Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   30 / 94

87K to 90K   out of 279.4K words

cewa komi tayi ganin yanda oga ya hade girar sama da Kasa ya kasa cewa komi, coffee don dake gab da shiga bakinshi ya sauke ya dauke idanunshi daga kanta, ita ko a jikinta ta kauda kanta daga ganinshi kafin ta juya ta nufi hanyar zuwa dakinta, dan dagowa yayi jin alamun tafiyarta don tantance inda ta nufa, take yaji wani abu ya daki kirjinshi, kura mata idanu yayi yanda take tafiya kamar tana taka kaya, kallon gefen m5 yayi ganin fuskanshi na gefe hanyar fucewa yasa yace “you’re dismissed”

Da sauri m5 ya juya don daman Allah Allah yake ya tafi, maida idanunshi yayi kanta Har ta haura sama, kafin ya sauke ijiyar zuciya, ammah dai kasa cewa komi Tayi don tabbas taji muryar mace, bata kawo komai ranta ba saidai tana mamaki don tasan baya aje maid mata a gidan, “hello son are you there?” ta katse shurun nashi 

“Yes ammah”

“Naji muryar…”

Baya son yi mata karya don haka yayi saurin katseta da cewa “zanyi breakfast will

Call you inna gama ammah”

“Toh Bari na barka ka gama” ta fada tana kashe wayan dip…

Aje wayan yayi a gefe, nadine kuwa wucewarta tayi sadaf sadaf tana tunani,kasa cin komi yayi sai dan coffee din daya kai bakinshi, he’s wondering meysa yaran sakani basu da kunyan jikinsu, meysa zata dunga yawo haka, ya tambayi kanshi kafin ya bama kanshi amsa “saboda Duk mata ne agidan”

Tsaki ya danyi don kwata kwata ya manta bai tsaida m5 daga shigowa cikin gidan ba kamar yanda ya dakatar da pablo daga aikin da yake mashi zuwa wani dan lokacin, aje coffee dinma yayi jin yanayi mashi daci a baki, runtse idanunshi yayi tunawa da yanda yake tafiya da yanda kayan yabi surar jikinta don Har shatin pant dinta yana iya hangowa don rigar ya kamata ba kadan ba,shi dai Har yau bai taba ganin kayan da sukayi mata daidai ba Duk gani yake suna dameta abunda bai sani a shine daga jikinta ne abun, Duk kayan da zata saka sai yayi haka don Allah yayi mata sura mai kyau.

Mikewa kawai yayi ya hau saman zuwa dakinta,

Amra dai tunda ta ganshi taji wani irin bacin rai yazo mata don abunda ya fada mata jiya ya bata mata rai, wainar Ma tureta tayi gefe ta Kasa cin wainar don tayi loosing appetite, saurin Kiran line haifa tayi ta fara kuka, nan haifa tace mata zatazo ta dauketa su fita yawo don ta samu fresh air na waje, agurguje ta shige closet ta zaro wata abaya mai kyau baqa da mayafin ta mai kyau ta aje kan ottoman dake cikin closet din kafin ta soma tube kayan jikin ta.

