kun dawo kawai”
Murmushi tayi ta miqe tace “okay son take care please” murmushi kawai yayi yana kallonta harta fuce daga dakin, at least yanxu yaji sauki aranshi tunda zata Har gidan for now kafin komai ya daidaita.
Wayarshi ya zaro ya Danna kira, Ana dagawa ya runtse idanunshi yace “do it now”
Yana kaiwa nan ya aje wayar hawaye na zubowa akan fuskanshi, he’s so sad.
Karfe Tara Amar ya fito daga dakinshi, shima bai samu tayi breakfast dazu ba, karasowa yayi inda suke zaune ammah da salima sai Salim Duk sun shirya tsaf, gaishesa salima tayi kafin ya karasa kusa da ammah ya gaisheta, suna gama gaisuwa tace “son breakfast fa?”
“No ammah Saina dawo zanyi”
Kallon agogon hannunshi yayi yace “let’s move ko,jet din has arrived”
Kallonshi amma tayi don tambaya chan kuma Tayi saurin kauda tambayar Tata ta miqe suka fito gaba daya, shima Aman fitowa yayi daga dakinshi idanunshi kan salima itama kallonshi take kamar yau ne ta fara ganinshi, lanatan ma Harda ita a Yan rakiya, suna fitowa harabar gidan ya fiddo da katuwar Range Rover dinshi, driver ne ya soma shiga da akwatinsu bayan motar kafin ya bude ma ammah gaban mota don already su salima sun shige baya, lantana Harda Yan hawayenta, wani irin horn akayi kamar yaqi, juyowa aukayi gaba dayansu Harda Amman dake shirin shiga motar don Ganin wanda ke shirin shugowa, gate na budewa a mugun speed daddy ya shugo da motarshi cikin gidan, baima kashe motar ba ya fito kamar a maye, idanunshi sunyi jaa sosai gadan gadan ya tunkaro inda suke tsaye ya kece da dariya ya kalli amar yace “dan ubanka Ka tsorata ne zaka dauke uwarka saboda kana tsoron karna kashe maka ita?”
Kallonshi Amar yayi shima Aman dai kalllonshi yake feeling so disappointed, runtse idanu ammah tayi ta kalli amar shima kallonta Hajo ya mata alamu data shige cikin motar kawai karta tambayi komai, bude kofar tayi tana shirin shiga daddy ya sake cewa “kinyi asarar haihuwa maryama, kina tunanin zaki iya guduwa daga wajena?, Har abada!!!!”
Juyowa tayi ta kalleshi irin kallon kodai Ka hauka ce ne, “Alhaji yanxu fisabillahi ya kamata Kana magana haka agaban yaranka? What is the meaning of this? You’ve gone so far this time around”
Wata irin dariya daddy yayi ya kalli amar yace “wow, so she’s your weakness huh?”
Dariya daddy ya sake yi yace “lallai tarihi zai maimaita kansa ubanka ma haka ya ganni kuma ya barni Har daukewar nunfashinsa balle kai karamin kwaro bazaka taba kaini kasa ba,”
Idanun amar ne sukayi jaa sosai, jijiyoyin wuyanshi sun Tashi sosai yace “don’t ever say a word about dada”
“Orrr kana tsoron Kar uwarka ta gano komai?”
Kallon ammah yayi yace “ke kuma dan da kike alfahari dashi shin kinsan sirrikan dayake boye maki?”
Juyowa ammah tayi don kwata kwata sun saka ta cikin duhu,bata gama processing komai a ranta ba daddy ya soma yi masu debar albarka anan tsaye,aman dai ya kasa cewa komai, suna nan tsaye karar jiniya ta karade
anguwan gaba daya, ahankali gate ya fara budewa nan take motocin sojoji kusan guda hudu suka shigo cikin harabar gidan ajere, nan take sojojin suka fara durowa daga cikin motar daya bayan daya suka zagaye gidan, amar dai mamaki yake karara haka zalika daddy da bakinshi ya mutu murus, asad ne ya karaso inda sukewsanye cikin maki yace “you’re under arrest” nan take asad ya dago warrant arrest paper ya nuna mashi,sojoji biyu ne suka zo gaban daddy suka dukar dashi kasa, saurin runtse idanu Aman yayi ya kauda kanshi gefe hawaye na zubowa, takowa asad yayi gaban Amar yace “sorry sir we have to do it, naga you looks surprised,Ka duba internet yau kuwa alhamdlh komai yazo da sauqi?”
