Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   62 / 94

183K to 186K   out of 279.4K words

toshe  wucewar jinin daga zuciyarta’’

 

Juyowa amar da aman sukayi atare suka kalli juna, abunda suke zargi ne dai ya tabbata, so all this while daddy ita yake hari, shiyasa yace suna tafun hannunshi Kenan, muryar doctor ce ta sake katse masu tunani inda yace ‘’bayan wannan akwai abunda ya daure mana kai, magungunan da doctor hafix ya daurata akai ya kamata ace sunyi protecting dinta don magunguna ne masu karfi sosai, bayan wannan alamu sun nuna symptom din da take samu na fidda jini ta baki da hanci ba tun yanxu ta fara yinsu ba, maysa kukayi gangancin barinta har jininta yayi kasa?, don badan jinin wannan yarinyar ba da tuni mun rasa ta gaba daya, jinin yarinyarnan shine kadai abunda ya ceceta, sai mu gode ma Allah, and by the way shes a brave girl, babu inda aka taba diban jini bag uku lokaci guda, wasu bag daya ake diba suke passing out,’’

Kallon doc din aman yayi yace ‘’alahamdullahi thank you so much doctor zamu iya ganinta yanxu’’

‘’no not now, shes in coma,  will advice zuwa gobe idan komai y agama regulating don yanxu haka muma dole sai mun sanya idanu sosai akanta’’

Tunda amar ya sauke kanshi kasa ya kasa dagowa har doctor y agama yi masu bayani.

 

Godiya sukayi mashi suka fuce daga office din, gaban emergency rooms da ake ajiye patients suka tsaya suna kallon ammah dake kwance akan gadon marasa lafiya babu abunda suke hangowa sai fuskanta don gaba daya an lullubeta fuskan nata ma an saka mata oxygyn hannunta kuma jini ne da ake kara mata, tunda suka kafa mata idanu ta jikin glass door din sunkai kusan minti talatin a tsaye, gaba dayansu duk sun firgice kamar basu ba, sun sauya gaba daya duk sun galabaice, jin ana kiran sallar magrib yasa aman yace ‘’muje muyi sallah’’

Jiki a mace amar ya wuce aman yabi bayanshi tare da salim, fadin irin kwanciyar hankali daya samu da akace bata mutu ba ma bata lokaci ne, har sukayi sallah suka dawo cikin asibitin babu wanda yasa ko ruwa a baki, suna dawowa amar ya tsaya a bakin kofar dakin ammah ya zuba mata idanu while su salim da aman suka wuce dakin da aka kwantar da amra.

Da sallama suka shiga nan suka tadda amra kwance idanunta a lumshe har an sauya mata kaya zuwa na patients, salima kuma na gefe ta na sallah tana idarwa ta mike zuwa gaban aman tace ‘’ya jikin ammah? An gama operation din? Hope babu abunda zai sameta?  Bazata mutu ba ko?’’

Haka ta dunga jero mashi tambayoyi, samun kanshi yayi da janyota jikinshi ya rungumeta yace ‘’calm down, the operation is succeccfull’’

Jin haka yasa amra ta bude idanunta don kamar a mafarki taji Kalmar, fuskanta yayi fayau sosai tayi haske saboda jinin jikinta da aka jiba, sai jijiyoyi da suka firfito mata, kallonshi amra tayi muryanta na karkarwa tace ‘’is she out of danger?tana lafiya? Is she okay now? ‘’

Saurin sakin salima yayi ya kalleta yace ‘’alhamdulillah, it’s a successful operation, but shes still in coma, yanxu we have to wait har saita tashi.’’

‘’alhamdulillah alhamdulillah’’ amra ta furta tana hawayen farin ciki.