Yana karasowa gaban dakin baiyi wata wata ba ya bude kofar dakin, kamshinta ne ya shiga hancinsa duban dakin ya soma yi ko’ina very neat babu datti ganin bata nan yasa ya tako zuwa cikin dakin hannunshi made a kirjinshi don Duk tunaninshi tana toilet, saida yazo tsakiyan dakin ta bude kofar closet ta fito, don goga deodorant dake kan dresser, bata san yana tsakiyan dakinba don haka daga ita sai pant da bra ta karaso gaban dresser din ta tsaya ta bashi baya tare da jawo deodorant din ta fara gogawa kamar ance dago kuwa idanuwanta suka sauka kan nashi ta cikin mirror, Amar da ya sandare a tsaye ya kasa kifta idanunshi akanta kamar magnet haka idanunshi ya sauka kan gadon bayanta zuwa structured ass dinta, Wai abu yaji yana mashi yawo tundaga tsakiyan kanshi, saurin kauda kanshi yayi gefe, gaba daya yama manta abunda ya kawo shi dakin don jinshi yayi kamar Ana rura wutar sha awar shi akan ta, she’s driving him crazy, bayason ya zubda ajin shi agaban yarinyar nan don haka ya dan tamke fuskanshi kamar bai kalleta amra kuwa ba karamin tsoronshi taji ba don batayi tsammanin ganinshi a daidai wannan lokacin ba, saida ta tattara natsuwarta ta tuna da yanayin da take ciki, da sauri ta juya zuwa closet don rufe jikinta don tayi alkawarin bazai Kara samun access to her body ba don baisan darajar jikin ya mace ba, itako data san darajar jikinta saita tattala kayanta, tare da kare mutuncin ta, tunda ta kama hanyar closet ya bita da idanu, yanda yake tafiya da dan sauri ya bashi daman ganin yanda ass dinta ke juyawa kallon da yayi ba karamin pressure ya sauke mashi ba don gaba daya ji yayi natikan kanshi na

kunce, wani irin zazzafan nunfashi ya sauke tare da furzar da iska chan kasan makoshi yace “ya Allah ….”

Yana mamakin yanda yar yarinya kamar wanda is driving him crazy, dukda yaqi accepting hakan don yaqi yake da zuciyarshi akanta sosai.

Amra ko tana shiga tayi saurin dafe kirjinta dake bugu, dakyar ta samu ta tattara natsuwarta ta saka abayar tare da nada veil din, saida ta dan taaya kafin ta fito don tunanin Ma ya fuce already, tana karasowa cikin dakin ta sauke ijiyar zuciya ganin baya nan, wayarta dake ringing ta daga tare da karasa a kunneta, tace “babe jin iso? Gani nan saukowa yanxu”

Bata dauka komai ba ta shafa spray ta fito da wayanta a hannu, a sitting room din part dinta ta hangeshi a zaune ya daura kafa daya kan daya, kallonshi tayi ta dauke kanta ta nufi hanyar wucewa, muryarshi ce ta katseta “keeee”

Dip ta dauke wuta ranta ya dan bacci wai ke, bata juyowa ba tayi banza dashi saida ya sake cewa “are you deaf?”

Juyowa tayi azafafe idanunta sunyi jaa, tana son fada mashi magana saidai gaba daya ya gama cika mata idanu, saurin runtse idanunta tayi ta kafa akanshi tace “please ka daina kirana da kee, sunana amra Idan Ma bazaka kirani da amra ba ka kirani da aisha”

Idanu ya zufa mata kamar yanda itama ta zuba mashi, Har yanxu mamakinta yake sosai, sannan yana mamakin kanshi shima ta yanda yar yarinya kamar wanna. Zata kalli tsabar idanunshi ta maida mashi magana, kwafa ya danyi tare da cije lower lips dinshi ya taso ya taho Har inda take ganin haka yasa ta soma tafiya da baya da baya yana biye da ita Har takai bango, gabanta na faduwa amma haka ta dake ta kauda kanta gefe, saida yazo dab da ita hannunshi na cikin aljihun shi ya dan rankwafo daidai fuskanta yace “repeat what you just said”

Kasa dagowa tayi don gaba daya yayi mata runfa sosai, hannun shi ya sanya kasan habarta ya dago fuskarta daidai fuskanshi ya sauke mata wani irin nunfashi da yasa ta rufe idanunta sosai, “I said repeat what you just said”

Ya fada da dan karfi da yasa ta razana kamar zatayi futsari, damko waist line dinta yayi ya rike gam yace “idan kika bari na sake magana sai ranki ya baci”

