shigo ba Har ya jita
“You know I hate repeating my self right”
Da sauri ta nuna kayan tace “daman Nace yau friday wannan kayan sunfi dacewa da rana irin ta yau”
Kallon kayan yayi yace “okay bring them out”
Haka kawai ta rai ci kanta da jin dadin zaben datayi ganin tana shirin fucewa ya sashi cewa “where’s the inners”
Da sauri ta juyo tace “huh?” Alamun bata gane ba
“Ina aka taba saka kaya babu shorts?”
Nan take ta dago abunda yake nufi, take taji kunyar da bata san ta menene ba saidai ta alaqanta hakan da abunda yace
“Bansan inda suke ba”
Nuni yayi mata da glass wardrobe dake gefen wajen kayan
Dole yanda ya tsura mata idanu ya sata wucewa gaban wajen ta bude glass din, suma a jere suke da yawa sosai, farin short ta dauko mashi tare da vest fara ta
juyo ganin ya fuce ya sata bin bayanshi,ganinshi tsaye gaban dresser ya sata wucewa bakin gado ta aje mashi su ta juyo tace “uhm ga kayan”
“Come here”
Ya fada Adan kausashe,
Takowa tayi ta tsaya daga bayanshi tace “gani”
Kallonta yayi kafin yace “about yesterday’s assignment?”
Da sauri ta dago don da kyar ta hana zuciyarta daga tunanin abunda ya faru jiyan Sai kuma yanxu dataji abunda ya fada sai ya sata shiga dan tashin hankali, tunawa da alqawarin datayi Ma kanta na kokarin shanye Duk abunda ya mata ya sata sauke kanta kasa tana rarraba idanu ta dake kamar batasan zancen ba ta dago ta kura mashi idanu kamar yanda ya zuba mata nashi Harda wani far far da idanu tayi tace “wani assignment kenan”
Haba wa nan take yaji wani abu ya daki zuciyarshi, lallai yarinyar nan ta raina shi, me take nufi kenan? Kasa tunanin komai yayi sai abu daya dake mashi yawo akai,she’s pretending kamar ta manta da jiyan, da baiga yanda pants dinta ya jike ba zai rantse bata ji komai ba ko bata amshi sakon daya aika mata ba a sunan assignment.
Kamar ta Kara kunnashi nan take ya hade rai tauuu ya fara takowa azafafe idanunshi sun soma jaa jijiyoyin kanshi sun fara firfitowa,
“Repeat what you just say”
Gabanta ne ya fadi ganin yanda yake binta tana baya, dakewa tayi tace “nifa bansan me kake magana akai ba”
Da sauri ya bugi bangon bayanta don harta kai jikin bango sosai ya mata rumfa, take gabanta ya bada wani dam tana hana kanta kukan data saba don gaba daya ya chanza ya burkice,
“Bakisan me nake nufi ba? Is that what you said”
Wata irin dariya yayi data fidda asalin kyawun fuskanshi Har dimple dinshi guda daya dake gefen bakinshi na lobawa, azafafe ya waigo ya zubama jikinta kallo daga sama zuwa kasa, dago da fuskanta yayi saitinshi, idanunshi ya cusa cikin nata kafin ya dan matso da jikinshi kusa da ita sosai don nunfashinsu na dukan juna sosai yace “don’t worry you’ll understand what I mean today, and mark my word Sai na koyama bakin ki nan da bai iya magana ba”
Yana kaiwa nan ya matsa daga gabanta ya koma gefen gado ya tsaya yana sauke wani huci mai zafi “get out of my room now, before i…”””
Baima kaiga karasawa ba ta futa da gudu don ta tsorata sosai dashi ba kadan ba, saidai tana futa ta sauke ajiyar zuciya da murnar dakewar datayi agabanshi “wohhh ashe Zan iya” ta fada harda yar dariyarta ta wuce daki.
