don haka yace “Bari na shiga daga ciki”
Harya soma tafiya tace “son dinner fah ko akawo maka dakin?”
Dan waigowa yayi ya sauke mata murmushi yace “thanks ammah”
Yana fucewa ta kira lantana ta hada mashi abunci a tray lokacin salima na saukowa, ammah na ganinta tace “karba abuncin ki kaima yayan naku”
Cikin murnar ta kuwa ta karaso wajen lanatana ta karba don tana son yi mashi hidima don ta haka ne zata saka mashi da alkhairi da yayi masu na zama gatansu kuma guardian angel dinsu.
Ammah na ganin yanda take nishadi lokacin data dauki abuncin ta tunkari dakin nasa, wani tunani ne ya zo mata arai,murmushi kawai tayi ta kauda zancen.
Washe gari da safe m5 ya kira shi a waya, lokacin bai dade da fitowa daga toilet ba, yana Ganin sunan m5 ya dauka wayan tare da sakawa a handfree don ya zauna kan dresser yana shafa bliot lotion dinshi mai kamshin berries,
“Morning sir” m5 yayi saurin cewa
“Uhm morning”
Dan Nunfasawa m5 yayi yace “madam tace za a kaita apartment dinta”
Dan shuru yayi yana nazari yace “why”
“I think she’s wants to stay over there”
Shuru Amar yayi saida ya gama shafa manshi cikin isa kafin ya kashe ba tare da yace mashi komi ba.
Number da m5 ya tura mashi lockacin da ya sayo masu waya ita da Nadine ya duba tare da dialing line din nata direct, lokacin da wayan ya shigo tana kwance kan gado idanunta a lumshe, ba barci take ba saidai tunani iri iri na yawo akanta, karar vibration din wayar ta ne yasata bude idanun ta bata motsa ba Har wayar ya katse, tsaki kawai tayi ta juya ta sake rufe idanunta don Duk a tunanin m5 ne don shi kadai ya taba kiranta lokacin da bata fito da wuri ba a asibiti shine ya kira don yaji tana ina ita kuma lokacin tana masallaci Har barci ya kwashe ta.
Nadine ce tayi mata knocking kafin ta shugo
Ta karaso gabanta tace “ma’am ga waya”
Bude idanunta tayi ta sauke su kan Nadine tace “idan wannan sojan ne ya kira kice mashi nayi barci”
Da sauri Nadine ta kalleta tace “sir is on the line”
Jin haka yasa ta saurin miqewa zaune, don tsoronshi daya durar mata lokaci guda wa tunawa dashi, saurin gyara natsuwarta tayi tunawa da Tayi alkawarin cire tsoronshi gaba daya dukda tsoronshi ya zame mata kamar a jinita yake, tabe baki tayi ta karbi wayar ta saka a kunnenta ahankali kamar mai rada, fuskanta a daure kamar yana kusa da ita tace “assalam alaikum”
Dan shuru yayi yana jin yanda muryarta ke shiga cikin kunyar kanshi, Har wani lumshe idanu yayi, yana mamakin kanshi don ya rigada yayi admitting he’s missing her, which he thinks that’s a normal feeling tunda ta zama wani page a cikin rayuwar shi da bazai taba goge wa ba amatsayinta na macen daya fara kusanta kuma macen da ya fara bama attention bayan ammah.
“Where did you keep your phone?”
A qage ta amsa mashi da “beside me!”
Yayi mamakin amsan nata saidai Baiji komi ba don shi ya tambaya
Ahankali ya soma jin saukan nunfashinta a kunnenshi wanda ke haifar mashi da shiga wani yanayi, jin yayi shuru yasa tace “zanje nayi sallah”
Yana jin haka ya gane ta qagu ta kashe ya kashe wayan, inda ada ne haushi zaiji saidai yanxu baiji haushinba kwata kwata saima neman abunda zai sake fada ya soma yi don he can’t lie he’s enjoying listening to her breath going in his ears and her voice that keeps turning I’m on and on,
“How’s your health?”
