ko Ina sai buqatar mace ne ya sakashi haka, harga Allah da tana da kawar da ke da ya budurwa ko auren dole ne zatayi mashi sai yaje chan su sasanta saidai babu halin haka don kwata kwata bata wani close muamala da mutane don kawaye ma bata dashi yawanci su ba a kasar ma suke ba kwata kwata, karasowa yayi ya zauna gefenta yace “morning ammah na”
“Morning son” ta amsa shi cikin fara a, “ son duk Ka rame,ya kamata Ka dunga cin abunci akan lokaci, I mean 3 course meal karya wuceka, breakfast lunch and dinner bawai coffee all the time ba”
Murmushi kawai yayi ya kauda kanshi gefe yace”Insha Allah awl give it a try”
Tasan halinshi na rashin son cin abunci don haka ta kauda abunda ke tantabda tambayar hakan,salima ce ta shigo hannunta rike da warmers, tana karasowa ta aje ta durkushe Har kasa ta gaishesa kafin ta koma ciki, tare suka fito da Salim dake rike da flask na kunu da lantana tayi,zama sukayi nan salima tayi serving din kowa Harda shi, ammah dai idanunta na kansu,tana gamawa ta zauna ta fara cin nata abuncin, saida suka gama tsaf lantana ta fito hannunta rike da cup green juice da take ma ammah time to Time, karasowa tayi dining din tace “hajiya ga koran lemon” dariya amma tayi Harda su salima kafin tace “oh lantana Har yau jin kasa haddace sunan lemon nan, green juice”
Dariya salima tayi Harda amma dinma tace “ammah kinga last week datayi maki ma saida na koya mata yanda ake fada don ta daina cewa koran lemo” dariya sukayi su duka Har Amar ya miqe ba tare da kallon su ba ya wuce
dakinshi,salima ne ta kalli ammah tace “ammah nikam wannan green juice din yana Kara lafiya da jini ko?”
Dariya amma tayi tace “this is the secret of my beauty, tun kafin na haifi ya Muhammad dinku nake shaa, yana gyara jiki sosai sannan its very healthy bakiganni ba Banda wani kiba sosai? Yana cleansing system”
Dariya salima tayi tace “wow ammah pls ki dan rage min mana”
Lantana dake kwashe kwanuka ce Tayi dariya tace “Toh shugaban Yan kwadayi, Wallahi babu dadi daci ne dashi, ranar na dandana,”
Dariya salima tayi tace “nidai Saina sha gaskia anty lantana”
“Toh Bari na hado maki wani saiki sha kiji inda da dadi”
Amma dai harta gama dariya take masu, don suna bata nishadi sosai,kallonsu amma tayi tace “Bari na wuce sama ayi kokari a gyara ”
Bata kaiga karasa hawa stairs ba aka bango kofar, saida ta dan dafe kirjinta kafun ta kalli aman dake shugowa,kallonshi sosai ammah tayi kana Ganin shi kasan ya bugu ya shawu sosai, don har wani jemewa yayi sosai kamar wani mai cutar, ammah dake shirin hawa stairs Tayi saurin saukowa tabi bayanshi da kallo har ya shige part dinshi, bin shi tayi har ciki gabanta na faduwa don this is the first time ta taba ganinshi a hargitse haka kamar mahaukaci,tana shiga dakin ta taddashi a kwance yana kelayar da amai, karasowa tayi har inda yake gani ya kiga ta tace “haba son, wannan wani irin rayuwa ne kake jefa kanka a ciki, dagirmanka da wayon Ka kana son salwanta rayuwar, wannan rayuwa daka jefa kanka ba mai bulls wa bane, dan dagowa yayi da jajayen idanunshi don kwata kwata baima san waye akanshi ba yace “hajiya ki fita daga dakina bana son Ganin kowa a gabana”
Hannunshi amma tayi kokarin kama wa ya fisge ya daka tsawa yace “malamaa ki futaaaaaaaa,kidaina kirana da danki niba danki bane wanchan dan iskan ne danki”
