Muhammad ya aiki?’’
Ba tare da ya kalli inda take ba cikin kamewa yace ‘’lafiya’’
kallon hanyar kitchen ammah tayi ta kira lanatana tana zuwa tace ‘’ki kwaso abuncin anan zamuci’’
Juyawa lanatana tayi ta dauko food mat ta shimfida kafin ta kwaso abunci, da plates duk ta jera a gabansu, nan Salim shima ya sauko hannunshi rike da game pad ya karaso ya zauna.
Ammah ce ta katse shurun tace ‘’ku sauko, daughters ayi serving’’
Saukowa duka sukayi banda amar daya hakimce, salima ce ta fara zubama ammah kafin tace ‘’yaya mey za a saka maka’’
Ta fada tana kallon amar, aman kuwa harara ya galla mata ya tareta da cewa ‘’samin malmala biyu’’ ya fada kamar shi ta tambaya
gwalo idanu tayi tace ‘’ya mu…’’
Dan mintsininta amra tayi alamun tayi shuru, aman kuwa ya danji haushi saidai baya iya fushi da ita don haka yace ‘’malmala uku zaki zuba’’ dariya suka soma yi mashi su duka harda ammah kafin salima tace ‘’kai yaya ina zaka kai har malmala uku’’ galla mata harara yayi itako ta sauke kanta kasa tana murmushi ta soma zuba mashi, amra na ganin haka ta dan dago ta kalli amar daya hade girar sama da kasa ya tsuke fuska, tace ‘’yaya mai zan saka maka’’
Bazan yayi da ita ammah na ganin haka tadan hade rai tace ‘’son bakaji ana Magana bane’’
Dan dagowa yayi yace ‘’anything’’
Wani irin rashin dadi amra taji amma hakan baisa taji haushi ba ta soma zuba mashi tuwon, dan bowl ta dauka ta saka mashi miya tare da namomi sosai tana gamawa tace ‘’bismillah’’
Dan kallonta yayi kafin ya kauda kanshi gefe ya sauko gefen ammah ya zauna, tana ganin haka ta tura mashi abuncin a gabanshi.
Anatse suke cin abunci suna yar hira, wani irin dadi ammah keji don kana ganinsu kaga complet happy family, addaua ta somayi aranta allah yasa su dauwama ahaka, fatanta yanxu allah yasa abunda take zargi tsakanin aman da
salima ya tabbata, don babu wanda zai kallesu yace basa son junansu, yanxu damuwarta shine amar da yanda yake nuna halin ko in kula da amra, don kamar ma ya amince ne saboda ammah ta hana ya saketa, tasan shi da kafiya son haka ta daura damarar dagewa akanshi.
Suna gama cin abunci lanatana ta kwashe komai,nan aman yayi ma salim connecting game a tv, wasa wasa sai gasu su duka suna game ammah na daga gefe tana kallonsu, amar dai ya hakimce yana latsa waya baice, jifa jifa yake dagowa yana kallon yanda salim da salima da aman ne buga game din suna dariya, amra dai kamar mara jini a jika itama tana daga gefe tana kallonsu, idan anyi abun dariya tayi dariya, ammah ma tana daga gefe tana dariya yanda salima ta hade rai saboda an kusa cireta a cikin game din, ‘’yaya wallahi ojoro kakeyi allah’’ ta fada taa kallon aman dake bugunta a game din da gangan, gwalo yayi mata yace ‘’kedai baki iya ba kawai’’
Hade rai tayi sosai tace ‘’nama hakura kawai’’
Amra ce ta sako bakinta tace ‘’why would you give up?, give it all, keep trying zaki iya kema’’
Juyowa amar yayi ya kafa mata idanu jin zazzagar muryarta da yanda tayi maganar, tadan lafe jikin kujera kamar ba ita tayi Magana ba tana lumshe idanu kamar mai jin barci, shagala yayi da kallonta da yanda take Magana, nan take wani abu ya darsu a zuciyarshi ahankali ya soma Magana yanda babu wanda zaiji dagashi sai ita yace ‘’how can ingrateful person like you have the courage of advicing someone ‘’
Sarai taji abunda ya fada wanda ya sata runtse idanunta ta sauke kanta kasa,kauda kanshi yayi shima ya maida kallonshi kan ammah yace ‘’zanje na kwanta, zan fita da wuri gobe, im preparing saboda zan koma’’
Atare duk suka dago suna kallonshi harda ammah datayi mamakin shi, mikewa yayi yace ‘’good night ammah’’
