/>
Kallon ammah amar yayi, ita dake kwance bata da lafiya shes showing so much concern for amra,bai kawo komai aranshi ba saima danganta hakan yayi da maybe taji cewa amra ce ta bata jininta.
Sun dade sosai wajen ammah hara man ya fita ya karbo masu lunch a kitchen, nan suka baje sukaci, banda amra dataci kadan ta ture tace zuwa anjima zata kara, salima kuwa haka ta zauna sukuku tana tunain maganr aman da yayi dazu, shiko ya lura da ita kuma yana karantarta saidai bai fassara hakan da komai ba don bayason ya sama kanshi false hope.
Da daddare nan yace wajen ammah zai kwana, amra dai ta kafe saita kwana while salima na ikirarin yau a wajen ammah zata kwana, ammah dai na zaune tana kallonsu tana jin dadi aranta, kallonsu duka yayi yace ‘’babu wanda zai zauna duk ku tafi gida’’
Turo baki amra tayi bata kalleshi bat ace ‘’ammah dan allah ki mashi Magana inason kwana anan’’
Dariya amma tayi tayi ‘’daughter kiyi hakuri ki koma ki huta abunki kinji, nida na kusa dawowa gidan ma, gobe da safe sai aman ya dawo daku’’
Kallon amr ammah tayi tace ‘’kaima son dam aka biyu you don’t have to stay tunda ga doctors da nurses, kuje ku huta’’
‘’no ammah I will stay with you, banason mu tafi gaba daya babu wanda zai tsaya a wajenki’’
Haka nan badan taso ba ta bisu suka wuce gida tana jin haushinsa na qin barinta da yayi ta zauna da ammah.
Suna fita shima ya fita ya kira doctor don ya sake duba ammah don ya tabbatar da babu abunda yake damunta, a cikin daren ya kira doctors yafi sau biyar duk after 20 mins, ammah dai kallonshi take tana jin kaunarshi sosai aranta.
Wajen karfe goma suna zaune yana matsala ammah kafafunta da suka kumbura don komai daga kwance take yinshi, kallonshi tayi tace “son,…!”
Yana jin haka yasan maganar da zatayi don haka yace “Ammah please mu bari saikin samu sauki inmun koma gida please”
“No, yanxu nake son muyi magana” ta fada seriously
Sauke kanshi yayi kasa bai sake cewa komai ba saida ta tace “will explain abunda ya faru kafin ku kawo ni nan ko Saina tambaya?” Ta fada tana kallonshi fuskanta a hade,
“Ammah Duk abunda nayi she deserves more than that, bazan taba tsayawa ina kallon wadda ke shirin illataki ba” ya fada ran shi Adan bace
“Muhammad sai yaushe ne zaka rage wannan halin naka na kaifin zuciya? Muhammad mace Ka kusa illatawa fah? Duk laifin ya bazaka kaita ga hukuma ba?”
Dago da jajayen idanunshi tayi da sukayi jaa sosai yace “ammah kashe kinga taso yi?”
“Yea na sani, and tun ba yanxu nasan da hakan ba” ammah ta amsa shi, sa mamaki yake kallon fuskanta don jin Karin bayani.