Ihun da yayi har dakin dake gefenshi na amar, salima ma dake zaune saida ta jiyo ihun da sauri ta miqe ta shiga cikin dakin, Ganin yanda yake maganganu marasa dadi yasa ta karasa gabansu ta jawo ammah dake zubda hawayen takaici saboda sai yau ta tabbatar da maganar mahaifiyar aman kafin ta rasu na cewa ubanshi ne zai lalata shi, wani irin kuka ne ya kufece mata lokaci da ya sake daka wata tsawa arazane salimata dago hawaye na bulbulo wa fuskanta tace “kasan da wa kake magana kuwa? Ammah kake yima wannan tsawa kamar tsarar Ka?” Bata gama fada ba ya kwasheta da Mari daya sa tayi ba tagal tagal kamar zata fadi ammah ta tarota, yana sauke hannunshi amar da shugowar shi kenan bayan sun shigo ya wankeshi da Mari,bai sauke hannunshi ba saida ya kwashesa da maruka uku a jere da yasashi zubewa wanwas a kasa, ammah ne ta kalli Amar tace “what’s the meaning of this son? Meysa zaka dakeshi? Ya girmeka fah”
Dan juyowa yayi da jajayen idanunshi ya kalli ammah azafafe yace “Ammah pleas!!!!!!“
Yana kasa karasa abunda yayi niyar fada kawai ya juya ya fuce daga dakin, kokarin karasawa inda yake kwance ammah tayi salima ta tarota Ganin tana shirin faduwa, “ammah please ki kwnatar da hankalinki muje na kaiki sama Zan kula dashi”
Kallon salima tayi hawaye kwance fuskanta tace “taimaka min ki kaini daki” da taimakon salima suka fuce zuwa sama, saida ta bata magungunanta tasha kafin ta fito, kitchen ta wuce ta dauko bucket da mop kafin ta wuce dakin nasa, a kwance ta taraddashi wanwas yanda suka barshi kamar babu rai, tabe baki tayi ta Galla mashi harara tace “Allah ya Kara maganinka kenan, sai iskanci fal ciki babu wani karfin kirkir, rubbish”
Gyara wajen ta fara yi saida ta tsaftace wurin kafin ta Debo ruwa cikin towel a bowl mai shegen sanyi ta kwara mashi, a furgice yayi sorbing tare da sauke ijiyar zuciya yace “la ilaha illah”
Kallon mamaki tayi mashi don bata taba tsammanin ma yana salla ba balle ya ambato sunan Allah, “ay saika Tashi, Wai mutumin daya shawu ne ke ambaton Allah imagine?”
Sai a lokacin ya ganta a tsaye, dafe kanshi yayi wani irin hawayen takaici na gudu a fuskanshi, wannan rayuwa daya tsinci kanshi me
Zai cema mahaliccin shi idan ya mutu? Why is he even blaming him self for what he has not done? Ba laifin shi bane ay Duk sharrin influence ne, wani irin kuka ne ya kufce mashi wand akana sauraronshi kasan kukan zuci ne dana fili a bayyane, “ya Allah, why me? Ya Allah ka kawo jin sauqin abunda ke raina” ya karashe da kuka sosai, sakin baki salima tayi Ganin babba da girman shi yana kuka wiwi,
For the first Time taji tausayinshi da son jin damuwarshi,da dalilinshi na fadawa wannan qazamiyar rayuwar.
Kokarin miqewa ya soma yi ya gagara don gaba daya he’s so weak,second attempt ya sake ya fadi tare da buge hannushi sosai da tiles, don gaba daya jikinshi kan hannun ya fadi, wata Kara ya saka dayasa ta saurin saki mop din ta karaso inda yake tare da riko dago hannun nashi,gaba daya ya kashe mata zuciya da yanda yake kuka tausayinshi kawai take ji “let me help you” yaji ta fada
Mamaki ne ya kamashi sosai don baiyi tsammanin haka daga wajenta ba, hannunshi ta janyo da nata hannun da kyar ya taimaka mashi tana nishin wahala ta dagashi suka koma kan gadon shi,sauke shi yar zuciya tayi kamar wadda tayi race ta kalleshi, yanda ya dafe kanshi ya Kara bata tausayi, juyawa tayi ta fuce ta aje mop din kafin ta zubo mashi abunci ta shigo dakin, yanda ta barshi haka ta tarar shi ya soma cire rigarshi da kyar don hannun Har ya soma tsami, ganin how he’s struggling yasa tace “do you need a helping hands?”