“Alhamdulillah” tayi saurin amsa mashi,
Saida yayi maganar health ya tuna da wani abu, jikinshi ne yadanyi sanyi ya kashe wayan, Kiran doctor shi ya fara yana dagawa ya soma tambayan shi akan progress din health dinta da kuma cikinshi da yake tsammanin shiga jikinta, nan take doctor ya bada shawarar dubawa ko cikin ya shiga, don she’s 4weeks ahead, dukda yana zuwa Duk bayan kwana biyu don duba ta duk cikin umarnin general din, nan ya yanke shawarar next zuwan da zaiyi zai diba jinita don yaje yayi blood test.
Tun bayan wayar shi da doctor hankalinshi a tashe da abunda zai biyo baya, dukda ya barma Allah komai don shine me bayarwa kuma me hanawa, shima ba yin kanshi bane lalura ce wadda Allah ya kaddara zaiyi rayuwarshi da ita, don haka komai ya biyo baya zai karbi kaddarar hakan da hannu bibiyu don shi mutunne mai yarda da kaddara mai kyau ko mata kyau,bayan wannan shi mutun ne me magana daya, baya chanzawa don haka ya yanke shawarar Duk abunda ya biyo maya zaiyi abunda ya dace.
Thursday morning…
M5 na sauketa ta wuce cikin asibiti jikinta yayi sanyi tunawa da Yan uwanta, don ko Barcin kirki batayi ba haka ta kwana tana kuka wanda ya haifar mata da ciwon kai mai tsanani, taso ta zauna a gida saidai zaman gidan ma Kara kuntata mata yake yi,don yanxu tana ganin dalilin qaddarar aurennan ta rasa chance din ganin kannenta data so yi, tare da jin haushin kanta na zaman da tayi na kusan wata biyu a gidanshi a gidan nashi Ma a nigeria tana blaming kanta akan abunda kwata kwata ba haka bane, Duk Karya ce dan plan ne, kullum inta tuna da wannan tana kuka da kanta na barin Yan uwanta ba tare da tasan halin da suke ciki ba dukda tasan ba laifinta bane dukda haka tana ji tana da kaso babba a cikin Duk wani mummunan abu da zai faru dasu don ita kadai gare su, tana jin tayi Ma iyayensu butulci, tana jin zafi da takaicin kanta.
Abunda ayanxu ta gama tsayarwa aranta shine, ya kawo ta nigeria ya hanata zuwa wajen yan uwanta saboda wani dalili nashi chan wanda ta bashi ma’ana na son amfani da ita don biyan buqatunshi,idan ta tuna da shine ya karbi budircinta tana kuka dajin zafin abun dukda tasan bawai sunyi ta hanyar haramci ba wato zina,abunda tafi bata mata rai shine ta yarda cewa ya kawo ta ne don ya samu abunda yake so bayan ya samu kuma zasu rabu, inta tuna da wannan tana kuka sosai don yasan dole Idan ta koma watarana zatayi aure, me zata cema mijin Idan ya gane ita ba budurwa bace, bayan wannan Ma waye zai yarda da aure tayi na sunnah.
Waennan abubuwan na damunta sosai, kanta a kasa ta shigo cikin asibitin don ko kallon gabanta batayi, da sauri ta dago jin an rungumeta, da sauri ta dago rinannun idanunta ta sauke su kan haifa, nan take hawaye suka zubo a fuskanta muryarta Har tana karkarwa tace “haifff…”
Haifa da take murnar ganin aminiyarta tayi saurin dagowa fuskanta dauke da murna don bata Lura da kukan da amra keyi ba da yanayi da take ciki tace “habibty,… ya rab I missed you so mu….”
