kaida bakinka kace min marayune yarannan, basu da uwa basu da uba, shin ka manta ayanxu kaine gatansu har ita matar taka?’’
Gabanshi ne ya bda dam, daman abun da yake tsro Kenan shiyasa yayi komai cikin sirri yanxu amah zata bata mashi plans din komai, anatse ya soma mata Magana cikin kwantar da murya yace ‘’but amah ita ta buqaci hakan, itama ta buqaci sakin’’
Kai tsaye amah tace ‘’ita tace maka ka saketa?’’
‘’eh’’ ya fada anaste
Kallonshi ta sakeyi tace ‘’wani irin zama kukayi muhammd kaida ita?har ta buqaci ka saketa’’
Dan dagowa yayi idanunshi sunyi jaa yace ‘’ammah please…bana buqatarta a rayuwata, yarjejeniya ce kawai mukayi kuma yanxu komai yazo karshe, just as I promise to freee her anytime I pleased yanxu lokaci yayi wallahi bana buqatarta’’
Ran ammah ne yayi mugun baci dajin kalamashi, lokaci guda taji kamar ma ba Muhammad ne ke Magana ba, her only Muhammad, saidai tunawa da halinshi yasa dole tayi buncike akan zaman da sukayi, rai abace tace ‘’wato ta gama yi mata amfani Kenan? You will free her when youre pleased?’’
Dan kasa yayi da kanshi don saida maganar ta gama fita daga bakinshi ya tabbatar da abunda ya fada,’’ammah please, wannan auren ba komai bane yarjejeniyace please’’
Dan daka mashi tsawa tayi tace ‘’shut up Muhammad, ka bani kunya’’
Tana kaiwa nan ta miqe ta barshi nan zaune ta fuce daga dakin.
Bangaren daddy yau kwananshi daya a headquter na sojoji an kaishi wani dakin buncike na manya manyan criminal, bait aba tsammanin case dinshi yayi girma sosai ba saida aka aje mashi prove da evidence din allegation akanshi, ba tare da tsoron komai ba yaqi accepting charges din don duk laifinshi da aka karanto mashi a wajen cewa yake bai aminta hakan ba sai an aje mashi prove da evidence, asad dake gabanshi dariya akwai yayi ya kalleshi kafin ya kunna mashi video dinshi dayaje viral, daddy dai tunda ya kafama laptop din idanu hankali a tashe ya kasa cewa komai, ya kasa gano waye yayi mashi wannan bankadar, saida video din yakare kafin asad ya mashi playing na meeda wanda ta dauka a cikin flash nan take daddy ya harzuka don baiyi tunanin an gano gaskia ba he cant even believe it, don zuciyarshi ta gama mutuwa to the extent that yasan asirinshi bazai taba tonuwa ba don yana da bokan da yake mashi sirihi akan business dinshi, hankalinshi gaba daya y agama dashi don yasan tashi ta gama karewa, kallonshi asad yayi ganin ya fara zarewa yace ‘’haba ay na dauka kai shege ne, da uban me da kake takama d kake tunanin gaskia bazata fito ba har kana cewa baka yarda da duk abunda ake zarginka dashi ba to ga evidence nan, wannan ma somin tabi ne’’
Takowa asad yayi daidai kunnenshi ya soma rada mashi ‘’ina ji maka tsoron haduwa da general, he will cut you into pieces for killing his father’’ arazane alhaji kabiru ya dago yana kumfar baki ‘’baku is aba, babu wanda ya isa ya kaini kasa’’ saida y agama ciga baki asad ya dago ya kalleshi, fuskanshi babu far a yace ‘’ka cigaba da cika baki, ka roki allah kada ya dauke ka daga nan Nigeria don kila anan kotu bazata yanke maka hukuncin kisa ba chan musammam case dinka da yaje international don wallahi gunduwa gunduwa za suyi dakai, kai anan dinma ni nayi maka alkwari zai kasha azabarda saika gwammace ka mutu kawai’’
Wata irin dariya daddy yayi ya kalli asad yace ‘’kai kana tunanin zan kara kwana guda anan ne? nan da 24 hours bazaka ganni ana ba’’
‘’lallai baka san girman laifinka ba alhaji, nasan yanxu tunaninka mutanenka ko da connection dinka?’’