Tana futa yabi kofar da kallo, don ya hasala sosai da abunda tayi yana cikin magana Ma bai gamaba ta fuce, lallai zai koya mata hankali,
Karfe goma daidai ya gama shirinsa cikin shigar manyan kaya kaftan sky blue, tunda ya zura rigar ya saka wandon na fara cewa “Masha Allah” shi kanshi yasan kayan sunyi mashi kyau ba kadan ba saidai bai cika saka su bane sbd sabawa da yayi da kananun kaya da kundura, kusan Sai iya cewa This is the third time manyan kaya tun bayan barin nigeria da yayi, Sai baza kamshi yake, bai saka hula ba don bata cika damunshi ba keys dinshi ya dauka tare da wayanshi ya fuce daga dakin nashi.
Koda ya fito bai tsaya ko Ina ba Sai gaban hadaddiyar range rover baka dake pake cikin moto in gidan da aka rufe, shi dai babu abubuwan zamani da baya saima kanshi, don babu amfanin kudin idan baka moresu ba kuma kayi sadaka wasu Ma suci albarkaci.
Yau bai jira driver ba don baiyi shirin fita da shi ba, saida yayi warming motar kafin ya fiddota waje ya fuce daga gidan don motocinsa basa sati ba a wanke su ba.
Direct inda asad ya tura mashi ta location ya wuce, ta taimakon map ya iso hotel din, saida ya kashe motar kafin ya jawo sun glasses dinshi ganin Ana rana sosai ya fito, tunda ya fito kallo ya koma kanshi, harya shige cikin reception din, mutanen dake zaune na ganinshi sukayi welcoming dinshi tare da tambayar ko lodging zaiyi, yamutsa fuskanshi yayi don wurin gaba daya is not decent dukda banban hotel ne a nan abuja saidai baya cikin class dinshi don baya zuwa hotel mai hayaniya haka, ba tare da bata lokaci ba ya masu bayanin zuwa shi, da yake asad din da yayi booking din shima bai dade da zuwa ba nan take daya daga cikin masu aiki a gaban reception din suka jagoranceshi zuwa inda zaije, ganin mutumin yabi hanyar stairs yasashi cewa “bakuda lift ne”
“Sorry sir lift din ne is faulty amma Ana kan gyarawa we’re sorry for that”
Baice komai ba yabi bayan gayen don da alamu dakin da nisa sosai”
Suna gab da shiga dakin ya hango commotion daga nesa saidai wannan ba damuwanshi bane, harya zai gifta ta wajen kunnuwanshi suka jiyo mashi babban zagin da yasashi dagowa ya kalli wadda ke zagin “Aman harka isa kace na futa maka a hotel room, aikin banza, ance maka so hauka ne, to hell with you and your behaviour,bazan Kara kawo kaina wajen ka ba har ka samu damar kirana da karuwa, asararre inda kasan abunda ubanka keyi da bazaka kirani da prostitute ba, kaje ka tambayeshi wacece meeda koshi ubanka bai isa ya fada min magana ba balle kai danshi”
daga cikin dakin saurayin ya daka mata tsawa don ita ta fito waje shi kuma yana ciki”get the hell out of here before you regret it, Ana dole ne? Ina amfanin mace mara kamun kai ki koma iyayenki su koya maki tarbiyya”
Da sauri Harda ihunta tace “thank god inada wanda zasu koya min, kaifa? Kana tunanin ubanka Alhaji kabir zai baka tarbiyar ne? Anyway Tashi tarbiyar ta watse inaga kai kuma, nidai ban taba ganin watsatsu ba kamar daa da uba, aikin
banza sunan Ma da kake taqama dashi ashe ba naku bane, masu sunan Ma basa iskanci da kukeyi da anyi magana kuce kune The TAURA’s rubbish”
Amar na jin haka harya wuce su ya tsaya jin abunda tace, tabbas abunda yake tunani hakan ne, muryar aman yaji, itakuma fah? Ya tambayi kanshi, karuwarshi kenan? Ya sake bama kanshi ansa, zagin datayi ne ya sashi juyowa karaf idanunshi suka sauka kan nata don itama ta juyo, wani irin disgusting kallo ya mata itako tunda ta kafa mashi idanu ta Kasa saukewa wani irin dadi ne ya ziyarci zuciyarta take abunda take shirin fada ya maqale a bakinta,
“ ya Allah gayen nan ne, the guy from the airport wayyo Allah na”
