Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   33 / 94

96K to 99K   out of 279.4K words

cikin shirinta, sanye take cikin abaya sky blue wadda ta haskata, fuskanshi fayau babu walwala kwata kwata,drivern dake kaita asibiti cikin kwanakin ne ya bude mata bayan mota ta shige kafin su fuce daga cikin compound din.

Suna isa headquarters ta fito cikin natsuwa hannunta rike da handbag dinta Sai wayanta, ciki ya wuce zuwa office, Ganin supervisor dinta bata ciki yasa ta saka lap coat ta aje laptop dinta da bag dinta cikin locket dinta ta fito domin zuwa round check,bata wani jimabata dawo office don babu patients da yawa, report dinta ta jawo ta fara filing taba cikin rubutun haifa ta shugo, da sauri ta karaso ta rungumeta fuskanta dauke da murmushi “babe ashe kin karaso,”

Kallonta amra tayi tace “tun wajen 7 na karaso Ay”

“Seven fah” haifa ta fada fuskanta dauke da mamaki

“Babe tun seven kikazo why? Working hours fah Sai nine yake farawa”

Kallonta amra tayi fuskanta babu walwala tace “Bana son zama ne a gidan, babe Wallahi na kosa na gama”

Zama haifa Tayi kusa da ita ta jama hannunta tace “babe i thought we’ve already talked about this, ki mance da komai ki cigaba da rayuwanki, kinga baifi mana 2weeks ba shikenan mun gama komai”

Hira suka danyi kafin suyi saurin futa daga office don an shigo da emergency.

Sojoji kusan guda biyar ne suka rautana don haka suka fara dressing din ciwukansu wasu kuma aka wasu dasu operation din gaggawa.

Sai wajen karfe biyu suka samu komai yadan lafa,fitowa sukayi suka wuce masjid don yin sallah, tunda suka shiga amra ke kallon wayarta, haifa data kafa mata idanu Ganin tana smiling Tayi saurin cewa, “Wai da wa kike chatting haka kike murmushi”

Kallonta amra tayi tare da aje wayana nata gefe tace “Wallahi wannan joker dinnan”

Kallonta haifa tayi ta dan tabe baki tace “Wai waye shi?, is there something that I need to know?” Ta fada tana kallon amra da kallon tuhuma 

“He’s just a patient danayi attending kwanaki Ay na fada maki” amra ta fada tana kauda wala ta gefe 

“Then meysa yake maki message haka all the time? Babe you should be careful fah”

Haifa ta fada mata still Tana kallonta 

“He’s just trying to befriend me nothing else”

Shuru kawai haifa Tayi suka fito daga masjid atare, suna cikin tafiya sukaji sallama da larabaci, dagowa sukayi gaba dayansu dan Ganin koma waye,amra ce Tayi saurin cewa “heyy it’s you?”

Dariya saurayin shima yayi sanye yake da kaki na sojoji, yace “yea it’s me friend how are you”

“I’m fine” ta fada fuskanta dauke da dan murmushi, hira ya dan soma Jan su dashi anan tsaye haifa na Ganin haka ta gaishesa itama hannunta cikin na amra,waiga wa haifa tayi Ganin Ana kallonsu yasa ta dan rankwafo tace ma amra “let’s go”

Saurin tarar nunfashin haifa yayi yace “1 sec”

Ya fada yana kokarin zaro wani abu daga aljihunsa, da sauri haifa ta janyo hannunta da karfi suka bar wajen Ganin general a tsaye da m5 a gefenshi sun fito daga masjid na bangaren maza kafa masu idanu yayi na Yan seconds  kafin ya kauda idanun shi ya wuce cikin headquarters, mutanen dake wucewa ma kallon inda suke sukayi, don Duk wanda yazo wucewa saiya Sara mashi shiko saurayin Ganin yanda haifa ta jata suka bar wajen yasa ya tsaya yana mamaki kafin ya wuce dorm din su, tunda ya shigo mutanen wajen ke yan kananun maganganu.