Dago da jajayen idanunta tayi ta sauke akan fuskanshi fuskanta har yayi jaa sosai tsoro karara ya bayyana a fuskanta don kwata kwata bata son jinshi a kusa da ita musamman da yanxu babu wani distance tsakaninsu ahankali ta soma motsa cute lips dinta don neman kalaman da zata fada mashi saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ta runtse idanunta ta dago tana fuskantanshi, tattaro kuzarinta tayi ta sanya both hannayenta ta Dora kan kirjinshi tare da juya idanunta kamar mai jin barci ta zuba mashi su tare da sauke muryarta kamar wadda ake koyama magana ta turo Bakinta gaba tace 

“Nace…ka daina…kiraa…na.. da keeee”

Kasa dauke idanunshi yayi akanta, he just feel like kamar Ana seducing dinshi, yanda hannunta  dake kan six packs dinshi dan tura shi baya tare da dan shigewa jikinshi.

Ganin yayi shuru yasa ta danyi murmushi da gefen baki tace “should I repeat what I just said cause it looks like kamar baka jini ba yaa..yaa”

Samun kanshi yayi da cewa “ni kike ma puking mouth ya fada yana nuna Bakinta da idoshi,

Turo bakin ta sakeyi tare da juya idanunta tace “yaushe nayi puking baki na, ni bansan nayi ba”

Jan yajiii yayi ahankli ganin kirikiri yarinyarnan na neman maidashi soko, Duk maganganunshi da cika bakinshi na neman tafiya a banza, 

Saurin runtse idanu yayi ya tattara natsuwarshi ya mata wa Ya watsa mata wani irin kallo ya damke hannnunta tunawa da dalilin shugowarshi dakin nata yace “the last time kika Kara yawo da kayan da kika saka a cikin gidan nan ranki zai baci, bana son rawar kai be  warned”

Ranta ne ya sake baci tayi saurin shanyewa tace “ wani kaya kenan?” Ta fada kamar bata gane maganar da yake nufi ba, sake jera mashi wata tambayar tayi tace “you mean banida right din din yawo a cikin daki da bra and pant dina?”

Ta karashe without feeling shy, saidai ta kauda idanunta don da kyar ta karashe maganar don ita kanta taji kunya,

Bai gama digesting abunda ta fada ba ta sake rafko mashi wata kwabar “ni Idan bakaso saika daina shigowa dakin ba tare da excuse ba kaga shikenan bazaka gani ba balle ranka ya baci”

Kasa magana yayi ya kafa mata idanu da yanda yake turo baki ashagwabe kamar bata san tana yi ba, kanshi ya gama kullewa, saurin kame kanshi yayi don gani yake kamar raini ya fara shiga da yawa , don haka yayi saurin hade rai yace “are you insane?, ni kike fada ma na daina shiga daki without excuse? Who d hell do you think you are da zaki fada min hakan?, what do you have,this???” Ya nuna jikinta tare da watsa mata wani disgusting look kafin ya dan matso kadan yace “ke yar yarinyarki dake, me kike dashi? A jikin naki? What else do you have apart from booobbbbs and ass that is common just like every other person nothing special?, you’ve gat nothing, ki kama kanki bana son raini kwata kwata” ya karashe afusace kafin ya fuce ya barta a tsaye tsamm haushi takaici baqin ciki ya hanata cewa uppan, ta Kasa gane wannan wani irin masifa ne, shike shiga harkanta, shike shiga alamuranta, ita bata buqaci ya dunga hakan ba, saiyayi sai yazo ya zabga mata baqar magana, kuka ne ya kufce mata anan tsaye, ta dauka kusan minti goma ganin wayan haifa yasa tayi saurin daga wayan tare da goge hawayen dake ambaliya a fuskanta tace “sorry babe gani nan”

Katse wayan tayi batama jira jin abunda haifa zata ce ba.