“Yea son, nasan lanatan tana saka min kwaya a cikin green tea kuma Ina sha” ammah ta fada kai tsaye
“But ammah why? Kinsan illataki zatayi kika sha”
“Kwarai kuwa kuma nayi hakan ne saboda idan har ban karba ba zasu biyo ta wata hanyar, shiyasa dana ga hakan na karba,”
Mikewa tsaye yayi yana zarya tsakanin dakin hannunshi Har karkarwa yake, “ammah whyyy, kinsan how tough it was for me seeing you akwance ammah? I thought zaki mutu, rayuwa a cikin kwananin turns upside down ammah”
Hannu ammah ta miqa mashi alamun yazo, takowa yayi inda take ya rike hannunta kafin ya zauna, anatse ya soma mashi magana, “son, Duk abunda kaga ya faru da mutun rubutacce ne, Allah ya kaddara hakan daman zai faru, yau kina mutu nasan nan barka kai kadai ba”
Nunfasawa tayi hawaye na zubowa a fuskanta, furgice yayi sosai idanunshi sunyi jaa ga hawaye nan kwance cikin idanunshi yaqi bari su sauko don yana son ya zama very strong, “son, nasan at this point kasan komai basai nayi maka bayanin komai ba, wannan azzalumin mutumin bazai taba gamawa da duniya lafiya ba, ya cuce mu ya cuci alummar musulmai gaba daya,”
Hannunta ya rike gam ya kalli ammah yace “hawayenki bazan taba bari su zuba a banza ba, tun bayan lokacin dana gane shine ya kashe dada, I can’t even imagine how you’ll feel shiyasa nayi alkawarin boye maki Har labari na saidai ayanxu bana jin Zan iya barin mugun mutumin nan ya sake nunfashi a dorar kasa, I will make his life miserable,“
Kallonshi amma tayi tace “no son, bazakayi haka ba, your hands are clean kuma bazan so hannunta ya baci ba Ka barshi da allah da hukumar ta mashi hukunci daidai da abunda yayi, mutuwar dada dai bazamu taba dawowa dashi ba, so promise me bazakayi komai ba, zaka barshi yaji da masifar duniya acahn kuma Allah zai saka mana”
Runtse idanunshi yayi baya jin zai iya hakan don babu makawa saiya kashe kabiru, don achan uae yana da rights din hakan don basa barin mai laifi nan kuwa saidai ace za ayi sentencing dinshi life in prisonment, girgiza kanshi ya soma yi ammah na Ganin haka tasan gardama zaiyi mata don haka ta hade rai tace “idan har kana jin magana ta a matsayin mahaifiyarka kuma kana bin umarnina dole kayi abunda Nace maka Muhammad, baka gani ne son, kayi tunanin akan dalilin dayasa na karbi kwayar nan nake sha over the years ban fada maka ba dukda nasan illatani takeyi slowly? It’s because I don’t want you to be like him wanda na tabbatar hakan yake so, yana son yaga Ka zama miserable baka da zuciyar imani which I’m seeing now, shiyasa yayi amfani da zafin zuciyarka da weakness dinka, kasan yanda kayi breaking heart dina lokacin da kake dukan lantana harna fadi? I never imagine my big zaiyi haka nan taba tsammanin zafin zuciyanka zaisa Ka daki mace ba Duk laifin datayi koda kuwa kokarin kasheka taso yi, na dauka kai mai tunani ne, yanxu haka zaka zauna da matanka da wannan zafin zuciyar?itama zaka duke ta kenan? Idan zaka iya dukan mace zaka iya dukana nima a matsayina na mahaifiyarka kenan idan ranka ya baci ko?
Saurin girgiza kanshi yayi dake kasa ya dago da sauri idanunshi yayi jaa “ammah I will
Never bazan taba yin hakan ba, not only you ko wace mace a duniya nan harma da aisha bazan taba yin haka ba,“,
Nunfasawa yayi ya cigaba “itama wannan bansan may ya shiga kaina bane, because ban taba tsammanin zatayi kokarin kashe ki ba, please forgive me ammah na”
Kauda kanta gefe tayi kafin ta ce “this should be the last time Muhammad da zaka saka hannu Ka akan mace,”
“Insha Allah ammah na” ya fada jiki a mace
Juyowa tayi ta sake kallonshi tace “and lastly naga kamar babu abunda ya sauya tsakaninka da matanka, dukda kaga yanda ta sanadiyarta Allah ya nufa zan rayu saboda jininta dake yawo ajikina” saurin cije lebe ammah tayi tunawa da wani abu kafin ta cigaba “Muhammad Wallahi ko bayan raina Ka rabu da aisha ban yafe ba, aisha macece ta kwarai mace ta gari, Wallahi bazaka taba samun mace kamarta ba a duniyan nan, kasa a yanayin da take ciki kuwa ammah dukda haka ta jajirce bata damu da hakin da zata shiga ba ta bani jininta, Muhammad muhammad hmm gwara ka bude idanun Ka tunda wuri yanxu ya kamata kasan cewa bazamu rayu ba atare Har abada dole dayanmu zai tafi.