Kallon mamaki Amar ya mashi kafin ya buqaci Ganin warrant arrest din karantawa ya somayi, kafin ya kalli asad yace “why didn’t you consult me? Kasan hakan da kukayi abunda zai jawo?” Ya fada yana kallon bangaren amma da gaba daya shock ya hanata bude baki tayi magana “so sorry sir, I have to do it,”
“Take him away” Amar ya fada kai tsaye kafin ya taka Har inda ammah ke tsaye ya dafa kafadarta, dan dagowa tayi ta kalleshi idanunta na kawo ruwa tace “what’s going on here?” Kasa magana Amar yayi sai rike hannunta da yayi trying to calm her down, daddy da ake shirin tafiya dashi ko ajikinsa ya soma dariya ya juyo ya kalli inda suke tsaye ita da Aman yace “this is just the beginning son,wannan ne babban kuskuren da zakayi a rayuwarka” kallon ammah yayi yace “maryama yanxu zakiyi alfahari da la’anann danki ko?”
Dariya ya kece dashi yace “Ina tausaya maki Maryama,anyways ga danki nan abun alfaharinki”
Kallon Amar yayi yace “ka kula da uwarka sosai kaji, because Ina nan tare da daku ina gaban ku Ina bayanku kai Har Kwanan abuncin ku nan bari ba Ina nan tare daku, and mark my words saina tarwatsa farin cikin ku, you’ll regret this”
Cikin sojojin ne wani ya taliyo kafarshi kasa Har yana kara don ya bugu sosai, dukda haka bakinshi bai mutu ba dukda suna shirin turashi cikin motar, dagowa yayi ya sake kallon inda suke yace “hope Ka fadama uwarka lalatar da kake yi achan wata kasar daban daya hanaka dawowa zama anan? Da auren da kayi achan”
Wata irin dariya ya kece dashi kafin a tura keyarshi cikin motar yace “Saina kawo karshe ku bakusan dawa kuke dealing ba hahahahaha”
Haka nan aka fuce da daddy daga cikin gidan.
Ahankali ammah ta cire hannunta daga cikin na Amar ta kafa mashi idanunta da sukayi jaa fusknata ma tayi jaa sosai, kallonshi disappointment take mashi tare da tuhumarsa, Amar dai tunda ta cire hannunta cikin nashi jikinshi yayi sanyi, bazai iya yi mata karya kuma ba, yanda Duk ta furgice yasa hankalinshi ya Tashi don abunda yake tsoro kenan, kallon mamaki take mashi don ko ba a fada mata ba tasan abunda daddy ya fada haka ne don fuskar Amar ta tabbatar mata da hakan ba tare da tace komai ba ta shige cikin gida kamar zata fadi, su salima ma fitowa sukayi don agaban idanu su akayi komai, cikin suka wuce Harda
Aman, Amar dai yana nan tsaye ya kasa motsawa, fuskan amma kawai yake hangowa da yanda take mashi wani kallo mai wayar fasaara, da kyar ya daga kafafunshi ya shiga cikin parlor, babu kowa a cikin parlor don haka ya wuce sama direct jiki a mace, ahankali ya bude kofar, a zaune ya taddata ta dafe kanta, karasowa yayi har inda take, ya dan tsugunnaa gabanta yace “ammah pl….”
Hannu ta daga mashi tace “bana son wani kwana kwana, you have played me for so long so just answer my question”
Gabanshi ne ya bada wani damm, kallonshi ta sakeyi fuskanta a daure kana ganinta kasa tana cikin damuwa tace “wace irin rayuwa kake yi a dubai?” Sunkuyar da kanshi yayi kasa yana jin wani daci aranshi, daka mashi tsawa tayi tace “answer me now!!!!!”
