that, zaka iya fada mash…..” saurin tsuke Bakinta tayi kamar ta hangoshi, “Nadine muje ko”
Hanyar fita sukabi m5 biye da ita, duban wayanta ta soma yi don duba ride din datayi order, ganin yana gabda inda take ta duba kudin inda zai kaita, “kai daman nan ne palm jumeirah”
ta fada tana kwalo ido, kafin tayi
saurin fuzge wa, tsayuwan kusan 10mins tayi shuru babu ride, wayar ta ta duba, da sauri ta bude idanu ganin mai motar yayi canceling tsaki tayi ta sake wani shima still
canceling yayi, saida tayi requesting kusan mota biyar shuru, juyowa tayi ta kalli m5 dake tsaye ya kauda kanshi gefe,bata buqatan taimakon shi don haka ta juya ta wuce ciki Nadine biye da ita.
Wani uban haushi ne ya turniketa babu damar fita kenan, daman apartment dinta taso komawa don bazata zauna a gidan shi.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 119
Update!!!
19/05/2023
Unedited
Sake Kiran general m5 yayi ya shiada mashi abunda tace saidai bai fada mashi kalamanta yanda zaiji haushi ba,Nadine na Lura da abubuwan da take don haka ta cigaba da sa mata idanu don karantar abunda take shirin yi.
Washe gari haka m5 ya sake zaman jiranta shuru babu labari, haka yasa Nadine ta hau saman ta dubota, koda ta karasa dakin a zaune ta taddata ta doka uban tagumi, karasowa Har inda take Nadine tayi tace “can I seat ma’am”
Dagowa tayi ta kalleta tace “yes”
Zama nadine tayi kusa da ita fuskanta dauke da murmushi tace “forgive my manners what’s your age ma?”
Fuskanta babu wani shakku ko jin haushin tambayan tace
“23”
Dariya nadine tayi tace “you’re 23 but you’re behaving like a 18 year old adult”
Kallon nadine ta tsaya yi sosai don bata gane me take shirin fada mata ba,
“I’m so sorry if…” da sauri ta katseta “go ahead, I want to know more"
Gyara ama Nadine tayi ta cigaba “idan Har kinason kiji saukin abunda kike ji sannan kiyi achieving Duk wani abu a duniya nan you have to be patient, first of all use your opportunity, use what ever you’ve got, then take action that’s the secret”
Shuru amra tayi tana nazarin abunda Nadine ta fada mata, ahankali ta soma gane inda Nadine ta dosa, dagoda fuskanta tayi ta kalli fuskanta dauke da murmushi tace “is that the only way?”
“Not the only way but the brilliant way and there are more ways but some of them are risky”
Da sauri amra ta miqe tsaye tace “I don’t mind, I will go for it” tana kaiwa nan ta wuce bathroom ta fara shirinta agurguje.
Karfe takwas da rabi saigata ta sauko kasa cikin shiri tsaf, abaya ne a jikinta me shekagen tsada daga dauko daga cikin sabbin kayan closet, koda ta sauko nadine da m5 saida suka kalleta suka sake kallonta don tayi mugun haduwa, hannunta jaka ce mai shegen tsada Vinci black color hade da takalminta, fukanata babu komi Sai doan kohl da lip gloss wanda ya karama fuskan kyau sosai.
Saurin kauda kai m5 yayi don Har wani kwarjini take yi,fucewa yayi daga sitting room din kasa ya wuce wajen motar don ya jirata,cikin Yan mintuna qalilan Sai gata ta fito Sai zabga kamshi takeyi, bayan motar ya bude mata ta hakimce kafin ya rufe ya shiga shima yaja motar, tunda ta shiga motar ta sunkuyar da kanta bata dago ba Har suka iso headquarters,m5 ne da kanshi ya bude mata ta fito, yake kallo ya koma wajen su, a hankali cikin natsuwa ta fara takowa Har zuwa cikin asibiti, saida ta fara zuwa office dinsu ta saka lapcoat dinta kafin ta fito don zuwa first morning round check, saida ta gama tsagaye ko’ina kafin ta fito ta wuce office dinsu, samun waje tayi ta zauna tana tunanin abunda Nadine ta fada mata.
