Auren Katin Kasa Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   75 / 94

222K to 225K   out of 279.4K words

ko zata sauko daga stairs,

 

Da sallama suka shigo dining din, kowa na zazzaune, ammah amar aman da salim, dukkansu harsun fara cin abunci, ‘’sannu daughter bismillah, salima zuba mata tuwo taci’’

Zama gefen shi tayi inda ammah tayi mata nuni da idanu tayi kafin salima ta soma zuba mata tuwo, ‘’adda wani miyan zan saka maki? Kuka ko egusi?’’

‘’kuka’’ ta amsata kai tsaye don bata jin zataci wani egusi, amar dai bai dagoba tun da ta shigo dining din hankalinshi na kan abuncin da yakeci, hes trying so had to control and maintain himself.

 

Anatse kowa kecin abunci sai karar cokali, amra dai tunda ta fara da cokali taga kamar baya shiga tayi saurin ajiyewa ta wuce kitchen ta wanko hannunta ta dawo ta zauna ta fara loma, duk motsinta akan idanunshi harta wuce kitchen ta dago, saidai bai yarda sun hada idanu ba sabod idonta na affecting dinshi sosai yanxu, dan wani duk yanda ta lumshe su sai tsikar jikinshi ta tashi.

Suna gama cin dinner suka dawo parlor kowa ya baje ana hira banda amra da amanr da sukayi tsit sua zaune opposite din juna ita hankalinta nakan tv ma tana shan agwaluma idan anyi Magana takan dan jefa bakinta a cikin hira while shi kuma idanunshi nakan wayarsa saidai duk hirar da sukeyi yanaji and time to time yakan dan dago ya kalleta.

 

Salima ce ta maido dashi daga tunanin daya fada ‘’ya muhammd gobe zamu gama exam fa kuma ranar Tuesday zamuyi graduation’

Dan dagowa yayi ya kalleta ‘’masha allah allah yasa asamu result mai kyau, and congratulation, wani gift kikeso’’

Gyara zama tayi don a kasa take zaune ta tankwashe kafa ‘’ya Muhammad digital drawing book nake so’’

Da sauri amra ta dago ta kalleta tana mamaki kafin ta jefa mata harara, ‘’shine baki fada min graduation din ba?

‘’toh ay adda kullum kina daki, idan nazo dakinki ma korata kikeyi shiyasa ni nama manta ban fada maki ba’’

‘’ay shikenan saikije grad din naki ke kadai’’ amra ta fada ranta adan baci

 

Kallonsu ammah tayi tace ‘’ayi hakuri yaya babba, mantawa tayi’’

Sauke kai amra tayi tace ‘’toh shikenan ammah,’’

Kallon salima ta sakeyi ta gallo mata wata hararar ‘’saboda ammah kawai na hakura’’

Amar ne yadanyi gyaran murya, salima najin haka tace ‘’sorry yaya, adda ta kaste mu, digital drawing board nake so’’

‘’okay’’ ya amsa ta kai tsaye yana latsa wayarshi

Cikin murna salima tace ‘’ammah ki tayani godiya thank you yaya’’

‘’allah ya saka da alkairi’’ ammah ta fada tana kallon, kowa amsawa yayi da ameen,

‘’toh yarinyar kirki ni me kikeso na baki?’’ ammah ta tambayeta tana kallonta,

Hannu salima ta saka akan habarta tana nazari, amra dai bat ace komai ba tana sauraronsu aranta tana cewa ‘’oh su salima an samu waje’’

 

‘’ammah, basai kin bani komai ba, kawai inason ki kasance a wajen idan akazo bani certificate dina’’  salima ta fada tana murmushi

‘’toh shikenan dear sai kuma me kikeso?’’ ammah ta sake tambayarta yayin da take shafa kan salim daya kwantar da kanshi kan cinyarta ‘’babu komi ammah na, wannan ma ya wadatar’’

Dariya duk suka danyi, kafin a kalli aman, ‘’toh su yaya aman me bazama a tambayi me za a bani ba’’

Hararar ta ya danyi kafin yace ‘’anqi tambaya din,’’

Dariya duk sukayi gaba daya harda amra don inkaga yanda suke kamar wasu tom and jerry kwata kwata girmanshi faduwa yake idan har suna magana da salima.

