stupid, I’ve been blaming my self all this while, what did I do to deserve this?”
Da sauri haifa ta tari nunfashinta tace
“Babe if that’s the case then why would he do that?,maysa zaiyi haka”
“Saboda yaga I’m helpless, saboda yaga banida kowa, haifa he slept with me, forcefully” tana kaiwa nan ta Kara fashe wa da kuka mai shiga rai
“Wahttttt!!” Haifa ta fada da dan karfi tayi saurin gyara zaman wayar a kunenta ta cigaba “he slept with you? How did you let that happen”
Nan take amra ta sake fashewa da wani kukan da zaka gane abun ya taba zuciyarta sosai tace “I don’t want to stay for a second in this house haif,I’m in pain”
“Babe calm down, ki kwantar da hankalin, karki yi saurin yanke hukunci,mubi komai a hankali”
Da kyar haifa ta tausasa ta tare da bata shawarwari, sun dauka kusan awa guda suna magana kafin suyi sallama.
Aje wayan tayi a gefenta ta wuce toilet ta dauro alwala,kafin ta fito ta tada sallah, ta dade sosai kan sallaya tana adduoi da neman taimko wajen Allah, babu abunda yakai tsayawa gaban Allah kakai kukanka, wannan zaman da tayi sai Tashi kashi 50 cikin damuwarta ya ragu, daman batada riko a ranta, saidai wannan ya tabbata sosai, mikewa tayi ta ninke sallayan ta zauna gefen gado, abincin da Nadine ma ta kawo mata bata kalleshi ba kwata kwata, tagumi ta tafka na tausayin rayuwar data tsinci kanta, tawakkali tayi tare da fawwala Ma Allah komai saidai tafiya kam Saitayi ta babu fasawa.
Shawarar da haifa ta bata ta dauka, cikin kwarin gwiwa ta mike shiga tattara kayanta tsaf babu abunda ta bari ta saka acikin akwatinta.
Karfe Tara na dare daidai ta sauko kasa, fuskanta a kubure idanunta yayi jaa sosai, samun waje tayi ta zauna akan kujeran sitting room ta rafka uban tagumi, zaman awa uku tayi anan zaune, idanunta kyam babu alamun barci tana zaman jiran dawowan shi, karfe sha biyu daidai da Yan mintuna taji karar horn hakan ya tabbatar mata ya dawo, gyara zamanta tayi tare da saurin cire tsoron daya durar mata lokaci guda don tayi alqawarin cire tsoronshi daga ranta.
Bude kofar yayi kai tsaye ba tare da tunanin komai ba ya iso Har sitting room din baima Lura da ita ba zaune, Har ya wuce sitting room din tayi saurin miqewa ta fuskanceshi tace “ sannu da dawowa”
Tsagaita tafiya yayi hannunshi duka na cikin aljihun wandonshi, fuskanshi na nan babu yabi ba fallasa Sai zallan gajiya shimfide a kan fuskar tashi, kamar bazai ce komai ba ya dan juyo kadan yace “yau..wa!”
A rarrabe kafin ya juya yana shirin Taka stairs tayi saurin bin bayanshi ta tsaya dan nesa dashi tace “inason magana dakai”
Dakatawa ya danyi bai juyo ba haka zalika bai ce mata komi ba, ganin haka ya sata saurin cewa “daman ina….” Bai bari ta karasa ba ya wuce sama “idan magana kike kiyi dani ki sameni a sama” bin shi tayi da idanu harya kauce Ma ganin ta kafin ta sauke wata nauyayyan ajiyar zuciya, ba tare da tunanin komai ba ta dake tare da tattaro Duk wani kizarinta ta hau saman,tunda ta tsaya bakin kofar dazai sadaka da sitting room gabanta ya soma faduwa, tana jin yanda heart dinta ke racing, saurin danne wa tayi fuskanta babu alamun fara’a ko murmushi Sai damuwa, saida ta fara knocking kafin ta bude kofar, a zaune ta taddashi ya daura kafa daya kan daya idanunshi na kan wayar yana dan latsawa, takowa tayi dan nesa dashi ta kauda kanta gefe don ko kallonshi bata son yi don abubuwa ne da yawa ke dawo mata a cikin zuciyarta data kalleshi ciki kuwa Harda tsiraicin shi data gani mura ran.