Ganin tsayuwanshi a wajen baida amfani ya sashi bin hanyar da yake tafiya, harya bace ganinta bata daina mamakin ganinba, saida ta dawo hayyacinta ta fara rokon Allah yasa baiji tujarar datayi ba, da sauri ta fuce daga cikin hotel din ta shiga katuwar lexus motarta, tabar wajen, Kiran layin kawarta ta soma yi babu qaqautawa Har saida ta daga “hello ke baby albishirin ki, wayyo Allah yau Allah ya amshi rokona,”
Da sauri baby tace “ke ihun me kike min? Duk kinji kin tayar min da hankali Ina kan network kin katsemin…”
“Dallah yi min shuru ki saurare ni, kin tuna guy din nan wanda muka ganshi a airport”
“ Niko na tuna, kice min gayen da kika mace mashi”
“Baby na ganshi yau, baby ya tafi da imani na innalillahi, ashe dan Nigeria ne ay nan sani ba da tuni na sa an bunciko min gaba daya tarihinsa, anyways ba wannan ba ma, Kinsan Nace maki naje wajen banzan,”
“Wai aman taura”
“Eh shi,”
“Kema in Banda masifa irin taki meeda, kina muamala da ubansa kika kafa ido akanshi, nidai ban taba ganin mayya irinki ba, da rana ki dandana uban da daddare kibi sahun dan, haka baisan kuna tare da mahaifin shi ba”
Da sauri cikin masifa tace “ay ko bai sani ba Yau ya sani,don Wallahi ba a tabani nayi shuru saina qunsa ma mutun,kuma ubanshi yanxu na fara haukatashi ta ruwan jikina,”
“Toh yanxu ya kenan? Idan uban ya gano shi kuma ba”
“Baby bazan taba bari ba, Ay kabiru yana tafin hannuna wallahi, kina tunanin zan sakeshi ne yanda yake sakarmin kudi Harda mota yakaini dubai da qasashen hutu “
Dariyar Yan iska baby tayi tare da cewa “yayi mutuniyar kina kasheni wallahi”
“Ina kan hanyar zuwa gidanki yanxu, dan Allah ki tattara kananun yarannan naki da suke kwashe albarkar ki ki korasu zanzo muyi magana mai muhimmanci”
“Chap Wallahi Saina gama jin dadi na, Yanxu haka ma Ina kan network kika katse min jin dadi”
Kitt meeda ta kashe Wayar tare da cewa “banza mara aji”
Amar….
Tun bayan abunda yayi witnessing ya kara jaddada iskanci aman, itama kwata kwata bai gane taba don haka kwafa kawai yayi ya shige dakin da asad ke ciki da bakinsu, yana shiga kuwa ya samesu a zazzaune da sauri asad ya mike yace “oga barka da isowa”
Musabaha sukayi kafin ya kalli mutanen dake zaune akan kujera fuskokinsu dauke da damuwa ,takowa yayi ya zauna gefe kafin ya gaishesu cikin kamewa,
Kallo su daya bayan daya asad yayi kafin ya soma magana “alhaji munason jin bayanin Duk abunda kuka sani da ganinshi na karshe da kukayi,karkiyi komai ku fada mana zamuyi kokarin ganin danki ya dawo gareku,
“Toh..Toh.. yallabai, mamuda shi kadaine danmu namiji, mun kasance masu rayuwa cikin talauci don da rufun asirin siyarca raken da mamuda keyi ne muke samun abunda zamu kai bakinmu,kamar yanda kuka gani ni makaho ne bana gani , abunda Zan iya tunawa shine ranar lahadi da daddare bayan mamuda ya dawo daga kasuwa don Sai bayan isha I yake dawowa, nan muka zauna yanda muka saba ga uwar shi nan ita ta kawo mana tuwan dare ma mukaci, nan take ya shaida min cewa ya hadu da wani babban mutumi ya saya rakenshi Har yabar mashi chanji, nayi mamakin kudin don wannan sun wuce chanji don kusan dala ce ta amuruka tun daga ranar Idan ya futa kasuwa ya dawo zai fadamin abun alheri da Alhaji nan keyi mashi na siyan rakenshi koda baiyi ciniki ba aranar,rana daya yazo min da zancen aiki daya samu wanda alhajin nan ne ya mashi tayin aikin a wani kampani, saidai aikin ba a nan kano bane a habuja ne irin aikin Gyaran kampani, wankin bandaki da sikuriti,farko ban yarda ba saida mamuda ya shiada min Ay sunada yawa wanda aka kawo masu tayin aikin na taimakon matasa, yanayin yanda rayuwar mu ke tafiya da ilimi da mamuda ke so yasa na amince akan yaje yayi aikin tunda ance wata biyu ne kacal anan habuja, da farko na soma jin tsoro sai kuma nazo na fawwala ma Allah komai, nidai ban taba ganin alhajin ba haka zalika mai dakina amma Akwai abokin aikinsa halliru wanda suke siyarda raken tare Ina kyautata zaton shima dashi aka so tafiyar Sai kuma ya fasa sbd rasuwar mahaifinshi Toh kaji yanda abun yake.