Tana karashe ta sauke zazzafan nunfashi yanda zaka san ranta ya Sosu sosai da zancen,
Saurin rike hannunta ya sakeyi idanunshi sunyi jaa jijiyoyin kanshi sun fito sosai, aduniyar nan babu wadda maganar ta ke sashi shiga rudani kamar ammah, “ammah I’ve accept her, Wallahi na karbeta bazan taba rabuwa da ita ba I promise you that”
“Look bawai sabodani ko dan na fada maka zakayi ba don Karan kanka zaka karbeta da hannu bibiyu, Ka sauke hakklinta dake kanka kuma Ka girmamata a matsayin matarka Ka kula da cinta shanta damuwarta da lafiyarta kai harma da Gurin kwanan ta,Ka aje wannan banzan tunanin naka Wai tayi maka kankanta karya ne wannan, Ka godema Allah ma ta karbeka hannu bibiyu kaida baka haihuwa, haka ta salwantar da Tata rayuwar ta karbe Ka ba tare da second thoughts ba hmm”
Shuru yayi kamar ruwa yaci shi haka ammah ta silleshi tass ta mashi fada tare da nuna mashi inda baiyi daidai hade da shawarwari da nasiha don tunatar dashi ilimi da yake dashi, tunda ta fara magana harta gama kanshi a qasa idanunshi sunyi jaa sosai, “yanxu ka kai shekaru 35 wadannan abubuwan bai kamata ace ni Zan fada maka ba da ilimin Ka da tunanin ka” ammah ta karashe tana kokarin gyara kwanciyanta, saurin mikewa yayi ya tallabota ta kwanta yace “Insha Allah za a gyara in Allah ya yarda”
“Allah yasa” ta bashi amsa tana rufe idanunta har barci ya kwasheta yana nan zaune ya dafe kanshi yana nazari daban daban, idan ya saka chan saiya warware nan, kwata kwata bai runtsa ba ko kadan maganganun ammah nayi mashi yawo akai,yanxu dole yayi abunda taa umarceshi ba tare da gardama ba.
Washe gari da safe shi da kanshi ya goge ma ammah hannunta da fuskanta da kafafunta don bata fara anfani da ruwa da kanta ba,saida ya gama, ya daura mata alwala ya zura mata hijab ta fada sallah anan zaune, fita yayi ya wuce
kitchen ya basu orders abunda doctor yace zata dunga ci da sha Mara nauyi kafin ya dawo dawo dakin, lokaci daya dawo harta idar da sallah tana zaune, kallonshi tayi harya karaso tana lazimi kafin yadan duqa “good morning ammah na an Tashi lpy ya kwarin jiki”
Dan sakin fuskanta tayi ba tare da ta kalleshi ba “morning, Ka Tashi lapia” ta amsa shi
Shuru ya danyi baice komai ba don ya Lura da yanayinta Har lokacin tana fushi dashi kenan
Sallamar doctor ce tasa suka dago gaba daya, gaisawa sukayi ya duba ammah, kallon doctor sun tayi tace “yau zaku sallameni ko?”