 Karfe goma daidai kowa ya fara waste wa, amar ne yafara  mikewa, ‘’ammah ina son coffee’’ ya fada baima tsaya sauraron response dint aba ya wuce bedroom dinshi, bayan tafiyarshi aman yayi masu sallama shima ya wuce kafin amra ta mike itama tana hamma, ‘’ammah saida safe na fara jin barci’’

Kallonta ammah tayi kafin tace ‘’’ki fara kai mashi coffee din saiki kwanta daughte’’

‘’tohm ammah’’ ta fada kanta a kasa don kwata kwata bataso zuwa part dinshi ba don wani irin barci takeji sosai.

Sama ta fara wucewa ta watsa ruwa a gaggauce ta sauya kaya zuwa doguwar rigar bacci cotton wadda ta dan sauko mata har kasa don ta gifta gwaiwarta, sai yar hula data saka same color da rigar.

Tana gama shiryawa ta sauko kasa direct zuwa kitchen.

 

Kitchen ta wuce ta hada mashi lafiyayyan instant coffee sai kamshi ke tashi ta zuba mashi a cup ta futo daga cikin kitchen din, lokacin data futo duk sun wauce sama har ammah ta rage hasken parlor don haka kai tsaye ta wuce part dinshi, da sallama ta shige cikin bedroom dinshi kai tsaye bayan tayi knocking daya.

Tana shiga ta rufo kofar kafin ta juyo, a zaune yake kan gado ya rufe kafafunshi da duvet sai laptop kan cinyanshi yana typing cikin kwarewa sanye yake da pjs dinshi milk color, takowa tayi ta karaso inda yake zaune ta ajiye mashi gefen bedside ‘’ga coffee din’’

Bai kalleta bay ace ‘’thanks’’ yana typing.

Juyawa tayi zata fita ya katseta ‘’come back here ‘’

Ya fada in a commanding way babu wasa, wanda yasa gabanta dan faduwa ta dawo ta tsaya dan nesa dashi ‘’gani’’

Banza yayi mata ya cigaba da aikinshi, saida ya dauka kusan minti goma yana aiki, ganin haka yasa ta zamu waje gefen gado ta zauna kusa da kafashi, saboda kafanta da baya juran tsayuwa.

Saida ya shafe awa guda yana aiki yana shan coffee harya gama kafin ya rufe laptop din, sai a lokacin ma yaji nauyi akan kafafunshi ashe hartayi barci abunta ba tare da snainta ba, ajiye laptop din yayi ya janye kafafunshi ya sauke su kasa ya mike tsaye, bathroom ya shige cikin mintuna kalilan saigashi ya futo, direct gaban switch ya wuce ya rage haske kafin ya kaarso bakin gado ya rankwafo ya gyara mata kwanciyanta gefe kafin shima ya kwanta dayan gefen ya lulluba masu duvet bayan ya masu addua….

***Auren katin kasa***

Romantic love story

written by QUEENMARH

Chapter 145

Update!!

Unedited page…

Wajen karfe uku na dare ya farka saboda wani irin zafi dayaji a jikinsa lokaci guda, bude rinannun idanunshi yayi ya sauke su akanta, ta maqalqaleshi gaba dayanta ta sauke mashi nauyin jikinta tana rawar sanyi, ga wani irin turirin zafi dake fita daga jikinta, saurin lumshe idanunshi ya sakeyi yi ya budesu tarr akanta sosai bakinta na gab da nashi lebanta na karkarwa sosai, saurin mikewa yayi zaune ya gyara zamanshi ya kalleta da kyau saboda akwai hasken bedside lamb dake a kunne,  kyawawan ya zubama idanu inda wasu siraran hawaye ke zarya akan fuskan nata, saurin taba wuyanta yayi ganin yanda ta fara kafewa bakinta har lokacin yana karkarwa sosai, wani irin zafi yaji daya sashi saurin cire hannunshi ‘’shes burning up’’ ya fada ahankali yana kallon fuskanta, saurin janyeta yayi daga jikinshi ya mike tsaye yama rasa abunda zaiyi don ya mata taimakon gaggawa, tunawa da yanda ammah ke mashi lokacin da yake karami yayi don haka ya wuce bathroom ya jiko hand towel kafin ya dawo gefen gadon ya zauna ya soma goga mata a fuskanta.

jikinta ne ya tsananta don har lokacin he can feel yanda take sauke nunfashi mai zafi sosai akan hannunshi, last option daya yake dashi wajen taimaka, kamar bazaiyi ba don yasan zaiyi affecting dinshi sosai, saidai ganin yanda take rawar sanyi ya sashi jin wani iri don haka ya mike tsaye ya kashe ac dakin ya wuce

ciki closet ya dauko babban duvet mai nauyi sosai ya sauya da dayan, yanda yake yin komai a gaggauce zaka gane hankalinshi a tashe yake.