Matsowa asad yayi ya dafe table din gabansu ya kurama alhaji kabiru idanu yace ‘’kana tunani akwai wanda zai fito don ya kareka ayanxu?babu wanda zaiyi risking kanshi don duk wanda ya shafeka yana hannunmu ayanxu’’ yana kaiwa nan ya fuce yabar alhaji kabriu cikin tsoro,don da za a auna jininshi akalla zaikai dari da saba’in,
After like 2 hour wasu sojoji murdaddu suka zo suka dauke daddy zuwa wani daki dake jere da karafuna, tunda aka shugo dashi hannayenshi nade da ankwa harda kafarshi hankalinshi ya gama tashi, kallon asad yayi daya zauna agefe guda ya daura kafa daya kan daya yace ‘’bakai kace zakayi mana taurine kai ba, to kuwa zaka ci ubanka dan yau jikinka saiya fada maka cewa kana cikin sojoji’’
Nan take asad ya bada commad ajanyo daddy, alahji kabiru na ihu yana zazzaga masu zagi haka suka janyo shi,asad ne ya kalleshi yace ‘’kana da bakin zagi yanxu Kenan? Uban me kake takama dashi? Youre nothing but a piece of trash,’’ yana kaiwa nan ya miqe da hannunshi da katuwar kaca ta keken hawa ya nannade a hannunshi kafin yace ‘’ku daure min shege’’ haka sojojin nan idanunsu jaja wur babu alamun rahama suka daure dadi, babu irin ihu masifa da cika baki da daddy baiyi ba, saida asad ya mashi jini da majina har bakinshi yamutu, don kusan suma uku yayi suna watsa mashi ruwa, basu barshi ba saida nunfashinsa ya soma daukewa, haka suka kwasheshi suka maidashi dakin da ake aje criminals suka rufeshi.
Hankali atashe amar ya fito daga dakin ammah yama rasa tunanin da zaiyi, dole fa saiya saki yarinyar nan don tun tasowarshi babu abunda ya taba shiga tsakaninshi da mahaifiyarshi saita dalilinta, ran shi amugun bace yake, haka ya sauko kasa ya wuce dakinshi yana furzar da huci mai zafi.
Salima dai tunda tabard akin da aka sauke amra ta wuce dakinsu ta kwanta kan gado ta fara kukan da take dannewa, harga allah duk duniya babu wadda suke su sama da amra, don ita kadaice danginsu kuma yar uwarsu ta jini, bazasu taba chanzata ba saidai zuciyarta na yi mata ciwo idan ta tuna da ta barsu sunsha wahala ba tare da ta waiwaye su, fadar irin wahala da suka sha ma bata lokaci ne, sai gashi ta dawo alokacin da basa buqatar ta, shiyasa ko sau daya bata taba maganarta ba a gidan, shi salim daman ba Magana yake ba,
Salim daya shigo dakin ganinta kwance tayi rub da ciki tana kuka yayi saurin karasowa inda take tare da dafe afadarta, dan dagowa salima tayi ganin shi yasa ta miqe zaune ta rungumeshi tana kuka sosai, shima riketa yayi sosai yana hawaye,saida sukayi mai isarsu ta dago ta kalleshi tace ‘’salim kaga adda ko? Sai yanxu zata dawo bayan mun gama shan wahala, ta manta damu ta gina rayuwarta achan sai yanxu zata dawo’’
Girgiza mata kai salim ya fara yi shi babu bakin Magana, yanxu yayi wayo sosai yasan duk abunda take nufi don yanxu yakai shekaru goma sha hudu, goge mata hawayen yayi ya mata alamun tayi smiling, murmushi salima tayi ta dungure kanshi tace ‘’kai wai yaushe zaka fara Magana ne? kodai ka zama kurma?’’ washe hakoranshi yayi ya ja hannunta suka fito daga cikin dakin zuwa qasa, nan suka samu ammah a zaune a sitting room hannunta rike dawayarta, tana ganinsu tace ‘’dear har yanxu kukan dadin haduwa da big sis akeyi’’
Dan murmushin yaqe salima tayi ta karaso gabanta tace ‘’ammah na yunwa nake ji’’
Murmushi ammah tayi mata ganin tayi doging tambayar tata tace ‘’ga abunci nan a dining kuje kuci ku gama a fara shirin islamiyya’’
‘’okay ammah’’
Suna gama cin abunci suka wuce sama domin shiryama islamiyya, karfe uku da rabi daidai suka sauko, kallon su amah tayi tace ‘’toh a dawo lafiya,dear ayi karatu sosai’’
Murmushi sukayi mata atare kafin salima tace ‘’insha allah ammah sai mun dawo’’
Suna fita ammah ta maida kallonta zuwa ga wayarta.