Dan dagowa yayi Ganin yanda hannnunta ke karkarwa yace “ammah na please calm down”
Wani irin kallonta watsa mashi tace “you’re asking me to calm down?, Muhammad answer my question before rabka ya baci anan” ta fada on top of her voice,
Gaba daya ya rasa abunda zaiyi don baya son ta ta da hankalinta, “idan ba zakayi magana ba get out of my room, I don’t want your presence” ta fada tana nuna mashi kofa, hannunta ya sake kamo ta fusge ahankali hawaye ya soma sauka a fuskanta tace “Muhammad fasiqanci kake yi daman? When? Tarbiyar dana baka kenan? Yardar danayi maka kenan? Whyyyy”
Wani irin kuk ne ya kufce mata, nan take hankalinshi ya Tashi, yau mahaifiyarshi ta zubda hawayenta akanshi, innalillahi wa inna iliahi rajiun”
A furgice ya dago yace “ammah please karkiyi judging din komai, I can explain”
Wani irin kallo ta watsa mashi tace “yanxu zakayi explanation kenan?”
Dan dago da jajayen idanunshi yayi ya riko hannunta da kyau yace “wallahil azeem nan taba fasiqanci ba, nan taba neman matan banza ba,”
“Okay so??? What are you hiding? You expect me to trust your words now?, son Ka bani mamaki” hawayen dake zubowa a fiskanta yayi sauri share mata yace “please ammah ki diana zubda hawayenki, allow me to explain”
Shuru tayi tana kallonshi, Sunkuyar da kanshi tayi kasa don kunyar kallonta ma yake yace “I got married 8 months ago”
Zumbur ta miqe tsaye ta kalleshi tace “you what?” Dawo da ita yayi ya zauna yace “dan Allah ki kwantar da hankalinki amma”
“How do you expect me na kwantar da hankali na? Muhammad aure fah? Aure kayi ba tare da sanin mahaifiyarka ba? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,”
“Ammah please kiyi hakuri ki yafe min dan Allah, karkiyi fushi dani idan kikayi fushi bansan ya zanyi ba”
Kauda kanta gefe tayi tace “give me one good reason”
Shuru ya danyi kamar bazaiyi magana ba don nauyin maganar ma yake ji sannan yasan she will hurt and disappointed at the same time, runtse idanunshi yayi kanshi a kasa yace
“I’ve been diagnosed with oligospermia “
Da sauri ta dago ta kalleshi, don she couldn’t believe it, wani irin hawaye ne ya sauko akan fuskanta,oligospermia data sani dai? Wanda mahaifinshi yayi battling dashi Har suka fidda rai suka barma Allah cikin ikonsa kuma ya kawo mata cikinshi daga shi kuma shikenan,
Kallonshi tayi tace “oligospermia? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,when did you found out?
“5 years ago” ya bata amsa
Runtse idanunta tayi take taji wani irin nauyi a zuciyarta “meysa baka fada min ba? Why??”
Shuru yayi ya kasa dago idanunshi ya kalleta “you’ll be disappointed kawai kuma nasan zaki saka damuwa aranki”
“Ni ba mahaifiyarka bace? Kana da wanda ya fini ne eh?” Ta fada rai abace
Shuru ne yadan ratsa kafin tace “who did you get married too? Dama chan kana da wadda kake son aura ne?”
Dan dagawa yayi yace “no, yarjejeniya kawai mukayi”
“Bring her this instance,” ta fada babu wasa a fuskanta
“Ka kawota koma wacece inason naji daga bakinta because I can’t trust your words”
Dan dagowa yayi kamar zaiyi kuka yace “Ammah please, everything has come to an end, Ina komawa Zan sake ta, the deal has been done”
Kallonshi ta sake yi tace “ni kake fadama the deal has been done? So Akwai more to this discussion kenan? Na baka dama Ka fada jin komai you wasted that chance now get out of my room na baka nan da awa 24 Ka kawo koma wacece ita”
Tana fada ta mike ta shige cikin bathroom ta barshi nan tsugunne hankali atashe,rasa abunyi yayi don this is the first time yaga fushin mahaifiyarshi, fita yayi daga dakin hankali atashe ya soma dialing contact din m5, yana picking ya bashi umarnin yayi booking flight ticket for amra, ayau yau dinnan.