Karfe hudu da rabi ta kammala ayyukanta ta fito, m5 dake jiranta na ganin isowan ta ya bude mata bayan mota ta zauna yaja motar suka bar headquarters, akan hanya ta buqaci ya kaita apartment dinta , abunda ya fada mata yayi mugun bata mamaki don kai tsaye yace Sai an fada ma sir tukunna, kauda kanta kawai tayi Har suka karaso gida.
Acikin satin nan wata irin rayuwa amra tayi wanda za ace a fili kamar komai ya lafa mata saidai a zuci kamar akan kaya take duk dare bata fasa kukan data saba, saidai yanxu ta maida hankalinta don ta gama housemanship dinta daya rage wata daya ta gama ta karba papers dinta, Inta tuna da wannan wani irin dadi take ji aranta ba, saidai kuma tana fargabar komawa gida.
Bangaren Amar kwanakin nan kamar yana cikin wuta don wani irin wahala yake sha Duk dare, a mugun buqace yace wato Sai bayan absence din mutun kake gane amfanin shi,don wannan Yan wasannin dayake yi da ita ba karamin taimakon kanshi yake ba, haka nan cikin kwanakin ya tsiri shan lemon tea Duk dare, ko karfe uku ya farka saiya nema lemon ya matsa a bakinshi ko zaiji sauqi, haka zalika Idan zai sha saiya dauka kusan guda goma daga fridge ya matse ya shanye kafin ya samu relief, Akwai ranar da ammah ta sauko kasan da sassafe ta wuce kitchen don shirin breakfast daman indai alh kabiru yana gida kusan kullum tana Tashi da sassafe don ta fara shirye shiryen breakfast don da wurwuri yake futa,kitchen din ta nufa tana “lantana!!!, lantana!!, kodai baki Tashi bane Har yanxu ga karfe shida ta gifta”
Lantana dake kwance zazzabi ya riketa da daddare tayi saurin miqewa ta nufi kitchen din don dakinta yana kusa da kitchen, Gyaran dankwalin ta tayi ta karaso gaban ammah “hajiya barka da safiya”
“Barka dai lantana, ya akai yau kika makara”
“Wallahi hajiya da zazzabi na kwana”
Kallonta ammah tayi cikin jimami tace “ayya sannu Allah ya sawaqa kinsha magani? Ko zaki kwanta”
Da sauri lanata tace “ah ah hajiya bari na fara tattara kitchen din Ay tunda nasha magani”
Dan waigawa ammah tayi don ganin abunda zata tattara a kitchen din don kusan kullum Duk dare Sai an tsaftace kitchen din kafin a kwanta,
“Toh fah, wa yayi amfani da wannan lemon tsami haka”
Dan jin lanata tayi kafin ta danyi dariyar yaqe tace “inaga yallabai ne, don shekaran jiya naga shi yazo neman lemon tsami”
Shuru ammah tayi tana sauraronta nan ta dago wa take nufi, murmushi kawai tayi tace “Toh tattara ki zuba bawan a dustbin sai a fiddo da Irish a fere”
Da Toh lantana ta amsa mata kafin ta fara tattara leman tsamin, futowa ammah tayi daga kitchen din ta wuce sama zuwa dakinta, koda isa dakinta zama tayi tana nazari, ko ba a fada mata ba tasan dalilinsa na shan leman tsami saidai tana mamaki don wannan ne karo na farko da ya nuna a buqace yace sosai tunda Har yakai ga shan lemon haka sosai,saidai ta Kasa gane dalilin shi na qin aure bayan ga alamu sun nuna yana buqatar mace a kusa dashi.
Tunani ta fara yi akan lallai ya kamata tayi wani abun akai don Idan ta zuba mashi idanu zai zauna haka nan baiyi auren ba.