Anatse ya soma fitowa cikin cikin shiri, kananun kaya ne a jikiinsa riga da wando wanda sukayi mashi kyau sosai kafanshi sanye yake da givenshi wanda ya fidda kyawun kafafunshi, cikin isa ya tako har parlorn yace ‘’ammah zan fita’’
Ba tare da ta kalleshi bat ace ‘’adawo lafiya’’
Wani iri yaji don normally idan zai fit aba haka ammah keyi mashi ba, da murmushi take kallonshi ta amsa shi tare da jero mshi addua,jiki a mace ya juya ya fuce daga gidan ranshi duk babu dadi.
Ammah na ganin fitar shi ta wuce sama don an kira sallar laasar, dakin da aka sauke amra ta fara wucewa don jin shuru, da sallama ta bude kofar ta shiga, ganin ta kwance a kasa yasa tayi saurin karasowa tace ‘’subhanallah daughter ya da kwanciya akasa?, bakisan babu kyau mace na kwanciya a kasa ba’’
Amra da tun budewar kofar da amma tayi ta farka tayi saurin miqewa zaune jiki a mace, muryarta dakyar ma take futowa tace ‘’barka da yamma hajiya’’
Saurin kama hannunta amma tayi ta jata bakin gadonta kalleta cikin kulawa tace ‘’ki daina kirana da hajiya, call me with ammah, kinji ko?yanda na dauki su salima haka na daukeki,’’
Sunkiyar dakai amra tayi cikin jin kunyar ammah tace ‘tohm ammah’’
Murmushi amma tayi tace ‘’yauwa dear, kina buqatan wani abu?’’
Akunyace amra ta amsata da ‘’ah ah’’
Hannunta amma ta kamat cikin kulawa tace ‘’karkiji kunya na don ina matsayin mahaifiyarshi kinji, ki daukeni kamar yanda su salima suka daukeni a matsayin uwa kinji ko daughter’’
Wasu irin siraran hawaye ne suka zubo mata tace ‘’toh’’
Da sauri ta goge su don kar ammah ta gani, ahankali ammah ta dan soma janta da surutu don ta sake saidai hakan bai samu ba sabda gaba daya a tsorace take, ga damuwa shimfide a fuskanta, ganin haka yasa ammah cewa ‘’daughter ki huta kinji ko?idan kina buqatan wani abu don’t hasitate to tell me okay?’’
‘’insha allah’’ amra ta fada cikin sanyi
Fita daga dakin amma tayi ta wuce dakinta, zama tayi tunanin abubuwa da dama, sai alokacin ma ta tuna da wani daddy, wayarta ta janyo ta bude social platform, nan take taga komai, kwat kwat bata wani tada hankalinta ba don ta dade da zargin yana da wata kullaliya, akwai lokuta da dama da take zarginsa
akan abubuwa musamman idan wannan baqon nashi wanda ke zuwa duk karshen shekara, wani lokacin bata sanin time din da mutumin ke tafiya bayan wannan ma saidai taji zancen tafiyar baqon a bakin yan aiki, akwai lokacin da ta tambayi lanatana ma nan ta shaida mata ay alhaji kabiru ya saukeshi a dayan part dinshi, shima part din tana zargin akwai abunda yake ajewa a ciki don kwata kwata baya yarda ana shigar mashi part din wanda tun tna damuwa akan sanin menene a part din har ta hakura.