Dan dagowa yayi Ganin ta kauda ido yasa yace “no thanks” still
Baibar hawayen ba, ganin haka yasa ta aje abuncin ta karaso inda yake ta taimaka mashi ya cire rigar, toilet ta shige ta Debo mashi ruwa a bowl ya wanke bakinsa kafin tura mashi abuncin gabanshi, futa ta sakeyi ta dauko panadol ta
aje mashi Ganin yana dafe kanshi alamun yana damunshi tace “kasha wannan kan zai daina”
Dan dagowa yayi fuskanshi shar da hawaye, he never thought zata kula dashi haka, samun kanshi yayi da cewa “thank you,”
Kallonshi itama tayi tace “kadaina kuka kai babba ne, ba a son babba yana kuka, Duk abunda ke damunka ka roki Allah ya kawo maka sauqinshi, getting drunk won’t solve anything”
Murmushi kawai tayi mashi ta fuce daga daki, kallon abuncin data aje mashi yayi, ya manta when last yaci abunci tun bayan barin gidan da yayi dalilin maganar da sukayi da daddy, samun kanshi yayi da goge hawayen yaci abuncin ya koshi yasha magani ya kwanta, rufe idanunshi yayi nan take komai Ya soma dawo mashi, yanda daddy ya kashe mamanshi merciless da taimakon shi ba tare da saninshi ba, tunawa da ranar yayi yanda ya bashi maganin da hannunshi ya bata tasha ba tare da ya tambayi koma menene ba ahanakli hawaye ke zubo mashi na baqin ciki, he can still remember her voice a kunnenshi, da yanda take kaunarshi da nuna mashi hanya madaidaiciya amaimakon bin ubanshi da yake yi, bude idanunshi yayi yace “daddy you even have the guts to look into my eyes and tell me that you killed my mother with my bare hands, ya Allah why me???ka cuceni dady ka cuceni,how can you be this ruthless, merciless”
Shuru yayi yana nazari, na farko dai uba uba ne, bazai taba kaishi ga hukuma ba don yana nan a matsayin ubanshi babu mai chanza wannan, na biyu shi kadai yasan how dangerous daddy yake, tsoron karya yima ammah wani abu yasa yake baya baya da ita don karya gane ya damu da ita, don idan yasan da hakan zai iya yin wani abu ba tare da saninshi ba saidai nuna mashi da yake yana tare da shi hakan kesa yake sanin abubuwa sosai da plans don daddy din, he can still vividly remember yanda daddy yayi introducing dinshi to business dinshi wanda yayi sanadiyar mahaifiyarshi saboda kawai ta gano sirrin daddy,baiwar Allah tsahon shekarun da sukayi ta gama sanin komai nasirrin shi haka ta hakura ta boye sirrikan mijinta ba tare da yasan tana sani ba saidai kwatsam lokaci guda daya ganin ta san komai ya kawo karshenta.
Ko alokacin daya bashi maganin akan ya bata acikin abun sha cemashi yayi kwayar zata sa ta mance da Duk abunda ta sani ba tare da sanin shi kan cewa maganin kasheta zaiyi ba lokaci guda.
Wani irin hawaye ne ke saukowa a fuskan shi masu dumi da zafi, ahankali ya furta “I will
Never let him do something this time around, I have to bring an end to all Of this,“
Runtse idanunshi yayi yana tuna plan din da
Daddy din keyi.
Barci ne ya kwashesa anan kwance.
Amar dai cikin fushi ya shige cikin dakinshi, wani irin takaici da kunshi ya tarar mashi arai,laifin daddy ya shafi Aman, don ko jinin daddy baya son gani a dorar kasa.