Bangaren amra kuwa suna shiga cikin office haifa ta kalleta tace “babe what do you think you’re doing? Kinsan rumor din scandal dinki bai gama warware ba kinason jefa kanki cikin wani, have you forgotten akwai mutanen da suka san you’re married?” Dukda ba kowa yasan who you’re married to ba, but kinsan kwanaki yanda aka dunga gossiping akanki?”

Tabe baki amra tayi tace “babe I don’t care, ni babu abunda ya dame ni as far as I’m concerned I’m no one’s property so ni babu abunda ya dameni”

Kallonta haifa tayi trying to make her understand, “but kinsan dai tunda baiyi freeing dinki ba akwai aurenshi akanki”

Shuru amra tayi bata ce komi ba Ganin haka yasa haifa ta cigaba “babe ni bana son ki saka kanki cikin problem”

Murmushi kawai amra tayi mata ba tare da tace komai ba haifa na Ganin haka ta fuce daga office din tana mamakin yanda amra ta sauya.

Zaune yake kan rolling chair dinshi, m5 na tsaye a gabanshi yana jiran command, shuri Amar yayi ya kafa ma laptop din gabanshi idanu kamar yana karanta abu saidai tunanin ya tafi chan nesa, yau Kwan uku kenan rabon daya ganta sai yau, yayi mamakin tsayuwar da ya gani tare da wani, Har tana dariya, don saurayin ya tare su ita da haifa lokacin ya fito shida Hammam daga cikin masjid, kallon m5 yayi ba tare da yace komi ba da sauri m5 ya kame azafafe yace “hamid abdallah, rank 4 operation department E36.

Amar ne ya kalleshi tare da daga mashi hannu ya juya ya fuce. Yana futa ya jingina da kujeran yana jin wani iri, ranshi ya mugun baci dazu daya ganta saidai taurin zuciyarshi yasa ya basar da komai.

Cikin Yan mintuna qalilan saiga m5 da wannan saurayin hamid,suna shigowa gaba Dayan su suka qame Har saurayin don shi mamakin neman gaggawa da aka mashi yake,don basu fiye zuwa inda ba department dinsu bane.

Binshi da idanu Amar yayi kafin yace “identify your self”

Da saurin saurayin ya kame yace “I’m hamid abdoullah rank 5 operational department E….”

Bai kaiga karasawa ba Amar ya daga mashi hannu in a commanding way akan yayi shuru, saida ya dauka kusan minti biyu kafin yace “when did you join service?”

Da sauri Hamid yace “about 5 years ago sir”

Jinjina kai Amar yayi fuskanshi babu annuri yace “have you read the listed rules and regulations before being appointed? Regarding any kinds of affairs between the staffs??”

Shuru Hamid yayi rasa abun cewa saida Amar ya dago azafafe yace “I don’t have to repeat my self”

Ya karashe yana daga hannun ya masu nuni da kofa m5 na Ganin hakan ya gane me yake nufi akan ya karashe abunda yayi saura, suna fita, m5 ya cire rank din hamid yace “kaje Ka sake reviewing akan military laws, and you messed with the wrong one”

Ya karashe yana cire rank din hamid, kasa motsawa Hamid yayi don bai gane inda ya Dosa ba, sanin ma’anar cire rank dinshi yasa hankalinshi ya Tashi, babu damar tunkarar m5 don yasan order ne aka bashi kuma bayan wannan ma ya fishi rank sosai.

Hamid dai cikin tashin hankali ya koma dorm dinsu, nan abokin aikin sa ke shaida mashi anyi suspending dinshi for violating military law.