Monday morning..
Uae
Amra dake cikin school taje submission na report dinta, bata wani dade ba tana gamawa ta fito daman m5 ne ya kawota, she was so excited komai yazo karshe don Har clearance sun gama yi certificates kawai za a basu, tana fitowa harabar makarantar m5 ya bude mata bayan mota kafin su fuce daga compound din, yanda taga yana tuki agaggauce kamar zasu Tashi sama yasa hankalinta tashi, bata ce mashi komai ba Har suka iso airport, dago da idanunta tayi kafin ta kalleshi, ba tare da wani bata lokaci ba ya fito tare da bude mata bayan mota,
dinkin ta futo, fitowa tayi tana kallon ikon Allah, me hakan ke nufi kenan? Kallonta yayi yace “ma’am you’ll depart in 10mins from now”
Azafafe ta dago da ta a bace tace “to where?”
Ba tare da wani Kwana kwana ba yace “Nigeria”
Shuru ta danyi tana nazari chan kuma ta dan sake aranta tace “faduwa tazo daidai da zama”
Gaba yayi tabishi abaya suka shiga cikin airport din, babu komi a hannunta daga ita sai handbag dinta, sanye yake da abaya orange wanda ta amshi jikinta sosai tayi mata kyau, aggauce m5 ya gama yi mata komai y bata boarding pass saboda babu wani kaya da zatayi weighing don haka yayi mata sallama ya wuce abun shi….
Kallon boarding pass din tayi Ganin a abuja jirgin zaiyi landing yasa ta tabe baki tace “not this time around”
Karfe uku daidai na yamma flight dinsu ya daya zuwa nigeria….
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 128
Arana irin ta yau duniya ta dauka kafar yada labarai da social media,kan video din Alhaji kabiru Taura,ceo na kamfanin taura oils, na miyagun business din da yake gudanarwa a boye, mutanen alhaji kabiru da ma karrabanshi sun shiga tashin hankali sosai don lokaci guda abun yayi blowing a social media ba tare da sun ankare ba, Alhaji kabiru ma abun yazo mashi a bazata saidai a koda yaushe a shirye yake don Duk tashin hankalin da zai shiga yana da mabiya bayanshi, wato Yan siyasa da yake bama maqudan kudaden musamman lokacin campaign don haka yasan ko an kamashi dole za a sakeshi saboda connection na mutane da yake dashi da suke mara mashi baya,cikin qanqanin lokaci maganar arresting din Alhaji kabiru ta gama karade Duk duniya wanda hakan yasa suka Kansu Yan siyasar da suke mara mashi baya suka fara kokari janye hannayensu don babban alamari ne da Duk wanda hannunshi ya shiga cikin alamarin zai iya affecting dinshi shima.