Yana kaiwa nan ya wuce dakinshi cikin kamewa, kallon amra ammah tayi don ta lura dasu tun lokacin da amra tayi ma salima Magana da lokacin daya kafe amra da idanu har zuwa time din da ya yi mata Magana wanda bata jiba, mikewa itama tayi ta wuce part dinshi, tana zuwa sitting room tayi knocking bedroom dinshi, amar dake zaune bakin gado yana jin knocking din yace ‘’yes come in’’
Shugowa ammah tayi ta karaso har bakin gadonshi ta zauna, sauke kanshi kasa yayi don yasa tunda ya ganta har cikin bedroom dinshi to babbar Magana ce,
Anatse ta sauke ajiyar zuciya tace ‘’muhammd,’’
Dan dagowa yayi ya kalleta kafin ya suake kanshi kasa yace ‘’yes ammah’’
‘’muhammad yarinyar nan tana da wani aybu ne da kake qin wannan aure?’’ ta tambayeshi tana kallonshi, dan shuru yayi kafin yace ‘’no ammah..but’’
Katse shi tayi da cewa ‘’ya isa answer da nake nema ka bani,its looks like nika auroma ita ko?, yaushe ka daina jin maganata muhammd?, why cant you accept the marriage now bayan achan baya kaika saka kanka ba wani ya saka ba?’’
Kasa dagowa yayi haka zalika ranshi duk y agama dagulewa yace ‘’ammah, bana sonta, shes too youndg for me, ni bana buqatar mace itama tunda amfaninta ya kare batada wani amfan….’’
‘’shut up…’’ ammah ta fada da dan karfi
‘’muhammad are you sure kana da hankali kuwa?, kasan mace kuwa? To bari kaji na fada maka, ba a yima mace haka, baa raina mace, mata suna da daraja, nima uwarka mace ce ni, ohh wato ta gama maka amfani ko? Bata da amfani yanxu saboda bata dauka cikinka ba?, ka bani mamaki son, toh wallahi bari kaji, babu saki arayuwarka kama cire wannan, wallahi ko bayan raina ka saki yarinyar nan bazan yafe maka ba, kayi imaging ace yanxu kana da kanwa hakan ta faru da ita, yarinya karama zaka maidata bazawara ? saboda ta gama maka amfani?, kayi saurin janye wannan aranka don wallahi youll regret this word muhammd’’ tana kaiwa nan ta miqe ta fuce daga dakin gaba daya.
Washe gari weekends aman ne ya fita dasu gaba daya zuwa saloon, salima na gaban mota ammah da amra na zaune abaya, gaban wani hadadden saloon and spa suka tsaya, ciki suka shiga su uku, ammah nag aba suna biye da ita abaya, dayake ammah special customer ce suna zuwa aka basu wani bangare na manyan baki, anaste matar dake running wajen tazo gaban ammah cikin girmamawa ta gaisheta, bayan sun gaisa ammah tace ‘’ ga daughters dina nan, agyara mun su,’’
Nuni da amra ammah tayi tace ‘’ita special package zakuyi mata’’
Murmushi matar tayi kafin ta fuce, cikin yan mintuna ta dawo tare da workers dinta, gaban su suka jere wasu product na gyaran gashi don daman haka sukeyi sai sun ajiye sunyi comparing gashin client da mayukan da zasuyi masu amfani dashi base on category din gashin kowa, Kallon amra matar tayi tace ‘’maam zamuga gashin naku don mu san wani product zamuyi maku amfani dashi ko’’
Girgiza kai amra tayi tare da cire veil din doguwar rigar bubun dake jikinta, tana cirewa ta zare ribom din kanta ta warware gashin, da idanu ammah ta bita da kallo , aranta tana jin dadin amar ya samu mata wadda ta hada komai,aggauce aka gyara ma amra kai harda pedicure da medicure mutanen wajen sai santin gashin ta sukeyi kamar ba gashin yar Nigeria ba,nan salima tace ‘’were half Nigerian half maroccan’’
Da mamaki ammah ke kallonsu tace ‘’shiyasa gashin ya fita daban da namu nan ba’’
Sun dauka kusan awa uku kafin aka gama, suna fitowa aman na karasowa, don yaje gida, tare ya dawo da salim a gaba, salima na ganin haka ta gallama salim harara, tana jin kunyar ammah gashi babu damar tace mashi ya koma baya don haka ta hakura ta koma baya, direct mall ammah ta umarci aman ya kaisu, daman haka yake so saboda yanason yadan samu ya kebe da yar masoyiyarshi.
