome ya buqata zatayi mashi indai bai saba addini ba don cika alqawarin yarjejeniyar.
Manta na Orel ta janyo ta shafe jikinta dashi kafin ta bude closet din dakin don ta jera Yan Kayyyakinta a ciki, kayan barci ta janyo riga da wando masu sulbi, rigar ta dan kamata daga sama wandon ka ya zauna dam a jikinta daman ga yanayin jikin nata irin na manyan mata ko ina yaji kaya, Dan turare ta feshe jikinta dashi kafin ta janyo hularta, bata kaiga gama saka hular ba Nadine tayi knocking, ta sako kai, ganinta a dan burkice yasa amra kallonta da kyau
“Ma sir yace kije yanxu”
Tana kaiwa nan yasa kai ta fuce, amra kuwa ganin yanda Nadine ta shigo yasa ta saurin bin bayan nadine hular Ma bata ida sakawa ba ta bude kofar da sauri ta fuce zuwa Kasa, ganin babu kowa a dining din Sai karar ruwa dake sauka a kitchen yasa ta bin hanyar kitchen din, ganin Nadine a tsaye tana wanke wanke yasata cewa “yana Ina ne”
“Laa Ma baki tafi ba, yana sitting room nashi na sama yana jira”
Juyawa amra tayi da dan sassarfa ta wuce hanyar sama, koda takai kofar dazai kaika ga sitting room din saman saida yadan tsaya ta saita natsuwarta gaba daya ta manta a wani yanayi take ganin yanda Nadine ta rufe zuwa kiranta, knocking ta fara yi, jin shuru yasa ta sakeyin wani knocking din, ganin kamar babu kowa a sitting room din yasata bude kofar Bakinta dauka da sallama, babu kowa wayan, takowa tayi Har wajen dining ganin baya nan yasa ta wasi wasi ko ta karasa bedroom din tayi mashi knocking, ganin tsayuwanta ma anan bata lokaci ne wanda baya son hakan yasa ta karasawa gaban kofar kanta a Kasa, bata kaiga knocking dinba ya bude kofar, kamshinsa ne ya daki hancinta wanda shima kusan hakan ne don kamshin turarenta mai sanyi ne ya bugi nashi hancin, idanu suka hada nan take tayi Kasa da nata wanda ya bashi damar kare mata kallo sosai tun daga sama Har kasa, sanyin baya tayi kadan ta koma gefe don bashi hanyar wucewa, fuskewa yayi ya soma takawa zuwa dining ba tare da yace mata qala ba saidai zuciyar wani irin mugun bugu take yi ganinta da yayi, zama yayi akan kujeran dining din, jin shuru ba ya sashi yin Gyaran murya yace “na kiraki ne don ki tsaya”
Cikin karfin hali ta tattara natsuwarta ta karaso gabanshi ta tsaya kyam, dagowa yayi ya zuba mata idanuwanshi nan da Har wani ruwa ne ke kwance a cikin kwayar idanun, Dan dagowa tayi ganin inda yake kallo yasata saurin kallon kanta, take taji wata irin kunyarsh dukda ba wannnan ne karon farko ba da ya ganta da kayan barci,
Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa “ni zanyi serving kaina ne, I hate it when my time is wasted”
Da sauri ta dunfaroshi har yana iya jin motsin jikinta ta soma bude warmers don, janyo plate tayi daga cikin dinner set din dake jere tayi ta soma zuba mashi tuwon, ganin tana shirin Kara dauko wani tuwon zata zuba yasashi cewa “ke zaki cinye shi kenan”
Jin hakan ta gane cewa ya mashi yawa, batayi wata wata ba ta maida shi ta bude warmer miyan, koda kanshi ya bugeshi saida ya lumshe idanu kafin ya budesu kan plate don ta da matso dashi kusa dashi, ararrabe ta bude baki tace “bis…millah..” bai dago ba ya kurama abuncin idanu, daukan glass cup tayi ta zuba mashi coconut drink din dayasha madara tayi ta aje a gefenshi cikin natsuwa, saida ya karemata kallo tass yanda take komi cikin kwarewa da natsuwa,
