da Nadine ta aje ba ta fuce zuwa sitting room din part din, zama tayi Nadine dake biye da ita tayi serving dinta aranta tace “rayuwa kenan mutun ya samu daula irin wannan Ay babu damuwar da zai shiga”
Har Nadine zata wuce kasa don zuwa nata bangaren don ta samu itama taci abuncin amra ta tsaidata ta hanyar cewa “let’s eat together pls”
Nadine taji dadin haka don haka ta janyo hadaddiyar kujerar dining din ta zauna ta zuba abunci yanda zai isheta tace “thank you ma’am”
Bayan sun kammala ta koma daki while Nadine ta sauka kasa zuwa dakinta kallon ledar Apple Store da Nadine ta shigo dashi ta bata tayi, sabuwar waya ne iPhone 14pro max same da wanchan da ya saya mata saidai wannan color din ya banbanta da wanchan don wannan milk color ne, sim pack ne a tare da wayar, tabe baki tayi ta cire wayan daga kwarin tayi resetting kafin ta kunna, babu wanda ya fado mata arai Sai haifa don haka ta fara tunanin yanda zata samu line dinta, plugging wayar tayi a charge kafin ta wuce toilet, wanka tayi da na hot bath kafin ta fito, ahankli idanunta suka sauka cikin closet room din dakin,
kofan ta bude ta shiga ciki, bin ko’ina tayi da kallo tana mamakin kayan dake shaqe a cikin dakin, daga kan dogayen riguna zuwa English decent dresses masu shegen kyau, tabe baki kawai tayi tace “ko kayan waye wannan oho” futowa tayi daga dakin don neman kayanta don Duk lokacin nan nadine ke dauko mata wanda zata saka, gaban dressing mirror ta tsaya nan ma ta karema ko’ina kallo tare da tabe baki ta juya, ko kallon wajen bata sake ba ta koma kan gado ta zauna, Nadine ce ta shigo hannunta rike da sabuwar wayarta iPhone 12, kallon amra ta tsaya yi, tana yaba irin kyau da Allah yayi mata,
“Uhm yauwa Nadine inata to ki shigo daman, Ina kayana”
Karasowa Nadine tayi tace “Bari na dauko maki ma”
Cikin closet din ta nufa amra ta bita da idanu tana mamaki harta fito, doguwar Riga ta Shan iska ta dauko mata, kallon kayan tayi tace “this is not my cloth”
Kallon kayan nadine itama nadine tayi tace “sune kayan da wannan soja yace naki ne da zaki dunga amfani dasu”
Kauda kai amra tayi bata ce komi ba, futowa nadine tayi don ta bata damar sauya kaya.
Tana gama chanzawa tayi zamanta a dakin Har aka kira sallar magrib, alwala ta farayi tana fitowa ta rasa abun sallah, closet room ta sake komawa ta janyo abaya da veil ta saka tare da nadawa ta shimfida sallaya ta fara sallah, tana idarwa ta duqufa da addua tare dakai kukanta wajen Allah, tana nan zaune Har lokacin isha’I yayi tana idarwa ta mike ta cire kayan ta maidasu, tana nan zaune Nadine ta sake dawowa ta shiada mata dinner is ready, futowa tayi ta zauna kafin nadine tayi serving dinta, tana shirin tafiya tace “dan Allah ki dunga zama Muna ci tare bana son zama ni kadai”
Dariya kawai Nadine tayi tace “okay ma”
Tare suka ci abunci suna hira jifa jifa, ahankali suka fara sabawa sosai da Nadine don Har tarihin rayuwar ta bata, da mamaki amra ta kalleta tace “Nadine daman kin taba aure?”
Dariya nadine tayi tace “yea ma, Harda baby ma, but babyn ya mutu”
“So sorry Nadine”
Da sauri Nadine ta kalleta “no it’s okay don’t be sorry ma’am”
Kallon mamaki amra tayi mata jin abunda yace, saurin kauda zancen tayi tace “badan jin fada min ba da kanki ba bazan yarda ba, dukda nasan kinada shekaru”
Hira sukayi sosai Sai wajen karfe goma ta wuce daki itama Nadine ta wuce nata dakin don ta kwanta.