Yana nan tsaye yana nazari kamar ana fusganshi haka ya soma zame kayan jikinshi ya rage daga shi sai dogon wando pjs dinshi.

Ahankali ya hau kan gadon ya zauna kafin ya janyota jikinshi ya soma zame kayan jikinta, saida ya cire kayan barcin nata gaba daya kafin ya hade jikinshi waje daya ya rungumota, wani irin shock ya soma ji saboda yanda fatar jikinta ke gogar nashi don babu bra kwatkwata  jikinta, runtse idanu kawai yakeyi jikinshi na vibrating saboda kusanci yayi yawa sosai, janyo duvet din yayi ya rufa masu gaba dayansu tundaga sama har kasa har lokacin tana cikin jikinshi tayi lamo.

Ahankali zafin jikin nata ke transferring zuwa jikinshi don shi temperation dinshi is normal, shida idanunshi suke a bude kuma yana cikin hayyacinshi shi kadai yasan irin connection din da zuciyoyinsu suka shiga, don heart beat dinsu kusan a tare suke bugawa, at the point ya tabbatar zuciyarshi is beating for her don kwata kwata ba haka zuciyarshi ke bugawa ba,

Bakinshi ya maotso saitin kunnenta ya soma karanto mata addu’oin samun sauki harta daina rawar darin da takeyi nunfashinta na sauka ahankali akan kirjinshi da gashi ke kwance akai.

 

Har aka kira sallar asuba bai runtsa ba ko kadan yana maqale da ita, sallar ma bai samu yayi ba don sai a lokacin barci ya fusgeshi saboda wani matsanancin ciwon kai daya fara kawo mashi ziyara.

 

Amra dai bata san wainar da yake toyawa ba saidai daren ranar taji wani irin sanyi a zuciyarta, daman duk dare saitayi wannan zazzabin wanda ayanxu ya zaman mata jiki don duk dare saitayi.

 

Basu suka tash ba sai wajen karfe goma na safiya, amra ce ta fara bude idanunta saboda wata irin yunwa data nuqurqusota, saurin bude idanunta tayi ganin duhu duhu yasa tadan razana don bata ma lura da ajikinshi take bay a lullubesu da duvet, mutsu mutsun da ta soma yi ne ya farkar dashi daga barcin, bude kyawawan idanunshi yayi ya sauke akanta, sai alokacin itama ta kalli fuskansa da kyau, janyota yayi sosai a jikinshi ya lumshe idanunshi da suka danyi jaa yace ‘’shiii go back to sleep’’

 Dauke idanunta tayi akanshi don yanda yayi mata maganar yasa ta soma jin wani abu chan kasan ta saboda whispering tone yayi using, dan turo bakinta tayi kafin ta soma Magana anatse ‘’ ni yunwa nake ji’’

Bai bude idanun nashi ba ya sake cewa ‘’baki isa ba fah, yanda kika hanani barci jiya sai kin koma’’

Ashagwabe ta sake cewa ‘’wallahil azeem yunwa nakeji, cikina yana ciwo’’

Banza yayi da ita, idanunshi a rufe to his surprise sai jin kukanta yayi kamar wata baby ashgwabe tana kuka tana gunguni tana Magana ‘’ni wallah yunwa

nake ji’’,ta fada tana harba kafarta har wani zungurinshi takeyi da kafafun nata wanda ya sashi runtse idanunshi ya danyi yar tsuka ya bude idanun ya saukesu akanta ‘’why are you so stubborn ne? ke ba’a isa a fada maki abu kiji ba’’

‘’toh nace maka inajin yunwa kaqi barina na tafi’’ ta sae fada tana kauda kanta daga gareshi.