Kallonshi salima tayi tace ‘’yaya muje inason naga ammah pls’’

Katse ta yayi yace ‘’bazaki samu ganinta ba saidai ki leka’’

Amra ce ta soma kokarin mikewa tace ‘’please zan dubata nima, wallahi hankalina bazai taba kwanciya ba inbanganta ba’’

Badan yaso ba ya jagorancesu suka fito, salima na rike da hannun amra don bata iya tsayuwa saboda jirin dake dibanta, anatse suka tako har gaban dakin inda amar ke tsaye ya zuba ma dakin idanu,kallonshi aman yayi yace ‘’zasu dubata’’

Dn waigowa yayi ganin amra a tsaye kanta a kasa, nan take yayi saurin kauda kanshi gefe, wani irin daraja da girmanta ne ya sauka a kanshi, bayan ammah babu mace a duniyannan da yake jin ta kamar amra ayanxu, ta samu wani matsayi a zuciyarshi wanda bazai taba hadata kowa ba bayan amma, yau yarinyar daya raina itace ta taimaki mahaifiyarsa, itace ta ceci mahiafiyart ayanxu da babu ita a cikin asibitin da saidai ammah ta mutu,

Samun kanshi yayi da yin baya ya tsaya daga bayanta salima ta taimaka mata suka tsaya bakin kofar, shafa kofar amra tayi tana hawaye babu abunda take

fada sai ‘’alhamdullah ya allah, allah mung ode maka, allah ya tashi kafadunki ammah, allah ya tausasa maki ya baki strength, muna buqatarki a cikin rayuwarmu gaba daya, allah ya baki lafiya’’….

 

Amar dai kasa tsayuwa yayi ya juya ya fuce daga wajen, don shi kadai aysan abunda yake ji a cikin zuciyarshi a wannan lokacin.

Sun dade sosai wajen kofar dakin ammah kafin su koma dakin amra atare.

 

Karfe goma aman ya kalli amar yace ‘’ya kamat muje gida sai mu dawo gobe’’

‘’no ka tattara yarannan ku koma gida kawai ni zan kwana anan,’’

Aman  najin haka yace ‘’okay ita kuma..’’

‘’kuje kawai zan kula dasu’’ yana kaiwa nan ya koma gaban dakin ammah, aman kuma ya juya dakin amra don sanar dasu salima sa salim su fito don su wuce gida

‘’salima ce ta kasteshi ta hanyar cewa ‘’yaya, adda fah? Ku koma kaida salim ni zan zauna da ita’’

Janta gefe yayi don amra nab arci karta tashi yace ‘’amar zai kula da ita shi yace na wuce daku gida ma’’

Jiki amace salima tace ‘’toh muje,’’

Juyawa sukayi ganin amra nab arci basu tasheta ba suka fuce daga dakin.

Suna wucewa amar ya wuce dakin amra, a kwance ya taddata tana barci fukantsa ya zubama idanu, ta rame sosai lokaci guda ta zabge, wani irin tausayinta ne ya dabaibayeshi, shi kadai yasan me yake ji game da ita a wannan lokacin, ya dade sosai anan kafin ya koma wajen ammah itama ya kai kusan awa guda a wajenta kafin ya sake dawowa dakin amra, sai ya zamana kamar shifting yake yi, idan ya duba nan saiya duba chan, gaba daya tausayinsu yake ji sosai, duk wata gajiya ma baya jinta ko kadan, karfe sha biyu ya dawo dakin amra, bai dade da shigowa ba ta bude idanunta ta sauke akanshi, kasa dauke idanunshi yay akanta, yana nazari abubuwa da yawa na yawo a kwakwalwarshi akanta, saurin kauda kanta gefe tayi batace mashi qala ba haka zalika shima baice mata komai ba, chan kuma ya juya ya fuce daga dakin, abunci ya nemo mata don yasan zata buqata anan cikin kitchen din asibitin, atare da chef din ya taho suka shigo cikin daki, kallonta ya sakeyi muryanshi kamar bazai fitaba yace ‘’aishaaa’’ dan waigowa tayi ta kalleshi jikinta duk ya zama weak, ‘’seat up’’ ya fada kamar bashi ba, da kyar ta fara kokarin mikewa saidai kash jikinta y agama tsami don haka tana dagowa ta koma, yana ganin haka ya matso kusa da ita ya tallabota ya zauna gefenta ya kalli cheaf din yace ‘’bring the food here’’

Katseshi tayi saurn yi tace ‘’bana jin yunwa’’

……..