Kasa cewa komai tayi yanda shima baice mata Kala ba don kwata kwata bai dago ya kalleta ba tun bayan kallo daya daya mata saidan kallonta da yake ta gefen ido ganin yanda ta kauda kanta gefe idanunta sun dan kumbura sunyi jaa, ganin tana shirin dagowa ya sashi kauda nashi idanun gefe
“Zan tafi gida, Ina buqatar rabuwar auren mu”
Dan dagowa yayi ya kalleta don yayi mamakin futowa daga zancen daga Bakinta saidai baice komai ba ya kura mata idanu yana son karantarta
“Da izinin za zaki tafi?”
Rai Adan bace ta kalleshi ido cikin ido, kafin ta sauke nata don yayi mata mugun kwarjini tace “bana buqatar izinin kowa, zama na anan bashi amfani”
“And who told you that?” Yayi saurin tarar nunfashinta
Baki a sake ta dago ta kalleshi, wani irin abu na tsaya mata a makoshi, saurin runtse idanunta tayi ta bude su yar akanshi tana kokarin tattaro courage dinta tace “bana buqatar aure a kaina tunda anyi banning dina daga uae babu amfanin
auren, daman anyi shi ne saboda yarjejeniya da mukayi, tunda ban samu abunda na nema ba Ina son ka sake ni”
Yanda take fada adan fada fada ya bashi mamaki sosai, wannan yar yarinyar ce ke mashi magana haka lallai ya jama kanshi raini, saidai zai koya mata hankali, rai Adan bace ya kike gadan gadan yayo kanta, saurin jaa baya tayi har tana turgudewa gabanta na bugu fat fat don koshi daya karaso gabanta saida yaji bugun zuciyar, saurin runtse idanunshi yayi idanunshi sunyi jaa sosai yace “how dare you talk to me like that? Bakya bukatar auren? Babu macen data isa ta kalli cikin idanuna ta fada min abunda zanyi, now open your ears ki saurare ni, you are going no where, zaki bar gidan nan only if I say so, and I will only free you when I’m pleased”
Da sauri ta dago ta kare mashi kallo, kallon kama raina kin hankali, shima ita yake kallo kuma tsaf ya gane ma’anar kallon, saurin hana kanta kukan da take shirin yi tayi, tana son bude Bakinta saidai mamakin shi ya hanata, kallonta yayi sama da Kasa kafin ya juya ya wuce dakinshi ya barta a sandare, wani irin haushi da takaicin shi yake ji, me yake nufi kenan? Ai kuwa zata nuna mashi ita ba yarinyar yake kallonta dashi ba.
A zafafe ta fuce daga dakin ranta ya mugun sosu sosai Kalaman shi sun mata zafi,koda ta karasa daki zarya ta fara yi acikin dakin “I will on free you when I’m pleased!!!!” Me yake nufi kenan, ta fada da dan karfi wannan kalaman sunyi mata zafi sosai.
Da kyar ta lallaba kanta taga Safiya ranar don hancin Ma qaurace mata tayi, kuka kam saida tayi shi don idan batayi ba bazata samu sassauci ba, Sai bayan sallar asuba barci ya kwasheta akan sallaya.
Karfe sha daya daidai ya fito cikin shirinsa kamar kullum na kananun kaya, sunyi mashi masifar kyau Sai kamshi yake, wayar shi ce kawai a hannunshi Sai laptop bag dinsa ,saukowa kasa yayi ya bi hanyar dazai kaishi zuwa bedroom dinta, hankali kwance ya danyi knocking ya bude kofar, a zaune ya taddata ta gefen gado ga akwatinta dake gefenta ta dafe kanta, ta dade da Tashi ta tayi wanka ta shirya tana tunanin yanda zatayi, gashi ta kira haifa yafi sau Nawa, idan ta kira baya shiga kwata kwata, knocking din da taji baisa ta dago ba don Duk tunaninta Nadine ce ta shigo dakin, ahankali kamshinsa ke shiga cikin hancinta wanda ke sa zuciyarta racing sosai, saurin dagowa tayi ta mashi kallo daya kafin ta kauda kanta gefe, takowa yayi dan nesa da ita kadan ya kura Mata idanu, saida ya dauke kusan minti biyar a tsaye baice mata qala ba itama bata ce mashi ci kanka ba,rai a bace ya fuce daga dakin ta bishi da kallo harya bace mata daga gani.