Kasa karasawa tayi ganin kuka shabe shabe akan fuskar amra data kafa mata idanu, hannunta ta janyo suka wuce office dinta, tana karo kofar amra tayi saurin rungumeta tace “babe ina kika shiga, na shiga damuwa, nayi kewarki sosai, banida abinki yar shawara, I was so helpless”
Hannunta haifa taja suka zauna agefe tace “I’m so sorry dear, yanxu gani nan Ay bazan taba barinki kiyi nesa dani ba I promise” dariya amra tayi itama ta soma dariya kafin ta fara tambayar ta abuh da ummi
“Suna nan lpy, abuh ne Har yanxu dai but Alhamdulillah! Dalilin leave din dana dauka kenan min kaishi spain yaga wani special doctor”
Dariya amra tayi ta goge hawayen fuskanta tace “Alhamdulillah, Allah ya bashi lafiya”
“Ameen ya rab”
Kallon fuskanta haifa tayi ganin yanda ta fada sosai idanunta sun dan kumbura “babe you cried ko? Why?”
“Haif so much has happened kamar yanda na baki labari, I’m shattered,”
Tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka, zuwan senior din haifa office dinne yasa ta goge hawayen nata, suna gaisuwa nurse din ta kalli haifa tace “Akwai blood sample collection a cikin headquarters da akayi requesting kece zaki karbo”
Kallonta haifa tayi tace “okay sister”
Futowa sukayi tare da amra, ta wuce office dinta don aje laptop dinta don suna shugowa office din haifa suka wuce ba nata ba.
Saida haifa ta rakata ciki tace “babe bari naje na dawo yanxu, wait for me here”
Murmushi kawai amra tayi mata kafin ta fuce.
Bangaren Amar tun bayan wayar da yayi da doctor yaji gaba daya kamar bashi ba, jikinshi yayi sanyi sosai alamun he’s nervous don baisan me sakamakon zai kasance ba saboda tabbas yasan cewa ospermia dake tare dashi tana da babban illa, illar dake lalata rayuwar wasu mutanen, he’s feeling so down, dukda bai taba blaming kanshi ba but yana jin ammah will be disappointed, she will feel bad saboda bata da magana daya wuce jikoki, dukda shima zaiso ya samu dan da nuna a matsayin nashi.
Shirinsa yayi cikin manyan kaya don yau Friday, futowa yayi ya wuce sama zuwa dakin ammah don babu kowa anan kasan, yana zuwa ya taddata zaune da files agabanta,tana gani shugowan shi tayi saurin tattara files din ta maidasu inda ta dauko, tundaga nesa ya gano files din da take boye mashi don yaga logo din Taura a jiki, murmushi kawai yayi ya karaso inda take zaune ya zaba gefen gadon nata yace “ammah na Har kin fara boye Mun abubuwa yanxu Kuma”
Dariya tayi don ta gane ya rafkota tace “nima you’re hiding a lot from me, saidai Zan baka dama ka fada min da kanka”
Dariya kawai yayi yace “ki kwantar da hankalin, I’ve already fix the issues na company,”
Mamaki Ne karara a fuskanta don tasan baya shiga sha’anin kampanin wanda tayi fada akan ya zo ya kula dukiyarshi da Kansa amma yaqi don gaba daya dukiyar tasa ce, kaso kadan ne nata a ciki, wani irin dadi ne ya ziyarceta tana fatan adduar ta na gab da karbuwa da take yi akan ya dawo gaba daya nan nigeria sai kuma aure, fuskanshi ta dan shafa tace “babana naji dadi sosai, haka ya kamata ka dunga yi, Sai kuma aure ko?”
Sauke idanunshi yayi kasa don bayason ta gane yanayin da yake ciki, dake uwa uwace take ta hango damuwa a tattare dashi ta Kasa gane dalilinshi na qin aure, ta rasa gane kiyayyar da yake ma auren dukda yanxu ta tabbatar jikinshi na buqatar mace a tare dashi
“Son is ther any problem? Is there something that I need to know”
Saurin qaqalo murmushi yayi ya fuzge yace “babu wani problem ammah na, it’s just that I’m not ready now”
“Hmm kawai tace mashi tana mamakin hali irin nashi da kafiya.