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 138

UPDATE

Unedited page

Ba tareda ya saurare ta ba ya janyo table din da chef din ya ajiye abuncin kafin ya fuce yace ‘’bana son gardama eat’’

Kauda kanta gefe tayi jiki amace tace ‘’toilet nake son shiga’’

Mikewa yayi ya sungumeta gaba dayanta, arazane ta juyo ta kalleshi, gaba daya bata da wani kuzari ajikinta don hka ta lafe a jikinshi har ya shige da ita bathroom din, yana shiga ya sauketa akan wc ya fuce daga bathroom,

Bayan fitarshi ta soma tube kayan jikinta tayi wanka da ruwan zafi sosai kozaji dadin jikin nata, tana gamawa ta dauro alwala  jiki amace dukda tana jin jiri sosai.

Tana gamawa ta maida kayan asibitin ta fito anaste,lokacin dta fito yana zaune kan kujeran dake gefen gadon asibiti, ya dafe kanshi dake sara mashi, baiji alamun fitowanta ba saida ta rufo kofar bathroom din, dago kanshi yayi ganinta tsaye tana shirin takowa harta karaso baking ado kanta akasa, tana zuwa bakin gadon ta janyo jallabiyanta datazo asibitin da ita ajikinta, kokarin komawa bathroom tayi ganin haka yasa yayi saurin ‘’let me excuse you’’

Yana kaiwa nan ya juya ya fuce, da mamaki ta bishi da idanu kamar bashi ba,gaba daya yayi laushi sosai, tausayinshi ta soma ji lokacin data maida idanunta kan abuncin day ace taci, yanxu haka shima baici ba ta fada aranta,jiki a mace ta sauya kayan jikinta zuwa abayar nata kafin ta zauna a kan carpet ta tada sallah.

Tan idarwa ta koma kan gado ta lafe jikin gadon ko kallon abuncin batayi ba don bakinta ma daci yake mata sosai.

 

Wajen karfe daya tana nan zaune kafin ta miqe ta gyara mayafin abayarta ta fuce daga dakin, direct emergency ward ta wuce zuwa inda aka kwantar da ammah, anatse take tafiya kamar zata fadi harta karaso wajen, batama lura dashi ba, yana zaune daga gefen kujerun reception din ya dafe kanshi dake sara mashi sosai,

Gaban dakin da ammah ke ciki ta tsaya, ta jikin glass din kofar dankin take hangota hancinta maqale da oxygen dake taimaka mata waje fidda nunfashi, ba karamin tausayinta taji ba, ta kasa gane dalilin da zaisa lantana ta cutar da wannan baiwar allah, dan zaman datayi da ammah ta karanci halayyanta, macece mai tausayi da kaunar kowa, bata da ha’inci kwata kwata ga son mutane ga hakuri uwa uba ga kyauta, batada matsala kwatakwata kowa nata ne, idan kowa bai shaide ammah ba toh tabbas ita da kannenta zasuyi mata sheda mai kyau don tayi masu komai a duniya, ammah uwace ta gari a gurin kowa.

Fashewa amra tayi da matsanancin kuka sosai tana wannan tunanin aranta harya dago kanshi don kwata kwata baijin motsin ta ba data karaso wajen ba sai yanxu, samun kanshi yayi da kallonta ba tare da tasan yana yi bama, kuka sosai takeyi kamar ranta tana tausayin ammah sosai, ayau koda ance ta bata zuciyarta zata iya, ba karamin tashin hankali ta shiga ba lokacin data ga lantana tana saa mata abu acikin drink, don bashine frist time da hakan ya faru ba, dukda bata kawo komai aranta daga farko ba saidai dole yanda lanata tayi acting kamar mara gaskia lokacin data shiga kitchen dinnan ya tabbatar matar mata da something is fishy, tana nan tsaye wani irin karar na’ura ta soma tashi daga dakin, ammah dake kwace ta soma jijiga, zaro idanu amra tayi kan kace me saiga nurses gaba daya sun taho hanyar dakin harda likitoci guda biyu, hankali atashe amar ya miqe yazo gaban dakin inda amra ke tsaye, nurses na ganinsu bakin kofar suka ce ‘’sir ku bamu waje,’’

Hankali atashe amar yace ‘’waaa…waaas…whats going on? Meke faruwa, you guys should fucking explain whats going on’’

Ba tareda sun bashi amsa ba suka wuce cikin dakin gaba dayansu harda doctors din, nurse day ace kawai ta tsaya bakin kofar tana kokarin yi masu explaining,’’sir dan allah ku kwantar da hankalinku, zamuyi iya kokarinmu akanta please’’