Juyawa tayi zata wuce yace “come back”
Dawowa tayi tadan rabe gefe ta tsaya, dagowa yayi ya runtse idanu ya sake cewa “bana son yawan magana,”
Da idanu ya mata nuni da kujeran dining, janyo wa tayi ta zaune chan nesa dashi, bismillah ya soma yi kafin ya dauka spoon ya saka a cikin plate din ya Debo tuwon hade da miyar allayhun da tasha kaji da kifi da mama Harda ganda, koda yakai bakinshi saida ya runtse idanunshi sosai, harta tauna, dan dagowa tayi don ganin expression dinshi, fuskan nan dai babu mai iya karantar ta don a hade take, tana ganin haka ta sauke idanunta kasa feeling so sad, bangaren general kuwa inba Ammah ba bai taba cin abincin da ya tafi da imani shi ba kamar wannan, yarinya karama with bless hand ya fada a ranshi, saida ya kusa loma biyar ya tsagaita chan kasan maqoshi yace “great cook “
Dan dagowa tayi din bataji me yace ba tace “uhm”
Mugun kallo ya watsa mata ba tare da yace komi ba ya janyo coconut juice din yakai bakinshi, shima saida ya lumshe idanunshi don ya mashi dadi, saidai bai wani sha sosai ba ya goge bakinshi ta tissue ya miqe tareda wuce hanyar dakinsa bai kaiga rufe dakinba yace “zo nan”
Gabanta ne ya bada daranmm dukda bata kawo komai ranta ba, Mikewa tayi tabi bayanshi harya shige dakin kafin tayi sallama ya shiga itama tsaye ta ganshi yana shirin cire jallabiyan saurin kauda kanta tayi gefe tare da damke hannayenta biyu
“Fix the beddings”
Yana fadin haka ya wuce toilet don harya zare jallabiyan ya aje kan gado ya rage daga shi Sai boxers dinshi tana ganin shigewarsa kuwa tayi saurin takowa gaban gadon ta soma gyara mashi, bata wani dade ba ta gama Gyaran gadon
nashi, tare da ninke jallabiyanshi bin dakin tayi da kallo don neman closet dinshi Sai a lokacin ta karema dakin kallo yafi nata girma da haduwa sosai kana gani kasan dakin master bedroom ne, idanunta ne suka sauka kan frame din dake gefen gadon, dauka tayi ta kura masu idanu sir general ne yayi kyau lokacin baikai haka ba Sai wani babban mutun a gefenshi wanda tana kyautata zaton babanshi ne yanda suke rungume da juna suna dariya sai abin ya sata yin murmushi harta sha’afa, general da kusan mintuna biyu da fitowanshi kugunshi nade da towel da karami don bai kaiga qwiwanshi ba Dayan kuma na kan sumarshi yana goge wa ya tsaya tare da rike kugu da hannu daya ya zuba mata idanu, yanda yake murmushi ya sanya dimple dinta da bai taba gani ba ya fito sosai, takowa ya soma yi ya tsaya a bayanta kamar Ana fusganshi, kamshinta na shiga hancinsa don yayi dan da ita sosai, amra kuwa jin sahun mutun a bayanta ya sata firgita frame din yayi kasa saurin saqala hannayenshi yayi wajen kugunta ya zamana tana tsakiyanshi ya taro frame din tare da dan dukawa kasa kadan, saurin juya kanta tayi jin hannunshi dake da danshi wajen kugunta, runtse idanu tayi sosai ta budesu akanshi shima ita ya zubama idanu sun dauka kusan minti daya a wannan yanayin ya kasa cire hannunshi daga kugunta don da hannu biyu ya taro