8:30pm…
Tunda ya fito daga masjid ya shige cikin estates ya hango motar daddy parker a compound din gidan, kasa motsawa yayi kwata kwata, fuskanshi tayi jaa sosai lokaci guda zafin zuciyarshi da yake dannewa ta soma bugu, runtse idanunshi yayi ya fara karanto adduao sosai, ya dauka kusan minti biyar kafin ya iya daga kafarshi ya saita natsuwarshi ya bude kofar, sallama yayi ya shige cikin parlor, ammah ce zaune sai Aman dake gefenta kanshi a kasa da daddy dake facing kofar shugowa, gyara tsayuwar shi ya karaso seating room, kokarin kauda komai yayi baima kalli inda dady dake zaune ba ya samu waje ya zauna gefen ammah, “son Ka dawo?” Ammah ta tambaya
“Barka da dare ammah, na shiga dakin ki dazun Ay kina barci”
Murmushi ta danyi tunawa da abunda ya faru dazun kafin tace “nasha magani ne”
Aman ne yayi gyaran murya tare da hade rai yace “ammah kadai Ka gani a zaune ne?”
Dan dago da idanunshi aman yayi ya kalli inda daddy ke zaune fuskanshi babu annuri yace “barka da dare”
Wata irin dariya dady ya kece dashi dayasa ammah dagowa ta kallesu su duka a tare, yanda kasan suna wajen yaqi fuskokinsu dauke da alamomin tambaya, wani irin tsana ta Hango kwance a fuskar Amar, shima daddy kamar yaga maqiyinshi,
“Muhammad dan yunus, kayi girma da sai an nemi gaisuwa daga wajenka kenan” hade rai Amar yayi still Baibar kallon dady ba kuma baice komi ba saida ammah tace “Muhammad!!!!”
Da kyar ya kauda idanunshi kan daddy ya maida kan ammah yace “yes ammah”
Da ido ta nuna mashi daddy, runtse idanunshi yayi yana qaqalo murmushi yace “ya aiki? Hope komai na tafiya smoothly? Naga company yana samun low sales cikin kwanakin nan hope komai ya daidaita”
Dariya daddy yayi yace “kaida kazo hutu menene damuwar Ka da company issues, kayi kokari Ka samu Ka nemi abunda kake nema saboda Ka koma bakin aikinka ko”
Murmushi Amar yayi yace “very soon kuwa Insha Allah,”
Kallonshi sosai daddy yayi kafin yayi murmushi yace “hope kana kula da familyn Ka ko?” Shuru ne yadan ratsa wajen,nan take Amar ya hade rai dady ko miqewa tayi ya wuce sama kamar bashi yayi magana ba ammah kuwa bata gane kan zancen ba don haka bata kawo komai ba, daddy dake shirin hawa stairs yace “maryama ya jikin maki? Hope kina Shan magani ko? Mubammadu a dunga kula da rashin lafiyarta saboda mu bama kusa kasan yanayin aiki son”
Yana kaiwa nan ya wuce sama ya sake waigowa yace “take care of your self also”
Ammah dai kanta ya gama daure wa da zancen nashi da ta kasa gane Ina ya Dosa, aman da Amar kuwa tunda daddy yayi maganar ammah gabansu ya fadi damm, aman dai daure wa yayi ya wuce daki shiko Amar kasa motsawa yayi nan ammah ta dunga mashi fada akan yanda yake magana da daddy kamar wani sa ansa baice komi ba saidai hankalinshi ya gama Tashi sosai don bayason wani abu ya sameta..