Tana kaiwa nan ta koma cikin dakin suka dukufa akan ammah da likitoci, amra dai kasa tsayuwa tayi saida ta dafe bango, amar kuwa tunda ya kafama kofar idanu yana hango yanda suke fidda wasu na’urori agaban ammah hankalinshi ya tashi, yanda likitocin ke zarya akan ammah suna kokari cetota, babu abunda amar ke fadi sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sun dauka kusan minti ashirin a gaban ammah suna kokarin daidaita bugun ziciyarta saidai kasha bun yaci tura, kafa masu idanu amar yayi ganin sun tsaya gaba dayansu, nan take gabanshi ya fadi dammm, bude kofar doctor yayi jiki a mace kanshi a kasa ya karaso inda amar ke tsaye yace ‘’im so sor….’’

Janyo rigarshi amar yayi yace ‘’what do you mean by that?, why are you sorry’’

‘’yallabai sai hakuri, zuciyanta ya tsaya chak bata nunfashi babu abunda zamu iyayi  im sor….’ Doctor bai gama fadaba amar ya katseshi ya soma cewa

‘’innalillahi wa inna ilaihi rajiun, innalillahi wa inna ilahi rajiun’’, nan take yayi baya yuuu zai fadi, cikin sauri doctor ya taroshi, mikewa amra tayi aguje ta karaso inda amar ke yashe a kasa babu numfashi yayi passing out, saurin kamo hannunshi tayi ‘’yaya yaya dan allah ka tashi na shiga uku’’

Gaba daya ta gama susucewa kamar wadda tayi karamin hauka babu abunda take cewa sai ‘’yaya dan allah ka tashi, ammah bata mutu ba bazata mutu yanxu ba insha allah’’ 

 

doctor ne ya kira nurses sukada janyo gado aka saka amar akai don yayi passing out gaba daya, amra  dake tsaye itama kunnuwanta zun gama jiyo mata abunda doctor fada ga amar a kwance shima kamar babu rai hankalinta ya gama tashi sosai har wani dishi dishi take gani, haka aka gangara da gadon da aka kwantar

da amar har zuwa wani daki amra na biye dasu duk ta gama susucewa, har aka kwantar dashi aka mashi allura don ya samu shock ne, amra dai babu abunda take sai maimaita innalillahi a zuciyanta, shikenan ammah ta mutu, innalillahi wa inna ialihi rajiun, kallon amar tayi kawai saita fashe da wani matsanan cin kuka, haka ta duga sintirya agaban gadonshi tana hawaye ga jiri na dibanta, hankalinta y agama tashi don bata san mezai faru dashi ba shima,gabanshi ta karaso ta tsaya tana kuka ta rike hannunshi da kyau ‘’yaya…’’ tana fadin sunan shi ta sake fashewa da wani matsanancin kukan sosai, ta dauka tsawan minti talatin a kusa dashi har ya soma motsa hannunshi, da sauri ta dago ta kalleshi lokacin harya bude idanunshi da sukayi jaa sosai, zumbur ya miqe ya dafe kirjinshi dake bugu fat fat fat, amra na ganin haka ta soma toshe bakinta ta kalleshi, shi baima kalleta bay a soma juya kanshi yana cewa ‘’no nooo nooo innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan wani irin mafarki ne haka’’ ya fada yana confusing kanshi, shuru amra tayi tana kallonshi ta kasa cewa komai har nurse ta shigo  don ta duba koya tashi don alluran da akayi mashi relaxing mind takeyi idan mutun ya samu shock, after 30mins kuma zai farka, don haka tana shigowa ta kaarso gabanshi zata duba yanayin bugun zuciyarshi tana karasowa ya daka mata uwar tsawa ‘’don’t fucking touch me, get outtttttt!!!’’ yanda ya fada saida ya razanar da nurse din harda amra, aguje nurse din ta fuce don idanunshi sunyi jaa sosai jijiyoyin wuyanshi duk sun mike, amra dai bata motsa ba dukda ta tsorata sosai baya ji baya gani haka ya sauko da kafafunshi kasan gadon yana kokarin fucewa daga dakin ‘’karya kuke wallahi, ammah na tana raye’’