Haka tayi spending weekends daga daki Sai sitting room, yanxu tana recovering sosai saidai damuwa da take yawan saka Ma kanta musamman da daddare Idan Nadine ta tafi, gaba daya rayuwarta ta fita aranta, general kuwa bata san wani matsayi zata sakashi a Yanxu ba don gaba daya tunda ta yanke Ma kanta cewa jikinta yake so taji tsanarshi na girma aranta.
Monday morning…
Karfe bakwai daidai Nadine ta shigo dakinta, dakinta is dim don haka ta kunna lights din ta karaso Har gaban gadon ta soma tashinta “ma, wake up”
Bude idanunta tayi da sukayi jaa ta kalli Nadine don jin Karin bayanin tashinta da tayi
“I’m so sorry ma’am, wannan soja yace zaki koma aiki yau shine yace na fada maki”
Shuru amra tayi kafin ta miqe zaune tace “shi yace maki Zan koma aiki yau?”
“Yea ma”
Shuru amra tayi ta danyi tsuka kafin ta Tashi zaune “okay ina zuwa”
Nadine na futa ta wuce toilet, bin toilet din tayi da kallo tana mamakin irin kudin a aka zabga a cikin toilet din don tsarinshi kamar wani daki guda, atsanake ta wanke bakinta tayi wanka da daya daga cikin sabbabin shower bath dataga an jera a kan cabinet, tana gamawa ta nado jikinta da towel ta fito, zama tayi da daki tana Mazarin abunda zata saka, ita fa Har lokacin bata yarda da kayan dake cikin closet ba, don bata son yin amfani da komai daya futo daga hannunshi a sunan shi ya bata ganin bata da wani option yasa ta mike ta shige cikin closet don ya janyo abayar datayi sallah dashi ta saka tare da bra da pants sabbi masu kyau, dukda ba size dinta bane, agurguje ta shirya ta fito, tana fitowa taga an shirya dining, ganin babu Nadine a wajen yasa ta wuce dining din ta zauna ta deba abincin daidai cikinta kafin ta fara ci ahankali, ta dauka kusan minti ashirin kafin ta gama, futowa tayi daga sitting room,idanu ta fara bazata ganin yanda corridor din between part din da stair case ya hadu, aranta tana ayyana wani irin kudine dashi haka, dukda tasan yana da babban matsayi saidai bata taba hango yanada arziki haka ba don ko gidan shi na apartment dinshi batayi mamakin gidan ba don rayuwar nan uae tana da tsada sosai, saukowa ta farayi saida ta sauka second floor kafin ta sauka 1st floor Har takaiga last floor, tana zuwa ta tsaya kyam ta daga idanunta sama, stairs din yayi roud ya zagaye part part din, Gyaran murya da akayi ya ankarar da ita, kallon inda yake tayi “good morning ma’am”
Dan tabe baki tayi don tana bala’in jin haushin sa take, yana ganin haka yace “we’re getting late ma’am”
Yana kaiwa nan ya juya ya fuce yana sauke ijiyar zuciya don daya taaya gabanta Sai yaji zuciyarshi na gudu sosai
Zama yayi cikin g-wag din general datasha tambarin sa na girma agaban motar harma da plate number.
Amra dake tsaye harya fuce ta kalli inda yabi kafin tabi bayanshi, haka ta dunga bin gidan da kallo don zata iya cewa Duk zamanta a dubai bata taba ganin gida irin haka ba Kodan anguwan da take ba anguwan manya bace, tana karasowa dab da kofar fita kofar ta bude da kanta, fitowa tayi ta tsaya ganin yanda harabar penthouse din keda girma sosai kamar palace, tsakiyan compound din Harda wani water fall, dagowa tayi idanunta suka sauka kan motar dake gabanta, horn
m5 yayi kafin ta wuce ind akayi parking yana ganin ta ya futo ya bude mata baya ta zauna, tana zama ya rufe kofar ya shiga shima ya zauna.