Amar na fita masallaci ya fara wucewa domin yin sallar laasar ana idarwa ya shige cikin daya daga cikin motocinshi dake pake a compound, bai tsaya ko ina ba sai nigerian headquarters, yana zuwa asad ya tarbeshi suka wuce investigation room, zama sukayi kafin asad yasa a fito da alhaji kabiru, yanda aka fito dashi ranga ranga zaka dauka kamar matacce ne, ajiye shi sojojin sukayi kan kujerar da ake aje criminals kafin asad yasa a watsa mashi ruwan sanyi, afurgice kuwa ya farka kamar zautacce yana surutai, dakyar ma yake bude idanunshi da suka kumbura suntum, kallonshi amar yayi yana jin wani irin zafi aranshi ace wai kanin mahaifinka ne haka, wani irin zafi yakeji aranshi idan ya tuan shine wanda ya kashe dada,
‘’I hope baka fara regretting rayuwanka bat un yanxu don this is just the beginning, I promise you the pain will be worst than this, wannan somin tabi ne, how could you? Baka tsaya da alhakin mutane akanka ba saika kashe rai? You killed dada? Just because ya gano sirrinka?’’
Idanuna mara ne sukayi jaa sosai, take yaji kamar ya kashe alhaji kabiru kozaiji dadi aranshi saidai bazaiyi hakan ba don so yake sai yasha azabarda saiya gwammace yam utu, kallonshi alhaji kabiru yayi da idonshi guda da yake iya budewa ya kyallyace da dariya yace ‘’kanason nabaka labarin yanda na kashe ubanka?hahah drug daya na jefa mashi a juice ya karasa’’
Azafafe amar ya miqe idanunshi yayi jaaa kirjinshi har wani irin bugu yake bammbamm ya shakoshi da hannu daya,take kabiru ya hango lahira don saida kullutun idanunshi ya fito, asad na ganin haka yayi saurin kama hannun amar ‘’oga calm down’’ ay inaa amar baya jin abunda yake fada kwata kwata, karshe dai hannu asad yasa don ya janye hannun amar daga wuyan kabiru bai Ankara bay a jishi a kasa duk girmanshi amar ya zubar dashi a kasa, kallon yanda alhaji kabiru ke tarin mutuwa asad yayi kafin yayi saurin kiran sojojinshi don su janye amar, suma dai suna karasowa da hannu daya amar ya zubar dasu duka, saida ya tabbatar alahji kabiru ya shaku da kayau kafin ya turashi baya gaba daya kasa a sume, miqewa asad yayi yana mamakin irin karfi na amar kamar doki, da hannu daya duk a watsar dasu su kusan uku.
Azafafe amar ya fuce daga cikin wajen ya shige motarshi rai abace, wani irin rough driving yakeyi wanda yasa mutane kauce mashi hanya, road safety kuwa da sunga plate number shi basa gigin tareshi ma kwata kwata,
Ikon allah ne kawai ya dawo da amar gidan, koda yayi parking ya dauka kusan awa guda a cikin motar, saida aka kira sallar magrib ya fito daga motar ya wuce masjid kai tsaye.
***Auren katin kasa***
Romantic love story
written by QUEENMARH
Chapter 130
Update
Unedited page
Bai dawo gidan ba saida ya tsaya akayi sallar isha’I dashi kafin ya shugo gidan, lokacin daya shigo main sitting room babu kowa a kasan don haka ya wuce bedroom dinshi direct don hes not in a good mood.