Yana shiga daki ya fara zarya tsakanin bedroom dinshi da sitting room dinshi, ammah is his only weakness and it looks like daddy yana son amfani da ita wajen Ganin asirinshi bai tonu ba, hasashe da yake yi kenan saidai baya fatan hakan ya faru, tunawa da yanda ya kashe dan uwanshi yasa Amar jin tashin hankalinshi na double ko kadan baya tsoron daddy saidai yana tsoron karya cutarda people that are close to him, don kashe amma Zan zama Ba komai bane a wajen daddy tunda Har ya iya kashe dan uwanshi kuma jininshi, wani tunani ne yazo mashi, da farko suna zarginshi daddy na cikin ku fitar empire saidai yanxu biri yafi kama da mutun don yanda daddy ke struggle akan sirrin shi yasa ya fara tunanin kodai shine empire din gaba daya? Gaba daya tunanin ya tsaya chak ya rasa tunanin da zaiyi, gashi babu wanda zai bashi amsa, wayar ya lalubo daga cikin aljihun shi ya soma dialing number investigator dinshi, yana dauka azafafe yace “any update? It’s been 5 fucking days?, I thought you’re one the best why is it taking forever?”
Magana akayi daga chan bangaren, kafin ya ce “money is not an issues, I’m willing to spend billions, just do what ever you have to do”
Daga wayan ne guy don yace “sir then I will
Have to dirty my hands, babu wanda zai fada abu cikin sauqi saida threat”
Dan shuru Amar yayi take gabanshi ya sake faduwa, kashe wayar kawai yayi ya yar a gefe yana sauke wani zazzafan huci.
After 2days…
Dady dai duniyar shi yake ci da tsinke don ya gama tabbatar da abunda yake buqatar sani, bayan wannan ma shi baya tsoron komai Dan he’s ready for war, while bangaren Amar ba dare babu rana yake bincike akan daddy, Duk ya gama toshe kowace hanya dazaisa a gano shi,Har asad na suspecting kodai ya saka sihiri a cikin alamarin, Amar dai doesn’t believe in any of those, don haka ya cigaba da bunciken shi silently, ammah dai kullum cikin damuwa yake don gidan gaba daya ya burkice, damuwar ta na farko Amar ne don gani take Akwai abunda yake boye mata wanda ke sata zullumi sosai,bayan wannan tana kokarin yi mashi kyakyawan zaro saidai yanda baya son maganar aure take tunanin maybe ya fada tarkon matan banza, Akwai understanding da mutual respect tsaknainta dashi harma da kunya don haka take mashi kyakyawan zaton tare da kore Duk wasu maganganu da daddy ke fada akanshi, damuwar ta na biyu shine
aman, ta kasa cika alkawarin data daukar ma mahifiyarshi, slowing yake lalacewa kuma ta dalilin daddy wanda mahaifiyar Aman ta roke ta akan ta kula mata dashi saboda influence din daddy da wasu abubuwanshi da bata fada mata ba har Allah ya dauki ranta. Ga daddy shima yanxu ya chanza sosai dukda dama chan haka yake saidai yanxu komai ya zama worse, don Inya zauna babu irin maganganun da baya gaya mata wanda ta dauki hakan da baqaqen maganganu saboda tayi mashi magana akan company da yanda ake samun kudade na bacewa a account din campanin.
Damuwa sosai ta saka a cikin ranta wanda ke haifar mata da jin nauyi a kirjinta, babu wanda yasan halin da yake shiga Duk dare idan ta tuna da wasu abubuwan, kullum tana kokarin hana kanta tunanin da take yi saidai Har yau har gobe bazata taba goge abun daga zuciyarta ba.
Bangaren amra yau Friday tayi submitting report dinta ta karbi certificate, abunda ya bata mamaki to her surprise taga wanda yayi signing, kowa yayi mamaki hakan ba ita kadai ba Harda head of health team don karkashin uae armed forces suke for over the years and Duk wani abunda ya shafi interns dinsu da employees dinsu baya shiga headquarters anan cikin asibiti akeyi, promotion ne kawai akeyi a headquarters da recruitment na staffs saiga shi an kafa babban tarihi anan asibitin inda general gaba daya yayi signing certificate dinta as one of the best, abunda yafi bata mamaki shine harda proposal of work aka bata, Don har permanent license suka bata idan tana sim ta cigaba da aiki anan asibitin, gaba daya ta rasa