Futa ya farayi daga harabar penthouse din har ya hau kan hanya, kallon gefenta tayi kamar ganin laptop da wasu papers kamar daman yana kallonta ta mirror yayi saurin cewa “those are your laptop and your resumption report files,”
Dan dagowa tayi ta kalleshi tace “maysa kazo ranar kace min za ayi arresting dina, maysa kace anyi banning dina, what was the reason for that”
“I’m sorry ma’am but I can’t say anything about that”
Wani irin haushi ne ya turniketa ya kawar da kanta gefe Har suka iso headquarters, entrance security na ganin plate number general sukayi saurin bude babban gate din entrance, said am5 ya tsaya ya nuna card dinshi kafin ya wuce ciki, parking yayi inda ake parking motar general kafin ya kashe motar ya fito tare da bude mata kofar, futowa tayi ta shaki iskan wajen, abubuwa da dama na dawo mata, tana jin kamar this is the first time ta shigo cikin headquarters, files din ya miqa mata da laptop ta ansa tayi wucewanta don Allah Allah take ta karasa ciki don dalilin zuwanta kenan.
Tana shiga reception da mamaki mutanen wajen da suka Santa suke kallonta,office din head of health ta wuce ta bada resumption report dinta kafin ta wuce office din ta, tana zuwa ta tadda Har an kawo sabuwar supervisor da zatayi aiki karkashinta, gaisheta tayi ta bata report din kafin ta wuce office din haifa, tana shiga ta tadda head of team din haifa, dayake ta sanya sosai gaisuwa sukayi kafin ta tambayi haifa, “she’s on leave”
Sallama tayi mata kafin ta fita, taso sun hadu da haifa saidai babu damar haka saboda tana hutu, yanxu zata san yanda zatayi taje gidansu ko ta nema number ta.
Karfe hudu daidai ta fito daga asibiti hannunta rike da Sabon lap coat data karba da laptop sai wayanta, bata kaiga karasawa gaban compound din wajen ba m5 ya karaso da mota inda take ya bude mata, wani banzan kallo ta zuba mashi kafin ta shige cikin motar yaja.
Hammam dake tsaye wajen motarshi yayi mamakin ganinta sosai don yayi zaton general ne ya dawo saidai kuma yasan ba yanxu zai dawo ba don last waya da sukayi ya shaida mashi saiya kammala abunda ya fara anan Nigeria.
Cikin motarshi ya wuce cikin zullumi, yana zuwa gidan shi kuwa wajen karfe goma ya kira haifa don yanxu kusan kullum saiya kirata don toasting dinta yake yi sosai, ba laifi tana dan kulashi sama sama, tana daga wayan ya soma magana, sama sama ta fara amsashi don tayi alqawarin saita gwarashi sosai kafin ta dawo mashi, ganin yanda take magana yasa shi janyo maganar da zaisa ta kulashi, “habibty ashe friend dinki fa dawo”
Bata dago zancen nashi saboda haka tace “wace friend din kenan”
“Generals wife”
Da sauri ta mike zaune tace “are you joking right now?”
“No I’m not, I saw her today at the headquarters”
Mamaki ya hana haifa ce mashi komai saboda bata dauka da gaske yake ba saidai tasan bazai mata karya ba
“How did you know it’s her?” Ya watso mashi tambaya
“She’s with the general personal bodyguard, shine ma yayi picking dinta a motar general”
Mamakin Hammam take, yana wasu abubuwan kamar basai he’s involve in it ba daman kallonshi kawai take don gani take bakinshi daya dashi general din don haka tayi alqawarin zuwa asibitin gobe don ta gane Ma idanunta.
FCT Abuja…
Tun bayan tafiyar amra ya samu kwanciyar hankali saboda ya maida hankali da waje daya wajen ayyukan daya kawoshi, Duk wani link dayasa alh kabiru na hada hannu dasu saida ya gano komai,yanxu kwakwarar sheda kawai yake nema wanda zai nuna daddy nada hannu dumu dumu da Duk wani laifukansa.