Aranta tace “like father like son”
Bai wani dade a dakin ammah ba ya fito cikin manyan kayanshi baqin yadi mai shegen kyau da hula itama black ta zauna mashi akanshi suman kanshi tadan fito ta baya wuluk ga sajen sa Ma dake a kwance alamun yana Shan gyara, yayi matukar kyau sosai ya fito a giant handsome rich young billionaire dinshi, fatarshi soma Kyalli takeyi kamar mace, shigewa yayi cikin motar shi don Ana gab da Kiran sallar, a babban masallacin central mosque yayi parking ya fito ya shiga cikin masallaci yabi sahu, lokacin daya iso Ana yin huduba kafin a tada sallah.
Ana idarwa ya futo ya wuce inda yayi parking motarshi, rana akeyi sosai don haka yayi saurin shiga motarshi ya kunna ac, kafin ya fuce daga harabar wajen, daidai cupilo restaurant yayi don nan ne address din da asad ya bashi na inda zasu hadu da yarinyar, wayar shi ya jawo yayi dialing number nata da ta kirashi yafi sau biyar yana driving, sarai ya gane ita ne yaqi picking don baya son rawar kai, infact komai nata Ma disgusting dinshi yake yi, futowa yayi daga cikin motar bayan ya saka black shade na maza afuskanshi, bai saka hula ba ya tunkari cikin restaurant,gaba daya ranshi a bace yake saidai yana kokarin danne wa don baya son anything related to matan banza, yana zuwa cikin restaurant din waitress biyu suka taho Harda gudunsu sunga kyakyawan guy, koda sukayi welcoming dinshi bai kalli ko daya daga cikin su ba ya dauki wayar sa ya soma dialing number din, meeda data hango shi tun daga nesa ta daga wayan ta miqe tsaye tace “heyyy I’m over here”
Dan dagowa yayi ya kalli inda take kafin ya wuce waitresses din da suka shagala da kamshinsa don sun kasa matsawa daga inda suke ma, dayar ce ta daki ta kusa da ita yace “shegiya yar iska dallah wuce mu tafi yar baqulu kawai”
Wucewa sukayi suna jin kunyar yarfasu da yayi a tsaye.
Tunda ya fara takowa Har inda take ta kafa mashi idanunta kamar mayya, Har ya zauna kujeran dake facing dinta, Gyaran murya tayi cikin yauqi tace “barka da zuwa dear”
Dagowa yayi ya watsa mata wani disgusting look kafin ya kauda kanshi gefe .
Sarai taga irin kallon da yayi mata saidai ta fusge ta kira waiter akan ya kawo masu mocktail, yana nan zaune tana kidan ta tana rawarta da abubuwan da take order baice qala ba saida ya gama ya dago ya kalleta daga sama Har kasa yace “I hope Kinsan ba wannan ya kawoni nan ba, infact banida time din wannan,look let’s go straight to the points, are you wiling to do as I requested in exchange of the money or…”
Saurin katse shi tayi ta hanyar kashe mashi murya tana gyara zaman rigarta da Nonuwanta da sukayi la’asar suka fito tace “haba ko dan drink Ay ka bari mu fara dashi ko”
Banza yayi da ita Har aka kawo drink din da ko kallon inda yake baiyi ba, saida ta gama kwarkwashe kwarkwashenta Har ta hakura ganin Ko takanta baibi ba don ko kallon inda take baya yi Idan Ma yayi wani irin disgusting look yake bata ganin haka yasa ta fito mashi da asalin ta tace “meysa kake kaucewa kamar baka so” ta karashe tana laso lips dinta,
Take ya watsa mata wani irin kallo daya sata shiga hayyacinta tace “hmm”
“You’re just wasting my time,”
Ya fada Yana shirin mikewa, ganin haka yasa tayi saurin cewa “20m and one request then the deal is on”
Zama yayi idanunshi kan wayanshi yana duba wani anonymous message da yake shugo mashi wayan tsakanin jiya da yau