Dagowa amar yayi yace “shi hallirun Kun sanshi ne,”
“Eh makocinmu ne yallabai”
Kallon asad amar yayi yace “get someone to bring him to abuja today and change this environment, a nema masu koda gida ne su zauna for now”
“Okay”
Kallon mutanen Amar yayi yace “ku kwantar da hankalinku zamuyi kokari Insha Allahu,”
Godiya sosai sukayi mashi kafin su futa tare da asad
“Oga naji an kira sallah, muyi sauri Kar mu rasa sallar juma’a “
“Okay muje”
A tare suka fuce zuwa motar amar, Allah yaso Akwai babban masallacin a kusa don haka sukayi parking suka hau sahu akayi sallar juma’a dasu,
Direct headquarters suka wuce, domin yin wasu ayyukan.
Karfe takwas da rabi daidai na dare suka koma masaukin da aka sauya ma mutanen, gida ne dan karami daki da parlor Harda bandaki aciki, malam makaho ne ya masu iso Har cikin gidan kafin su zazzauna parlor, hallilu da bai gama dawowa daidai ba don hankalinshi a tashe yazo abuja yanda akazo daukashi saika dauka ko wani mai laifi ne, abunka da bakauye dukda sanyin ac na motar data taho dashi bai hanashi shiga rudu ba sosai.
A gaggauce asad ya soma magana “bawan Allah ka kwantar da hankalinka nasan ka san waennan ko?”
Ya nuna malam makaho da matarshi
“Eh yallabai na sansu makotanmu ne kuma iyayen abokin Sana’a ta”
Nunfasawa asad yayi kafin ya cigaba da tambayarsa “ance tare aka yi maki tayin aiki ko “
“Eh yallabai, Muna tare alhaji mai rabon dala ya mana tayin don nima harna amince, da farko dai naji tsoro don Har Mun nuna mashi bazamu yi ba sai kuma daga baya ya nuna mana cewa aikin kampani ne zamuyi don Har katin kampanin ya bamu”
Da sauri asad yace “kana tare da kafin yanxu?”
“Ah ah yallabai baba tare da katin, amma yana gida na aje shi cikin kayana”
Kallon Aman asad yayi ganin yanda ya kosa sosai, idanunshi ya maida kan hallilu yace
“Akwai wanda zaka sa ya dauko katin yanxu daga gidanku yakai waje”
“Eh babata tana nan zata iya daukowa, Zan iya kiranta Ma yanxu don tanada yar karamar nokia saita dauko”
Wasu numbers asad yayi dialing kafin ya bada umarnin aje gidansu a karbo, suna nan zaune hallilu ya kira babarshi ta dauko katin ta kaima sojan dake waje kafin shima ya kira oganshi, Wayar da suke tsammani ce ta shigo da sauri asad ya mike ya fuce daga cikin parlor ya dauka yace “send me the picture of the card” yana fada ya kashe wayan, cikin Yan mintuna saiga hoton katin tarr a
screen dinshi, gabanshi ne ya fadi sosai da kyar ya samu ya tattara jarumtarshi ya dawo parlor ya kalli yanda amar ya dau zafi kafin yace “sorry daga gida ne aka kira hajiya bata jin dadi, ko zamu bari sai gobe mu dawo”
Amar dai bai gamsu da abunda yace ba saidai ganin kusan karfe goma ta gifta yasa sukayi masu sallama suka fito daga cikin gidan.