Kwana biyu kenan da tafiyar ta acikin kwanakin nan Duk wani movementnata sai m5 ya kawo mashi report, saidai yana cikin fargaba don satittikan da doctor ya deba na conceiving da ya kamata tayi suna gab da karatowa hankalinshi ta wannan bangaren a tashe yake,Duk dare kuwa he can’t like he’s missing body her badly, damma yana daurewa sosai yana kauda wasu abubuwan dake hawa kanshi.
Washe gari weekend tunda ya Tashi yaga anata Yan shirye shirye, bai samu ya Tashi da wuri ba don haka yana fitowa ya wuce sama zuwa dakin amma, yana shiga yaga batanan, yana gab da saukowa salima dake shirin jawo wa saman tayi saurin cew “barka da Safiya ya muhammad”
Bai kalleta ba yace “thanks ina Salim”
“Yana kitchen tare da ammah” tayi saurin amsashi, saurin matsawa tayi ya wuce
Kafin ta karasa zuwa dakinsu, yana sauka kasa ya bi hanyar kitchen din wanda ranar ne rana ta biyu da ya taba shiga cikin kitchen din, ammah dake fidda wasu kula’s masu kyau tana ganin shi tayi saurin cewa “morning son, ka Tashi bari akawo breakfast”
Takowa yayi har inda take tsaye yace “morning ammah, ayyukan me akeyi ne”
Murmushi tayi tace “yau mai gidan zai dawo, sannan zaizo da baqo”
Kallonta yayi sosai yanason Karin bayani saidai baya son ya fara mata tambayoyi don zata iya tanbayar dalilin tambayoyin nashi
“okay”
Kawai ya amsa mata ya Futa zuwa dining,ammah ce da kanta tayi serving dinshi don su already sun karya, saida yaci ya koshi tukunna ya wuce dakinshi ya karasa shirinsa ya fuce daga gidan.
Karfe biyu daidai Alhaji kabiru ya karaso da baqonshi cikin katuwar Land Cruiser baqa wuluk baka ganin komai daga wajen motar kwata kwata, tunda
suka tunkaro titin dazai sadaka da taura estate Amar ke monitoring shida asad babu yanda asad baiyi dashi ba akan yayi zamanshi don wannan ba aikin shi bane zaman jira yaqi yarda,karshe Ma ya hanashi sanya wasu sojojin saboda yanason suyi komai cikin sirri don haka ya shirya zaman dakanshi, tun kafin ammah ta fada mashi yasan da dawowan alh kabiru gidan saidai baqon ne baisan wani baqo ne ba, suna nan zaune motar tasu tazo ta wuce ta gabansu saidai basu samu damar ganin waenda ke cikin motar ba.
Suna wucewa ya dan daki steering din, yasan cewa daddy bazai taba bari clue ba koda kuwa an kamashi dumu dumu, don haka ya kalli asad yace “I have to do this,dude”
Kallonshi asad yayi kamar zaiyi mashi magana chan kuma ya fuce daga motar zuwa Tashi dake Parke a gefe, fusgarta motar yayi tare da horn ya shige cikin gidan,parking yayi a tsanake ya fito yana futowa ya wuce cikin gidan kai tsaye, yana shiga bakinshi dauke da sallama suka waigo suna kallonshi shima kallosu ya tsaya yi, ganin kamar basu da gaskia saidai bazaka taba gane hakan ba Sai kwararri wata yar dariya alh kabiru yayi ya mike tare da karasowa gaban Amar yace “Alhj sammani ga dana fah, general Muhammad taura”
Da mamaki Amar ke kallonshi, tsohon dake hakimce gefe ya juyo don ganinshi, bakinshi dauke da murmushi yace “ah lallai kabiru Mun tsufa “
Hannunshi kabiru yaja Har zuwa falon ya zauna yace “saukar yaushe son?”