 Bai saketa ba haka zalika bai sake ce mata qala ba harta karaci kukan nata ta gaji ta rabu dashi, don kukan ma galabaitar da ita yakeyi sosai.

Saida suka dauki kusan minti atalatin a haka, har lokacin bai saketa daman dalilin qin sakinta nata da yayi was erection din data tado mashi wanda bayason ta ganshi a haka ta samu kofar sake rainashi shiyasa ya ki sakinta saida ya bari komai ya dan lafa mashi.

 

Sauke duvet din ya farayi kafin ya sassauta rikon da yayi mata ya sauke kafafunshi kasa ya wuce bathroom anatse ba tare da ya waigo inda take zaune ba don har lokacin engine dinshi na nan a tsaye bai sauka ba, ya shiga bathroom ya soma zame kayanshi ya fara wanka.

 

Tana ganin ya shige bathroom ta mike zumbur, sai alokacin ta lura da babu komi a jikinta said an pants dinta, wani irin takaici ta danji a ranta don yanzu kiriri ta gane buqatarta yake sosai, wanda tayi alqawarin bazata taba bari ya kusanceta ba sai ya karbeta a matsayin mace kamar kowacce mace a wajen mijinta.

Yar tsuka tayi ta zura rigar barcinta, bata ma staya saka hula ba ta fuce daga dakin aranta tana rokon allah yasa babu kowa a parlor, koda ta futo daga dakinshi ta karasa wajen kofar fita daga parlor nashi saida ta dan tsaya ta bude kofar ahankali ta zuro kanta, babu kowa a parlor kuma bataji wani hayaniya ba ko karar spoons don haka tayi maza ta bude kofar ta fuce fit tana dan sassarfa kamar munafuka.

 Batayi landing a ko’ina ba sai dakinta tana shiga ta sauke wata ajiyar zuciya tana haki, saida ta dan dawo daiidai kafun ta wuce cikin daki ta soma rage kayan jikinta ta wuce bathroom tayi wankanta.

 

Tana gama wanka ta fito daga bathroom tana tsane jikinta da hnd towel data ruko a hannunta, agurguje ta soma shiryawa ta saka wani doguwar riga wanda ta dan kamata kadan, tana gama shiryawa ta hau kan sallaya ta tada sallah, tana idarwa ta mike tsaye tana kokarin cire hijab din jikinta saiga sallamar ammah, cikin sauri ta sauke hijab din kasa ta wuce wajen dresser ta tsaya tana murmushin yaqe don bazata so ta ganta tana sallah yanxu ba don duk wand aya ga haka sai ya kawo wani abun, ammah dai ta kamata lokacin da ta  bar wajen sallayar haka zalika taga fitowarta daga dakin nashi don tana tsaye tana shirin futowa daga kitchen ta hangota.

Fuskan ta dauke da murmushi ta tako cikin dakin tace ‘’daughter yau kin Makara sosai’’

Adaburce amra ta saukar da kanta kasa tana wasa da yatsunta tace ‘’ina kwana ammah?’’

‘’lafiya kalua daughter ya kwanan ki da na baby?,’’ ammah ta sake tambayarta

‘’alhamdullillah’’ ta amsata anatse muryanta baya futowa ma sosai.

‘’zo ga breakfast na kawo maki, na sanki da son dumame’’ ammah ta fada tana karasowa baking ado ta ajiye mata akan carpet ‘’bismaillah, zoki zauna kici dear’’

Cikin jin dadi amra ta karaso inda ammah ke tsaye kanta har lokacin a kasa fuskanta fayau said an murmushi da ya wanzu akan fuskanta ‘’thank you ammah, daman dashi na tashi wallahi’’

Murmushi kawai ammah tayi mata kafin ta juya hanyar futa tace ‘’idan kin gama ki sauko kasa, yaudai kid an zagaya estate din, ga salim nan saiya rakaki’’

‘’tohm ammah’’ amra ta bata amsa.

 

Ammah na fucewa ta zauna ta nadi tuwon nan sosai, saida taci ta koshi harda sude hannu kafin ta wuce bathroom ta wanke hannunta, tana wanke hannun ta fito ta dauki plate din ta fuce daga dakin.