frame din, amra kuwa yanayin daga shiga mata misaltuwa ne, nan take wani baqon yanayi yazo mata jinshi dab da bayanta, tana son kufce mashi saidai babu hanyar kubucewa, shiko oga ya Kasa yin komi ne sbd towel dinshi da ya soma warwarewa dalilin dukowan da yayi, yana son cire hannayenshi daga kugunta saidai yana tsoron yin kwakwaran motsi Kar ayi abun kunga gaban yarinya,wata da bata ce ta fadi mashi ya rankwafo kanshi daidai wuyanta tare da saqalo kanshi wajen ya daidai kunenta ya sauke nunfashi wanda ya sata runtse idanu tare da damke hannayenta sosai ta rufe ido, sauke mata wani nunfashin nashi yayi this time around harda Jan nunfashin yayi alamun yana don yin magana saidai wannan abu ya kawo mata baqon yanayi, ahankali kamar mai rada yace “close your eyes”
Idanun data rufe ta gwalo su waje,ganin kamar bata cikin hayyacinta ya sashi dan fada da karfi “I said close your eyes”
Firgigi ta dawo hayyacinta ta rufe idanun gam don a tsorace take sosai
Yana ganin haka ya dauke kanshi a hankali tare da rike frame din da hannu daya ya riko towel din da Dayan hannun, sauke ijjiyar zuciya yayi don yanda yayi hasashe kuwa towel din na gab da sauka kugunshi ja yayi da baya ya karema bayanta kallo sosai, how curvy she’s is giving him hard hard, sanin yanayinshi ya sashi dauke idanunshi daga kanta gaba daya yace “get out”
Juyowa tayi ahankali idanunta sunyi dan jaaa zata bude baki tayi magana ya tari nunfashinta “out!”
Wani iri taji, hawaye na shirin zubo mata mara dalili don a tunaninta ta dauka fasa mashi frame data kusa yi ne ya sashi haka, hanyar fucewa ta bi saida ta bude kofar har zata futa ta dan daga murya murya tace “dan allah kayi hakuri yaya”
Wani kallo ya wurga mata daya sakata saurin janyo mashi kofar ta wuce daki Harda dan hawayenta.
Tana futa kuwa ya lumshe idanunshi gam yana jin yanda dumin jikinta ke dukan nashi lokacin daya tsaya a bayanta.
Niko Nace anya general bai kamu ba kuwa, lolsss
Tunda ta futa ya kwanta kan gadon tare da janyo bargonshi dake kamshinsa kayanda bai saka ba kenan sbd jin kamar feelings na taso mashi kadan kadan tunanin maganr doctor ne ke yawo a qwaqwalwarshi.
Tana komawa daki ta kwanta tana tunin rayuwarta da lokacin da ya shigo cikin rayuwarta, yunwa ke nuqurqusar ta saidai ta Kasa Tashi don wata kasala ce tazo mata wanda ta Kasa ganin dalilin zuwanta.
Tana nan cikin tunanin data fada barci ya kwasheta mai dadin gaske.
Karfe 2 na dare taji wani irin qululun ciwo ya dunfarota a mararta, zumbur ta miqe zaune, chaf ta manta da period dinta dake hanyar zuwa, mikew tayi cikin sassarfa ta bude Jakarta ta fara buncikar maganin ta saidai duban duniya tayi bata ganshi ba hankali tashe ta tuna ta barshi achan dubai cikin dayar jakarta ta office, rasa abinci tayi don kadan kadan ya soma zuwan mata, samun waje tayi ta zauna a Kasa tare na hade kafafunta don daman haka take yi don samu sauki, wasa wasa Har karfe hudu tana nan tun tana iya miqewa harta galabaita ta natsu waje daya anan kasa, kuka kuwa wiwi kamar an mata mutuwa, tana nan zaune har aka kira sallah lokacin ta soma jin zubowarshi, toilet ta wuce da sassarfa nanma saida ta dauka kusan