Bangaren amra tun bayan fitar ammah wani irin zazzabi ya rufeta, babu wanda yasan da situation din da take ciki, don ko sallar magrib kasa tashi tayi don ta samu tayi, tana nan kudundine cikin blanket akayi knocking kafin a shugo, lantana ce ta shigo hannunta dauke da tray da ammah ta zubama amra abinci, da sallama ta karaso dakin ta aje a kasan carpet, ganin amra a duqunqune tana rawar sanyi yasa ta karaso gaban gadon tace ‘’anty baki da lafiya ne?’’ kasa Magana amra tayi don gaba daya ta zama very weak, sai karkarwa da jikinta keyi, ganin haka yasa lantana fucewa daga dakin zuwa part din ammah, da sallama ta shiga sitting room din ammah don bata shiga cikin bedroom dinta kai tsaye, tundaga bedroom ammah taji sallamanta don haka tace ‘’shugo’’
Ahankali lantana ta bude bedroom din ta shugo daga bakin kofa ta tsaya tace ‘’hajiya nakaima bakuwar abunci saidai na ga kamar bata jin dadi,’’
Ammah dake zaune gaban dresser ta juyo ta kalli lantana tace ‘’subhanallah, bari nazo dakin’’
Futa lantana tayi ammah ma ta miqe tabi bayanta, amar dake shirin hawowa part din yana ganin ammah da yanda ta rude yayi saurin kallon inda take shirin shiga,ammah ma bata lura dashi ba don yana tsaye wajen stairs, dakin amra ta shige direct cikin sassarfa, lanatana na biye da ita,kai tsaye gaban gadon ammah ta tsaya ganin yanda amra take rawar sanyi, idanunta na neman rufewa, hankali atashe tace ‘’daughter meke damunki subhanallah’’ tallafota ammah tayi ta janye duvet din data qanqame a jikinta kallon lantana ammah tayi tace ‘’jeki dubamin ko Muhammad ya dawo akaita asibiti’’
Lanatana na juyawa don kiranshi sai gashi ya shugo dakin shima kai tsaye, sanye yake da doguwan jellabiya fara har kasa, hannunshi cikin aljihun rigar ya zuba masu idanu, juyowa ammah tayi ganin shi tsaye tace ‘’yaka tsaya anan, shugo mana ka dauketa Mukai ta asibiti’’
Kasa daga kafafunshi yayi, ranshi ya a dagule, ganin ya tsaya kyam ya qi motsawa yasa ammah juyowa ta kalleshi tace ‘’muhammad? Kana jina kuwa’’
Anatse ya bude baki yace ‘’I will call doctor yazo ya dubata’’ yana kaiwa nan ya janyo wayarshi yayi dialing contact din family doctor dinsu, doctor na daga ya fuce daga dakin.
Kauda kai kawai ammah tayi tana mamakin hali irin nashi, me Kenan yake nufi? Badai yana kan bakarshi na sakin yarinyar ba, tasan shi da kafewa akan abu saidai wannan karan zata nuna mashi ta isa dashi don ita ta haife shi bashi ya haifeta ba, kallon lanatana ammah ta sakeyi hannunta rike dana amra dake karkarwa ‘’shiga bathroom ki kawo min luke warm water da towel’’
‘’toh hajiya’’ lanatana ta fada tare da shigewa bathroom din dakin, agurguje ta debo ruwa a cikin bowl da towel ta karaso gaban ammah tare da dukawa, karwan towel din ammah tayi ta jiqashi kafin ta fara gogama amra a fuskanta da wuyanta,ta dae sosai akan amra tana shafa mata ruwan don taji dadin jikinta saidai kamar ma kara mata zazzabin akeyi don jikin yayi zumm sosai, nunfashinta ma kanshi da zafi yake futa daga bakinta, ganin haka yasa ammah tace ‘’wannan wani irin zazzabi ne oh ni Maryam, yarinya daga dawowa’’ kallon lanata ammah tayi tace ‘’ke rage min ac nan’’
Mikewa lanatana tayi don itama a furgice take ta kashe ac, suna nan zaune after like 20mins saiga doctor, amar ne ya shigo dashi har cikin dakin, ammah na ganin haka ta bashi waje ya fara dubata, futa lanatana tayi don ta basu waje shima gogan bai tsaya bay a fuce ganin irin kallon da ammah take jefanshi.
Cikin gaggawa doctor ya dubata harda drip ya saka mata ganin ta zama weak, kafin ya mata allurai da zai saukar da zazzabin, saida ya tabbatar shes stable kafin ya kalli ammah yace ‘’hajiya bamu gaisa bama ina wuni’’
Murmushi ammah tayi don tana zaune daga bakin gadon tace ‘’lafiya kalua doctor, ya jikin nata?’’
‘’alhamdullah its just a fever, nayi mata allurai da zai saukar dashi sannan ga drip nan na saka mata zuwa anjima idan yak are sai a cire mata’’
Godiya sosai ammah tayi mashi kafin ya ta rakoshi har kasa, doctor na tafiya ta wuce dakin amar kai tsaye, tana knocking kofar tace ‘’muhammd’’
Amar dake kwance daga shi sai shorts yayi saurin miqewa ya janyo