Karfe bakwai da rabi kowa ya sauko qasa Harda su salima da suke sanye da uniform dinsu ita da salim, salim na zaune kan dining salima kuma na tare da ammah suna fito da breakfast daga kitchen da taimakon lantana, Aman ne ya fara fitowa ya hakimce kan dining, sanye yake da kayan barcinsa,kallon Salim yayi kafin ya dan kauda kanshi gefe, salima ce ta fito daga kitchen da warmer a hannunta dake cike da fried chips da plantain, tunda ta doso hanyar dining ya kafeta da idanu kamar koda yaushe,dagowa tayi suka hada idanu, saida ta zabga mashi harara kafun ta kauda kanta gefe, tana shirin aje warmer din Amar ya fito cikin shirinsa gwanin burgewa, takowa yayi har dining din ya ja kujera nesa da Aman ya zauna, da sauri salima ta tsugunna Har qasa tace “good morning ya Muhammad”
“Morning”ya amsa mata fuskanshi babu yabi ba fallasa kamar kullum, bata damu ba tayi murmushi don dan zaman nan ta gane haka yake rayuwarshi.
Aman dake gefen su kamar ya shake sa haka yake ji, itama badan zuciyar shi naso ba Harda ita zai hada ganin yanda take gaishesa yana wani babbasarwa,tsaki yayi wanda ya jawo hankalinsu gaba daya harda ammah data doso ta kallesu su duka tace “ashe Duk Kun fito”
Amar ne ya fara kallonta fuskanshi Adan sake yace “morning ammah”
Da murmushi dauke a fuskanta ta amsashi,
“Morning son”
Aman ko saida ta kalleshi tace “morning son”
Kafin ya dago ya kalleta yace “morning ammah”
Amar yaji zafin abun saidai bai cika tsoma baki akan sha’anin Aman dinba don haka ya basar kawai, suna nan zaune alh kabiru ya sauko kasa shima cikin shirinsa na zuwa office, tunda ya tunkaro dining din ya kalli Amar yasha Jinin jikinsa, washe fuskanshi yayi karaso ya zauna tsakiyan dining din yana facing kowa “madallah Duk an Tashi kenan”
Wannan Karin ma Amar ne ya dago yace “morning”
Kafin aman shima yace “morning daddy”
Kallo su yayi daya bayan daya yana jin zafin rashin kiranshi da daddy da Amar baiyi ba, kauda zancen yayi aranshi yace “morning boys”
Salima Ce itama ta tsugunna Har kasa tace “Ina kwana daddy”
Bai kalli inda take ba yace “lafiya an shirya makaranta kenan Allah ya bada sa a”
Dan dagowa tayi fuskanta dauke da mamaki ammah Ma haka don wannan ne first time daya taba amsa gaisuwan ta su zaman da tayi a gidan, don wani kallo wulaqanci yake masu dukda bata damu ba saboda ammah ta gama yi masu komai tunda ta karbesu hannu bibbiyu babu dangin iya bare na baba.
Wannan breakfast dai anyi shi ne kawai ammah kowa is feeling awkward musamman su salima wanda kwata kwata basa zaman dining Idan alh yana gidan, babu yanda ammah batayi ba akan su dunga zama Sai su dinga zillewa.
Agaggauce su salima suka karasa cin abuncin sukayi masu sallama suka wuce don driver na jiransu a waje.
Amar ne ya fara miqewa yace “ammah Zan futa wani dan aiki, I will be late”
“Okay son Allah ya kiyaye ya tsare yasa asamu abunda akaje nema”
Da Ameen ya amsata kafin ya fuce daga gidan, alh kabiru de da idanu ya bishi don Har yanxu ya kasa gano dalilin zuwanshi nan Nigeria, dukda yana son yin Magana da alif don shike da ido akanshi saidai Har yanxu baya samunsa shiyasa ya yanke shawarar Idan komi ya lafa zaije dubai din cikin sirri kamar yanda suka saba Idan zasuyi meeting don shi alif Sai shekara shekara yake zuwa nan Nigeria sbd tsaro.