Kasa ta fara saukowa babu kowa a kasan don haka ta wuce kitchen kai tsaye ta ajiye plates din, gaban fridge ta tako ta dauka bottle of ice water kafin ta fuce daga kitchen din.

Tunda ta gifta ta wuce kitchen ya dago ya kaleta harta futo daga kitchen din batama san yana wajenba, itako amra bata lura dashi ba kwata kwata kanta a kasa saida tazo daidai wuce hanyar dining din ta jiyo karar spoon, duk a tunaninta ma ammah ne a wajen don haka ta dan dago da idanunta, karaf idanun nata suka sauka akan nashi, hannunshi rike da toasted bread yana kokarin kaiwa baki, samun kanta tayi da galla mashi harara tayi wani farr da idanu tare da turo mashi baki kafin ta kauda kanta gefe tana kokarin amsa kiran da ammah dake zaune a sitting room takeyi mata ‘’daughter daughter, kin sauko ne?’’

‘’eh na sauko ammah, plate na ajiye ne a kitchen’’ tana kaiwa nan ta sake mashi kallo daya ta dauke kanta ta cigaba da catwalk tafiyanta kamar wata tarwada,mazaunanta yabi da kallo har saida ta gifta ma kallonshi kafin ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ‘’ya allah,’’ ya furta ahankali, tunani ya soma yi aranshi har lokacin bread din na hannunshi bai kai baki ba, ‘’yarinyar nan na neman haukatani’’ ya fada aranshi kafin ya danyi wani murmushin da shi kadai yasan ma’anar shi ‘’zanyi maganinki ne’’

Tura bread din yayi abakinshi, da farko kwata kwata bayajin cin komai saidai yanxu daya ganta da yanda tayi wannan abun da tayi mashi da fuskanta saiya tsinci kanshi da jin dadin cin abunci,.

 

Amra kuwa wani irin haushinsa takeji yanda yake kokarin maidata kamar wata toy dinshi, don sai ayanxu ta lura da take takenshi na neman coffee da daddare, saboda yasan ammah zata ce takai mashi, tun kafin ta karaso parlor ta soma

Magana a zuciyarta ‘’ay kuwa bazan kara kai maka ba wallahi, daman na lura da take taken ka’’

 Kaarsowa tayi parlor har lokacin tana tunani aranta,muryar ammah ne ta katseta ‘’daughter kayannan baya damunki?’’

Dan dagowa tayi kafin ta maida idanunta kan kayan ‘’ah ah ammah, baya damuna’’

‘’toh shikenan, ki dauko mayafi salim ya rakaki ku zagaya’’ ammah ta fada tana maida kallonta ga tv

‘’tohm ‘’ tana kaiwa nan itama ta wuce sama anatse, tana shiga daki ta dauka dankwalin doguwar rigar ta tsaya gaban mirror ta daura dankwali, ba karamin kyau daurin yayi mata ba dukda bata iya ba, tana gama daurawa ta dauka kohl ta sanya a idanunta da suka dan fada kadan, tana gamawa ta dan jaa baya ta karema kanta kallo, dan bumb dinta ya futo sosai don sai a lokacin ta lura dashi saboda yanayi rigar jikin nata daya fiddashi dan kiff, shafa cikin tayi tana murmushi, ‘’yanxu da baby anan wajen’’ ta fada tana shafa cikin nata tana murmushi, ta dauka kusan minti biyu a tsaye tana shafen cikin nata kafin ta tuna da wani abu, take yanayinta ya sauya tana tausayin kanta, duk sanda ta tuna yanda ya Muhammad ke treating dinta tana jin rashin dadi aranta, ta rasa dalilin dayasa hes always cold to her, kowani aure tasan koda babu soyayya akwai mutuntawa da kulawa da juna saidai ita batayi sa’a ba, don ko fara’arshi baifi sau biyu ta taba gani ba, baya sake mata ko kadan, doguwar Magana ma bata shiga tsakaninsu saidai fada, har lokacin ta kasa gane wani irin mutunne shi, da farko bayan rashin lafiyar ammah har tana cewa ya chanza ashe ashe bai chanza, koda yake what did she expect? Baka taba chanza mutun daga yanda yake dlilin wannan yasa ta kasa tantance a wani matsayi ta sakashi a zuciyarta, bata

75 / 94