“Ah ah hajiya sai nan da kwana hudu haka”
Yana kaiwa nan ya fuce, kallon Amar tayi tace “kaje kasan yanda zakayi su sallameni yau yau dinnan idan ma zasu hadani da home care taker ne su hadani da ita dan bazan zauna ba”
Ta karashe tana kauda kanta gefe, sum sum ya juya ya fuce daga cikin dakin ya wuce office din doctor, nan ya buqaci a bata sallama, da farko doctor yaso qin amincewa sai daga baya Ganin ran shi a bace yake yasa ya bata sallama ya hada ta da home care taker nurse don ta dunga monitoring dinta,
Dakin ya koma nan ya tadda har an kawo mata tea tana kokarin sha hannunta na karkarwa, saurin karasowa yayi ya karba cup din don ya taimaka mata, bata hanashi ba ta bashi cup din, haka ya dunga bata tea sun harta shanye kafin ya aje ya janyo white carrot soup, kauda kanta gefe tayi “tea din ma ya isa”
Bai kusa ba ya aje bowl din ya tura shi gefen, sallamar su salima ce ta sa suka juyo gaba dayansu daga shi Har ammah, salima ce ta fara shugowa hannunta rike da basket sai Salim a gefenta, kafin amra sai Aman dake biye da ita abaya yana latsa waya, gaba Dayan su matan sanye suke da abaya mai shegen kyau,
Kallonsu ammah tayi fuskanta dauke da murmushi idanunta kan amra tace “daughter maraba lale shugo,”
Da fara’a amra ta karaso hannunta rike da water flake babba, kallon food flakes din ammah tayi tace “yanxu babu wanda zai dauko flakes sun saike daughter? Ki bar masu su dauka mana karki wahalar da kanki”
Salima ce ta turo baki tace “oh ammah wannan yar warayya da akeyi mana ni ban ganeba fah, nice na kinkimo garin basket fah amma ko kallona bakiyi ba”
Dariya ce ta kufce ma amra “kedai Allah ya sawaqe maki wallahi”
Murmusa wa ammah tayi tace “ahh dear harda fushi kuma, kema na ganki Wallahi, bismillanku ku shigo”
Atare Duk suka karaso gabanta suka gaisheta cikin girmamawa, amsawa tayi tana jin dadin gani su kafin su zazzauna, “daughter zo daga nan naji lafiyanki”
Takowa amra tayi feeling so shy yanda ammah ke nuna kulawa a gareta ta karaso, hannunta ammah ta rike tace “Ki ci abunci dai ko? Hope babu abunda ke damunki?”
Girgiza mata kai amra tayi tace “babu komi ammah na, I’m perfectly fine, yanxu burinmu kema allah ya Baki lafiya mu tafi gida atare”
“Ay yanxu ma kuwa zamu tafi, Yan yakaddun sallama muke jira”
Salim ne ya karaso wajen ammah ya rungumeta don murna tana Ganin haka itama ta rungumeshi tace “yaron kirki you can’t wait mu koma gida ko?”
Girgiza mata kai yayi yana fidda set of hakoranshi.
Suna nan zaune Madina ta shigo da sallama, kallonta duka sukayi gaba daya Harda ammah “lale maraba likitar mata, sannu da zuwa”
Cikin fara a Madina ta karaso Har bakin gadon ta zauna tare da dan dukawa tace “Ina kwana hajiya? Ya jiki? Allah yasa kaffara ne”
Gaba daya suka amsa da Ameen,
“Ay jiki yayi sauqi my dear, yau zasuyi min sallama ma Insha Allah”
“Masha Allah Allah ya Kara sauqi” Madina ta sake fada, bata wani dade ba tayi masu sallama don zata wuce office.
Karfe goma sha daya daidai doctor ya shugo da paper sallaman ammah,Ka karamin dadi duka suke jiba musamman salima da amra don sunyi missing dinta sosai gidan babu dadi kwata kwata, don itace farin ciki kowa gaba daya.
Akan keken marasa lafiya aka saka ammah while aka hadota da wata nurse da zata dunga dubata daga safe zuwa dare, atare Duk suka fito Amar ne ke tura keken ammah Har zuwa parking space, bayan motarshi aka bude ya sanya ta aciki kafin nurse din ta zagaye gefen ammah ta zauna, amra dai juyawa tayi zata shiga motar Aman inda su salima ke zaune, saurin tsaidata yayi “Aisha!!!!”
Chak ta tsaya bata sake motsawa ba saida yace “get in”
Juyowa tayi ta nufi gaban motar ta bude ta shige ciki ta zauna shima ya shige mazaunin driver ya kunna motar ya saka seat belt, kallonta yayi fuskanshi babu yabo ba fallasa yace “fasten your seat belt”
Dan juyawa tayi ta kalleshi don this is the first time daya taba ce mata ta saka seat belt yawanci shike saka abunshi,dan tabe baki kawai tayi ta janyo seat belt din, haka ta fara kokawa da seat belt din saboda yayi stocking, waigowa yayi ya kalleta, kafin ya dan matso kusa da ita sosai ya janyo belt din ya saka mata, yana saka mata ya koma mazauninshi, Duk wannan abun nasu akan idanun ammah dake smiling tana sunnar dakai kasa, she’s so happy seeing them like this fatanta Allah yasa ya dore a hakan…
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 141
Update!!!