yana miqewa ya fara tangal tangal zai fadi, da sauri amra ta taroshi, nauyinshi ne ya rinjayeta nan take suka fadi gaba dayansu a kasa, da sauri yafusge jikin shi ya juyo da jajayen idanunshi ya kalleta, kafin ya yunkura zai sake tashi, bai kaiga daga kafarba ya sake faduwa kasa,yana ganin haka ya dafe kanshi kawai, amra na kuka matso kusa dashi da kyar ta karaso hannunta na rawa ta fara kokarin dafashi ya daka mata tsawa ‘’leave me alone, ki fitaaaaa’’

muryanta na rawa ta dafa ‘’ya…ya’’

‘’ki futa nace, bana son ganinki’’ ya fada yana sunkuyar da kanshi, idanunshi sunyi jaaa sun tara ruwa, kwata kwata hawaye suqi futa daga idanunshi, abunda yakeji kadai ya fi kuka ciwo, yau ta kasance rana mafi baqanta a cikin rayuwarshi, har lokacin ya kasa believing abunda kunenshi suka jiyo mashi, yana nan zaune ya dunqule hannunshi ya fara bugun tiles din dakin,amra na ganin haka tayi baya tana hawaye ta fara girgiza kanta ta toshe bakinta da hannunta tana, gaba daya ya sauya kamar bashi ba, babu abunda ke shimfide afuskanshi sai pain,he’s in so much pain, bugun hannunshi yake akan tiles din yana ‘’noo noo nooo ammah noooo’’

Yanda yake bugun nan saida tiles din ya fashe, hannunshi ya soma fidda jini, arazane amra ta karaso gabanshi jikinta na bari fara kokari rike hannunshi nashi, kasa hanashi tayi don kamar ta rike rock har jini ya fara Malala akasan dakin,

tana kuka haka ta miqe ta rungumoshi gaba daya zuwa jikinshi ta kankameshi, ‘’yaya dan allah ka bari, zaka jima kanka ciwo’’

Baya jinta ma kwata kwata don y adage sai bugun hannunshi yake yana ‘’nooooo ammah na nooooo’’

Rukoshi tayi da kyau ta soma karanto mashi addua a kunenshi, tana jin yanda kirjinshi ke bugu kamar zuciyarshi zata futo, har razana saida tayi saidai hakan baisa ta sake shi ba saima dagewa datayi tana mashi addua a kunneshi,ta dauka kusan minti goma tana yi har ya daina bugun hannunshi nashi ya fara sauke ajiyar zuciya, ‘’shikenan, ammah kin tafi abu ya tafi,kun barni ni kadai, innalillahi wa inna ilaihi rajiun,’’ ya fada yana kankame amra sosai, kwata kwata ya kasa fidda hawayen dake cikin idanunshi, zuciyarshi is so tough, when it comes to ammah hes so weak, itace weakness dinshi, lokaci guda yaji kamar an toshe mashi farin cikin rayuwarsa gaba daya.

Yanda yake maganganu ba karamin karya zuciyar amra yayi ba,fadin irin tausayinsa da take ji a lokacin ma bata lokaci ne, she can feel his pain don ta shiga irin yanayi daya shiga lokacin da nasu iyayen suka mutu, tana kuka shabe shabe ta soma mashi Magana anatse cikin kunnenshi ‘’yaya, youre not alone, you have us you have me, allah yana tare dakai yaya, dan allah ka sauke hawayen dake cikin idanunka ko zaka samu sauki,’’

Gaba daya ya gama sandarewa ya zama kamar dutse, zuciyarshi ta dashe gaba daya ta sauya daga haske zuwa baki.

Suna nan zaune saiga doctor ya shgo dakin……

 

Update

Unedited

Suna nan zaune saiga doctors sun shigo, dagowa amra ta ‘[taimaka mashi ya zauna bakin gadon, tunda ya zauna ya dafe kanshi bai dago ba amra na gefenshi ta rike hannunshi, har lokacin bata barkuka ba idanunta sunyi jaa sosai, kallonsu su duka doctors din sukayi kafin daya daga ciki ya soma bayani, ‘’ alhamdulillah sir, shes still alive’’

Saurin runtse idanu amar yayi kafin ya

62 / 94