Suna zuwa mall ammah tace ‘’daughter ki dauka duka baunda zaki buqata,’’
Kallon salima ammah ta sakeyi tace ‘’ki rakata ku zagaya, bari na shiga wani shop anan baya’’
Ammah na wucewa salima ta janyo trolly, amra dai binta tayi abaya tana kallon ikon allah, haka suka dunga zagaye saida salima ta debo mata duk abunda tasan zata buqata daga kan brass panties, mayukan shafa, turare, babu abunda bata say aba, sauna gamawa ammah ma na shigowa, aman da salim a gefen ta hannunsu niki niki da ledoji da suke shake da manya manyan atamfofi da laces masu shegen tsada, duban abubuwan da suka sayo ammah tayi, ganin sun debo kala uku uku yasa ta kallesu tace ‘’ya haka, kuje ku karo dozen, naga babu night gowns ma,muje na taya ku zaba’’
Ammah is such a classy woman, wadda ilimi ya zauna ajikinta sosai, da kanta ta dunga kwaso ma amra nighties hadaddu da panties da bras, salima na gefe tana taya, babu abunda bata dauko ma amra ba, trolly dinma daya cika saida suka karo wasu, sun dade sosai cikin shop din kafin su gama danan, ammah da card dinta tayi payment din komai kafin su fito su shiga wani shop din,amra dai is speechless ga kunyar ammah data gama dabaibaye ta don koda suka tsaya wajen sayen nighties kasa dago kai tayi ta kalli kayan,har sammah tayi payment suka fito tana mamakin kudin kayan,ganin amra nasan abayasa yasa ammah ta jasu suka shiga wani jamine abaya shop, nan ma ammah ce ta kwaso mata kusan kala sha biyu masu shegen tsada da kyau kafin su fito atare.
Basu suka dawo gida ba sai wajen karfe biyar na yamma agajiya, sama duk suka wuce gaba dayan su, saida sukayi sallah suka huta kafin su fito zuwa kitchen, yauma amra ce ta dora abuncin, salima da lanatana suna daga gefe suna tayata yanke yanke har suka gama.
The next day basu tashi da wuri ba saboda gajiyar fitan jiya, sai wajen karfe sha biyu su salima suka fito,a kasa suka tadda ammah da baquwar datayi, har kasa suka duka suka gaisheta tare da baquwarta kafin su wuce dining, anatse suka fara cin abunci har suka gama, suna gamawa ammah ta kira amra, salima kuma ta tsaya kwashe kwanukan da suka bata, karaso amra tayi cikin natsuwa ta zauna gefen kujera, kallon baquwar ammah tayi tace ‘’ta chadi, gata nan, inason ayi mata wankan amarya package wanda kika taba yimin kwanaki’’
Dariya matar tayi tace ‘’wai hajiya da alamu kinji dadin wankan amaryar nan, ay kuwa zaiyi mata kyau sosai idan akayi mata,na kwana daya ma ya isa, nan gaba idan lokacin yayi sai ayi na sati guda a jere’’
Murmushi ammah tayi tace ‘’toh shiknan,bari na kira lantana ta taimaka maki ku kwaso kayan amfanin naki ko’’
Kallon amra amma tayi tace ‘’dughter kuje dakinki zatayi maki bayani’’
Kai akasa amra tace toh ammah
Sama suka wuce lantana biye dasu har zuwa dakin, matar tace ‘’an taaba maki waxing?’’