Unedited…
Tunda ya kunna motar yayi reverse ya bar harabar compound din ya dau hanyar zuwa gida, motar tayi tsit sai karar ac, motar su salima na gaban tasu inda salima ke zaune agaban motar sai Salim a baya har suka karaso gida.
Tunda sukayi parking kowa ya fito ya nufi inda ammah ke zaune a bayan motar Amar na shirin fitowa da keken da za a sakata, da taimakon nurse Amar ya fito da ita, kafin su wuce cikin gidan gaba daya,babu wanda yakai su salima jin dadin dawowarta,suna biye da ita har suka shiga parlor, bin parlor ammah tayi da kallo kafin ta fara hamdala, salima ce Tayi saurin cewa “welcome back ammah, gidan was so empty bakya nan, yanxu ya zama complete Alhamdulillah!”
Dariya Duk sukayi ammah dake zaune kan wheelchair ta fuskanceta tace “Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kaddarar hakan zai faru, Ina rokon Allah ya tsare mu daga Duk wani sharri na fili dana badi’ni”
Gaba daya suka amsa da Ameen, sama Amar ya wuce da ita tare da nurse, saida ya tabbatar she’s comfortable kuma babu abunda zasu buqata ita da nurse din.
“Son kaje Ka huta, hidiman ya isa haka, tunda ga nurse nan zata taimaka min” ammah ta fada tana kallonshi bayan ya taimaka mata ta zauna bakin gado, murmushi kawai yayi ya kalleta cikin kulawa “Akwai abunda zaki buqata a sayo?”
Hannunshi ammah ta rike don yana tsaye bakin gadon “no son, kaje Ka huta you look stressed”
Murmushi kawai yayi mata kafin yayi mata sallama ya futo daga dakin, da amra yaci karo dake shirin shugowa, batayi expecting mutun zai bude kofar ba don haka yana bude tayi baya saboda ta ciki aka budo, saurin rike hannunta yayi don yayi tunanin faduwa zatayi “careful!!!!”
Ya fada ahankali kamar ba Amar ba, saurin cire hannunta tayi daga nashi tace “thank you”, bai tsaya ba ya bar wajen, ya dauka kasa, yana wucewa ta shige cikin part din ammah, dakinta ta wuce direct ta bude kofar da sallama, kallonta sukayi gaba daya daga nurse din Har ammah fuskanta dauke da murmushi ta karaso bakin gadon ammah ta zauna tace “ammah kina buqatan wani abu? Me kikeso na daga maki?”
Kallonta ammah takeyi tana murmushi fadin irin dadin da take ji idan ta kalli amra ma mai wuya ne, Nunfasawa ammah tayi fuskanta duaie da murmushin bata daina ba tace “daughter daga dawowa ko hutawa bakiyi ba, gashi alamu sun nuna jin fara nauyi, karki damu kinji, bana buqatar komai yanxu kije ki kwanta ki huta, Kisha barcinki kinji ko?”
Sauke kai amra tayi dukda bata gane akalar zancen ammah ba sai kawai ta tsinci kanta da jin kunyar ammah lokaci guda, kallonsu nurse din tayi fuskanta dauke da murmushin tace “gaskia kam, barci nada amfani a wannan stage din da drinking lots of water”
Shuru amra tayi don bata gane kan zancen ba,gaba daya sun gama confusing dinta, ammah na Ganin haka Tayi saurin cewa “kije ki huta daughter dake da son bansan waye yafi wani damuwa akaina ba, I will be fine”
Mikewa amra tayi jiki a mace tace “Toh shikenan ammah, Zan dawo anjima”
“Toh daughter