Breakfast kawai yayi ya fuce daga gidan, saida ya tsaya wajen masu gadi kafin yaja motar ya bar anguwan gaba daya.
Yana fita daga dakinta ta janyo mayafin abayar jikinta tayi rolling akanta tare da janyo wayarta, taba shirin fita saiga Nadine ta shigo hannunta dauke da tray na
abinci data saba kawo mata, da ido Nadine ta bita ganin ta janyo akwati, bata shiga hurumin da ba nata ba shiyasa tayi saurin cewa “ma’am ga breakfast”
Ba tare da ta kalli Nadine dinba tace “thanks Nadine baba buqata I’m okay”
Tana kaiwa nan ta janyo akwatin nata ta fito daga dakin, tana shirin sauka dashi Nadine ta karaso tace “let me help you ma”
Kasa suka sauko tare ta karbi akwatin tace “thank you Nadine” ta fuce daga parlor, ahankli cikin natsuwa take tafiya Har tazo bakin gate, da sauri security ya futo daga dakinsa don ya hangota ta cctv camera da aka saka a kusa da gate, “good morning ma’am”
Morning tayi saurin amsa mashi, ganin baiyi yunkurin bude kofar ba kuka tasan smart gate ne yasa ta juyo ta kalleshi shima ita yake kallo tace “ka bude gate Zan fita ne”
“I’m sorry ma, but sir yace Kar abar kowa ya fita daga gidan nan”
Kura mashi idanu tayi ta sake cewa “what do you mean?”
“I’m so sorry ma’am I can’t let you out”
Rai abace ta sake kallonshi tace “lub yaushe yace maka Kar abar kowa ya fita”
“Dazu ne ya bada umarni I’m sorry ma”
Rai abace kamar ta shakeshi take ji, wani irin kuka ne yake neman kufce mata, ta wuce cikin gidan rai abace, Nadine da taga shigo wants saitayi makakon ganinta sosai Har ta wuce sama, da sauri gate man ya janyo akwatin nata ya shige dashi Nadine ta karba ta wuce mata dashi sama, koda ta hau sama kuka ta fashe akan gado, ta rasa wani tunani satayi, mai yake nufi da ita kenan, wannan wani irin masifa ne,a dake ka a hanaka kuka, ranta a bace yake sosai, haushin sa ya ninku a zuciyarta.
Koda Nadine ta shigo mata da akwatinta ta tausaya mata ganin irin kukan da take yi
“I’m sorry ma’am bansan meke damunki ba but ba kuka ya kamar kiyi ba, try and fine d solution to your problem”
Dago da jajayen idanunta tayi ta kalli Nadine tace “Nadine please help me out, Ina don barin gidan nan, bana son zama”
Takowa Nadine tayi Har gabanta ya zauna gefenta tace “Bana son shiga hurumin da ba Nawa ba, kuka bazan tambayeki ba, but inaso kiyi hakuri ki daina kukan”
“Nadine Wallahi bana son zama acikin gidan nan, ko Inuwa daya bana son hadawa dashi”
Shuru Nadine tayi don kanta ya gama rikidewa tace “na taba shiga irin halin da kika shiga na tsabar wani abu lokaci guda lokacin ina kamar shekaru ki, saidai na tabbatar matsala ta da taki ba daya bace don bansan menene matsalarki ba”
Nunfasawa tayi kafin tace “you need to be strong and believe in your self, kuka ba solution bane karshe Ma zai Kara maki ciwo ne don kuka ke tunzira mutun, ki gode ma Allah you have everything in life, baki rasa ci ba Baki rasa sha ba, you have a family you can turn to, kinada yayanki wanda ya dam….”