Cikin dakinta koma ta wanke fiskanta ta sako kwalla kafin ta fito ta sauka kasa zuwa parking lots, tana shiga haifa taja motar suka Har wajen, kallonta haifa tayi tace “babe kin dade sosai kusan 30mins fah Ina jiranki”

Bata juyo ba idanunta akan wayanta tana duba new message dake shugowa cikin wayarta da unknown number tace “sorry babe, kayan dana saka ne suka matse ni saida na chanza wasu”

Shuru ne ya dan ratsa don tunda ta bude message din ganin anyi mata sallama da larabci yasa ta soma nazarin ko wanenen yayi mata message din, samun kanta tayi da amsa sallamar 

Haifa ne yadan dago ta kalleta jin shurun yayi yawa tace “babe keda waye ne haka kika kafama waya idanu”

Nunfasawa amra tayi tare da aje wayan ta maida kallota kan window glass tace “just a spam message”

Da dabara haifa ta dunga janta da surutu ganin kamar jikinta yayi sanyi harta wartsake suka wuce mall, window shopping sukayi kafin su fito, wani restaurant suka shiga sukayi orders abunci kusan Kala biyar, basu wani ci sosai ba suka fito, nan haifa ta jata zuwa sky driving, suna karasawa dake haifa tana da membership card suka samu early bookings, cikin kankanin lokacin suka shiga ciki suka hau chan sama, amra dai tunda suka hau ta fara tsoro don harya cema haifa su fasa SkyDrive din, da kyar haifa tayi convincing dinta suka hau sararin samaniya, tunda suka sauko haifa take mata fari don gaba daya cikinta ya gama tsurewa, they had so much fun sosai daga nan suka wuce wani women’s beauty event wanda akeyi Duk and of d month, amra dai wannan rana ta zame mata one of the best days tun bayan dawowa, ta samu sakewa sosai, tayi magana da manya manyan beauty influencers da therapist, she’s so happy Har makeup demo saida aka koya masu karshe dai sai gasu da kayan makeup niki niki da haifa ta sayo masu anan event din, nan haifa tasa akayi ma amra light makeup masu kyau ta dauketa pictures, Har wani Mauritanian henna saida akayi masu a hannu da bayansu sai yayi kamar henna don abun ya burgesu sosai babu abunda ba ayi anan wajen daya danganci beauty na mace, Harda wasu  aphrodisiac perfumes da body bath amra ta saya mata da take ganin ummi na amfani dasu, suna gab da fita suka hango wata mata tana sakama wata mata nose ring, kallon matar amra tayi sai ta burgeta yanda nose ring din ya haskaka fatarta kallon ind a yake kallo haifa tayi tace “you like it?”

Shuru amra tayi kafin tace “yea I love it Harda leg chain saidai mu a Nigeria Ana mashi wani fasaara sosai”

Janyo hannunta haifa tayi tace “come on Mun wuce wannan era din, muma nan Akwai masu surutu kan dole sai mace tayi aure,look” haifa ta ta nuna mata hancinta dake da yar bula saidai babu nose ring din a jiki tace “I had this when I was in england, I so much love it sosai, dana dawo ummi ta hanani sawa Wai sainayi aure but dukda haka ina saka abuna and bata damu ba indai ba cikin relative Zan shiga ba so let’s go don’t mind what ever peoples will say, it’s beauty”

Binta amra tayi with so much excitement suka karasa gaban matar lokacin har an gama yima balarabiyar kallon matar amra tayi tace “you look so beautiful” murmushi balarabiyar tayi mata tace “and it will Look more beautiful in you”

Murmushi kawai amra tayi kafin haifa ta fadama matar tayi mata bulan hancin but irin wanda akeyi karami cute one, zama amra tayi matar ta fara prepearing

machine din bulawa,haifa kuwa tsayawa tayi gaban inda show glass din collections din nose rings din da anklet Harda bracelet,zabo  masu tayi da yawa kusan Kala goma ganin wani daban ta kalli mata tace “shima wannan anklet ne”

Kallonta matar tayi cikin fara”arta don sune customers din da sukayi mata ciniki sosai tace “are you married?” Ta tambayi haifa