Karfe biyar suka fito ita da haifa, tun daga nesa ta hango m5 dake tsaye jikin mota, Tayi mamakin ganinshi don cikin kwanakin bashine wanda ke kawota ba, sallama sukayi da haifa kafin ta tunkari inda yake cikin natsuwa, tana karasowa yayi saurin bude mata baya tare da gaisheta, tsayuwan Tayi kyam taqi shiga don yana bude kofar ta hangoshi a zaune yana latsa waya ga kamshinsa dake fitowa daga cikin motar, kasa motsawa tayi, bai kalli inda take ba akausashe yace “get in”

Gabanta ne yadan fadi don babu alamun wasa a cikin kalaman shi, samun kanta tayi da shigewa ciki ba tare da musawa ba, kauda idanunta tayi gefe kafin m5 ya jasu.

Tunda suka kama hanya babu wanda yace qala,itakam kauda kanta ma tayi gefe tana kallon window, kallon m5 yayi ta jikin mirror yace “stop the car”

Da sauri m5 ya gangara da motar chan gefe yayi parking tare da fitowa don ya basu waje.

M5 na fita yace “why did you choose to lower your standards?,kinsan irin darajar da Allah yayi maki as mace kika tsaya kina magana da wani namiji a public, I never knew you have a dumb brain da Har zaisa ki tsaya magana da namiji da aurena akanki are you that stupid? Can’t you wait na sallameki sai kiyi Duk abunda kikaga dama?” Ya karashe yana kallonta fuskanshi dauke da bacin rai, juyowa tayi ta kalleshi ranta ya mugun baci sosai itama, tace “daman kasan darajar da Allah yayi min ne? Why would you care idan na tsaya da maza dubu ma matsala ta ce ba Taka ba Ay, naga dai rabuwa zakayi dani”

Ta karashe tana turo Bakinta cikin tsiwa, azafafe ya janyota Har tana bugewa da kirjinshi yace “are you insane? Ina magana kina maida min”

Da karfi tace “Toh why would you care? Idan na kula maza dadi ba damuwa Ka bane daraja kuma da kake magana…”

Saurin toshe Bakinta daya buge tayi Ganin yanda fuskanshi ta sauya zallan baccin rai bayyane akan fuskanshi hankali atashe ta fara rarraba idanuwa tana son kwacema rokon daya yi mata 

“It looks like Saina koya maki hankali zaki gane da wa kike magana, babu macen data taba kallon cikin idanu na ta fada min magana kamar yanda kike fada min, the next time kika sake hakan you’ll regret it, nasan maganin ki da zanyi,”

Ganin yanda ya dauka da zafi yasa taji wani iri don yanxu fatanta ya saketa ta bar rayuwarshi, kalamanshi ne na karshe yafi tayar mata da hankali hawayen takaici na bullowa a fuskanta  tace “na rokeka da Allah kayi freeing dina, I’m tired of all this”

Kallonta yayi ya watsa mata disgusting look yace “not until Na koya maki hankali, not until kin gane cewa ni ke da ikon rabuwa dake bake ba, ni ke da ikon sawa da hanawa, I will only free you when I feel like, mind you” ya sake watsa mata kallo ya cigaba “you’re not special in any way, Inkinga dama kije ki kula thousands of men I don’t bloody care idan nayi freeing dinki that’s your problem but not da aurena akanki so be warned”

Ya karashe yana hankadata gefe, wani irin baqin ciki takaici ne ya tsaya mata a maqoshi, ta kasa gane wannan wace irin masifa ce, haka nan ta dunga rera kuka, shima saida ya dauka kusan minti goma yana sauke ajjiyar zuciya don ranshi yayi mugun baci, kallon yanda take kuka yayi ya daka mata tsawa data furgita ta yace “shut the fuck up and wipe those tears”

Arazane ta soma goge hawayen dake kwance a fuskanta, tsanarshi da tsoronshi na ninkuwa aranta don tana jin tsoro da take mashi kamar mutuwar ta, tana guntse Bakinta ya Danna ma m5 kira a waya kafin ya shugo su wuce.

Tunda suka fara tafiya ta toshe bakinta tana kokarin haba sautin kukanta fitowa Har suka iso gida, suna isowa ya fuce daga motar, itama fitowa tayi tana matse kwalla Har ta wuce sama.