Da sauri amra data kura mata idanu bayan ta tsagaita kukan ta kalleta jin abunda ta fada, saurin kauda kanta tayi tace “how can I calm down bayan bana da kowa bana tare da family’s nawa, banma san a wani hali suke ciki ba”
Cikin mamakin kalamanta Nadine ta kalleta. Ta Kasa dago zancen amra din
“But ma’am you have your brother, you can talk to him”
Dago da jajayen idanunta tayi tace “he’s not my brother, he’s my…husband”
Nan take Nadine ta dago zancen, tayi mamaki sosai, don bata taba tsammanin Akwai aure tsakaninsu ba, Toh indai mata da miji ne maisa babu alamun haka a tattare dasu ta tambayi kanta.
Nadine ta dade sosai a wajenta ba tare da ta tambayeta matsalarta ba ta bata shawarwari wanda ya sata jin sauqin zafi da ranta keyi mata harta samu tayi breakfast ta kwanta don kanta dake mata ciwo sosai.
Bangaren Amar tun bayan fitarshi bayan ya jama driver kunne akan Kar yabar kowa ya fita daga gidan ya wuce wajen da suke haduwa da asad,sun dade sosai suna tattaunawa, ya dade sosai waje shi don har sallar juma’a tare sukayi.
Karfe takwas daidai ya Koma gida, lokacin daya shiga cikin gidan babu kowa a parlor direct ya wuce bedroom dinshi yayi wanka ya sauya zuwa wasu kayan daban wanda suka amshesa kafun ya fito rike da keys dinshi da wayanshi, baibi takan dakinta ba don yaga alamu zatayi kafiya akan abu don haka shi kuma baya son haka don yana ganin hakan kamar raini ne gashi yanxu yaga kamar tayi growing wings don ko gaishesa batayi, abunda ya bata mashi rai kenan daya sashi takaicin…. Saurin kauda zancen yayi don zuciyar shi ta fara masa hasashen moments din su tare, cije lower lips dinshi yayi, ya runtse idanunshi daman kwana yake da tunanin abun a ranshi, don gaba daya Duk Safiyar asuba Sai manhood dinshi tayi kuka alamun how healthy he is,don shi Ma buqaci ne sosai don tunda yayi testing abun ya fara loosing home training dinshi shiyasa ya qaurace Ma ganinta cikin kwanakin bayan dawowar ta daga asibiti.
Daidai gaban gate din Taura estate yayi horning, securities na ganin plate number shi sukayi saurin bude gate din jikinsu na bari don babu wanda yayi expecting sir general zai iso, yaa shiga katafaren estate din yayi parking wajen parking lots dinshi dake shake da motoci kusan guda goma, gefe kuma na kowa ne, shi nashi daban ne daman, yana parking ya fito hannunshi rike da wayanshi Sai briefcase dinshi, da sauri securities suka karaso gabanshi tare da mashi barka da zuwa, kamar koda yaushe rafed daya ya zaro ya basu ya nufi hanyar cikin gida ba tare da ya saurari godiya da suke zabga mashi ba.
Gaban entrance door ya tsaya ya Danna door bell, cikin Yan mintuna kadan lantana ta bude tana hamma don barci ne ya kwasheta ita dasu salima suna kallon wani series anan kasa, tana ganin shi ta watsake tare da rarraba idanuwa tace “barka da dawowa yallabai” jiki na bari ta matsa mashi ya shige ciki kamar basarake, parlor ya karema kallo, kusan shekara uku kenan rabon shi da
kamshin gida, wani irin dadi ne ya ziyarce shi, maida idanunshi yayi ga parlor ganin su salima yashe a parlor suna barka barci yasashi juyowa ya kalli lantana dake karasowa gaban shi tace “Ina wuni yallabai an iso lapiya”
Kamar an mashi dole yace “lafiya, yaran nan fah maysa suke barci anan”
Da sauri ta karaso gabanshi tace “kallo sukeyi ne barci ya dauke su”
Tattara books dinsu tayi tare da fara tashin salima, bai tsaya ba ya wuce bangarenshi daban dake gefen na aman saidai nashi yafi girma sosai don parlor ne da daki Sai bathroom.