Ko a mota babu wanda yace da wani qala harya saukesa a gidansu dake maitama sukayi sallama kafin ya juya akalar motarshi zuwa gidansa. Kwata kwata ya manta da ita gaba daya saida yayi parking kafin abunda ya faru tsakaninsu ya dawo mashi, cije lower lip dinshi yayi kafun ya janyo wayanshi dake kan dash board ya fito ya rufe motar, cikin natsuwa ya tunkari kofar ya Danna door bell din kofar, lokacin tana daki, mamakin karar door bell din ya sata saurin zura hijab dinta akan rigar baccinta don hartayi shirin barci, ta fito don zuciyarta bata kawo mata shine ba Saima tunanin qila Nadine ce ta dawo Daga asibiti don tunda tun bayan fitarta daga dakinshi ta wuni a dakinta gudun sake haduwa dashi,don bata Ma san ya fita ba, sai wajen yamma ta fito ta don yunwa ta ciyota sosai bayan wannan Ma ganin yanda da safe alamu suka nuna yana jin yunwa yasa ta dafa da yawa hardashi,rice and stew tayi sai pepper chicken daga gefe, stew din taji kayan kamshi da naman rago, tana gamawa ta zuba a hadaddun warmer ta aje a dining bayan ta diba nata.
Karasowa tayi bakin kofar ba tare da wani tunani ba ta bude kofar, kallon kallo suka shiga yi, ta bangarenta yayi mugun yi mata kyau sosai don this is the first time ta ganshi da kayan hausawa, kayan ya amshesa sosai, tundaga kanshi Har kafarshi ta kare mashi kallo kafin ta maida idanun kanshi, gashinsa ya kwanta lubb sbd bai saka hula ba, dan tabe baki tayi a da ta tace “dama ya saka hula dayafi kyau”
Chan kuma ta maida idanunta kanshi don ta shagala sosai, ganin yanda fuskannan babu yabi ba fallasa yasata dan kunququni chan kasan maqoshi tace “mutun kullum fuska a hade”
Sarai ya jita yayi banza da ita yace “kallo ya isa haka karki cinyeni da wannan idanun kamar maje”
Yanda ya fadi maje din ya bata dariya har batasan lokacin datace “mage ake cewa ba maje ba”
Kurama fuskanta idanu yayi yanda take dariyan sai yayi mata kyau sosai Har pinkish oval lips dinta na dan turowa gaba, kauda kanshi gefe yayi ya raba gefenta yace “Zan ga Idan anjima kinada sauran bakin magana”
Bata gane me yake cewa ba saima dariya datayi ta rufe kofar ta sake cew “Wai maje”
Tana rufewa ta hango shi tsaye bakin stairs ya zura hannayenshi cikin aljihunsa dan nesa dashi ta tsaya kafin ya nunfasa yace “what’s that”
Ya fada yana nuni da warmers din dake dining
Da sauri ta maida idanunta Kasa tace “uhm daman abunci nayi ne dazu shine na…”
Bai bari ta karasa ba ya fara Taka stairs yace “ki kawo min sama”
Kyam ta tsaya ta bishi da kallo ta Kasa cewa komai Har ya bace mata daga gani, zuciyan ta ne ya soma bugawa, harga Allah bata san zuwa dakinshi, kamar wadda kwai ya fashe Ma ta wuce sama dakinta ta zauna tafara tunanin yanda zatayi “da zaman nan da kike da Tashi kikayi kika aje masa a parlor kafin ya fito saiki gudu”
Shawara take da zuciyarta kafin wata zuciyarta tace “what if kika kai mashi kika gudu