Girgiza kai amra tayi tace ‘’éh’’
Murmushi matar tayi mata tace ‘’okay baru mu fara’’
Anatse matar ta fiddo da kayayyakin gyran jiki wanda take kawowa daga chad, daukan wata robar madara matar tayi ta wuce bathroom ta tara ruwa a bthtub ta zuba ruwan a ciki tare da cika bath din, tana fitowa tace ‘’ki rage kayan jikinki zamuyi waxing yanxu,
Anatse matar ta fara mata gyaran jikin, abubuwan tada shafama amra ajiki kamar za asauya mata fata, ta dirjeta tass, kafin ta jata har bath tube,ciki ta umarceta data shiga, ruwan wani irin kamshi yake fidda wa kamar ruwan madara, ta dauka kusan rabin awa aciki kafin ta bata wani hadin sabulu tace ‘’kiyi wanka kizo’’
Futa tayi ta bar amra donta tayi wanka, tunda amra ta soma goga salulun nan tajii fatarta kamar audiga, luwai luwai gwanin burgewa, ga wani irin sheki da fatar keyi, tana gamawa ta nado towel ta fito, kallonta matar tayi ta sake kallonta tace ‘’masha allah, kinada kyau’’
Murmushi amra tayi mata don wannan kalma ta saba jinta sosai,wasu hadin ruwan madaran ta bata tace ‘’shafa wannan’’ karba amra tayi ta shafa, kafin matar ta sake bata wani nasha, babu gardama amra ta karba tana mamakin wannnan abubuwan da ammah tasa ayi mata,tasan kayan mata ne saidai bata kawo komai aranta ba don haka ta zauna tana kallon ikon allah ana gamawa matar ta kunna turaren wuta akan kujeran zama ta saka mata tare da luluba mata, saida ta kasu sosai kafin tamtar ta bata wasu turarruka na chad tace ‘’ki dunga sahsafawa da safe inkin tsahi sai kuma da ddare idan zaki shiga turaka, wanna special hadi ne daga chad, zaiji dadinki sosai’’ amra bata kawo komai aranta bat ace ‘’nagode’’
Kallon wata roba dake dauke da waist beads amra tayi cikin zumudi tace ‘’wannan sayar dashi kikeyi?’’ dariya matar tayi tace ‘’kina son irinsu ne’’
Nan amra tace ‘’eh’’ ganin haka yasa matar ta fiddo mata su tace ‘’zabi wanda kike so’’ nan amra ta zabi haddade, matar na gani tace ‘’wannan ma yana da kyau, yana daukan hankali’’ godiya amra tayi mata sosai.
Sun dade sosai don sun dauka kusan awa uku, har lalle chad saida tayi mata a damtsen hannayenta, wanda sukayi mata kua sosai, matar na gamawa ammah ta shigo daki, kallon amra data sauya lokaci guda tayi tace ‘’masha allah daughter, youre beautiful’’
Sunkuyar dakai amra tayi cikin jin kunya, godiya sosai ammah tayi ma matar harda kyautar zoben gold, ba karamin dadi kuwa matar taji ba sosai kafin tayi masu sallama.
Matar na fita ammah ta zauna gefen amra ta rike hannunta tace ‘’haka ya kamata ki dunga yi koda yaushe kinji, koda bana nan ki zama mace mai gyaran jikinta’’
Kai a kasa amra tace ‘’insha allah ammah’’
‘’daughter, yau inason ki koma part din mijinki’’ dammm amra taji gabanta ya fadi bata dago ba haka zalka batace komai ba saida ammah tace ‘’karki ji tsoro kinji ko’’…girgiza mata kai kawia amra tayi kafin ammah ta fuce.
Ammah na fuce ta mike tsaye gabanta na bugu, part dinshi?, nan take taji tsoronshi ya durar mata, harga allah shes not ready to face him saidai bazata iya cema ammah bazatayi abunda tace ba don haka jikinta yayi sanyi…………..