Yana shiga daki ya cire kayanshi ya wuce bathroom, wanka ya farayi kafin ya fito ya tsaya gaban mirror yana kallon kallonshi, mamakin yanda yake acting cikin kwanakin yake, tunawa da abunda ya faru dazu yasa ya runtse idanunshi ahankali ya furta “tunda you’re stubborn Zan koya maki hankali”

Harga Allah yayi niyar rabuwa da ita a cikin kwanakin saidai abunda tayi dazu yasa ya yanke shawarar sai ya koma gida ya gama settling din issue dinshi da daddy kafin ya dawo ya sallameta don plan dinshi was idan zai koma sai tafi da ita ya hadata da Yan uwanta don already ya rigada yayi signing report dinta da certificate dinta na shaidar cewa ta gama housemanship dinta anan uae armed force specialist hospital.

Washe gari da zazzabi ta Tashi don haka bata samu damar zuwa asibiti ba ta kwanta.

Wajen karfe biyar ta samu jikinta ya warware sosai, wayanta ta dauka suka sha hira da haifa inda take bata labarin sun dawo ita da Hammam kuma yana son ayi maganar aure tsakaninsu, amra dai bata ce komi ba sa saidai tayi masu murna don soyayyarsu  mai karfice, suna gama waya ta aje wayan a gefenta wasu siraran hawaye na zubo mata, yanxu shikenan idan ya saketa ta Tashi daga budurwa saidai ace bazawara, dukda achan Nigeria babu wanda ya sani saidai Tsoronta ta daya idan aka gane, don tasan wataran itama zatayi aure,me zata cema mijin da zata aura? She can’t say tayi aure saboda katin kasa bayan wannan ma babu wanda zai yarda da hakan qila ma wasu cewa zasuyi iskanci tayi anan uae din asunan karatu.

Headquarters…

A zaune yake kan kujera shi yana duba wasu files, m5 ne yayi knocking kafin ya bashi umarnin shugowa,Sara mashi yayi kafin yace “sir I’ve make the bookings, your flight will be tomorrow morning by 10pm, I’ve sent the details to your mail”

Bai dadi ba yace “thanks”

M5 na futa daga office din ya jawo wayanshi ya sake dialing number ammah, yau kwana uku kenan tunda sukayi waya da ita rabon data dauka wayanshi kenan, to him it looks like kamar tana fushi ne dashi, dialing number ya sakeyi Har ta gama ringing ba a dauka fah, aje wayan kawai yayi ya dafe kanshi yana wani nazari kafin ya maida hankalinshi kan laptop dinshi.

Yau da wurwuri ya fito daga office suka fuce shida m5, wani irin heavenly guarded place sukaje a wata maboya da babu wanda zai san wajen nan kusa da headquarters, wurin yana da very strong security inda aje aje manya manyan criminals, tunda ya fito ya karema wajen kallo yau shekara gida kenan rabon da ya zo wajen,m5 ne ya mashi jagora zuwa interrogation room din da aka aje alif shuraim da wasu mutanen shi,ciki suka shiga kafin amar ya zauna kan kujeran dake facing ta alif shuraim.

Kallonshi Amar yayi, ya sauya sosai mutumin don zaman wajen kadai zaisa ya sauya, saidai shi Ana bashi special treatment don Har yanxu investigation ake akanshi ba a samu kwakwarar hujjar da aje nema ba akanshi.

Agurguje Amar ya mashi tambayoyi wanda su m5 sukayi ma alif din tun kafin zuwan Amar saidai yaqi basu hadin kai, gashi babu daman dukanshi ko yi mashi wani abu da zaisa yayi magana, azafafe Amar yake mashi magana saidai ko gizau alif baiyiba saima dariya dayayi ya kalleshi yace “bazaka samu komai daga wajena ba, you are just wasting your time, you don’t know who you’re messing with”

Ya fada yana dariya mata dadin sauraro

Amar daya shaka sosai ya kalleshi ranshi a mugun bace yace “I will bring you down, you and your entire empire I promise my self, just watch and see”

Yana kaiwa nan ya miqe Har yakai bakin kofa alif yace “you don’t know what your doing to your life,not just your life but your entire family”

Alif Ya fada fuskanshi babu annuri ko kadan, Amar dai bai juyo ba ya fuce daga cikin interrogation room din tsabar bacin rai.