Murmushi haifa tayi tace “no I’m not but my friend” ta fada tana kallon amra, murmushi matar tayi ta kalli amra tace “you should get this” ta janyo jigidar da haifa ta rike tace “this is aphrodisiac waist beads, it’s very good for married couples,”

Dan matsowa tayi kunnen amra tace “he will go crazy seeing you in this”

Kallonta amra tayi ganin tana dariya saidai bata gane inda zancen nata ya Dosa ba haifa ba ganin haka ta deba kusan Kala ashirin different colors tace “she will be getting all of this”

Ta karashe tana yima amra dariya, 

Cikin minti daya aka bulama amra hanci, koda matar ta dauko wani nose ring mai shekin diamond ta saka mata saida tace “Masha Allah you’re so beautiful habibty”

Murmushi amra tayi ta kalli kanta ta cikin mirror tace “thank you”

Haifa ma saida ta yaba da kyawun nata, juyawa matar tayi ta bude wani box ta fito da wasu haddadun anklet ta Mika ma amra tace “this one is for married couples “

Kallonta haifa tayi tace “sister you’re spoiling her to much”

Dariya matar tayi tace “I love how decent and calm she is”

Guda uku ne a cikin box din don haka matar ta saka mata daya a kafarta nan take kafar ta fito fess daman tana da doguwar kafa a cike babu gashi ko digo daya,sauke kafan amra tayi ta juya nan take anklet din ya bada wani sensational sound, kallon matar amra tayi tace “thank you so much may Allah bless you for this I love it”

Murmushi kawai matar tayi don ita tasan sirrin dake tattare da anklet din ba kowa take bama Ma sai mai rabo don Duk shekara Sau daya ake kawo mata sai wanda taga dama yake bama, don ko matan shugan kasar da kyar suke samu Duk uban kudin da suke zubawa, godiya sukayi mata kafin su bata kudin sauran abubuwan da suka saya saidai kirikriri taki karban da kyau yar anklet din data bama amra guda daya na kafarta.

Daga nan saida suka tsaya suka tsaya cinnabon suka saya cinnamon rolls da boba tea Harda ice cream dayasha toppings kafin su juyo gida.

 

Basu iso gida ba Sai wajen karfe Tara, saida haifa ta fara sauketa kafun suyi sallama ta kwaso kayan da suka sayo niki niki a paper bag biyu, da hannu daya ta rikesu dayan hannun kuma ta rike cinnabona da ice cream din.

Danna door bell tayi cikin Yan seconds Nadine ta bude kofar fuskanta dauke da murmushi tace “sannu da dawowa ma’am”

“Thanks Nadine” ta amsa mata tare da karasa shigowa 

Tunda ta sako kafarta cikin sitting room karar sound anklet dinta ya dauka eco, amar dake zaune yana kallon news jin sound din yayi cikin kanshi Har cikin zuciyarshi yake, kasa hadiye non alcoholic wine din dake hannunshi yayi, tsaki ya danyi ya juyo ya kalli inda take don baiyi tunanin itace ba, mamaki yayi sosai ganin ta da tsaye, Sai yaga fuskanta ta sauya mashi sosai, dukda he prefer seeing  her naturally yau Sai ya zama kamar ba itaba, sauke idanunshi yayi kan hancinta dake a mike Sai dan kyalli dake shiga cikin idanunshi kamar diamond, saurin kauda kanshi yayi itama bata ce Kala ba ta wucewarta, sound dinne ya dunga echoing a kanshi ya rasa abunda yake ji, it was so attractive don Sai yake jin abun kamar melody, sake juyowa yayi ya zuba mata idanu don ya juya mashi baya tana shirin hawa stairs, idanunshi ya sauke hannunta dayasha Mauritian henna kafin ya sauke zuwa kafanta dake fidda sensetional sound din, saurin dafe gabanshi yayi jin yanda shaawarshi ta taho mashi gadan gadan, ahankali

30 / 94