Yana fita alh kabiru shima ya mike, kallonshi ammah tayi kafin ta kalli plate dinshi tace “harka gama?”
“Yes Saina dawo”
“Okay a dawo lafiya”
Dan tsayawa yayi ya juyo ya kalleta kamar tasan me yake nufi da hakan tayi saurin cewa “Allah ya bada sa a”
“Ameen” yana kaiwa nan ya fuce daga gidan.
Amar na futa daga gidan ya wuce inda suke haduwa da asad, saida ya jirashi ya iso don ya rigarshi zuwa kafin su shige ciki tare, waje ne kamar office, suna zama asad ya soma mashi bayani, “oga Ina ganin fah dole mu saka mace cikin wannan alamarin”
Da kallon mamaki amar ya bishi don jin Karin bayani
“Yea, Idan Har Muna son wasu bayanai cikin sauqi to saifa mun nemi yarinyar dake tare da alhaji kabiru, infact nayi Duk wani buncike akanta na bari ne nan fada maka ba don Ina tunanin maybe zamu samu wata hanyar”
Dan dagowa amar yayi yace “who’s she?”
“Sunanta Hameeda abdallah, sun kai shekara daya tare da alhaji kabiru don itace number one a Yan matan barikin shi, and base on what I research it looks like yana ji da ita sosai don kwanaki ya saya mata mota,and the funny part is tana bin wasu mazan bayan shi don Harda….”
Dan dago idanunshi yayi ya kalleshi da kyau don neman Karin bayani
“Danshi Ma na cikin wanda suke nemanta”
Tabe baki yayi yace “disgusting!!!”
Dariya asad yayi yace “oga ay yanxu mutane na ganin normal ne wannan abun fah”
Hade rai Amar yayi yace “so what can she contribute?
“Alot!!!, the sweetest part is she’s interested in you”
Yana kaiwa nan ya fashe da dariyar yaqe, shuru Amar yayi yana nazarin maganar asad din, Idan Har ya fahimta shine shima Har dashi kenan, tsaki ya buga ya kalleshi fuskan nan tamau yace “what sort of nonsense,”
Da sauri asad ya tari nunfashinsa yace “haba oga calm down mana, bawai Ina nufi ka nemeta ba no, you can actually use her, don babu macen da zatayi resisting dinka,and besides matan yanxu can do anything for money”
Jin haka yasa Amar cewa “okay make all the arrangements, ka bata proposal din 20m if she’s interested fine Idan kuma tana buqatar Kari ma ba damuwa, it’s just that inaso muyi komai cikin gaggawa, I’m tired of seeing that moholo old man behaving like a good man”
Dariyar asad yayi yace “ba damuwa oga”
Adaren ranar bai tsaya ko Ina ba Sai guest house din alhaji sammani,tarba ta mutunci sammani yayi mashi sanin koshi wanene,zama Amar yayi ya hakimce kamar shine mai gidan don ya gama cika idanun mutanen dake gidan, daya bayan daya ya kallesu, fuskanshi tam ya kalli sammani yace “I have an offer for you, from 100m and above, you know what I need basai nayi maka bayani ba just one word, if you’re interested call my line”
Aje katin shi yayi ya miqe ya masu wani disgusting look ya fuce daga gidan dan ko ba a fada mashi ba ya gane shi kuma wannan ba mata yake kawo wa guest house dinshi ba sai maza which means neman juna suke, dalilin zuwanshi wajen sa kuwa tun bayan haduwa da sukayi da shi haduwa ta farko lokacin da sukazo shida alhaji kabiru ya soma bincike akanshi, Adil binciken da yayi bai samu sa hannunshi a cikin dirty work din sammani ba hasali ma shine babban maqiyin alhaji kabiru shima he’s wearing a mask of old friendship don ya samu abunda yake so wajen kabiru, zuwan Amar yayi mugun bashi mamaki, kamar yanda yayi warning din alhaji kabiru ya tabbatar da hasashensa, yazo
Don shi kenan.