Suna shiga cikin motar m5 ya buqaci sanin inda zasu je, “take me to my apartment” ya bashi amsa.

Direct apartment din Amar m5 ya aje shi kafin ya juya, shi kuka ya shige ciki, tunda ya sako kafanshi cikin apartment din gabanshi ya fadi, nan take komai ya fara mashi flashing, rayuwar da sukayi shida amra a cikin gidan, shiga ciki yayi ya tsaya a sitting room yana karema ko’ina kallo,ko’ina is clean babu datti ko

daya, saima kamshi ta daya dauki parlor saboda zaman da tayi a cikinshi a lokacin.

 Dakinshi ya wuce, nan ma babu wani datti kamar bai yi kusan wata biyu ba bai shiga ba,bin dakin ya fara yi da kallo, ahankali idanunshi ya dauka kan blanket dinta dake kan couch din gado, he remember lokacin data dawo dakin tana kwana akan kujeran, saurin kauda tunanin ta yayi ya maida idanunshi kan gadonsa ya zauna tare da cire boot din kafarshi, tunawa da lokacin dayayi rashin lafiya yayi da yanda ta rikece, how she treated him, how she showed him so much care, runtse idanunshi yayi ya Tashi ya wuce closet nan ma dai tunaninta ya dunga yi, abun na bata mashi rai don ya kasa haba kanshi tunanin don Duk inda ya gifta saiya tuna wani memories dinshi tare da ita, wanka ya samu yayi ya sauya kaya zuwa masu sauqi kafin ya sa m5 ya kawo mashi abunci,

Lokacin sallah nayi yayi sallah yabi lafiyar gado, wani irin barci nw mai shegen dadi ya kwashesa, Harda mafarki sai wajen karfe goma ya tashi, agurguje yayi sallah ya fito da key din daya daga cikin motoci shi dake parke anan apartment din, yana shiga cikin motar ya fuce da mugun speed.

Bai tsaya ko’ina ba sai a penthouse dinshi, Nadine na bude mashi kofa yabi sitting room din da kallo saiya ga wajen yayi fadi da yawa, kauda kanshi yayi ya hau sama zuwa dakinshi, da kanshi ya soma shirya karamin akwatinshi da yake zuba abubuwan personal buqatunshi don Duk tafiyar da zaiyi saiyayi hakan,baya diban kaya da yawa saidai few abubuwan buqatun mashi don haka bai wani dade ba ya gama komai, zama yayi ya sake dialing number ammah still bata dauka, at this point hankalinshi ya fara Tashi, rasa abunyi yayi don this is the first time hakan ke faruwa, dialing number Aman yayi wanda shine kusan third time tana kiranshi, shima ringing kusan uku ya mashi bai dauka ba haka nan ya hakura ya kwantar da hanaklinshi.

Kamar wanda ya tuna wani abu ya miqe ya sauko second floor, a hankali ya bude kofar parlorn ta, ganin ko Ina dimm yasa ya wuce bedroom din, tsayawa yayi tare da saura hannunshi kan handle din kofar ya bude, shima dakin babu haske sai bedside lamp dake kunne, a hankali ya maida idanunshi kan gado inda take kwance, takowa yayi har gaban gadon ya zuba mata idanu, sanye yake da pjs masu laushi mai gashin kasa light green color, kanta da yar hula datayi baya gashinta a bayyane, samun kanshi yayi da kallonta tun daga sama Har kasa don bata rufe kanta da duvet ba, ta takura waje guda, fuskanta fayau babu walwala, Bakinta yayi jaa sosai kamar ta saka jan baki, take ya tuna da lokacin da yayi kissing dinta for the first time, that was his

33 / 94