Aman da ya koma daki zuciyarshi na bugawa, hawaye na gangarowa a fuskanshi, saurin janyo remote din tv dake jikin bangon bedroom dinshi yayi ya kunna news, inda timeline din ke nuna cewa “ayau ne aka kama babban attajirin shugaban kamfanin da yayi suna a duniya gaba daya wato TauraCom bisa ga zargin shige da fuce na miyagun kwayoyin da safarar mutane acikin video da ya yadu a duniya a Safiya yau litinin goma ga watan April, acikin video an shaida
shi a matsayin shugaban kungiyar daya kafata shekaru a shirin da suka wuce, baya wannan yana hada hannu da manya manyan kasa inda jami’an tsaro da kula da hakkin dan Adam suke buncike akan wannan, Alhaji taura dai dan asalin jihar Adamawa ne inda ya samu muqamin ceo na kamfanin taura yayin da dan uwanshi Alhaji Yunus taura wanda aka sani da Taura ya kafa kamfanin Har ya mutu Alhaji kabiru ya karbi ragamar companying, acikin video an shaida wasu maqudan kudi a maajiyar Alhaji kabiru da yanda suke safarar kwayoyin da production din kwayar”
Gaba daya jikin Aman saki yayi ya kasa motsawa, hawaye da yake hana kanshi yi suna sulalo, samun kanshi yayi da zama bakin gadonsa ya kura ma tv din idanu, nan aka hasko video din daya dauka yana zagaye dakin daddy lokacin daya shiga, dafe kanshi yayi yana kuka yace” ya Allah ka dubeni, I’m I doing the right thin?” Ya tambayi kanshi yana kuka,tunawa da shine ya tona asirin mahaifinshi da kanshi yana mashi ciwo a zuciya saidai hakan shine abun da ya kamata yayi tun farko,tunda ya dafe kanshi yake kuka wiwi kamar karamin yaro.
Yau dai gidan kowa yana cikin tashin hankali, waya kam babu irin wadda ba a ayi masu, kofar gida ya cika makil da reporters,Amar dai tunda ya fito daga dakin ammah yake zarya a cikin nashi dakin, babban tashin hankalin da bai taba shiga ba yau ya shigeshi, ammah ta zubda precious hawayenta akanshi wannan wace irin masifa ce ya fada aranshi, babu abunda yake sai innalillahi a zuciyarshi, gaba daya matsalar da take tunkaro shi musamman kamfanin taura da yanxu image din company din yayi tarninshing ba problem dinshi bane, shi ammah ce damuwarshi, because he can see how shock she is da taji yayi aure, yanxu inaga taji cewa daddy ne ya kashe dada kenan? She will be miserable qilama ta samu heart attack, abun saiya fi mata ciwo sosai saboda itake auren daddy ita ta zauna dashi ba tare da sanin cewa shine makashin mijinta ba.
Da sauri ya girgiza kanshi dake Sara mashi yace “no I can’t let that happen, no matter what bazan bari wannan zancen ya fito ba”
Zama yayi seating room din part dinshi ya dafe kanshi, shima news din ya kunna don bai gane bayanin da asad ya soma yi mashi ba akan abun daya yadu a social media, nan take aka hasko video din komai, ga daddy a zaune Harda alif shuraim da wasu mutane suna yin meeting, next video kuma dakin sirrin shi ne da yake aje kudade da kwayoyin, idanu Amar ya kurama tv din yana karantar environment din da kyau, idanu ya zaro ya furta “what???? Acikin gidan nan”
Bai gama tunanin ba salima tayi knocking kafin ta shigo tana baki tace “ya Muhammad wasu mutane sun…zo”
Kallonta yayi ya miqe ya wuce tabi bayanshi, yana karasowa parlor din yaga dandazon maza kusan su goma a tsaye da suit sun Dora wata rigar akan kayansu da tambarin efcc a jikin, kallonsu yayi fuskanshi a hade ya kallesu daya bayan daya yace “who gave you the permission to enter my house?”
Ogan ciki ne ya karaso gabanshi ya miqa mashi hannu sanin koshi waye yace “we’re very sorry sir but this is strictly official, we have to search the whole house”
Ba tare da wani bata lokaci ba ya jawo wayarshi yayi connecting line dinshi dake da rank dinsa na uae ya kira head of financial crimes wato executive chairman of the efcc, call din na shigowa chairman din Ganin international rank code yayi saurin dagawa cikin respect suka fara magana, baima tsaya introducing kanshi ba don mukamin shi ya wuce yayi introduction nan yace “kana da masaniya akan buncike da ake shirin yi a cikin gidana?” Nan take cikin girmamawa yace “sorry sir, I think it’s a mistake saboda nayi mamakin Ganin call din, ayau buncike guda daya muka tura shine na gidan alhaji kabiru taura…”
Katseshi Amar yayi yace “withdraw the investigation,”
Ba tare da wani jin