Yana shigewa salima na bude idanunta “anty lantana kinga barci harya daukeni”
Kallonta lantana tayi dake shirin tashin tace
“Nima barcin ne ya daukeni saida naji karar door bell na Tashi”
Tabe baki salima tayi kafin tace “yanxu haka hala wannan shugaban Yan yawon ne”
Shuru lanatana tayi tana dariya ciki ciki tace “kedai salim keda mutumin nan Allah ya kawo ranar da zakuyi mutunci”
Da sauri ta kalli kanta tace “anty lantana ni ba haushinsa nake ji ba kawai bana son halinshi ne, baya girmama na gaba dashi ga girman kai mteww”
“Ahh lallai wannan fada Sai ku, bashi bane ya dawo dan uwanshi ne yallabai na dubai”
Da sauri salima ta Tashi zaune dakyau farin ciki bayyane a fuskanta tace “ya Muhammad ne ya dawo? Laaa wayyo Allah yana Ina?”
“Eh yanxu ya dawo ya shige dakinsa ma”
Cikin murna da farin ciki ta kalli lantana “kai naji dadi sosai zabga ya Muhammad nasan mammah zataji dadi sosai daman tun dazu take jiran isowarshi Yanxu haka nasan tayi barci ma”
Sama suka wuce kafin lanata tayi masu sallama ta wuce nata dakin don kusan karfe sha biyu saura.
Yana shiga daki ya bi ko’ina da kallo, an gyara shi tsaf tsaf babu ko dogon datti sanin shi mai tsafta ne yasa ammah tasa lantana ta gyara mashi, dakin nashi bai kai na chan gidansa girma ba amma yasha kayan alatu na duniya Har parlorn shi ma,aje briefcase dinshi yayi akan gado Ya wuce cikin changing room dinshi, daki ne babba sosai wanda yasha wardrop daya zagaye dakin na glass kaya shake a ciki.
Saurin tube kayan jikinshi yayi ya sauya zuwa pjs dinshi kafin ya fuce ya dawo daki yabi lafiyar gado don ya gaji sosai bayan wannan Ma yasan ammah ta rigada tayi barci don tana Shan maganin ta na diabetes da take dashi.
Washe gari murna baibar su salima ba saida suka shiga dakin ammah da sassafe don babu schools an shiga hutun weekends, samunta suka yi tana azkar don haka suka samu waje suka zauna Harda salim, salima dai zumudi ya hanata rufe
baki, ammah na shafawa kuwa tayi saurin dawowa gefenta ta zauna tace “good morning ammah ya jikinki”
Da murmushi ta bisu da ido daya bayan daya tace “morning, Alhamdulillah jiki da sauqi Kun Tashi lafy” ta fada tana shafa fuskar Salim dake mata murmushi shima
Salima ce tayi saurin cewa
“Lafiya Lau ammah albishirinki ammah” yar dariya ammah tayi tace
“Toh fah, goro”
“Ammah yaya Muhammad ya dawo jiya da daddare”
Fuska a sake tace “waya fada maki? Jin ganshi ne?”
Da sauri salima tace “Wallahi anty lanatana ta fada min ya dawo, lokacin muna barci a qasa”
Da sauri ammah ta kalleta don bata yarda ba da farko tace “kira min lantanar”
Da sauri ta mike ta fuce daga dakin cikin Yan mintuna kadan ta Sai gata tare da lantana, Har gaban ammah ga karaso ta duka ta gaisheta
“Lantana jiya Muhammad ya dawo?”
Da sauri lanata ta dago tace “eh ya dawo jiya wajen karfe sha daya da rabi”
Da sauri ammah ta mike tsaye tace “shine baki fada min ba,”
Ayi hakuri hajiya daman naga inkin sha magani kin kwanta ba a tashin ki”
“Muje kasan”
Saukowa sukayi su duka cikin zumudi kafin su shige bangarensa, ganin