Yanda Amar ya kura mashi idanu zaka san mamaki yake da irin abubuwan da alh kabiru keyi wanda ya zame mashi Sabon abu don bai taba kallonshi da sunan da ba Sai gashi yanzu yana nuna kamar nashi ne, ammah ce ta shigo kanta nade da mayafi ta zauna gefen su tare da gaisuwa da baqon, bayan an gaggaisa ta umarci akawo abubuwan tabawa snacks da juices, kallon Amar tayi tace “son harka dawo, naga baka dade da fita ba”
Dago da jajayen idanunshi yayi yace “na manta wallet dina ne”
Alhaj kabiru ne ya katse su “ay daka kira driver ya aiko maka”
Dan murmushi Amar yayi nan ya tabbatar da ya suna bibiyarshi kenan, dariya kawai yayi yace “ ay banyi nisa ba,”
Yana kaiwa nan ya miqe ya wuce daki amma Ma dakinta ta wuce ,alhj sammani ne ya kalli Amar yace “kaii mazaa wannan yaron fah daga gani tsagera na saika kula sosai”
Dariya kawai daddy yayi yace bismillah ga kayan zaqi ko”
Dariya suka kyakyace wanda Duk a kunen Amar da bai idasa shiga daki ba.
Saida sukaci abunci kafin su fara hira ta business, nan Amar ya fito ya taddasu kafin ya ficewan shi, yana fitowa tsakar gidan yabi ko ina da kallo tana son tuna wani abu saidai ya kasa tunawa, kallon gefen bangaren alhaji kabiru yayi, ya dade a tsaye yana nazari kafin ya fuce daga gidan gaba daya.
Sai wajen sallar asr daddy da sammani suka fito suka shiga bangaren sa wanda yake sauke baqinsa a ciki.
Uae…
Next morning…
Wajen karfe takwas Nadine ta shigo dakinta jin shuru bata fito ba,kallon amra tayi dake barci hankali kwance,ahankli ta soma tashinta, idanunta ta bude ta sauke su kan Nadine “ma’amki Tashi you’re getting late for work, wannan sojan tun dazu yazo yana jiranki”
Tsaki tayi tace “tell him bazani ba”
Shuru Nadine tayi kafin ta sauka kasa don kai mashi saqon ta, “I’m sorry but na tashe ta tace bazata je ba”
Shuru ya danyi don Duk tunanin shi ko bata da lafiya ne, wayar general yayi dialing ringing biyu ya dauka baice komi ba yayi shuru da sauri m5 yace “morning sir, I have a report today”
Shuru yayi still baice komi ba Sai sauke nunfashi da yayi yace “go ahead”
“Nazo daukan madam tace bazata je aiki ba yau”
Gyara kwanciyarta yayi yace “why?”
“I don’t know sir, maybe bata da lafiya”
“Go and ask for reason” ya karashe in a commanding way
“Okay….sir”
Komawa yayi wurin Nadine ya kai mata sakon shi, saman ta sake komawa saidai wannan karan ta shiga toilet don haka ta bari ta fito, parlor ta dawo ta zauna, tana nan zaune ta fito cikin shiri, kallon Nadine tayi tace “yauwa daman bana son cin breakfast ni kadai”
Kallonta Nadine tayi ganin ta tunkari dining tace “Ma wannan sojan yace sir yace meysa bazaki jeba?”
Tanajin tace sir ne ya aikoshi ta dan dakata, ta fara tunani, me yake nufi kenan, tsaki tayi ta kalli Nadine tace “seat muci abunci”
Zama sukayi Nadine tayi serving dinsu, Har Nadine ta gama saida ta dauka kusan 30mins taba chakalar abunci, ganin haka yasa Nadine cewa “wannan soja…”
Katse amra tayi tace “Nadine please..”
Tana jin haka taja Bakinta tayi shuru, saida ta gam tsab ta sauko Nadine biye da ita a baya, m5 dake tsaye a sitting yana jiran abunda zai fadama oga yana ganinta yace “morning”
Wani kallon banza ta zabga mashi, saurin kauda kanshi yayi gefe kafin yace “sir yace meysa bazaki je aiki yau ba?”
Kallonshi tayi da kyau kafin ta soma magana “idan Nace bazani ba Akwai wanda ya isa ya sani zuwa ne?, bazani ba and no reason for