Amar na fucewa kabiru ya maida idanunshi kan abokin harkar sa, ya kece da dariya yace “hahaha yaro yaro ne, saidai wannan ya fita daban bai san gona da yake shirin tsallakawa ba, inda inada hali Ay da nan bar kabiru yakai inda yake ba Har azo neman bayani akan yanda za a tarfashi”
Wata dariyar ya sake kecewa, abokin luwadin shi dake gefenshi mamaki ya gama cika shi jin uban maqudan kudaden da aka kawowa sammani, tunani ya fara yi dama shi aka kawo wa wannan proposal din da babu abunda zai shashi tona asiri.
Kallon sammani yayi yace “maza, wannan fah Kanajin maqudan kudin da yake ambatowa kuwa”
Dariya alh sammani yayi yace “kai latso kana wasa, wannan yaron ko dan goge bazai nuna mashi Dukiya ba”
Matsowa wanda aka kira da latso yayi kusa da alh sammani yayi tare da shafa kanshi yace “oga me Yake nema ne haka ya zuba kudi haka?”
Dariya sammani yayi yace “inda nasan abunda yake nema Ay da tuni na fada mashi tun kafin ya fuce Ma,”
Murmushin mugunta sammani yayi don shi kadai yasan abunda ke ranshi, kwata kwata ba zai taba fadama sammani haduwar shi da amar ba, zai taaya ya zuba idanu don yana daga zaune fansarda yake son dauka za a dauka mashi saidai yana da sirrin alh kabiru guda daga da Duk duniya babu wanda ya sani wanda shima kabiru bai sani ba, sai bari sai komai yayi zafi zafi kafin ya bayyanawa amar don shima ya yagi rabansa”
Amar na fitowa daga guest house din alh sammani ya wuce gida direct,saida ya tsaya yayi sallar isha’I a masallaci kafin ya shige da motar shi gida, salima ce ta bude kofan, tana sanye da doguwar Riga datayi mata kyau sosai, kammaninta sun fito sosai da amra, kallonta ya tsaya yo sosai don harya shagala, fuskan amra ke mashi yawo,“ya Muhammad bismillah”
Saurin kauda kanshi yayi dan sai lokacin ya farga da kallon nata daya tsayayi batare da saninshi ba, Duk tsayuwar nan da yayi akan idanun ammah wadda tun shigowa shi ta kace shi da idanu don taga yanda ya kurama salima idanu, murmushi kawai tayi tana ayyana wani abu a ranta.
Yana gab da shigewa part dinshi ya hango ammah a sitting room, karasowa yayi har inda take ya zauna gefenta yace “barka da dare ammah”
“Barka son ya ayyukan sannu da dawowa”
“Thanks ammah na” ya fada fuskanshi dauke da murmushi, kallon Salim da ya soma barci a kan carpet kafin ya maida kallon nashi kan salima data karaso inda suke yace “wake him up yake sama ya kwanta”
Karasowa tayi gaban Salim ta tasheshi suka wuce sama.
Kallon Amar ammah tayi tace “son, inason muyi wata muhimmiyar magana”
Bai dago ya kalleta ba yace “okay”
Nunfasa tayi tace “su waye yarannan? Ina iyayen su?”
Dan dagowa yyi ya kalleta ganin fuskanta so serious yasa yadan sauke kanshi kasa yace “marayu ne, iyayen su sun mutu due to an accident,I can’t say everything in details”
Da sauri ta katse shi “basu da dangi ne? Look don is not like I’m questioning you ko bana son zaman su tare da mu, I’m so happy having them besides me, saidai inason sanin komai gane dasu”
Dan murmushi yayi y kamo hannunta yace “ammah na, kiyi hakuri when the time comes I will explain everything in details,I know you trust me right?”
“Of course I trust you 100% son,”
Dan murmushi yayi shima yace “karfe Tara Harda rabi baki sha magani kin kwanta ba”
“Ay mai gidan bai dawo ba,”
Ya gane dalilin zaman nata don tayi serving alh kabiru