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 132
Update
Unedited page
Karfe shida saidai salima ta shugo dakin, sanye take da kayan islamiyya, kallonta amra tayi tace ‘’har kun dawo’’ karasowa salima tayi fuskanta dauke da murmushi tana kallon amra tace ‘’waiii adda yanaga sai kyalli kike yi’’
Murmushi karfin hali amra tayi mata tare da matsa mata gefen gadon donta zauna ‘’babu wani kyalli, kedai akwai zuzuta abu’’
Zama salima tayi agefenta tare da janyo hannunta tace ‘’wallahil azeem kyalli kikeyi adda, kinji fatar hannunki kuwa kamar auduga’’
Dariya amra tayi ta dan harareta ‘’kedai da zuzuta abu wallahi, kije ki sauya kaya saimu sauka kasa tare’’
Cikin zumudi salima ta miqe ta fuce daga dakin nasu, tana fita amra ta sauke ajiyar zuciya don har lokacin tana fargabar haduwa dashi, da kyar ta samu ta danne abunda ke ranta ta miqe tsaye, gaban dresser ta tako ta tsaya tana karema kanta kallo cikin mirror, tundaga kanta zuwa shafaffen cikinta dake cikin doguwar rigar data sauya take kallo, ita kanta tasan kyan datayi yau naturally na dabanne don ya fito sosai, sauke ajiyar zuciya tayi kafin ta juya ta nufi hanyar kofa, tana fitowa salima na fitowa itama, atare suka sauko kasan suna hira kasa kasa, tunda suka shiga kitchen suka fara preparing dinner salima ta lura da yanda jikin amra yayi sanyi, bata kawo komai aranta ba don haka ta dunga janta da hira har suka gama abunci suka jera a dining table, sama amra ta wuce don ana gab da kiran sallar magrib, salima kuma kitchen ta koma don ta karasa kwaso plates da za ayi amfani dashi.
Shogowa kitchen din aman yayi ya kafa ma bayanta idanu, yanda take goge plates da rag anatse, murmushi yayi ya tako har cikin kitchen din, bataji motsin shugowarshi ba saida yadan rankwafo daidai kunnenta yayi mata whispering wasu words daya sata dan razana har plate din hannunta na neman faduwa, saurin juyowa tayi ta kura mashi idanu fuskanta dauke da murmushi ‘’yaa aman, ka bani tsoro’’ ta karashe a shagwabe, dariya yadanyi yace ‘’I missed you baby, yau gaba daya da tunaninki na wuni ah office’’
Dan harara tayi mashi kafin ta gifta ta gefenshi ‘’babu wani nan,’’ saurin riko hannunta yayi don tana gab da wuce shi, shima cikin shagwaba yace ‘’baby sal,
dan allah ki karbi soyayya na, ni wallahi kina wahalar dani sosai,zan hadaki da ammah ko sister inlaw wallahi’’
Kallonshi tayi da yanda yake shagwaba kafin ta kyalkyace da dariya ‘’yanxu shagwaba ka koyo kuma?’’
Dariya shima yayi ya kara shagwabe fuska yace ‘’wallahi da gaske nake sonki zai kasheni baby sal’’
Banza tayi dashi tana murmushi ta wuce dining, haka ya dunga binta daga dining zuwa kitchen, karshe dai guduwa sama tayi ganin yana neman shagaltata da shagwabarshi, wani irin son shi da kaunarshi take ji a jininta, hes so good with words, duk sanda ya fara mata Magana tsintar kanta take da blushing kamar wata zautacciya.
Amra na shiga daki ta wuce bathroom ta dauro alwala, tana fitowa ta zura hijab, ta tada sallah, tana idarwa ta zauna saida aka kira sallan isha’I, tana nan zaune salima ta shugo dakin da sallama kafin ta kalli inda amra ke zaune kan sallaya, ‘’adda mu sauka kasa, naga ammah ta sauka already’’
Juyowa amra tayi ta kalleta ‘’bana jin yunwa, kije kawai sai zuwa anjima zanci’’
‘’okay,’’ salima ta fada tana bude kofar futa daga dakin.
Tana fita amra ta mike tsaye ta cire hijab din,baking ado ta zauna gabanta na faduwa sosai, wayarta ta janyo tama rasa abunda zatayi da wayar,sai a yanxu take missing din haifa sosai, aje wayar tayi a gefe ta kwanta tana tunani, gabanta na faduwa sosai.
Bayan fitar salima kasa