“What’s the request”
Dan matsowa tayi gab dashi dukda tana zaune kan kujerar tace “your stick in my hole”
Dan dagowa yayi ahankali yayi wata yar bazawarar dariya yace “in my entire life ban taba ganin disgusted creature kamar ke ba, you even have the guts to look in my eyes and ask for that?, wannan rayuwa da kika dauka Ma kanki kin cuci kanki shawara daya Zan baki, tun da kuruciyar ki kiyi kokari ki gyara rayuwar ki da lahirar ki tun anan duniya other wise zakiyi nadamar wannan kazamiyar rayuwar, your young and pretty I wonder why zaki salwantar da rayuwar ki wa mutane kamar old folks dinnan ba, you’re worth more” yana kaiwa nan ya mike ya fuce, jikinta ne yayi sanyi, duk duniya babu wanda ya taba fada mata maganar shiryuwa daya tsaya mata kamarshi don haka tabi bayanshi da sauri Har yana gab da shiga mota tace “na yarda, I will Help you out indai abunda zanyi shima aikin lada ne, I don’t need the money”
Tsayawa yayi yana karantarta tabbas ya hango nadama karara a fuskanta don haka yace “send in your account details you’ll Still have your 30m” yana kaiwa nan ya shige mota ya fuce daga harabar wajen aguje.
Murmushi tayi tace “ya Allah na tuba,meya kawoni cikin wannan haramtacciyar rayuwar da ake mana kallon kaskantattu, wannan Gaye na daban ne, na hakura dakai Har abada dukda da lalata na so muyi”shuru ta danyi tunawa da last statement dinshi, gwalo idanunta tayi tace “waiii 30million ni hameeda, uhm kudi suna inda suke”
Uae
Saturday morning…
Da sassafe ta Tashi ta sauko kasa don murnar zuwan haifa, Nadine dai Sai aranar taga ainihin murmushin amra da zallan farin ciki a fuskanta, ba karamin dadi taji ba ganin yanda take murnar zuwan kawar tata don tunda sukazo bata saukowa kasa saidai Idan zata je aiki, tunda ta sauko yake bin ko’ina da kallo Nadine na biye da ita, kallon sitting room din kasa takeyi dakyau don sa ayau ne ta samu damar ganin kasan da kyau, sitting room din nada girma sosai don kamar parlor biyu ne aka raba, daya complete set of chairs ne Dayan side din
kuma set of English royal chairs ne dauke da kayan alatu Harda tv, girgiza kai amra tayi tace “tv biyu a parlor daya koda yake wannan wajen yayi girma Ma parlor daya” dariya nadine tayi tace “ma Ay nima saida nayi mamakin nan,wanna parlor Allah kadai yasan irin kudin da aka kashe, tabe baki kawai amra tayi tace “Ina ne kitchen?”
Hanyar nadine ta nuna mata suka nufa, tana shiga Tashi wani sanyin dadi na ac da kamshin room freshner, Pablo dake tsaye da assistant maid dinshi suna rubutun provision da za a sayo sukayi saurin juyowa jin taku tafiya da sauri Pablo ya sauke kanshi kasa yace “morning ma’am”
Da dan murmushi a fuskanta tace “morning sannu da aiki”
“Thank you ma” ya amsa mata
Maid dinma saida ta gaisheta kafin su juya ita da Nadine, a cikin 1st sitting room dake kusa da hanyar futa suka zauna, basu wani dade da zama ba saiga m5 da doctor biye dashi, bata motsa daga inda take ba ta kauda kanta gefe, karasowa sukayi m5 ya gaisheta shima doctor din sanin ko ita wacece sai ya gaisheta, take taji wani iri don sun girmeta kuma ita ya kamar ta gaishesu don haka a maimakon ta amsa saita maida masu da gaisuwar “good morning doc, good morning”
M5 ne yayi Gyaran murya yace “ma, doctor is here for your check up and…”
Kallon doctor yayi alamun ya mata bayani,
“I will